ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 2 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 2 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Sai Inna ta yi karaf ta ce,

“Wai kanta ke ciwo amma na ba ta magani, nima so nake ta tada ni karatuna

Baba ya ce,Allah ya sauwake”

Ta kawo masa abincinsa, dama

dambun masara ta yi. Bayan ya gama cin abincin sai ya ce,

“‘Aisha ina son shawara da ke”

Ta ce,To Malam ai gani zaune

Sai ya gyara zama ya dan kishingida bisa filo,

ya ce,Yau wani abin alheri ya same mu, wato

gwamnatin tarayya ta bai wa ma’aikata kudi wato (Odoji), shine na ga ya dace in shawarce ki me kika ga za mu yi da wadannan kudi??

Ta yi ‘yar dariya ta ce,

“Kai Allah ya karowa Kasar nan tamu albarka, yanzu abin da na ga ya fi

gara ka sai mana mahalli wato gida, tunda ga zuri’a Allah na- bamu kuma muna rabe gidan kanin tsohonka, ka ga idan gidan kanmu ne za mu shakata mu wala, babu maganar jin kunyar kowa kenan”. Ya yi dariya ya ce,

“Ni kuwa niyyata in roki

Baba ya hada mini wancan filin in gina daki in yo miki abokiyar zama”. Tayi

dariya ta ce, Eh, wannan ma wata

shawara ce, amman a daure ayi mana mahallin a hankali sai Allah ya ba da na yin amaryar”Baba ya yi dariya ya ce,

“Haba Aisha har

yaushe zan yi haka, wanda kullum burina in ga

Allah ya ban gidan kaina, ina zama tsakar gidana ina koyawa ya°yana karatu, ina hira tare dasu ina jin lafazin bakin kowanne, ke kuma kina shirya mana

abinci kina kai wa kina komo wa, ina kallon ki ina jin dadi”

Gaba daya sai suka kyalkyale da dariya.

Bayan sati biyu da wannan maganar muka

tare a sabon gidanmu na Kofar Fada, sauran kudin ya Kara aikin gona dasu. Gidanmu

yanada dan girma daidai

gwargwadon na talaka, kofar gidan yana da baranda

inda yake kallon yamma yana daga gabas, sannan sai zaure da dakuna biyu a zauren suna kallon juna, sai ka Kara shiga wani dan karamin zaure, sannan ka

zarce tsakar gidanmu shafaffe da sumunti.

Gefen gaba s falo ne da dakuna biyu, gefen

yamma makewayin zagawa ne. to dakunan dake

cikin falo Inna ta dauki daya, dayan kuma aka barmana ni da Zainab. Shi kuma dakin da yake tsakar

gida na mahaifina ne, Abubakar kuma da yake ya

shiga sakandire aka gyara masa dakin zaure.

Gidan dake jikin namu gidan Malam Ibrahim

ne, shima matarsa daya da babban dansa Aminu dake sakandire aji hudu, da Kanwarsa tsarata ce sunanta Hadiza.

Abubakar ya yi sa’a ya samu Aminu wanda

ya zama abokinsa da suke hira idan sun zo hutu, sannan yana koya masa abin da ya shige masa duhu a makaranta.

Kullum suna tare ko masallaci ko a bisa

dakalin gidan su Aminu, duk da ya girmi Abubakar sosai Bayan Aminu ya gama karatun sakandire sai  ya kama aiki a makarantarmu, a wannan zamani ina

aji biyar ni da Hadiza kanwarsa. Idan mun taso daga Islamiyya da daddare Aminu yana koya mana karatu ni da Hadiza a dakin mahaifiyarsa Hafsatu ko a gidanmu. A makaranta ya zamanto kullum na biyu nake dauka itama hadiza bata wuce na biyar aminu saurayi ne dogo fari mai kyan kira ga fadin kirji da kafada, yana da idanuwa a kafe irin

wanda in ya tsareka dasu idan har ka yi laifi a

makaranta yanzu jikinka ya dau rawa, shine dalilin da yasa aikin da yake na koyarwa yara basa wasa, dole su iya.

Mahaifinsa kuwa ba shi da wata sana’a illa

lodin shanu yana kai wa Kurmi. Uban Aminu

Malam Ibrahim ya ji dadin hulda da mahaifina,

saboda yana danka amanar gidansa a hannunsa a duk lokacin da ya yi tafiya.

Dalili kenan da muka shaku da Hadiza

kwarai, shi kuma mahaifinsu ba ya bambanta mu, haka nawa Baban. Ita kuma Inna Hafsatu kullum muna tare da ita, haka Innata suna koya mana ayyukan mata na cikin gida.

Ganin haka Aminu ya hada mu yana yi mana

karatu, babu inda aka yi masa iyaka a gidanmu, ya saba da Innata sosai, balle kuma Baba na, sai ya yi

shawara da shi bai yi da mahaifinsa ba.

Aminu yana da budurwa mai suna Zulai tana

makarantar sakandire a Kankiya, a lokacin tana aji uku, kullum mu ne ‘yan aike muna kai mata wasika idan ta zo hutu.

Zulai tana matukar son Aminu ainun, har

gidanmu wurin Inna take zuwa don ta ji labarin

Aminu kawai, su biskit da alewa kuwa mun sha ci.Haka nan ni da Hadiza sai mu shirya mu je gidansu muce

“Aminu yana gai da ita

“‘. Don dai ta bamu

alewa kawai mu fito muna dariya.

Ya zamanto fensir da littafi sai Aminu ya

saya mana, ba iyayenmu sun sai mana ba. Kwance tashi har muka shiga aji shida ni da Hadiza, abin namu gwanin ban sha’awa. Yaya

Aminu ya Kara tsayawa tsayin daka

yana koya mana jarrabawa. Da lokäcin jarrabawa yaZo mu kan ji kwarin gwiwa ba tare da zullumin komai ba, ganin duk abin da aka tambaye mu mun sani.

Da muka fita makarantar firamare sai muka

dage zuwa Islamiyya ba dare ba rana, ganin bamu da wani karatu

bayan shi. Muna nan muna jiran

sakamakon jarrabawa, ranar wata asabar muka tsinci kanmu cikin wani mummunan bakin ciki.Da misalin karfe uku na wannan

rana mahaifina ba ya zuwa wurin aiki, haka shima Yaya Aminu, da yake ranar hutun ma’aikata ce. Sai

kwatsam abokan tafiyar Malam Ibrahim suka iso da gawarsa, Allah ya yi masa rasuwa a kan hanyarsu tadawowa ciwon ciki ya murde shi.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”

Haka muka kasance cikin kuka da bakin cikin

rashin mahaifin su Hadiza har na tsawon lokaci.Yaya Aminu ya koma abin tausayi, saboda ko magana ba ya son yi duk da daman magana ba ta dame shi ba. Mahaifina ya zama kullum yana ba shi magana.

Bayan Inna Hafsatu ta fita daga takaba da

‘yan watanni, rannan kwatsam sai muka ji an daura

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE