BAƘAR AYAH BOOK 1 CHAPTER 2 BY SADI-SAKHNA

BAƘAR AYAH BOOK 1 CHAPTER 2 BY SADI-SAKHNA

 

________________”Ina jinka ZULUNGUM ya kake ganin za’ayi toh yanxun,nidai duk yanda zakayi kayi,kawai so nake ayi mata kisan wulaƙanci,saita ƙwammaci bata shigo rayuwar mijina ba.
Duk wata mace data rabeshi banda maƙiyiya sai ita,zan iya komai kuma domin rabashi da ita.
JABEER JAAN(JJ) nawane ni kaɗai a faɗin duniyar nan,ƙaddarar sa ce ya zauna dani ni kaɗai,duk da kuwa bana haihuwa,yanda bazanga ƙwaina ba a duniya,shima bazai taba ganin nasa ba har ya bar duniyar nan, saidai idan nina haifa shine zai gani,amma idan baniba babu wata ƴa kuma.wannan alƙawarina ne ni LUBNAH ƴar URWATU”
“Shikenan yanda kika ce aikin bazai gagara ba,saidai kafinnan zaki ajiye nairah Miliyan ɗaya da rabi kafin a fara aikin,dan zubar da cikin a yanzu zayyi wuyah,saidai a bari idan yakai matakin haihuwa sai a hanashi fitowa,koya kika ce toh”
“Hmmm idan hakan zaifi ayi hakan,amma ni da son samuna ne kafin na koma gida na sameta anyi filla filla da naman jikinta,babu wani abu dazai nuna itace,vazaka gane bane boka,natsani na buɗi idona na ganta a cikin gidannan,da wannan tsinannan cikin tana turashi,nafiso a kasheta irinnna waccar matar,kafin ma takai ga wani samun ciki”
“Kai……!! Tsiyata dake lubna gaggawa,inkika bi a sannu,kuma kina bawa Aljanu jinin da suke buƙata,babu abinda bazaki samu ba,har matakin zaman ki na CEO ma duk zai cika nan da zuwa gaba.
Idan aka kawar da itama rufe idonsa za’a yi daga kan duk wata ƴa mace da take doron duniyar nan,ke ɗai zai dunga kallo a duk inda idonsa ya sauƙa”
“Shikenan nidai duk yanda zakayi ma kayi”
“Amma fah akwai ƙa’idoji da dole saikin kiyayesu,na farko;dolene kijata a jiki,ta yanda zata yarda dake har ki dunga sanin ya take ciki,na biyu kuma akwai wata ƴar tsana da zan baki,ki tabbatar kin saka jininta a jiki,lokacin da tazo haihuwa ki dunga karya jikin tsanar,zai zamo tamkar jikinta kike karyawa,daga lokacin da kika karyata tayi laushi,ita kuma sannan zata fuskanci tata mutuwar tareda abin cikinta”
“Naji wannan bayani naka,za’ayi yanda kace ba matsala,lokacin dazata dunga ihu sannan zuciyata zata wanke da zama min da tayi a cikin gidana.
Nagode gaskiya yau da gagarumin abinda ka bani,zan tafi,dan yau zai dawo daga taron daya tafi England”
Tashi lubna tayi daga ƙasan da take zaune tareda kaɗe zaninta tana murmushin samun nasara.
Hanyar fita daga wajen ta nufah mai matuƙar bada tsoro,amma hakan ko a jikinta,dan akan kishin mijinta babu abinda take ganin zai iya saka mata zani yarabata dashi.
Saida ta ɗanyi tafiya mai nisa kafin tazo wajen inda ta ajiye motarta,Wai hausawa suna cewa SA KAI YAFI BAUTA CIWO.
Saida tayi tafiya mai nisa kafin ta shigo garin abuja,direct JAAN ESTATE ta wuce da baƙar motar ta.
Nufar babban get ɗin tayi cikeda ƙasaita da izzah,wanda hakan a jininta yake.
Titin dazai kaita apartment ɗinsu tabi,wanda take ɗan ciki kaɗan da bakin babban get ɗin.
Saida ta wuce nasu Hajiya Zeena kafin ta iso nasu part,shima da get ɗinsa mai zaman kansa,yana ɗauke da part biyu,amma a haɗe suke ta tsakiyah,inda side ɗin Jabeer yake.
Ba hanyar nata part ɗin ta nufah ba,da alama wajen Hafsa zataje.
Fuskarta a murtuƙe take saboda tsanar baiwar Allahn,amma haka ta danne saboda zancen boka ta saki fuskarta kaɗan.
Da sallama ta shiga tangamemen falon,mai adon Green da purple,yayinda nata kuma yake fari da ja.
Haushi ne yakamata ganin kayan Alatun da mijinnata yasaka mata,tafison komai yazama ita kaɗai take dashi bada wata matar ba.
“Assalam ƙanwata kina cikine””
Hafsace ta fito daga ɗaki da doguwar riga a jikinta marar nauyi tana tura zungureren cikinnata.
Kallon Lubna take da mamaki,dam yanda taga murmushi akan fuskarta abune da bata taba gani ba a faɗin rayuwarta,a ranta addu’oi take jerowa duk wacce tazo bakinta.
“Lafiya ƙalau Anty lubna,sannu da dawowa ya hanya”
“Hanya ƙalau,har zan shige nace bari nazo naga ko lafiya kike,nasan babu kowa a gidan saike kaɗai,ga Honey ma bayanan,an barki ke kaɗai ga ciki”
Ƴar dariyah Hafsa tayi,har sannan bata share tantamar inaga antynnata ba lafiyar ta ƙalau ba,dan in ana neman rashin imanin matar to a tambayeta”
“Ayyah ba komai anty,akwai Alawiyyah ai ƙanwata,tana taimaka min da abubuwa,Hajiya ma kuma tana shigowa akai akai”
Mintsine bakin lubna tayi tareda cewa “munafukar tsohuwa” a ranta.
“Ohh kinga shaɗaf na manta da hakan,dama saidai ta hakan ai,akwai abincine ki bani,yanzu na fawo gashi banci komai ba”
“Ah….ehhh barina duba kitchen ɗin,ki zauna akan kujera naje na dawo”
Murmushin yaƙe Hafsan take dan kwata kwata abin bayyi mata a gaske yake faruwa ba.
Bayan tabar wajen tashi lubna tayi tana kalle kallle a cikin falon,yaune zuwanta na farkon wajen da niyyar arziƙi,saidai tazo tayi tijara ko kuma kashedi,dan haka har tazo ta tafi bata gane mai yake wakana a wajen sai yanzu.
Tana cikin kalle kallenne Hafsa ta dawo ɗauke ta plate a hannunta,ta rufe da wani a sama.
Karba lubna tayi tana murmushi tareda cewa.
“Yawwa nagode ƙwanta sosai,amma zan iya tafiya dashi saina kawomiki plate ɗin?”
Ɗaga mata kai Hafsa tayi cikin ladabi.
“Lahhh ki tafi dashi Anty babu komai”
Daga haka lubna tajuya ta fita da plate ɗin abincin a hannunta.
Tana shiga part ɗinta ta buɗe kwandon shara ta zubashi a ciki,tareda jefa plate a ɗin a wajen wanke wanke tana kaɗe hannu kaman ta dauki kashi.
Ɗaya daga cikin masu aikinta ta ƙwalawa ƙira.
“Bishirahhhhh!!!!!”
“Naaama ranki ya daɗe”
Ta karisa magana tana zurowa da gudu.
“Gyaran gidannan bayyimin ba kwata kwata,ku tabbar kun sake gyarawa kafin magriba”
Bayan ta wuce wacce aka ƙira da bishira ta samu waje ta zauna,tareda sakin wata ajiyar zuciya,banda neman na halali mai zai sakasu aiki a wajen wannan dujal ɗin.
Bayan ta fito daga wankane taji ƙarar motoci suna shigowa cikin apartment ɗinnasu.
Shafe shafe tafarayi,dan tasan mai gidanne yadawo daga taron shekara da sukeyi da sauran companies..
Har lubna ta gama shiryawa ana ta ƙiran Sallah amma bata ga Jabeer ya shigo ba,abinne yafara bata haushi,dan tasan yanzu haka yana sashen Hafsa,saboda ita tana da ciki ita kuma batada shi.
A bangaren J.J kuwa yana fitowa daga motar muhimmin ƙira ya shigo wayarsa,ana nemansa da gaggawa,dan haka a take ya ɗau ƙaramar motarsa personal ya koma.
Bashi ya dawo gidanba sai bayan isha.
Sallama yafara a bakin falon lubnan,amma shuru bata kulashi ba har ya shigo cikin ɗakinta.
A zaune take akan kujerar dressing mirror tana danna waya,tacika tayi famm kaman zata fashe.
Mamaki abin yabaww J.J,dan yasan babu abinda yayi mata kafin tafiyarsa,hasalima sanda ya fita daga gidan bata nan ta tafi gidan ƙawarta batareda yasani ba,shine ma yakamata yayi fushi,amma kuma wai itace dayin fushin.
“Lubna inata Yin sallama kinaji kaman ba musulma ba?”
“Hmmm banyi niyyar amsawa bane,dan tsabar rashin adalci wato,tun ɗazu kashigo gidan amma kana wajenta,ita gamai haihuwa koh,sai nayi magana tsofi suce banida haƙuri”
“Ke suwaye tsofin,iyayena koh? Yayi miki kyau,wai yaushe zaki sanja haline kam,dawowa ta fah kenan,yanxune ma nashigo gida,hmmm ALLAH ya shiryeki,banida lokacinki tunda lafiyarki kalau fine,na sauƙe miki haƙƙinki,saida safe”
Yana gama faɗin haka ya bar sashennasa cikin bacin rai,tasashi kuwa sarai,idan yayi zuciya da ita ta ƙwammaci ya mareta daya tura mata aniyarta,dan sai yayi sati bai kalli inda take ba.
Tsuka taja duk da taji tsoron fushinnasa,dan Allah ne kaɗai yasan irin yanda take so tajishi a tareda ita,dan ita kanta shida ce shiɗin jarumin namijine a ta kowacce fuska,badai mace ta rainashi ba,saidai ma ta gaza.
Dama ƙarin haushinnata kenan,ba a sashenta yake ba,shiyasa take wannan kumbure kumburen.
Hafsa tana kan sallayah ya isa ɗakin cikin fushi.
Sallama tayi tareda sake masa murmushi lokacin da suka haɗa ido.
Shima murmushin yayi mata,duk wani bacin rai da lubna tayi masa sai yaji yana sauƙa.
“Ka dawo lafiya ya hanya?”
“Alhamdulillah,ya zaman gidan da lafiyarku”
“Muna lafiya kalau,barina kawo maka abinci”
“Ahah ki barshi,barina yi wanka tukunna”
Tashi yayi ya rage kayan jikinsa tareda shiga banɗaki.
Kafin ya fito ta fitar masa ƙananna kaya marasa nauyi.
Da safe suna cikin yin break fast lubna ta shigo sashen riƙeda plate ɗin jiya a hannunta.
Tasha wani matsatstsen lace kalar zinare da baƙi riga da skirt,ba laifi tanada yar ƙiba,amma kuma bayada kunkumi sosai mai cika ido,sannan ba fara bace,saidai sanadiyyar mayuka na zamani,tayi fari tass kaman fatalwa.
Wani shu’umin murmushi tasake mai,dauke da ma’anoni kala kala.
Hafsa ce ta gaishe da ita tareda yi mata bismillar abinci,Jabeer kam ko kallon ta bayyi ba,sauri yake yagama cin abinci yafita wajen aiki.
“Ayya wai break fast,naga kam kuna cikin nishadi sosai,plate ɗin jiya na dawo miki dashi”
Ta faɗa tamkar mutuniyar kirki. Jan kujera tayi babu kunya a kusada Jabeer ta zauna tareda yimasa kallo ƙasa ƙasa.
Hafsa tana kallonsu amma ta kawar da kanta tareda zubawa Lubna itama abincin.
Bayan kamar minti biyune Jabeer ya ɗago ya zabgawa lubna harara,saboda yanda take ɗaga ƙafar wandonsa da kafarta ta ƙarƙashin tebur ɗin.
Har ya buɗe baki zayyi magana ganin bata daina ba ya fasa,saboda yanda Hafsa ta ajiye cokalin hannunta tana rike cikinta.
Tun kafin Jabeer ya taimaka mata,lubna ta riƙeta tareda yimasa magana ya ɗakko key ɗin motarsa.
Cikin sauri suka nufi asibitin da itah da gaggawa,sai bayan sun isa an shiga da ita ɗakine tukunna suka samu damar ƙiran Hajiyah zeenah,wanda cikin ƙankanin lokaci ta tashi hankalinta,sai gata itada Laylah,matar baffansu ABDULLAHI. Sayyada-tateen kam ba’a sanar mata ba,saboda kowa yasan halinta da surutu da ɗaga hankali.
Safa da marwa suka fara a bakin labor room ɗin,itadai luban kallonsu kawai take,duk sanda suka nuna damuwa ƙara bata haushi suke,musamman yanda jabeer yafasa tafiya ko ina,kowa addu’ar ta sauƙa lafiya yake,ita babu wanda ya kula da ita.
Ƙara wayarta tayi a cikin jaka,wanda hakan yasa ta nufi wani dan waje gefe da inda suke tsaye.
“Hello Hajiya na ɗebi miki jinin,yanzu zan fito daga ward ɗin,sai ki bini zuwa nurse section na baki”
“Okay babu matsala”
Tana kashe wayar tayi murmushin mugunta tareda kallon inda hafsan take kwance,fitowa nurse ɗin tayi kanta a sunkuye ɗauke da test tube na jini ta nufi sashen su,babu wanda ya kulada ita,domin kowa yayi zaton abu zata kai wani wajen.
Lubna tana ganin hakan ta bi bayan nurse din,saida sukaje inda babu kowa kafin ta tsayah,
“Yawwa gaskiya kinyi ƙoƙari sosai,ai dama yanda kika faɗa cewar kin bata maganin naƙuda tasha da safe,shiyasa na shiga sashen domin na biyosu asibitin.
Aikinki ya cika,na tura miki miliyan ɗaya acct ɗin yanda mukayi nagode ni barina na tafi”
Lubna ta faɗa bayan ta karbi jinin tasaka a jaka.
“Kwanan ki ya ƙare Hafsatuwa kema kaman ɗayar,nariga na faɗamuku,duk wacce ta rabeshi to kabarinta ta tona,koda kuwa wacece”…….!!!!!

 

 

DOMIN CI GABA DUBA👇
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE