Ayshat Ɗansabo lemuNAILAH CHAPTER 4 BY
Anwar anashi ɓangaren koda ya isa part ɗinsa,kansa akulle yake ya kasa gane wani irin ƙaddarane ke shirin afka masa,take maganganun abokinsa Doctor Khaleel ke dawo masa shi ɗinma abu ɗaya yake sanar dashi shine ya amince da xaɓin iyayensa ya haɗesu duk su biyun ya aure kawai.
Face ɗin Nailah ne ke haskawa azuciyansa baisan taya xai iya rayuwan aure da yarinyan da yake jin tsananta babu gaira babu dalili ba,baisan taya xai iya haɗa jikinsa da wacce baisan cikakken asalinta ba,sai dai xuwa yanxu ya tabbatar bashida zaɓin daya wuce amincewa auren Nailah itada Hudah,tunda har iyayensa suka haɗe masa kai to tabbas cikan burinsa na samun Hudah yana nufin amincewa auren Nailah ne,da ƙyar ya iya miƙewa ya nufi toilet ya sakarwa kansa shower,ya jima sanyin ruwan na ratsashi kafin ya fito ɗaure da towel,ya yafo wani ƙarami akansa yana goge sumansa daya jiƙe da ruwa,koda ya gama kintsawa ya kasa neman Hudah kaman yadda yace mata,saima kashe wayansa da yayi baki ɗaya ya kwanta badon yana jin bacci xai iya ɗaukansa nan kusaba.
Da ciwan kai sosai Nailah ta farka da asuba,bayan ta gabatar da sallah tayi su azkhar da karatun qur’ani kaman yadda tasaba,saita koma gado saboda sunday ne babu aiki bare suyi shirin zuwa local govt inda nan suke service ɗinsu,bata farka ba sai wajen 10am wanka ta farayi da brush ta shirya cikin simple straight gown,daya amshi jikinta face ɗinta powder kawai ta murxa sai kwalli ta fice,side ɗin Dady ta nufa kai tsaye don miƙa gaisuwa gareshi shida Momy don tasan tana can.
Da sallama ta shiga falon na Dady cikin sa’a yana zaune da alamu bai jima can da gama yin breakfast ba,domin ko kayan dayai anfani dasu nanan ba’a riga an kawar ba,ta durkusa ta kwashi gaisuwa ya amsa cikeda fara’a yana mata inkiya da hannu akan ta zauna sosai,zamanta yayi dai-dai da fitowan Momy daga bedroom ɗinsa ,Nailah ta gaida Mon ɗin cikeda ladabi,kusada Dady Momy ta zauna tana faɗin.
“Nailah tashin kenan keda baki jimawa a baccin safe gashi har 10 ya wuce.”
Nailah tayi murmushi tana faɗin.”Wallahi Momy da ciwan kai natashi yau shiyasa amma naji sauƙi.”
“Allah ya sauƙe maza tashi kije ki nemi abinda zakici saiki sha magani.”
Cewan Momy kenan Dadyma sannu yaiwa Nailah kafin ya dubi Momy yana faɗin.” Momyn yara ai nine natsaida ƴar taki magana zamuyi.”
“Toh Allah sa dai balaifi ɗiyan arzikin tawa tayi ba.”
Cewan Momy tana sakin dariya ganin yadda Nailah da Dady suka saki dariya jin yadda Mom ɗin tayi maganan.
“Ɗiyata saura wata nawa ya rage muku kugama services ɗinku?”
Dady ya jefawa Nailah tambayan kansa tsaye,Nailah ta bashi amsa da cewa.”Saura 2 month ne ya rage Dady.”
“To masha Allah Nailah jeki idan kun gama ki kirawo min ƴan uwanki ku sameni anan falon xanyi magana daku.”
Dady ya furta yana maida dubansa kan Momy dake sakin murmushi ba tareda ta tofa uffan ba,har Nailah ta amsa tana me tashi ta fice duk suka rakata da ido kowanne da abinda xuciyansa ke saƙawa akan Nailan.
Koda ta fito direct hanyan kitchen ta nufa,tunda ta doshi ƙofan shiga take jiyo dariyan su Nafeesa da Amal,da sallama ta shiga duk suka jiyo suna duban Nailah tareda amsa sallamanta,ta isa garesu tana faɗin.” Kuce kuna nan kuma sai yanzu zaku karya kenan,Nafees shine koki tadani da kika tashi ko. “
Tayi maganan da ƴar shagwaɓa kaman yadda take taɓawa some times,Amal dake juya wainar egg cikin pan ta dubi Nailah tana faɗin.” Yau kuma shalelen Momy shagwaɓa akeji da sanyin safiyar nan.”
Suka saki dariya Nailah na faɗin.” Kai ya Amal bafa wani shagwaɓa,yanzu dai me kuke shirya mana ne Dady yace da mun kammala mu sameshi akwai maganan da zaiyi damu.”
“To Allah sa dai muji alkhairy kinga chips kawai na soya,sai Nafeesa data dafa indomie.”
Baki Nailah ta turo tana faɗin.”Nidai chips ɗin zanci ya Amal Allah sa ya ishemu wanda kika soya.”