ARNE CHAPTER 7 BY Surayyah.M.S

ARNE CHAPTER 7 BY Surayyah.M.S

 

 

 

Kasa xama tayi ,hankalinta ya kasa kwanciya domin kuwa bata san halin da raphael yake ciki ba

Tana so ta je…

Amma kuma tsoron mummyn ta takeji.

Chan anjima shirun yayi yawa ba maiko motsi agidan

Faryal CE ta mike straight zuwa dakin da Raphael yake ,ihu ta sake ganinsa har yanzu akwance duk jikinsa shatin bulala

Da gudu  tayi hanyar waje Inda suka ci karo da baba mai gadi,chief security na gidan.

Janyo ta yayi yace faryal lpya? Ke da waye haka

Ba…Ba  dan Allah ka taimaka ma Yaya raphael zai mutu tafada tana fashewa da kuka sosai

Subahanllah yana ena?

Yana daki _nan zafar ya iske su hanyar tahowa da baba chief security ,

Sallamewa kawae yakeyi ganin yadda raphael ya kwanta akasa baya ko motsi

Ena Hajiya  ku kirawo Hajiya a rude baba yake Fada musu

Ganin yadda sukayi tsuru tsuru da idonsu ne yasa ya CE

Zafar ena maka magana ka tsaya,

Umm uhmm baba mummy ne ta buge sa.

Dan Allah ka taimaka mukaisaa asibiti kafin tafito

Nan hawaye suka fara tsilala a idanun zafar din

Taimaka masa sukayi har yakai raphael asibiti batare da Sanin Hajiya mariya ba

Bayan sati biyu Wasu bakaken range rovers ne sunsha tint baka

Su shida aka parking a gidan alhaji abdullhi.

Da gudu faryal ta fito ta rungume sa abba na tafada da murmushinta

Shima mayar mata yayi da murmushin yace my princesss yakamo hannunta suka shige ciki

Komai a tsare yake a gidan kamar kullum zafar ne ya sauko shima ya tarbi mahaifin nasa.

A kitchen kuwa kunnensa taja da karfi,

toh saura ka ketare dokokin da nafada maka …wuka ta zare ta nuna shi da shi

kaga wannnan? zan chaka maka Shi na kashe arnen banza.

Hawayensa ya goge,yace toh Hajiya

Harara ta watsa masa tace Da Allah bace min

kuma ka wuce ka canza kaya kafin ku hadu da alhaj yaganka ahakan.

Wawa kawae.

Nan tafice tabarsa ta nufi site din alhaji

Da sauri ya kammala mopping din dayakeyi ya kama hanyar dakin sa

Yana shiryawa yana godewa Allah zai samu ya dan huta ,yasan dai dole tabar masu aiki gidan su kama aikinsu yanzu

Don’ dama Hutu taba mai aikin shara mopping da goge goge, ga shi gidan ba kadan ba ita kuwa

Ko zai kwana ya wuni yanayi ne ba damuwarta bane kuma bai isa yace ya gaji ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE