ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 3 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 3 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
mata aure da wani dattijo yana zuwa nan gidan su Yaya aminu ran aikin ta. Shi kuma Yaya Aminu ganin haka ransa ya
Baci, sai ya fara fafutukar neman makaranta zuwa kasashen waje.
Cikin ikon Allah sai ya yi sa’a ya sami wata
jami’a a kasar Rasha. Nan da nan ya fara
*yan shirye-shiryen tafiya:
A nan fa hankalin masoyiyarsa Zulai ya yi
mugun tashi kusan kullum tana gidanmu, muna jinta tana cewa,
“To yanzu Aminu idan ka tafi sai yaushe
kuma?” Ya kan ce,
“Gaskuya Zulai idan na ce ga
ranar dawowa ta na yi karya, ke dai Allah ya
tabbatar mana da alheri kawai, idan na bata miki ki yafe mini?*
Ita kuma ta kan ce,
“Aminu maganar aurenmu ita ta fi damuna”
Ya ce;Haba Zulai babu macen da ke auren
mijin wata sai mijinta, idan ke matata ce, sai ki ga Allah ya kawo sanadin yin auren namu, idan kuma ni ba mijinki bane, sai ki ga Allah ya kawo miki naki mijin”
Zulai ta kan yi kuka kamar ranta zai fita, har
Allah ya kawo ranar tafiyar Yaya Aminu. Zulai ta dangana ta sawa ikon Allah ido.
Bayan tafiyar yaya aminu da yan kwanaki sai jarrabawarmu ta fito, muka yi sa’a
muka tafi makarantar yammata ta G.S.S.S Malumfashi dani da Hadiza, aka yi mana
‘yan kintse-kintse muka tafi.
A kwana a tashi har muka fara
sabawa da makarantar, kuma gashi a
cikin garnmu. Idan mahaifina ya
sami dama ya kan zagaya wajen
maigadin makaranta ya kiramu mu dan gaisa, ko kuma ya ba da sako a bamu.
Saboda halina na ko in kula da rashin tsoro ya
sa na fara fice a makarantarmu,
har ya zamanto shugabar makarantarmu
Ta sanni sosai, aka ban monitan ajinmu na
Shugabannin makaranta suka rinka ja na da
wasa suna kira na mai (billen tsiwa),
ni kuma a gaskiya ban ga tsiwar da nake yi musu ba, iyaka dai
ina da irin halin mahaifina, ba zan wulakanta ka ba, kaima kuma kada ka wulakanta ni. Saboda ina basu hakkinsu, duk inda suka aike ni zan je, amma idan na ga abin zai kai ga wulakanci zan yi musu firi-firi. To da haka na
amshi kaina, kowa yasan Ni
a makarantarmu.
Lokacin da jarrabawar da aka yi mana ta fito,
na yi ta uku, ita kuma Hadiza ta yi ta biyar. Bayan nan ne aka bamu hutun sati uku muka zo gida. Ranar
kwana mu kai muna ba da labarin makaranta.
Bayan kwana biyu kanwar mahaifiyata wadda
muke cewa Mama ta aiko in je mata hutu gidan mijinta a Kaduna, wanda wannan ba shine aikenta na farko ba.
Tun ina firamare take fama da mahaifina amma sai ya ce a,a har dai wannan karon mahaifiyata ta ce,Wai don Allah Malam mene ne dalilinka na hana Uwani zuwa Kaduna hutu wajen kanwata wadda muke uwa daya uba daya kuma ka sani?”Mahaifina ya ce,
“Na ji dadi da kika yi mini
wannan.-tambayar Aisha, abin da yasa kika ga bana son yaran nan su je wani waje, saboda gudun abu daya.
Kinga mu talakawa ne, ba mu aje ba, ba mu ba wani ajiya ba, kullum kokarin abin da zamu sa a bakin salati muke yi.
Ke ma kanki sana’ar da kike yi ta ‘yan sake-
saken huluna, yanzu rannan da kika bani na kai kasuwa na sayar miki ba murna kike yi ba za ki sai wa Uwani zanin yayi? Amma me zai faru? Sai ga wata wasikar Abubakar cewa yana da bukatar littattafai,
kinga dole da nawa kudin basu kai ba kika rushe maganar sayen zanin yayi aka yi hidimar Abubakar. To ni a gaskiya abin da nake hange, yanzu yaran nan su fara leka irin gidan su Inki masu halin gaske, wajen cima ta abinci ba daya ba, haka wajen
sutura balle wajen kwanciya, ina gudun kada su rinka gudunmu su fi son zama da inda suka ga hannu da shuni.
Kinga kuwa daga nan sai tarbiyya za ta sha
bamban, mu rasa yadda za mu tankwasa su, daga nan
sai su nemi shiga wata hanya mara kyau kenan. Amma idan aka hakura nan gaba idan Uwani ta fara sanin ciwon kanta sai ta je,
a lokacin ta san Allah ke
bayarwa kuma shi ke hanawa”.
Mahaifiyata ta nisa ta ce,
“Eh, kana da gaskiya
saboda dan yau ba a sha masa alwashi, Allah ya kara rufa mana asiri, amin”
Mama Inki Kanwar mahaifiyata ce, su biyu ne a dakinsu, sai kaninsu namiji guda daya. Mama Inki tana yawan zuwa wajen tsohuwata a lokacin muna
kanana, sai rannan Alhaji Muntari ya ganta ya nuna mata kauna ainun, shi kuwa matarsa daya amma ta rasu ta bar shi da ya’ya uku ‘yan mata biyu da namiji
daya. Alhaji Muntari yana aiki a matatar mai ta
Kaduna, kuma babban ma’aikaci ne. A nan aka shirya
maganar aure da shi da Mama Inki, da yake mutumin
Malumfashi ne iyayensa aminan Malam Bawa ne, saboda haka Malam
Bawa shi ya yi tsaye
a kan maganar, har Allah yasa aka dace. Yanzu haka Mama
Inki “ya’ yanta uku ita ma a gidan, maza biyu mace daya.
Rannan da la’asar sakaliya Inna tana tankade,
ni kuma ina dakan kubewa, bayan na kwashe ina tankadewa, sai Inna ta umarce ni da in je in kada miyar.
Bayan na kada ta nuna na sauke, na fito na fara sharar tsakar gida, har na share, tas na yiwa mahaifina
shimlidarsa saboda na san yana gab da shigowa, na sanya kujera “yar tsugune kusa da Innata na zauna na
fara tambayar ta labarin zuwa hutu Kaduna.
Ta ce,Ki yi hakuri Uwani mahaifinki na da
dalilai masu karfi na kin yarda ki fara zuwa hutu yanzu, amma ya ce nan gaba zai rinka barinki kina zUWa Na yi murmushi na ce,
“To shi kenan Inna
Allah ya nuna mana lokacin Zuwa can sai ga Baba ya shigo, na ce,Sannu da zuwa Baba Ya Ce, Yauwa Uwani, zo nan ki amsa Na yi hanzari na mike na amso ledar da ke
hannunsa. Ya ce in yanka masa lemon in kuma debar wa Hadiza da mahaifiyarta.
Na zauna na dibar wa su Hadiza na bai wa
Zainab ta mika musu, sannan na dibar wa
Yaya Abubakar nasa na kai wa Yusuf ya kai masa dakinsa.
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe