ARNE CHAPTER 10 BY Surayyah.M.S
ARNE CHAPTER 10 BY Surayyah.M.S
Fitowar su alhji a masallaci bayan sallar asubahi da yaronsa zafar abayansa
dan ja da baya yayi yana kara dubawa
Raphael yagani zaune a kofar haraban duk hankalinsa na cikin wajen
Raphael? Alhaji ya kira
Em ummm ena kwana Abb..ah yafada da dan e,e nah
Me kakeyi anan ga sanyin asubahi
Ba komai ABBAH ,
Abba kullum yakan fito shima ai,kawae Baku taba haduwa bane zfaar yace
Dan murmurshi alhaji yayi yace raphael ai ba sallah kakeyi ba y not kayi baccin ka kar sanyi ya kama ka
No abba bana iya baccin ne kuma…..sai ya shiru ya rasa abunda zai CE
Toh shikenan ,muje ciki nan suka dunguma zuwa ciki su uku
Haka raphael ya cigaba da binsu yana zama a bakin haraba yanajin duk abunda akeyi
Hakama idan mallam mamman yazo weekend tun yana buya abayan window har ya fara zama tare dasu..anayi yanajin su a gefe…..
Musamman ma ranar waazi da tarihi ,domin kuwa raphael na matukar jin dadin kissoshi da tarbiyan da mallm mamman ke koyar da su zafar
Aransa kuwa wani bangaren na mamakin yadda agidan hajiya mariya CE kawae ba ruwanta da abunda ya shafi karatun Addinin yaranta….ko zuwa Inda suke bata yi
Hakan ne ma yabashi damar hllatar wajen ba tare da wani matsala ba
Ranar asabar bayan Malm mamman ya gama yan tambayoyin sa,
Alhaji ne ya taho ya iske su anata dariyar raphael da ya nace shi ma sai an masa tambaya shima.
Da murmushin sa ya mika wa Malm mamman hannu
Barka dai alhaji an fito lpya?
Lpya lau mamman ,enada ai ba wata matsala
Ahh bakomai masha Allahu
Yawwa kutashi ku shiga an gama na Yau..yafada yan dubansu
Ganin yadda raphael yayi fuskan tausayi yasa Malm mamman yace abokina kar ka damu zan tambayeka next week sai ka shirya
Da dariyarsu suka kalleshi, yana cewa toh oga mallam
Shima dariyar ya mayar musu
Toh alhaji ni zan wuce,Malm yace
Hannu yasa a aljihu ya Ciro kudi yabasa
Ka Sha ruwa a hanya an gode fa,
Godiya shima yayi ya fice_
Zafar,alhaji ya kirashi gefe yace ku shirya dukkan ku
zamu Fita kai da faryal da raphael
Murna yake ya Shiga dakin raphael yace masa kayi Saurii ka shirya abba zai fita damu yau
Minti 15 sai gasu sun fito, faryal tareda haj mariya kowa yayi kyw tubarkallah…
Nan shima Raphael ya fito cikin shigar Riga red da bakin wando jean ,ba karya shima ya fito
amma tsoro ne da fargaba cikin ransa yadda yaga hajiya na doka masa harara da gefen ido
Sunkuyar da kai kawae yayi ya wuce shima ya Shiga motar
Haka fir ta hanasa sakewa a motar duk da alhaji na nan shima aciki
Wata babban super market aka sauke su, kana ganin haduwar wajen kasan daga wane sai wane agarin abujan ma….
Duk su faryal sun sake abunsu amma Raphael jiyake kamar ya Shiga wata duniyar ta daban ba a Nigeria yake ba
Sai kalle kalle yakeyi
Dariya sukaji haj mariya takeyi kamar anbata kywtar wani abun
Subhanallh da Sauri alhaji ya karaso ganin Raphael ya makale akan stairs na zamani mai tafiya da Kansan nan
Bakauye an shigo birni,haj tafada tana dariya
zo nan mu wuce faryal.
Hannu zafar ya mika masa ya sauko kafin alhaji ya sa ya gwada masa yadda a ke yi
Kaga raphael ba takawa zaka nayi ba,tsayawa zakayi akan Wanda ka fara takawa shi zai kai ka har sama sai ka sauka
Zafar yafada yana gwada masa
Nan alhaj yace Toh ku je tare da Raphael zafar sai ka na gwada masa abunda bai gane ba
Toh abba,suka nufi sama su ma
Nan zafar ya fara deba musu kayan sakawa kala kala dayake designers ne ,tareda da expert artist suke wanda ke binsu yana basu opinion da zabi akan yanayin kowani kayan sawa da suka zaba
Duk da fargaban dake zuciyar raphael zafar bai barshi ba sanda ya jida masa kaya fiye da nashi ma.
Haka ma takalma turare, wristwatches da mayukan jiki, wanka, Dana wanke kai…
Cikin awowi 4 da rabi aka kammala komai suka kama hanya
Wani mugun kallo take masa
Wanda yasa jikinsa karkarwa duk hankalinsa baya jikinsa
Ji yayi ance raphael da karfi,a firgice yace naam Zafar
Abba na maka magana
Yace muje dakinsa mu same sa yanzu
Toh muje mana …….tare suka jera suka nufi dakin da sallamarsu