ARNE CHAPTER 8 BY Surayyah.M.S
ARNE CHAPTER 8 BY Surayyah.M.S
Sum sum yafito har yadan canza da ga asalin kamar sa kamar marar lpya…
,
Tsugunawa yayi cike da biyyaya ya CE alhaji sannu da dawowa ,ya hanya?
Ahh raphael zo nan ka zauna ,ya nuna kusa da shi
Zuciyarsa cike da tsoro ya mike ya nufi Inda alhaji yake ya zauna
Ya kake? Ina fatan kana having good time da yan uwanka su zafar?
Kai ya daga baice uffan ba
Wani paper ya Ciro a brief case yace gashi Raphael, wannan list din makarantu ne kazaba inda zaka karasa secondry schl dinka yakamata kafara zuwa ko?
Idonsa cike da kwalla ya kalli alhaji yace ,alhaji makaranta?
Yes ,son ure free to choose, make your choice
Ko abaka lokaci ne kayi tunani?
Ahhh no sir,Barin duba
Yafada ne kawae amma harga Allah baisan ko makaranta daya a cikinsu ba,domin kuwa makarantun yaran manya ne zallah
Lura da shi zafar yayi sannan ya gano abunda yake ciki
abba y not ASA shi a makarantan mu sai muna zuwa tare ,
Dan kallonsa raphael yayi yace eh alhaji hakan ma yayi,
Raphael ,abba ya kirasa I’m your father kadaina CE min alhaji kaji,call me ur abba
Murmushin jin dadin dukansu uku sukayi
Inbanda Hajiya mariya da ta cika FAM saura kiris take jira
Sauka kasa yayi ya sake rusunawa gaban alhaji…
Nagode abba ,Allah ya saka maka da alkhairi…
Dagosa yayi yace no thanks my son, ka dauka nan kamar gidanku ne kaji? Yace toh abba na gode
Toh ku tashi ku je daki ,nan dukansu suka mike cikin farinciki suka nufi dakunansu
Murmushi alhaji ya yi yana cewa alhamdullhi,
Dogon tsaki yaji taja,tace hmmmmm
Allah sitiri bukwui inji kishiyar mai kusumbi
Kana bani mamaki wallhy
Dan dai daiita kallonsa yayi yace name fa?
Yadda kake buga kai akan Arne mana,wallhy wannan ba dabian musulmi bane
Dariya alhj yayi yace Mariya kenan,a naki sanin ba?
amma musulmi na kwarai ai baya walakanta dan wani
Arne ?haba alhaji yaron nan fa daga kazanta ya fito,mutanen da basu tsarki masu fitsari a tsaye?
wai meyasa ka rife idonka ne haka
ARNANCi Kazanta CE tabbas ,amma ai shi mutum ne ko? Kin manta da kissar fasikar karuwa da kare? Sanadiyar bashi ruwan Sha da tayi Aljanna ta shiga fa
Haba mariya,ko qurani ma cewa yayi ka zamo mai kywtata wa dukkanin mutane,..baice lallai sai musulmi ba…..meye laifin rikewa da taiimakon yaro karami kuma maraya ba uwa ba uba?kika sani ya samu kykkwan rabo ta sanadiyar mu ko ma mu mu rabauta sanadiyarsa?
Kifada min mariya….me asalin dalilinki na tsanan yaron nan
Shiru tayi batace komai ba
Hmmm ki nutsu fa, ni bana son yadda kike aibanta yaron nan
Tashi tayi shiru abunta ta wuce dakinta tana kukkuni.