ARNE CHAPTER 3 BY Surayyah.M.S
ARNE CHAPTER 3 BY Surayyah.M.S
Bayan wata daya had yanzu gidansu alhaji abdullhi acike take tam da jama’ah ana faman debar gaisuwa,
Mun gode,mun gode allah ya saka da alkhairi,mahaifiyar alhaji inna dake zaune a babban central palorn gidan take fada ayayin da jama’ah ke zirga zirga wasu na fita wasu na shigowa.
Hm Mariya ena shikuma yaron nan ,
Ohh kina nufin arnen nan,emm yana chan daki na CE mar karya kuskura ya fito
Ban isa da abun kunyar nan ba
Gaskiyarki,ko ni nan shafaatu abun nan ya mugun Sosa min rai
Kiga yadda alhaji ke tarairaya yaron nan tun a asibiti
De na tunamin shafa’atu,.ga yaron munafuki naga sai wani shige ma yara na yakeyi
Chab,to kitashi tsaye Mariya,karki sake ya arnatar miki da yara,kinsan fa baida tsarki,kiyi takatsan tsan da shi sosai
Hajiya Mariya,, Hajiya zainab ta katse hirar tasu,
Alhaji nasan magana dake
Toh ena.zuwa,juyawar ta ke da wuya
Haj shafa tace ,hmm kinga makira ko,yanzu haka labe take mana.munafukar banza
Kyaleta,shafa barinje naji abunda zaice
Toh jeki ena nan,sai kindawo
Sallama ta yi tare da shigowa cikin spare faloun sa,
Alhaji gani.
Haba mariya banga Raphael ba ena yake ne?
anata gaisuwan nan is a perfect opportunity da zai ga dangi ,dangi su gansa’ anata tambaya kinsan labari ya riga ya fita.
Wani dogon tsaki taja,haba alhaji yanzu akan wannan maganan ka daga ni akan mutane,
Mariya? Tsaki fa kika ja min,lallai naga abun naki yafara zarcewa…
Marairaicewa tadanyi,Alhaji kayi hakuri dan Allah, nifa gaskiya nakasa sabawa ne da yaron nan
Haba mariya,Sa’ar danki ne fa zafar,meye wahala aciki,? Bake kika rike su ba meyasa bazaki iya rike dan wani ba
Dan Arne? Haba alhaji mu fa ba daya muke da arna ba…ya zakayi ma kace na karbi Arne a matsayin da na,wallhy bazai yiwu ba
Mariya? Kina cikin hankalinki kuwa…meyasa kike magana kamar bakida tausayi,you should be grateful shi yaron da kike kira arne shi ne sanadiyar rayuwata a yanzu.
Ke ba abun kunya bane ace kina wannan haukar akan dan karamin yaro Sa’ar dan cikin ki,toh daga Yau bana so naji ko na sake ganin kin kirasa da wannan sunan.
Tashi ki fice ,mikewa tayi ta fice rai a bace.
Cikin faryal zafar ya taba ke chop chop kawae
Kyal kyalewa da dariya tayi Yaya zafar stop it ,kaima haka ne,sunata wasan su gwanin sha’awa
Kallon su kawae yake yana murmushi,
Hey raphael, ya ka tsaya da cin naka chokolate din.
xafar yafada yana kokarin sa masa a hannu..EAT
Murmushi Raphael yayi wanda ya fito tareda hawaye
Oh my GOD ya zafar why is he crying?
Nan suka tsura masa ido su biyun
Bakomai,natuna wani Abu ne,
Really what’s dat,?
Babu komai zafar,I think I miss my parents yafada yana share makalallen hawayensa….
Gaba daya jikinsu yayi sanyi,faryal duk da ita karama CE amma tanada tausayi sosai har hawaye ya cika mata ido
Zafar ne ya riko hannunsa yace, c’mon Raphael you are now part of us,kasake jikinka da mu pls kaji?
yes ..faryal ma tace, yay raphael don’t worry we will share our mummy and daddy with u.
Idonsa cike da hawaye ya sake musu murmushi,nagode muku
I really like u guys am feeling like I know you for long…and I……….
Ok ok enough of this drama raphael,no more crying promise?
Faryal ne tazo da gudu ta cahkule shi.
Nan suka fashe da dariya dukansu
Zafar,cikin tsawa mai gigitarwa Hajiya mariya ta kira shi,
me kukeyi haka? Mexan gani? Faryal da ta gama tsorata sai bari take a gefe,
Ki wuce kufice anan,kar na ci muku mutunci,
get out “to your room,tafada
tana Nuna musu hanyar kofa
Dagudu suka fice