ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 9 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

zauna ina bisa kafadarsa. Iyayena duk da ba su da komi, amma ba su son abin da zai sosa mani rai, ke sai ya zamanto ba ni karatun komi a makaranta don tsabar shagwada, saboda malaman ma sona suke yi, duk hutu nice ke daukar na utel, Aminu ya koya mini har ya gaji ya sanya mani ido.

Saboda son da yake mani ya sami Jami’ar

Sokoto amma ya ki zuwa ya yi karatusa a Poly Kaduna har ya hada H.N.D, ya kama aiki a gidan

Rediyon Tarayya na Kaduna.

Ni kuwa lokacin da hankali ya fara zuwa mani, ina firamare aji hudu ke nan, tsiwar da nake yi na fara ragewa, na fara kishin ‘yan matan ajinmu yadda zan ga ana fiddo su ana basu kyauta wajen kokari, ni kuwa duk da kyawuna ba a bani, sai na fara damun Aminu idan an yi hutu ya kan ya koyar dani Turanci da sauran ayyuka.

To daman a son sa, idan ya taso daga tasu makarantar nima na taso Islamiyya ba ‘ni da sauran sukuni sai koyarwa, farkon shiga na aji hudu sai na fara daukar ta sha biyu cikin mu talatin.

Aminu ya Kara zage dantse a wani hutu na dauki ta biyar, har na shiga Queen Amina Kaduna.

Da farko saboda haduwa da Kabilu na rika daukar ta shida, amma kin san yaro idan ya sa son abu a zuciyarsa, sai gani daga na daya sai ta biyu. Abin da na dauka a tsakanina da Aminu na farko da na ji ana kirana matar Aminu, sai na yi zaton kowa ma haka ake masa, sai daga baya na fahimci yadda lamarin yake, shi dai Aminu kusan in ce maki ya fi ni kyau, don dai ina ‘ya mace.

Aminu ya dauko fasalin gidanmu, yana da dogon hanci da baki mai fadi irin wanda ake so a jikin maza, yana da fasalin hakora masu hade da

‘yar siririyar wushirya, sai kuma ya debo farin mahaifiyarsa Gwaggo Badijo, idan kin ga Aminu sai ki ce Balarabe ne. Ga sumarsa a nade, dogo ne dan siriri, yadda kika ganni ‘yar siririyar nan, to wallahi har na fishi kiba, idanuwansa kuma in yana kallon ki sai ki dauka da biyu yake kallon ki, kullum idonsa kamar mai jin bacci Aminu ke nan.

Na yi mugun sabo tun ina Karama kullum ina jikinsa, kai har na girma haka abin yake. Ba ni mantawa wata rana Asiya lokacin ina sakandire aji hudu, duk wata sura ta daga mace ta gama fitowa a kaina.

‘Ina kwance a dakina da la’asar ina baccin rana, sai Aminu yazo bayan sun gama hira da Gwaggo Karima ya zarto dakina, ya sami kujerda ya zauna yana karatun jarida.

Can na farka amma sai na makale idanuna ina satar kallonsa, sai in ga ya daina karatun ya dube ni, ya ja dogon numfashi ya yi ajiyar zuciya, na rika tunani shin wai me yake rayawa a zuciyarsa ne?

Ya yi tagumi ya sanya mani ido ya rika yi mani firfita da jaridar hannunsa, na yi farat na tashi kamar da gaske, na ce, “Lah! Magaji na saka aiki. ko? Don Allah yi hakuri ban san zuwan ka ba”

Ya yi murmushi ya ce, “Ai dadin bacci ne” ya ci gaba da cewa, “Tashi ki yi wanka hoto za mu dauka”

Na ce, “To”

Na je na yi wanka na zo ina shafa mai, sai na rika jan shi da hira, shi kuwa ya rika rufe fuskarsa da jarida kamar yana karatu.

Na ce, “Aminu don Allah shafa mani mai a

baya”

Ya yi mani wani irin kallo ya ce, “Haba Lami da can wake shafa maki?”

Na ce, “A makaranta Kawayena, a nan gida kuma, wani lokaci Gwaggo, wani lokaci kai ne”.

Ya ce, “To lokacin ai kina yarinya, yanzu kuwa akwai canji

Na ce, “To Magaji ba kai ne mijin ba, ko ka fasa auren ne?”

Aminu ya dube ni duba cikin nutsuwa, ya dan dakata kadan can ya ce, “Dama lokaci ya yi da nake son in yi maki wata muhimmiyar tambaya. Shin Fadimatu don Allah ki gaya mani abu daya, wai kuwa kina sona kamar yadda nake son ki? Abin nufi a nan, ba wai son ‘yan’uwantaka ba, a’a, so irin na sha’awa da kaunar mutum a zuci”

Na yi shiru, sannan na ce, “A gaskiya Magaji a da ni dai na san kullum ina son ganinka, in har ma ba ka zo ba a lokaci raina ya kan baci, na kan dauki hakan sabo ne da zaman kadaici a wannan gidan, ba ni da abokin dauke kewa.

Wani lokaci kuma ina son in ganka saboda ina son ganin wasu abubuwan jikina wanda na fi so, amma a yau da ka zauna kusa dani sosai na ji wani abu da ban taba ji ba a rayuwata, wanda ina ganin shine so. Ba ni jin akwai mahalukin da zai sanya in ji hakan in ba…

Na sanya hannu na rufe idona. Can Aminu ya tallafo ni ya ce,In ba wa ba, don . Allah Karasa mani”

Na yi dariya na boye fuskata bisa kirjinsa, a nan dadi ya lullude shi ya rika neman fuskata wanda ya yi mani dabarda ya rika sumbatar kuncina, na yi karfin hali na ce, “Don Allah Aminu ka sake ni”.

Ya ce, “Sai kin gaya mani abin da na tambaye

ki”Da dai na tabbatar ba zai saken ba sai na yi masa zancen da yake so, sai na ce, “Wallahi Aminu bani da miji sai kai”. Na karasa da Turanci na ce, “/ love you”.

Ya Kara makale ni a bisa Kirjinsa, da kyar na zare jikina.Ya ce, “In same shi a kofar gida wajen motarsa in na gama”Na saka wani jan yadi mai walkiya da saitin zinarena wanda Baba Sule ya sawo mani da ya je aikin Umara, na gyara gashin kaina na tura shi zuwa baya tare da matse shi da wani tafkeken ribon mai launin ja, na sanya dan siririn dan kwalin wannan yadin na daurda a inda tsakiyar gashina ya fito tare da wanda na daure a baya.

Na sagala farar jaka da farin takalmi rufaffu, ba tare da na dauko gale ba, sai na fesa turare na fito na yi ma Gwaggo sallama na iske shi kofar gida.

Ya bude mani kofa na shiga ya mayar ya rufe, sannan ya zaga ya shiga mazaunin mai tuki, muna tafe yana mani bayanin yadda nake a zuciyarsa, tun daga wanna rana Aminu ba ya shakkar gaya mani komi, ni har yasa na fara jin kunyarsa.

Lokacin da muka isa wajen mai hoto muka yi kala-kala, wani ya tsaya a bayana ya dafa kafadata, wani kuma in zauna cikin kujera ya zauna bisa hannun kujerar, mun yi da dama ke da kin ga hotunan kin san jininmu daya, mutane da yawa kan

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE