ARNE CHAPTER 9 BY Surayyah.M.S

ARNE CHAPTER 9 BY Surayyah.M.S

 

Bayan  wata biyu a gidan alhaji ,raphael ya warware

normal kamar bashi ba

Zaune yake a kofar masallacin gidan yana sauraron zafar dake karatun Qur’ani bayan sallar asubahi.

Nitsuwa yayi tamkar wanda yasan abunda ake cewa…….har cikin ransa abun na Sanya shi jin nitsuwa  

Shyasa ma ya nace kullum sai ya biyosa ko a sace ne ya labe yana ji

Karfe 7.saura suka nufi gida tare ,asace raphael ya shiga dakinsa domin kuwa Hajiya ta hanasa hada hanya da su zafar

Shikuwa kullum yana like duk enda zasuje dashi

musamman ma zafar da ke sa’arsa ne,,,sai ya buya a gefe guda har ya gama harkokinsa kafin su dawo

Hajiya kuwa bata damu ba ma saboda a dakinsa tace yadinga zama kar ya fito mata cikin gida.

Alhaji abdullhi dan kimanin shekaru 45yrs bafulatani ne dan asali kauyar Adamawa a Nigeria

mahifinsa alhaji Muhammad ja’EH da

,mahaifiyarsa Hajiya salima ita kuma asalin yar Ethiopia cr…

a tsaye yake duk da shekaru tafara ja, kynwun halittarsa bata boyewa,

mutum ne mai ilimi sosai da sanin yanayin zaman takewa …..kafaffen mai kudi ne wanda ya samo asali ne tun daga mahaifinsa….ya mallaki kamfanoni a Nigeria da kasashe daba daban a waje.

Alhaji abdullhi da Hajiya mariya auren zumunta akai musu …ita kuma yar Ethiopia ce

ta wajen mahaifinta

,mariya dai yar dangin mahaifiyar su alhji abdullahi ne Hajiya salima

Farace Sol ,tanada kyw Nagani nafada,..sai dai arziki da rurin mallakar duniya tasa ta zarmewa cikin tsananin son abun duniya

Hajiya mariya bata haihu da wuri a gidan alhaji ba kasancewarsa mai wahalar zama waje daya da kuma Kaddaran Allah…

shekarunsu na hudu da aure  ne Allah ya fara bata haihuwa nan aka samo zafar.kafin faryal da ta fito bayan shekara 4  da haihuwar zafar….

Farare ne sol ga bakin gashi yaleyale mai tsayi kwnce akansu sai manya manyar idanunsu,,in kagansu ma zaka dauka yaran larabawa ne…

,taso ta sangarta su da son nuna abun duniya da sakalci irin na yaran manya

amma ena ‘enna salima mahaifiyar alhaji da shi kanshi alhaji sun Sha karfinta wajen tarbiyartar da yaransa

Don’ kuwa ilmin addini ya fara nema musu a gida tun suna kanana sosai ana musu kamr lesson, da malaminsu malam mamman wanda yake zuwa

Wekend tun 10na safe

Faryal duk da ma ita karama CE shekarunta 9 a duniya kawae amma Allah ya azurtata da tausayi da kaifin basira, tanada taurin kai amma zuciyarta Nada saukin tarairaya…

Ga shi Allah ya bata ilimi domin har takara suke da yayan ta wajen daukar karatu…..

Sun girma cike da kauna da tausayin junansu,

nasihohi da wa:azi. Da malam mamman ke yawan musu na mussamman shine yayi tasiri akan Dada gyra tarbiyansu da nagartan su

Domin kuwa Alhji abdullhi  ya umurce shi da ya ware lokaci na mussamman na koya musu dabia bisa ka idodin musulunci da basu tarihin akan

halayen manzon Allah SAW.

Komai tare ake musu gurin bacci ne kawae kowa da nashi

dakin.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE