ARNE CHAPTER 4 BY Surayyah.M.S
ARNE CHAPTER 4 BY Surayyah.M.S
Mikewa tsaye yayi yana bari tsabaragen tsoro
Zauna,shege munafukin yaro….bana hanaka magana da su zafar ba
Ki ….yi ha…kuri mummy,
Pas ta make bakinsa kace me?
Mu…what? Ni ba uwarka ba CE,
Chabdi lallai yaron nan ka ci dani Yau,da kazamar arniyan uwarkan zaka hada ni,Allah ya kiyaye na haifi Arne,
.
Dan kara yayi sakamakon zafin da kunnensa yake masa yadda ta kama da karfi ta murde
Kanaji na,? Daga Yau sai yau kar na sake ji ko na sake ganin ka da yarana …
Idan ba haka ba,sai na maka abunda yafi haka kanaji na?
Eh.,.yafada yana shesshekar kuka,
Eh what? Bakada tarbiya ai dole zaka na amsa min kamar ni Sa’ar ka CE
Daga Yau sunana Hajiya abakinka,
karkasake naji ka kira ni wani suna da zai dangata ni da kai ,ARNE kawae
Nan hajiya mariya ta hankade sa yafada kasa ta kuma taka shi ta wuce abunta
Kuka Raphael yakeyi ,cikin tsananin shauki da tunanin iyayensa har bacci ya daukesa a hakan
Bayan sallar isha ‘i an watse mutane an koma gida
kowa ya hallara wajen cin abinci
Faryal da zafar da suka yi shiru bakamar yadda aka saba jinsu awajen ,domin kuwa Hajiya mariya ta kashe musu warning akan zuwa dakin Raphael,
My princess ina yaya Raphael? Abba ya tambayi faryal,
Zare ido kawae take tana mutsu mutsu….
Yana daki abba zafar ya Fada ,meyasa Baku taho tare da shi ba zafar
Haba alhaji kabar yaran nan suci abinci mana,ai yanada kafa yafito mana ko so yake ana Goya sa…? Cikin ranta tana cewa kamar dan sarkin Arna ko hmm
Baice komai ba ya tashi ya wuce sama ,bayan mintuna kadan sai gashi ya sauko da raphael biye a bayansa
Zauna anan, laraba serve him,yafada ma mai girkin gidan dake tsaye
Ke ,da Allah ki tashi mana akai,ki kyale shi zaisa,
Wani mugun kallon da alhaji ya mata yasata tayi shiru ta nitsu
Nan laraba ta sa masa abincin idonsa akasa,kirjinsa na dikan uku uku
Ci mana raphael
Nan ya dago kansa sannan ya fara ci ahankali,
Tsaki Hajiya mariya taja ta tashi ta barwajen