ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 4 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 4 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Sai na yanka sauran na aje wa Baba nasa gab da shimfidarsa, na aje wa Inna nata kusa da ita tare da nasu Yusuf da Zainab. Daga nan na zauna gefe guda ina

Shan nawa muna hira da mahaifina.

A gaskiya mahaifina mutum ne mai kokarin

kula da iyalinsa, duk da talaucinmu muna samun kula ta hakika,

kusan duk maraice na Allah da wuya

mahaifinmu in ya fito daga masallaci ya shigo gida hannunsa biyu, ko dai ya shigo mana da lemo ko yar ayaba ko karan rake, ko kuma abin masarufi kamar omo ko sabulun wanka.

Haka dai muke, ko babu komai gidanmu Allah

ya azurta mu da koshin lafiya tare da ilimin boko da na Islamiyya. Kuma a gidanmu kewaye muke daso da kauna wanda muka girma cikinsa. Iyayenmu na nuna

mana. SO matukar  haka muma

muna SOn

junanmu, inda idan

daya daga cikinmu babu lafiya

gaba daya gidan babu mai kuzari, balle kwanciyar hankali. Bani mantawa a

wannan hutun ne Yaya

Abubakar ya kamu da zazzabi mai zafin gaske, babu mai cewa zai tashi. Haka muka kasance masu zullumin ko zai tashi

Gaba daya muka kasance a cikin babban falon gidanmu, a nan muke wuni a nan muke kwana muna

kewaye da Abubakar, kai idan ka ganmu za ka dauka idan mutuwa taz0′ daukarsa muna da ikon hanawa. Wannan hali muka kasance da shi har Allah ya ba shi sauki ya warware, aka fara mana shirin komawa makaranta.

Ana sauran kwana biyu mu koma makaranta sai ga direban su Mama Inki ta aiko mana da tsarabar makaranta, kamar su biskit da kayan shayi da madara,da sukari da su makilin da dai abubuwa masu yawa.

Áka raba mana ni da Abubakar, amma ni sai na rage wasu a gida. Bugu da Kari kuma ni har da dinki ta aiko mini da shi na yadi boyel mai tsadar gaske. Mun yi murna kwarai da wadannan sakonni,

muka rubuta wasikar godiya a gare ta. Ran da zamu tafi makaranta sai ga Baba ya shigo da wasiku daga Yaya Aminu ya rubuto wa Innarmu da Inna Hafsatu da Babana. A nan fa mu kai ta murna ganin wasikunsa ya

tabbatar mana yana nan lafiya.

Ranar lahadi da azuhur mahaifina da wani

makwabcinmu aka dora mu bisa keke aka daure kayanmu bisa kariya, muka rankaya sai makaranta. Muna tafe muna hira da mahaifina, can sai nace,

“Baba nan da shekara hudu da rabi shi kenan mun gama wanna makarantar

Ya yi murmushi ya ce,Eh, haka ne Uwani,

daga nan kuma sai a nemi wata a ci gaba da neman ilimi ko kuwa aure za a yi?”

Na ce, “Ka ji Baba, ni da aure ai sai na ga ina

da ilimi isasshe na kuma samu aikina wanda, zan taimaka muku kamar yadda kuka taimaka mana, a kan dagewa ga neman ilimi”Ya yi dariya ya ce,” Allah ya nuna mana lokacin Uwani, ya kuma sa muna raye”.Na Ce,

” Amin”.

Mun kama aikin makaranta ga dan-gadan, babu abin da ke damun mu, ni da Hadiza komai zamu yi tare muke yin sa,

dakin kwanciyarmu daya, ajinmu daya,

hatta a dakin cin abinci tebur dinmu daya. Idan har bamu da abin yi muna nan makale bisa duwatsu muna karatunmu, har siniya suna mana dariya, saboda zafin karatunmu.

Su kan Ce,

“Wannan idan kun shiga aji biyar sai

ya ya kenan?” Na kan ce musu,

“Siniya ai lokacin abu

a yi shi tun da karatun nan aka turo mu ai gara mu tsaya mu yi shi kada mu sha sanyin banza da iska mu tashi. a tutar maho”.

Wata rana su kan mayar da amsar cewa,

“Lallai kuna da hankali,

sauran kawayenku ai sai kidan

shantu da wakar samari suka iya Allah ya Sa

duk da son karatuna inada

sha’awar wasan Kwallon tebur (table tennis) kwarai, wanda har ya a na koyawa Hadiza, sai ya zamanto kusan kullum idan ban yi wannan wasan ba, ba na jin dadi. A cikin shekara uku na zama *yar gaban goshi a

cikin makaranta, kullum na ukun nan’nake dauka babu fashi.

Wajen huldar aikin makaranta kuwa, kamar tsabtace harabar makaranta da cikin

dakunan kwananmu, sai na zamo kamar hakimar makaranta (prefect) saboda kwazona da rashin jin tsorona, ko ina

nice mai sanya yara su gyara.Haka a

wajen taron kungiyar musulmi ta makaranta ina daya daga cikin masu karatun

Alkur,ani. Wajen wasanni kuwa dan dai table tennis ne, to nice mai fidda makarantarmu kunya, in dai na

buga, to lallai in ciwo mana na dayan nan.

Lokacin da na shiga aji hudu, wato sauran

shekara daya mu gama, haba sai kyauna ya Kara fitowa sosai, idanuwana na dara-dara farare sol, ga gira gazar-gazar, ga hancina dan siriri da labbana masu sulbi,

masu taushi da ko da yaushe suke walkiya kamar ina sanya masu wet lips. Hakorana ‘yan yar-yar kamar ni

na shiryawa kaina, ga ni

“yar doguwa siririya da

wuyana dogo, kirjina cike da dukiyar fulani.

Wani lokaci idan ina tafiya kawayena har bina

baya suke yi suna kwaikwayon tafiyata, wadda nake takawa dai daya kamar ba na son taka kasa, kuma ni har ga Allah ba yanga nakeyi ba haka Allah yayi ni amma sai ka ji wasu malamai na cewa, Asia tunda kina da kokari yangarki ta biya. Sai in yi murmushi

kawal in wuce

Ba ni mantawa da wata mahawara da muka yi

tsakanin makarantarmu ta Malumfashi da yan

makarantar Kankiya, a kan maganar tsarin

iyali. A inda na wakilci ‘yan matan makarantarmu, su kuma

*yan Kankiya wata Rabi Lawal ta wakilce su.

Ni na dage cewa, tsarin iyali yana da kyau,

saboda ganin yadda rayuwa take juyawa. Na ci gaba da cewa

“Tsarin iyali ya dauko asali tun zamanin da na

sulhuntawa tsakanin lafiya da yanayin zamantakewar

jama°a. idan kuma mutum zai duba yadda jama’a ke haihuwa suna kusan konar da kansu ne. tun a wajen

yin auren ma ba abin sharuddan da addinin musulunci ya gindaya kafin namiji ya yi shi.

-Shari’a ta ayyana cewa, sai mai lafiya, mai iko da halin ciyarwa da tufasarwa da daukar gwargwadon lalurar matar. Ashe kenan mazaje na auren mata daidai

Karfinsu ne idan ba za a iya ciyar da mataye ko suturar dasu bisa kaida ba, to aure bai wajaba a kan mutum ba.

Shi yasa shari’a ta karkasa halaccin yin aure ga mazaje inda tace akwai inda zai iya zama wajibi ko sunna ko mustahabhi ko karahiya. Wani sa”ilin ma, sai ya zama haramun.

Har wani wurin akace Idan mazaje ba za su

Iya adalci ba Su tsaya ga mata daya. To amma yanzu

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE