ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 8 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ma sun zo garin Kaduna har dai zama ya kama su, ya nemi auren ta mahaifinta ya ba shi.
Sunanta Badijo ma’anar wannan sunan a fulatance shi ne, matar da ta cika ja. Bayan an gama biki ya saka matarsa a gaba suka je har Yola a wani Kauye ya gano “yan’uwanta wadanda ba su ko jin
Hausa sai tsabar Fulatanci.
Da suka samu kamar kwana goma sha daya suka yi shirin dawowa Kaduna, har wata kanwarta mai suna Karima wadda suke ‘yan walki daya, wato
“ya’ ya maza ta makale mata sai ta biyo ta Kaduna:
Mahaifinta ya ce, “To su je da ita, amma idan sun iso su bai wa kaninsa mahaifin Badijo”
Baba Sule ya shaida wa matarsa ta gyara masa da fullanci-shi ya dauki amanar rikon Karima a hannunsa.
A wannan lokaci shekarun Karima goma da haihuwa, aka hado masu sha tara ta arziki suka dawo gida Kaduna. Ran nan Gwaggo Badijo ta sami ciki ta haifi danta namiji, aka sanya masa sunan kakanmu Amadu.
Baba Sule kam al’ amari ya bunkasa sosai har ya zama babban dan kasuwa, sai ya nemi Babana da ya baro Kano ya dawo wajensa da zama. Hakan aka yi Baba Sule ya sayi gida a nan Tudun Wada. A shekarar da Badijo ta sake haihuwa aka sanya wa jaririn sunan Babanta wato Aminullah, aka rika kiran sa Magaji. Har wayau a wannan shekarar ne Baba Sule ya je aikin Hajji.
Karima ta zama budurwa cikakke, kyawunta ya fito fili, kin san dai Fulanin Yola wajen kyau Asiya. A nan fa jama’ a masu hannu da shuni suka yi mata ca, Baba Sule ya ce, ta fito da wanda ya kwanta mata rai don a tura shi ga iyayenta.
Ta ce, “Ita ba ta da zabi wanda ake ganin ya dace da ita a tura shi gidan su Baba Aminu kawai”.
Baba Sule ya bai wa wani abokinsa aka kai shi wajen Baba Aminu. Sai dai kin san abin da ya faru Asiya? (Sai na girgiza kai na yi murmushi). Ai idan mahaifina ya shigo gidan sai ta rinka jin kunyarsa, idan cin abinci take sai ta mike tsam ta shige dakin yayarta, idan an kira taga kofar gida samari muddin yana nan sai ta ki fita, ke idan ma an aike ta gare shi ta fara noke-noke ke nan, har dai ran nan Babana ya gane kunyarsa take ji.
Sai wata rana ya tsare ta a gaban Badijo ya ce, lallai shi sai ya san dalilin jin kunyarsa da take yi haka, domin a da ba haka take masa ba.
Suka buga suka raya shi da Badijo ta ki daga kanta ta dube su, har dai ya kare ya ce, “To ko ni zan zama angon ne?”, Haba sai ta rufe fuska ta tashi ta shige daki tana fara’a.
Daga Karshe dai kauna mai karfi ta wanzu, da kanta take zuwa dakinsa su yi hira. Ita kuma Gwaggo Badijo ta gaya wa Baba Sule, shi kuwa sai haushi ya kama, don ya ya za a mai da shi karamin mutum bayan an sanya ya yi magana gemu da gemu kuma a ce ya bai wa kaninsa, ke in dai kai ki da nisa Baba Aminu ya yi tsaye ya daura auren iyayena aka bar Baba Sule da haushi.
Da farko mahaifina ya koma gidan haya da
Innata, a cikin shekara uku ta yi Bari da yawa. Da dai Baba Sule ya ga bai ganewa bisa harkokinsa, sai ya nemi mahaifina don su shirya. Baba Sule ya gina wani sabon gida kusa da na shi ya bai wa iyayena tsohon nasa Wannan shine usulin zuri’ armu.
Baba Sule “ya’ yansa shida duk zunzurutun maza, mahaifina kuwa bayan sun sha bari, sai barin-ma ya tsaya, sun dade ba su sami haihuwa ba. Ran nan kwatsam aka sami cikina, da na cika wata tara na shiga cikin na goma ranar wata alhamis aka haife ni. A lokacin A minu na da shekara goma sha biyu. ai sai
so a cikin zuriyarmu. Idan kin tuna
tunanmu Amadu ba shi da ‘ya mace har
zuwan Sule sai Babana. A ranar da na kwana biyu a duniya kakanmu
Alhaji Amadu ya zo har Kaduna tun daga yola gani na, kakanmu ya sami Aminu Magaji ya kasa ya tsare a gidanmu, shi ne mai aiwatar da komi saboda murnar zuwana, nan da nan ya yiwa Alhaji Amadu shimfidun tabarmi a tsakar gida, ya shiga ya amso masa ni ya kawo masa, ya koma gefe ya zauna.
Ga mahaifina ga Baba Sule zaune gefe guda, ga aminan Alhaji Amadu da suka rako shi, sai suka dube ni suka ce tsarki ya tabbata ga mahaliccin yarinyar nan, Allah shi raya ta, aka ce amin.
Aminu ba kunya ba tsoro ya cewa kakanmu,
“Wallahi saboda ita na dawo gidan nan, ban taba ganin yarinya mai kyanta ba a duniya”
Sai kakanmu suka fashe da dariya, Alhaji Amadu ya. ce, “Ina ganin dai Aminu kai za ka yi
• mini fashin mata ko?”
Magaji ya dubi sashin iyayenmu cike da jin kunya ya ce, “Ni dai ina son ta”.
Alhaji Amadu ya gyara zama ya fara maganar manya yana mai duban iyayenmu, ya ce, “Ina son ko bayan ba raina don Allah don Annabi ku rike alkawari, idan jaririyar nan Allah ya raya ta ku bai wa Aminu, domin wannan hadi ne daga Allah” Sai mahaifina ya ce, “To Baba in Allah ya yarda za mu cika wannan alkawari idan har muna raye”
Shi kuwa Baba Sule cewa ya yi, “Ni ban dauki wannan alkawarin ba, idan har ta tashi ta ce mani ba ta son sa, ba zan mata auren dole ba”
Alhaji Amadu ya dube su ya ce, “An yi mata huduba ne?”
Suka ce, “A’a, daman kai ake jira”.
Sai ya ce, “Ko kuna da sunan da kuke so?’ Suka ce, “Sun ba shi zabi”
Ya tambayi Aminu wane suna za a sanyawa matar taka?
Aminu ya ce, “Na fi son sunan matarka wato
Fadimatu-al-Zahra’ u”
Alhaji Amadu ya fashe da dariya ya ce, “Ho!
Dan neman takadari ka iya fashin mata ko Aminu?”
To kin ji mafarin sunana. Lokacin da na. isa makaranta Aminu ya gama sakandire, shine ya kai ni firamare a nan unguwarmu Tudun Wada, ya sanya mani Zahra’ u Ahmad. Na zama shagwababbiyar gaske ganin ni kadai ce mace a zuriyarmu, babu ma kamar wajen Baba Sule, komi nawa ya fita daban, haka nan wajen kakannina, wajen Aminu kuwa ai kamar ya kwanta in rika taka shi, har na shiga aji biyu inda duk ya
Hmmm