ARNE CHAPTER 1 BY Surayyah.M.S
ARNE CHAPTER 1 BY Surayyah.M.S
Cikin sanyin Daren damina ga duhun hanya,tafe suke wajen karfe 2saura na dare,alhaji abdullhi da drivern sa Musa
A daidai hanyar da yabi Jos zuwa abuja,
Dan sassauta tukin motar yayi domin hasken touchlight da aka buga akan idanunsa
Innalillhi wa inna ilaihi rajiun,Alhaji bar….aayi
Park,park park akace musu,nan Musa agigice ya kashe motar kusa da wata bus din kasuwa da aka faffasata da harsashi
Cillo su waje sukayi ,suna binsu da naushi
Lie down flat, don’t raise ur head or I will shoot,.
‘Bari kawae suke Kansu akasa….kimanun su shida ne sun rufe furkansu da mask
Daya daga cikin ya tukare Musa bayan yagama duba shi baisami komai ba,
Nan ya masa lilis,sai da ya ga baya numfashi,
Alhji kuwa hatta agogan sa da takalmansa sanda suka cire…..
Abun mamaki shine..duk da hakan .su biyu ne suka tsaya kansa inbanda jibgarsa ba abunda sukeyi,
In banda Azaba da radadi ba abunda alhji abdullhi ke Sha,
Daga bisani dayan ya kwada masa gindin bindiga a kai,nan jini ya fara zubowa tare da jiri dake nemar kwantr da shi
Oga yakamata amasa aiki lokaci na tafiya,
Daga hannu ,yayi ma wani shakiki acikinsu,da tuntuni a tsaye yake bai motsa ba
Alaman ya harbe alhaji abdullhi su kauce
Nan ya fara karasowa,
Dan Allah kumin rai,na rokeku
alhji da ya kusa fita cikin hankalinsa yake furtawa zan Baku dukkan abunda kuke so
Shut up, waya gaya maka Yau zallan sata muka fito,
Bushewa yayi da dariya yace Kowa xai mutu ,dole kaima ka mutu
domin gwmnatin ku ta kashe mana ogan mu dan uwan mu
Nan ya cahkamo alhaji,yace duba chan yana maida kallonsa kan motar haya wanda ba mai rai acikinsu
Said wani yaro da baiwuce shekara 13 ba makale da gawan iyayensa yana shesshekar kuka
Innalillahi wa enna ilaihi rajiun,hasbunaAllah wa neemal wakeel
Dariya suka bushe dashi dukkansu suna wani ihun cike da rashin imani…
Gunner finish him,nan ya danna harsashin zai buga kan alhaji
Ji yayi an chukwikuyesa anrike rigarsa
Ka kashe ni ka barshi,
Ni yakamata ka kashe,zan bi su mama
Banida amfani ka kasheni
Wani wawan mari ya sake masa wanda saida ya gigice
Ahakan yaron ya sake yunkurowa ya damke rigarsa sanda ya yaga gefe daya
Nan faffadan kirjinsa wanda ya ji zanen tattoo na kan biri(monkey) yA bayyana
A fusace ya danna bindiga kan yaron zai buga
Stop gunner don’t shoot him,kill d man
Karar siren din sojoji ne suka faraji,da sauri drivernsu ya fito da motarsu a jejin
nan suka fara yunkurin tatarawa
Gunner kuwa danna bindiga yayi setin kan alhaji ya danna kat
Ihun yaron ne ya farkar da alhaji da tuni yagama sallamewa idonsa a rufe yana faman Kalmar shahada
Jini ne ya mamaye kafadan yaron, kwance a jikin alhaji ji yayi yace Jesus save me,kafin nan ya rufe idonsa sumamme,
Karasowar sojojin ke da wuya aka dura su alhaji ambulance aka fara basu taimakon gaggawa ,ba a tsaya ko ena ba sai babban asibitin abuja,
Nan aka wuce da yaron nan theatre .
Su alhaji da Musa kuma aka kaisu emergency room.