AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 10 KARSHE BY SUMAYYAH ABDULKADIR

 AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 10 KARSHE BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mammah ta ce. Saboda me?

Yo, Yaya Maryamu tsiransu a haihuwa shekara uku, yanzu ne yake shekararsa ta farko a jamia ita kuma tana ajin karshe a secondary, sannan iyayensa sun ce ba za su yi masa aure ba sai ya gama degree ya yi hidimar kasa ya samu aikin da zai iya rike iyali. A matsayin Saima na mace yaushe za ta tsaya jiran wannan mijin?

Wata ajiyar zuciya Mammah ta yi cikin jin dadi, ta maida akalar zancen ga mahaifiyarsu. Adda ki roka min Mariya da Luba, su baiwa yayansu Usman da Haleem auren Halima da Saima, shi Ismael ya zabo wadda ta yi masa tuni, su kuma sun bani zabi da yake sun fi shi son kwanciyar hankalina. Ni kuma na hanga na ga gida ba ta koshi ba baa kai dawa ba. Yayan nan ina da su yammata har ukku, ban da Ismael ya kawo wata Wasila da sai a hada har Khalisa (yar Furera).

Hajiya maryam sai gani ta yi kannen nata sun fashe da kuka. Da fari ta tsorata kafin Mariya ta soma bayani.

Yaya Maryama anya akwai sauran mutane irinki a duniya? Yadda zumuncin zamani ya koma mutum ko ciki daya ku ka fito in shi ba shi da shi kai kana da shi ba ka jawo shi jikinka, neman yadda za ka nesanta kanka da shi ka ke, amma ke yayanmu za ki aura wa yayanki yan gata irin haka?

Ta ci gaba da kuka. Aunty Furera ta ce, Tunda Ismael ya kawo wadda yake so kada ki kara zancen Khalisa, da Saima da Halima da Khalisa duka daya ne. Yaya Maryama mu da yayanmu naki ne ba sai kin roke mu ba. Iyakaci mu gaya wa iyayensu maza saboda hakkin haihuwa. Allah ya tabbatar mana da wannan abin alkhairin. Ya sa zumuncinki shi ne silar shigarki aljannah.

Adda ma albarka ta yi ta sa mata, ta ce, Maryam har gobe ina alfahari da haihuwarki, daya tamkar da goma. Allah ya albarkaci gabanki da bayanki.

Sun tsayar za a fara yin bikin Ismael da Wasila, Usman da Haleema in sun kammala hidimar kasar da suke yi. Zaa jinkirta na Haleem da Saima sai ya gama karatunsa nan da shekara biyu lokacin ita ma ta gama secondary watakila har ta fara tertiary. Hafsat na gefe tana jinsu tana shayar da danta Khalipha ita ma abin ya gamsar da ita. A ranta ta ce Fitinanne ya je ya nemo yar Abuja haka za ta zo ta fitine su kamar yadda ya fitine su.

Suna haka suka ji sallamar Abdulazeez, dare ya yi sosai don sun soma jin barci ma. Aunty Murja ce ta amsa masa Mariya sai harara. Kai kuma lafiya da tsohon daren nan? Kai da ke da tafiya a gabanka da asubahi ya kamata a ce yanzu ka kwanta.

Hafsat na ganin shigowarsa ta yi maza ta cire yaron ta gyara rigarta. Ya dubi Aunty Mariya cikin lallashi. 

Wai don kawai na ce bai isa goyo ba ki ka dauki gaba da ni haka?

Ta ce, Au, wato haka ka ce ko? Wallahi sai in fallasa abinda idona ya gane min….

Da sauri ya ce, Mammah ki bata hakuri, kuma ni ba da wani nufi na ce Khalipha bai isa goyo ba, don kada ya samu gocewar kashi ne kasancewar kashinsa bai yi kwari ba.

Mariya ta ce. Ita Addar har a bakwaininta mun goya ta a Saudiyyah, nata kashin ya goce? Balle wannan shekararre a ciki?

Wani irin bata fuska ya yi. Ni Dana bai shekara a ciki ba.

Mammah ta kalle shi, sai da ya ji kunyar da yake jin ba shi da ita yanzu. Ya hau shafa kai ya ce. Wai sallama na zo muku.

Mariya ta ce. Ka zo mana ko ka zo musu?

Dukkanku. 

Ta ce To, mun karbi tamu. Allah ya kiyaye hanya. Ke Addah ku je daga falo ku yi sallamar mu muna magana.

Ya kuwa juya ya fita yana ce da Anty Mariya. Dadina da ke zuma ce, ga zaki ga harbi.

Ta ce, Ka ce min kunama ma duk daidai da kai ne.

Ci gaba suka yi da maganganunsu, Murja ta lura Hafsat ba ta da niyyar tashi ta dube ta ta ce Addah ba jiranki yake yi ba ne?

Anty Mariya ta ce, Bar munafuka jira ta ke sai an maimaita don a ce mata saliha, ni yau a tafin hannuna suke.

Da sauri Hafsat ta zura hijab ta sauko daga gadon ta doshi kofa saura kadan su yi dariya amma ban da Mammah, magana suke ita da Adda Hafsatu. 

A falo ta tadda shi a zaune da alama a kagare yake da zaman jiran da ta sa shi. Yana ganinta ita daya ta ce. Koma ki dauko shi.

Kamar za ta yi kuka ta ce Ni wallahi ba zan iya dauko shi a gabansu ba.

Mikewa ya yi ya koma dakin, sai ga shi ya dawo da yaron a hannunsa ya zauna yana ta aikin kallonsa. Can ya lura har yanzu a tsaye ta ke kamar a ce Kyat ta arta a na kare. Ya ce, Kin min kerere a ka!.

Ta dosana can nesa da shi ta zaune a dofane. Wani haushi ya kama shi ya zube shanyayyun idanunshi a kanta.

Is that the kind of farewell you choose for Us(wannan ce irin bankwanar da ki ka zabar mana)?

Ya yi maganar ne cikin kwantaccen sauti yana danne bacin ransa.

To wace iri za mu yi? Ita ma ta tambaya cikin irin yanayin da ya yi tasa tambayar.

Au tambaya ta ma ki ke yi?

Ta mirgina kai, Yaya Azeez we are not alone. Muna tsakiyar iyayenmu ne, please ka tuna wannan.

Su suka ce ba za mu yi sallama ba saboda suna nan?

Ba su ce ba,we are to make use of our senses, mu yi abinda ba zaa ga rashin kawaicinmu ba.

Muryarsa a sanyaye ya ce.

Madame! Yanzu ni me na yi na rashin kawaici? Ko dakin da nake ban ce ki je ba, ko soro ban ce ki je ba. Im going thausand miles away, amma ko kusa da ni ba za ki zauna ba. Ba za ki zo mu kalli Khalipha tare ba. Ba za ki gaya min abin da zan ji dadi ba in dinga tuna shi yana debe min kewarku ba. Guduna ki ke yi kamar zan sace ki, in wannan ita ce kunya, toh Allah wadaranta! Wuce ki ba ni waje, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi.

Kasa tafiyar ta yi duk da kafin a yi hakan ita ce abin da ta fi so ta yi, sai hawaye da ta soma sharewa. Bai kara bi ta kanta ba ya ci gaba da kallon Dansa yana sumbatarsa. Daga karshe ya mike ya shiga da shi ciki ya kwantar ya zo ya wuce ta ya fice.

Ji ta ke kamar ta bi bayansa ta bashi hakuri, amma ta san ba za ta iya ba. Hawayenta ta share da gefen hijabinta, sannan ta shiga dakin. Daga ita sai Mammah suka kwana a dakin, tana daga kasa kan carpet. Dukkansu a daya bedroom din suka kwana, Addah Hafsatu da ma (kwana sallah) ce kaman Dadanta.

Washegari gida ya watse kowa ya koma inda ya fito. An nemi wayarta kafin a gano Abuja aka baro ta, Mammah ta ce za ta bayar a kawo mata ko za ta sayi sabuwa? Ta ce a barta, yanzu kam ba ta da bukatarta, in za ta yi kira za ta yi amfani da ta Adda. In za a kira ta a kira Addan ta ba ta.

Ta fadi hakan ne sanin halin kayanta, in ya yi fushi da ita punishment dinta a yi barring dinta zuwa sanda aka ga dama.

  ******

Alhamdulillah! Yau Abubakar (Khalipha) ya cika kwana arbain a duniya. Sun yada wanka. A washegarin ranar gidajen yan uwa suka wuni. Uncle Ibrahim ya kakkaisu har AKTH gidan Dr. Idris Dakata. Mammah ta ce da Adda Hafsatu Hafsat ta shirya ta wuce Jimeta daga Kano ta yi sati daya sannan ta koma Abuja.

Ibrahim autan Addah shi ya kai su filin jirgi ya yankar musu tickets ita da Zulai mai sa mata ruwan wanka wadda tsohuwar mai aikin gidan Malam Abdullahi Dakata ce. Ita Adda ta sa ta rakata Jimeta don ta taimaka mata da hidimar Khalipha. Sun samu Imamu na jiran saukarsu ya dauke su zuwa Demsawo.

Dangi sun ga Khalipha sun more. Haka ake kwantar da shi a gefen buzun Mallam a kan yar katifarsa mai laushi wai ya je taya shi hira. Su ne har Numan, daga karshe a gidan Abbanta ta kwana biyu. Suka dawo babban gida Daada ta soma yi musu shirin komawa. Gyaran haihuwa ta ke mata bana wasa ba irin na fulanin usli da nono da madara da tukudi da hakukuwansu na gado. Ta kuma yo mata guzurinsu. Ranar Lahdi Abba da kansa ya kai su filin jirgi shida su Modibbo. Aka sa Zulai a jirgin Kano, Hafsat da danta a jirgin AZMAN mai zuwa Abuja.

                 *****

Hafsat ta iso Abuja lafiya ta tadda dalleliyar kankanuwar motarta tana jiranta. Tafiyayya tun daga General Motors din Amurka, sakon Baban Khalipha matsayin gift dinsa na haifa masa Abubakar Sadik. Usman ne mai wannan bayanin ganin ta tsaya tana shafa motar tana tambaya ko Daddy ya yi sabuwar mota ne?

Maimakon ta yi murna, kunya ta yi ta ji ba ta kara zancen motar ba. Ismael ya ce, in ba ta so ta ba shi ya samu ta kai Wasila shopping. Harara ta dalla masa, Mammah na bada baya ta sassauta murya ta ce da shi.

 Ashe ba sonta ka ke ba, tunda ba za ka iya saya mata mota ba.

Tafi ya yi har sau uku. Cikin ransa yace haihuwa ta bude idon Addar su. A fili kuma a yace Sannu matar so! Ki bari in samu aiki ki sha kallo, Wasila ta fi karfin mota wallahi, private jet zan gwangwaje ta da shi in ta haihu. Ki ma daina murna wai SO ne ya sa aka siya miki, wallahi arzikin Sadik ki ka ci, da can me ya hana a saya miki aka bar mu muna jigilar kai ki makaranta da dauko ki?.

Ismaeel ya kunnata yadda yake so, ya tashi ya bar gidan yana mata dariyar keta.

Hafsat sai ta koma gefe ta zama yar kallo tana kallon yadda ake soyayyar jika da kaka tsakanin Daddy da Mammah da jikansu Khalipha Abubakar As-siddiq. Ita dai ta san ta haifi Abubakar ne, amma wadannan bayin Allah sun fi ta kaunarsa. Daddy in ya dawo kafin ya ci abinci sai ya ga Khalipha cikin gadonsa a gefensa, yana wutsilniya da kyawawan kafafu da hannayensa cikin koshin lafiya. Mammah kuwa goyo, ko umh ya ce za a jefa shi a baya a daure. Ita da shi tsakaninsu shan nono, ko Jummai ba ta taba musu jika sai dai ta yi wankin kayansa.

A wannan lokacin sai ta ga ba abin da ya kamace ta irin ta ba da kaimi wajen ibadah da gode wa Mahaliccinta. Ya yi mata komai a rayuwa, burinta a yanzu shi ne cikawa da imani da ganin dawowar mijinta kasar haihuwarsa lafiya.

A wannan satin suka koma makaranta, bayan dogon hutu da suka sha na gama zangon farko na shekara ta uku. Sun fara (second semester) na level three Usman ya soma koya mata driving. Dole ta ajiye tsoron don tana so ta koya din ko don ta ragewa Abdulazeez hidima, ta lura da yadda yake takura kansa sosai wajen kaita makaranta da dauko ta sanda suke gidansu. Cikin sati biyu da farawarsu ta soma ganewa, shi kuma zai koma Edo inda yake hidimar kasa. Don haka ya makala mata katuwar L ta ke tuka kanta. A gida ta ke barin Khalipha kasancewar ya fara shan madara. Cikin satin nan suke sa ran dawowar Abdulazeez gida bakidaya.

Daddy ya sa an fidda komai na gidansu an zuba sabo na yayi, hatta fenti an sake. Gida ya koma kamar ba a taba zama a cikinsa ba. Mammah ta yi wa Daada magana a nema wa Hafsat rikon ya a dangi, wadda ba ta haura shekara goma ba saboda ta taya ta da Khalipha, Daada ta ce gara babba wadda ba sai ta bi su makarantar ba, akwai Lantana kanwarta da ke aure a Girei mijin ya mutu shekarar baya, kuma ba ta taba haihuwa ba, za ta yi mata magana in ta amince za ta koma wajensu. Sosai Hafsat ta ji dadi, don kuwa mammah ta sangartata da rainon Khalipha ba wani iyawa ta yi ba. Ta fara tunanin yadda za su karke in sun koma gidan nasu da wannan kukan daren nasa da goyo kadai ke rufe bakinsa, ita ba ma iyawa ta yi ba, ji ta ke kamar zai fado ko kafarsa ta goce kamar yadda Abdulazeez ya ce.

Saura kwana biyu Abdulazeez ya dawo Lamtana ta iso Abuja.

A washegari Daddy da kansa tare da maidakinsa suka zuba su a mota suka maida su gidansu. Salisu ya biyo su da motarta. Sun dade suna tofe gidan da adduoi. Mammah ta jaddadawa Baba Lamtana yadda za ta dinga kula da Khalipha sannan suka shake musu store da kayan garar Hafsat da aka kawo daga Jimeta. Na freezer ma ba abin da Mammah ba ta ajiye musu ba. Danfulani dan amana, har yanzu shi ke kula da gidan bai je koina ba don Abdulazeez ba ya wasa da hakkinsa.

Daga Mammah har Daddy sun kasa sakin Abubakar su tafi, shi kuma kamar ya gane sai kuka yake yi. Sai da Mammah ta goya shi ta yi ta jijjigawa ya yi bacci, sannan ta je ta shimfidar da shi a gadonsa suka bar gidan kamar kar su tafi. Ina ruwan abin cikin kwai ya fi kwai dadi!. Haka Lamtana ta ce bayan fitarsu.

Hafsat ta ce. Ai sauri zan yi in yaye shi in kai musu abinsu.

                 ******

A zaton Hafsat da aka ce washageri Abdulazeez zai dawo ta sa a ranta irin da yamma ko da rana ko da daddare. Tunda dai ita ba waya suke yi ba. Karfe biyar da rabi na Asubahi ta idar da sallah, tana so ta yi lazimi amma wani irin mayataccen barci ke cin idanunta, kasancewar Khalipha bai barta ta runtsa ba daren jiya saboda kuka, ba ya bude jiniyarsa sai tsakiyar dare, Lamtana ta zo ta buga mata kofa don ta taimaka mata ta ce ta je ta kwanta ba komai za ta iya da shi. Goya shi ta yi, ta yi ta yawo da shi a dakin ba dama ta zauna. Ta ba shi ruwa, ta ba shi nono duk a banza kuma ta san lafiyarshi kalau. Haka yake yi a gidan Mammah ba ta san yana yi ba baccinta ta ke shaka komai a kan Mammah yake karewa.  Sai jiya ta san yaya Mammah ke shan wannan hidima. Ba ta samu ya yi bacci ba sai goshin asubahi, ita ma da ta idar da sallar a nan kan dardumar ta bingire tana bacci. Wani bacci mai tsananin nauyi da ta dade rabonta da irinsa.

Har Abdulazeez ya shigo ya shiga toilet dinta ya yi alwala ya fito, ya yi sallah a gefenta ba ta sani ba. Ya dade yana addua yana gode wa Allah da ya dawo da shi cikin iyalinsa lafiya. Zuwa ya yi ya ciro Khalipha daga gadonsa ya maida shi tsakiyar gadonta. A ransa yana fadin.This is punishment. Ta jefa yaro a gado shikadai tana can tana bacci ba ta san me yake ciki ba. Kamar ya tashe ta sai ya lura tana jin dadin baccinta.

A hankali ya dauke ta ya maida ita gadon ya sanya Khalipha a tsakiyarsu ya ja quilt din ya rufe su iya wuya. Shi ma da gajiyar zaman jirgi ya dawo, don haka bai dade yana kallonsu admiringlyba shi ma ya yi bacci.

Yunwa ce ta tashe ta, kasancewar ba ta ci abincin dare ba ta yi baccin. Ta sha mamaki da ta ji ta a kan gadonta, ba ta fita daga wannan mamakin ba ta yi arba da danta a gefenta. Kusa da shi mahaifinsa ne Barrister Abdulazeez Hamzah Attikou, yana ta barcinsa freely irin baccin warware gajiyar zaman jirgi. Wani dakace (INAMA A CE!) Da ta taba yi a can a baya… Ita da Abdulazeez matsayin maaurata na din-din-din da BABY (in between) yana kicking kwance a tsakaninsu. Yau Allah ya cika mata wannan dakace da ba ta taba mafarkin zamansa reality ba.

Ci gaba ta yi da kwanciya a yadda take a kan pillow tana kallonsu; her heart SWELLING with love and pride (zuciyarta na kumburi da soyayyah da alfahari). Ba ta jin in za su shekara a haka za ta gajiya da kallonsu. Wani naushi da Khalipha ya sa kafa ya kirba wa ubanshi ba shiri ya soma bude idonshi a hankali. A kanta ya sauke su, suka yi wa juna kuriiii da ido. Babu wanka, ko kwalliya,ko wani special artificial abu a tare da ita sai kayan barci masu tsananin taushi, amma a haka ta kawatu a zuciya da idanunsa fiye da duk matan duniya da ya taba cin karo da su a rayuwarsa.

Sannu da zuwa!. Ta fada cikin nutsuwa da farin cikin da ya gaza boyuwa a cikin muryarta.

He is kicking me. 

Ya yi complaining.Ba tareda ya amsa sannu da zuwan nata ba.

Me ya sa ka rabo shi da gadonsa toh?

Because I want him to do so. (Saboda ina son shi da yin hakan).

Murmushi ta yi.Then why are you complaining? (Me yasa kuma kake korafi?)

Because Im appreciating (Sabida ina jin dadin hakan). Ya ba ta amsa.

To Allah ya raya maka shi rayuwa mai tsayi da albarka.

Ke ban da ke? Ke ba kya son shi ko Hafsat?

Murmushi ta yi. Ta ya ya zan ki son dan Abdulazeez dina?

Lumshe ido ya yi kalmar karshe ta yi masa dadi.

Ban ga alamar hakan ko daya daga gare ki ba. In fact a gabana sai an roke ki ki yi breast-feeding dinshi. Wannan abu ya dade yana mun ciwo.

Ka yi hakuri, lokacin ban saba ba ne, ina jin zafi sosai.

To ba za ki daure saboda shi ba? Na san dai duk zafin bai kai na labour ba, horon yunwa ga Dana Hafsah!

Girgiza kai ta yi, ta san Abdulazeez da mita akan hakkin sa. Ta dade da sawa a ranta zancen nan bai wuce ba idan ya tuna sai ya dawo dashi sabo. Ka bar abin da ya wuce ya wuce don Allah, na ji na yi laifi, ina ba ku hakuri dukkanku.

Sosai ya ji tausayinta, domin tuni har kwallah ta taru a idanunta.

Ba za mu hakura ba, sai in kin yarda ki samo mana kani ko Babata Habibah a yau.

Zaro idanu ta yi, Haba-haba Abban Khalipha! Ku ji tausayina mana!

Sosai ya ga tsoro da fargaba cikin fararen idanunta, duk kuwa da dadin da ta ji na jin cewa da ya yi zai yi wa Habibah marigayiya takwara. Mikewa ya yi ya dauke yaron daga tsakaninsu ya maida shi gadonsa. Dawowa ya yi ya daga duvet din ya shige jikinta sosai. 

Ni, da ke, da shi, wa ya fi cancanta a fi tausaya wa? Ni da na shekara babu mata,a gabadayaya shekarun kusan uku da aure baifi sati biyar kacal na mallaki matar ba, da ke da ki ke tsoron wani cikin bayan kina cikin koshin lafiya, ko kuwa shi da ko yau aka haifi wani zan taya ki mu yi ta rainonsu?

Hafsat ba ta iya ta yi magana ba sakamakon sakonnin da ya soma aikawa cikin illahirin gangar jikinta. Ga son mijin, ga kewarsa, ga kuma matsanancin tsoron rainon ciki da gumurzun nakuda. Su suka taru suka hana mata nutsuwar da Abdulazeez ke so ta yi. Ya fahimci halin da ta ke ciki, kuzarinsa ya ragu kashi talatin cikin dari, ya rungume ta sosai cikin rawar murya ya ce

 I will not to anything without your consent (bazan yi komai ba sai da amincewarki), ko da hakan na nufin ni zan cutu, sai dai na yi alkawarin zan taya ki da hidimarsu ko kullum za ki haifo min dozen.Ina da yadda zan kula da ku Hafsah, da zan iya zan cire miki ciwon nakudarsu, amma da ba zan iya ba zan yi wanda zan iya. Its a promise.

Hawayen tausayi da kauna suka kwaranyo mata. Ba ta yi magana ba, amma martanin da ya soma karba daga gare ta shi ya tabbatar da amincewarta. Ita din mai kunya ce ya sani, amma yau ta ajiye ta a gefe. Burinta daya ta faranta amsa da iyakar iyawarta ko da hakan na nufin duk bayan wata daya za ta haihu. Idan za ta haife kasuwar Kwari duk shekara in dai da Abdulazeez ne, tana maraba da ita…….!!!

A wannan ranar, sai ya zamanto kamar dukkaninsu are new to the system….. Kamar koyar da juna suke yi… Kamar kuma directing juna suke yi….. Kamar kuma wani abu makamancin hakan bai taba faruwa a tsakaninsu ba!!! Kowannensu tsoro yake ji, tsoron kada ya bude ido ya tarar mafarki yake yi, mafarkin cewa haka za su rayu da juna har karewar numfashinsu. 

MURFI

BAYAN SHEKARU GOMA

Abubuwa da yawa sun faru a wadannan shekarun guda goma masu kama da kiftawar ido. Auren Ismael da masoyiyarsa Waseela Faruk, Usman da Halima diyar Anty Luba, Arch. Haleem Dakata da amaryarsa Saima diyar Anty Mariya. Wadannan dukkaninsu manyan maaikata ne yanzu, Haleem na aiki da kamfanin gine-gine na Julius Berger, Ismael software Engineer ne da kamfanin Microsoft Corproration reshen birnin Honk-Kong din China, Usman maaikacin kamfanin oil and gass na Oriental Energy mallakin Muhammed Indimi. Yayin da mai gayya Yayan kowa Uban Abubakar ke ta taka matakai na nasara kala-kala a aikinsa (as a Civil Lawyer) mai tsayawa alummar kasarshi Nigeria masu rangwamen gata da aka zalinta ko aka dannewa hakki dadukkan karfinsa,ilmin sa har ma da aljihunsa,da jerin hulunan nan masu wuyar samu guda uku; LLB (Civil Law), BL, L.LM (Civil Law), tare kuma da jerin yayansa guda biyar, maza hudu mace daya; Abubakar, Umar, Usman da Aliyu, ga kuma auta Habibatu (Hibbah). Bayan kwashe shekaru goma yana (practicing Bar), yayi applying a (Judicial Service Commission),bada jimawa ba aka yi shortlisting dinsa cikin masu yin jarrabawar (conversion from Bar to Bench)yayi interview. Kamar koyaushe Abdulazeez mai nasara ne balle akan aikinsa da wannan enthusiasm din nasa na komawa Mai shariah daga Bar.

A wannan lokacin Hafsat-Suhaanah Allah ya cika buri; B.A ED, M.ED, PhD in Geography.Dr. Hafsat Hamza Atiku kenan uwargida ga Justice Abdulazeez Hamza Atiku. Ta fito da kwalin doctorate ne a wannan Shekarar. The tsruggle contineous as an educational researcher……. Yau an kawo hula ta karshe komai ya zama tarihi. Bayan kammala Doctoral dinta da shekara daya a yanzu haka shirin bude makarantarta ta kanta iyayenta da mijinta Justice Dakata ke yi wadda za a bude a garin Jimeta/Yola. Makarantar sakandire ce mai hade da Primary da Nursery. 

Ba da jimawa ba aka yi luncheon din bude makarantar mai suna HABIBAH BABBAH MODEL SCHOOL. Wannan makaranta private school ce, amma ba mai tsadar da mai karamin karfi bazai iya biya ba. Yan uwanta maza uku Modibbo, Imaamu, Abdurrahman da kawunta Nuru autan Daada wanda dama tsohon malamin makaranta ne su suka kama mata komai. Don haka yanzu tana yawan zuwa mahaifarta Jimeta a matsayinta na principal. Abbanta wanda yanzu ya yi ritaya shi ya maida ita ta maye kujerarsa a FUTY  (as a part-time lecturer). Duka yayanta maza suna hannun Mammah, Hibbah ce kawai tare da ita, wadda ta zame mata cingam a duk inda ta shiga, ita ma don ba ta isa shiga makaranta ba ne Mammah ta kyale mata. A cewarta mutanen da ba sa wuni a gida ba za ta bar musu yaya a hannun su ba da ranta da lafiyarta tunda ita bata aikin. Ko basa wannan jigilar ayyukan nasu butin Mammah ne rike dukkan jikokin ta. Abdulaziz din ne dama mai kulaficinsu ban da Hafsat wadda ke jin ko yaya dari ta haifa Mammah ta ce ita za ta rike a shirye ta ke da yin hakan wholeheartedly, sai dai shakuwar Abubakar (Khalipha) da mahaifinsa wata irin shakuwa ce ta daban data sauran yayan da kowa ya san Abdulazeez ba zai iya barwa Mammah shi gabadaya ba. Duk Jumaah in ya taso aiki yake sa wa a dauko shi tunda a weekend suna gida shi da Addah sai lahadi da dare ake maida shi Asokoro.

Sun dade da tashi daga gidansu na Sun-City, Abdulazeez ya yi gini da kansa a Apo. A cewarsa gidan Sun City mallakin Abubakar Sadik Khalipha ne.

Amintarsa da abokan aikinsa, Ahmad, ESQ Abdallah da Taufeeq sai abin da ya yi gaba, wanda zumuncin ya shafi matansu da yayansu, Sagir kuwa wannan mai dungurugum ne matsayinsa na kawun Hafsat. Duk da yanzu kowannensu ya bar Abuja da tarin ci gaba; Ahmad na Lagos, Taufeeq na Court of Appeal ta jihar Oyo, Abdallah na garinsa na haihuwa Taraba da kotun jihar (Magistrate Court) matsayin Judge, surukinsa Sagir kuwa an maida shi Porthercourt.

Hafsat ba ta yada Rabia Sada ba, bayan sun gama degree a Nile aka yi wa mijinta Sadik sauyin wajen aiki suka koma Kaduna. Har kaduna Abdulazeez ya kai Hafsat wajen Mami saboda ta gaya masa irin taimakon da ta ke yi mata in ta kara hutu, haka da laulayin cikin Khalipha Mami ta taimaka mata sosai. Hafsat ta gane cewa, kawaye da ta ke gudu ba duka ne bara gurbi ba a kan Rabia Sada, tsakani da Allah Mami ta ke kaunarta, tuni ta sallama suke zumunci ta waya har gobe. Mammah ma na bayan wannan kawancen, don haka ko hanya ce ta bi da su Kaduna in za su Kano sai sun tsaya wajen Mami.

Mammah ta samu surukarta Wasila matar Ismael ba yadda ta ke tsammani ba, ta gane ba duka yayan masu kudi ba ne marasa tarbiyyah. Ba duka girman Abuja ba ne marassa kunya ba. Ya danganta da tarbiyyyar cikin gida da yammatan suka samu. Wasila dai a Abuja aka haife ta, ta kuma girma a can ta yi karatu a kasar Russia amma yadda ta ke bin Ismael sau da kafa ta ke karrama ta kamar sauran ya sa Mammah ta yi saranda. Ba a gane mutum mai tarbiyya by social status, abin a zuciya ne. Mutum na gari Allah daban yake halittar sa. Duka surukan nata ba ta da matsala da su, don Saima da Halima ita ta karasa rikonsu a gidan mazajen a hannunta suka bude ido da rayuwar aure. Ko gobe suka hadu da Ismael sai sun yi ta sun kasa jituwa har gobe. Wasan kanin miji mai shegen zafi (sunan wani littafin TAKORI).

A wata sharia da Abdulazeez ke jagoranta a Federal High Court Abuja, rannan cikin lauyoyin shariar ya ci karo da Muazatu Rufai matsayin lawyer mai kare wanda ake tuhuma. Ya gane ta, ita ba ta gane shi ba saboda canzawar da kowannensu ya kara yi. Dadin dadawa ba ta yi tsammanin ganinsa a wannan matakin ba. Bayan gama shariar ita ta yi winning. Kamar yadda yake mai sharia shi ke fara tashi bayan kammala shariah. Muazatu tana tattare takardunta lokacin da Justice ya mike zai wuce ta hanyar da ya shigo, karaf! Suka hada ido. Murmushi ya yi ya dan dakata ya ce da ita, Congratulations Barrister Muazatu, I know you can make it tunda na hangoki.

Itama murmushin ta yi cikin kore shakku da dimbin mamaki.Thank you My Lord. I  Absolutely believed you will come to Bench someday, but I never ever thought it will be so soon like that. A gaida SUHAANAH.

Jinjina kai ya yi, tare da yi mata godiya da fatan alkhairi. Ta bi shi da kallo har ya kulewa ganinta, wani abu na dan taba zuciyarta mai kama da tasowar tsohon miki, amma da ta tuna Barrister Muntada da irin rayuwar farin cikin da ta ke samu tare da shi, ga albarkar zuria har shidda, a take ta daga hannu ta godewa Allah.

Ta ce a ranta, Ba duka abin da muke so a rayuwa muke samu ba, in mun yi tawakkali mun bi iyayenmu, sai mu zauna lafiya.

******

Lokacin da zaayi bikin baiwa Abdulazeez (Chief of the Justices of the Federal High Court) ma sun sake haduwa, wannan karon Hafsat da yayanta suna tare da shi itama tareda mijinta Muntada da nata yayan. Kallo daya Hafsat tayi mata ta gane ta, ko don hotonta da ya shekare mata a falo. Ko taji wani abu a ranta yau kam tafi karfin kishin ta. Duba da cewa Muazatun bata nuna komai ba sai kauna da kulawa ga yayanta. Itama sai ta ja nata a jiki har sukayi hotuna tare.Sun zo ne musamman tun daga jihar Lagos don halartar wann kasaitaccen bikin karin girma da kasar Nigeria ta baiwa Justice Abdulazeez Dakata  sakamakon jajircewa da sadaukar da kai irin nasa na tsahon shekaru ga kotunan Nigeria, ba kuma karkashin gayyatar kowa ba sai kasancewar su karkashin umbrella guda na aiki da proffession. Justice ABDULAZEEZ HAMZAH ATIKU da HAFSAT-SUHAANAH nima ina fatan alkhairi. 

              

Masha Allah laquwwata illa billah.

Nan na kawo karshen littafin AUREN KWANGILA. Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah Ya yafe mini. Darussan alkhairin da ke ciki Allah Ubangiji ya hada mu cikin ladan ni da ku baki daya.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE