ARNE CHAPTER 5 BY Surayyah.M.S
ARNE CHAPTER 5 BY Surayyah.M.S
Kwanan alhaji biyu da tafiya Lagos,ko abinci raphael baisamu yaci ba haka ya kwnta
Ruwa mai sanyi yaji an watsa masa .
Tashi….
Da sauri ya mike da jikaken kayan jikinsa
Tace ya biyota backyard
Nan ta ajiye masa wasu kayan da it a kanta batasan amfaninsu ba kawae a store ta debo
Wanke mun su yanzun nan
Tafada ta juya abunta
Jiri ne ke dibarsa tsabr yunwa da kasala da yakeji,ga sanyi
Amma haka ya kafa kansa akan wankin nan sai famar yi yake
A hankali yaji ana sa key ma kofar backyard da ya shigar dasu cikin main house din
Zafar da faryal ne suka taho cikin hadadden pyjamas na barci…..tasa pink Riga da wando iya ankle wrist shikuma zafar yasa sky blue Riga da wando
Shhhhhhh zafar ya masa ,Inda suka karaso da niyyar tayasa wanki
Meya fito da ku? Yafada a hankali
Munje dakin ka ne bamu ganka ba
Hhnm karya zafar fadi gaskiya
Toh munjiyo ka da mummy ne shyasa muka zo shikenan?
Dan zaro ido Raphael yayai ,zafar pls Ku koma ciki kar ta zo
Yaya raphael ai na kulle kofa kafin tazo zamu gudu mu buya karkadamu
A cikin rada suke maganar kamar wasu marasa gaskiya su uku akan wankin
Faryal karkisa ya isa haka kar sanyi ya kamaki……zo ki zauna anan
Nan ta fara commentator tana musu game akan wayafi iya dirza kaya.
Ya zafar ure too lazy 8/4 fa… yakamata point dinka ya dan karu
Dariya suka fashe dashi,ai dake ne anan da 0/10 ne zaki samu
Tura baki ta zaro ido waje tace, stop it, ya zafar kamance I’m princess Elsa the snow warrior fighter (animation cartoon da suke kallo)
Kajita hmm sai shegen son kallo
Ehh yay Raphael ya akayi ka iya wanki haka? Pls tell us we want to learn too
Ke kina nufin ni ban iya bane ko me.
Hey calm down bro..yafada yana dafa zafar
,faryal zan koya miki kar kiji komai
Amma waya koya maka mu bamu taba yi ba sai yau.
My mum,yafada cikin sanyin murya kansa akan aikin daya keyi
Where is she now? Faryal tafada cikin son taji komai
She’s dead, yafada da dan murmushi and
My dad too
Shiru tayi tana kallon reaction din fuakarsa idonta yana nemar kawo hawaye
Bugun kofar aka fara da karfi,kai raphael ko wa kake da suna waya baka izinin kulle min kofa
Nan suka dabirce suka fara Neman hanyar buya acikin shukar dake wajen
A hankali ya bude kofar,bai hankara ba saukar mari yaji tas a fuskarsa, dan ubanka wani munafurcin kake kullawa anan
Nan tafara dube da dube tanayi tana zaginsa ,
Tsoro ne cike a zuciyansu zafar da suka dukunkune a kasan katoton shuka da ta tsaya a tsakiya awajen
Hajiya kiyi hakuri,wankin nakeyi,
Yimun shiru kazami arnen banza dan wuta ….
Allah ya tsine haihuwar ka wallhy shegen yaro ka zo ka fancama cikin rayuwar mutane
Hannu ta mika zata sake wanka masa mari a kunburarren fuskarsa ..ya dan ja da baya bata same shi ba
Wani uban tsawa tadaka masa ,nice zaka kaucewa ehh lallai kam
Kafara fuka fuki tun ba aje ko ena ba? Toh biyoni ciki Yau zan banbance maka tsakanin mutum da dabba.
Nan ya fara binta zuwa ciki zuciyarsa cike da tsoro da fargaba