BAƘIN DARE CHAPTER 5

BAƘIN DARE 
CHAPTER 5
Ogansu Sai daya gama sheka ayarsa da linder ya fito ya shirya a cikin manyan kaya kai ahaka idan ka ganshi zaka dauka mulumin arzuki ne Dan har dasu hula yasa 
Yana fitowa daga dakin su Lion suka mimmike har da Akram da kansa ke balain ciwo Hannunsa a sakale yake a kugun Linder ya sakar musu wani jairin murmushi yana 
“Killer lion scorpion black Akrarn NI zan tafi Port Harcourt wajen iyalaina zan dan huta haka kamar na 2weeks kafin mu kuma fita wani operation din inda nake tunanin wanan karon kano muka nufa dan akwai wani Alhaji Buba mai gwala gwalai yana da bala,in kudi ina nan ina monitoring dinsa akwai wata servant dinsu Habiba ita nakeso na jawo jikina in sakar mata kudi ta bani details dinsu sosai da yanayin gidan immediately ina gama samun Duk wani information akansu zan kiraku Ku fara shirye shiryen daya kama ” “Sanan kamin lokacin idan kuna da wani uzuri zaku iya zuwa kuyi amma kwana uku kawai na Baku dukanku Ku dawo do I make my self clear”? Da sauri dukansu suka gyada Kansu suna yes boss 
Daga haka ogansu yasa kai ya fice daga palon suna take mishi baya s yana rike da kugun Linder dan shi zaiyi dropping dinta a hanya Sai da  yasaka mishi brief case din kudinshi abayan boot kafin yaja da baya Ogansu kuwa yaja katon jeep din yabar harabar gidan Ciki suka koma gaba daya kowanensu yafara shirin tafia uzurinsa akwai masu zuwa su duba iyayensu irin su Lion da sukayi wa iyayensu karya akan aiki suke a Abuja akwai irinsu black dake da iyali da suma suka shirgawa iyalinsu karya akan suna aiki ne a abuja . 
Akram ya matsu ya shirya gabadaya dan ji yake kamar akan kaya yake Kallonsu Lion yayi fuskarsa dauke da murrnushi adai dai lokacin da yake sanya jakarsa a kafadarsa yace ” toni kunga tafiyata zanje naga parent dina da sublings dina zan kai musu dan abunda muka samu Insha Allahu bazan wuce 3days da boss ya dibar mana ba’ Dukansu murmushi sukayi dan haka kawai Allah ya hada jininsu da Akram shiyasa ma koda an fara operabon dashi koda baiyi komai ba basa damuwa Killer ne yace ” same here muma zamuje muga namu iyayen akwai kanwata ma da za’ayi bikinta nasan suna nan suna zuba ido dan dani suka dogara Nima zan kai musu abunda ya 
samu’ Murmushi kawai Akram yayi a zuciyarsa yana tausayin halin da suka jefa Kansu sabida talauci yana tausayinsu ranar da asirinsu zai tonu asaka musu ankwa a hannu all they are doing is for d sake of their family Duk rashin aikin yine ya janyo musu fadawa halaka ciki kuwa har da rasa imaninsu tunda basu dauki kisan kai abakin komai ba 
Daya bayan daya ya bisu ya rungume yana ce musu sai sun dawo nan da kwana uku daga haka yasaka kai ya fice daga gidan dayake ji tamkar prison bai zame ko ina ba sai head Quarter dinsu Agajiye ya karasa offlce dinshi ya dafe kansa dake Sara mishi har yanzu yanajin ihunsu Samha a kunensa ko yaya ya runtse idonsa sai ya hango abubuwan da suka faru a Daren jiya 
Haka kawai yaji ya tsani kansa yana tuhumar kansa shima da laifin shi awajen kisan Hajiya Nafeesa sai yanzu yake mugun daya sani da ya dauki mataki tun a lokacin daya sani ya harbesu duka dayaga yanda Hajiya Nafeesa ke fadi tashi akan ta kare martabar ‘ya’yanta idan kuma ya tuna kwanan tane ya kare sai ya rage ganin laifinsa ahaka ya zauna wajen minti ashirin kafin ya iya mikewa ya Shiga bandakin dake cikin office din ya daura alwala yazo yayi sallar Azahar yana idarwa ba tare da bata lokaci ba ya nufi office din ogansu 
Bayan sun gaisa kamar yanda suka saba da tambaye tambaye ogansu ya tambayeshi abubuwa daya kara samo musu akan Alhaji Bala Akram jiki Asanyaye ya mika masa ‘yar karamar Camera dake hannunsa ogansa kuwa ya karba a dokance Cikin minti biyar ya hada camerar da system din dake gaban table dinsa 
Tun daga yanda suka shirya da zasu tafu operation har zuwa yanda suka daure mai gadin gidansu Hajiya Nafeesa daya bude musu kofa tagumi ogansu yayi yana kallon system din dake gabanshi jikinsa sai rawa yake yabi ya jike da gumi duk da sanyin Ac dake ratsa office din Wani irin kadawa idonsa yayi ya mike jikinsa na wani irin kyarma ‘innallllahi wa inna ilalhi rajiun’ kawai yake maimaitawa ahankali ya kalli Akram daya dafe kansa da hannu biyu kwalla na zuba a idonsa dan wani irin zafi yakeji a zuciyarsa da yakejiyo sautin kukan Hajiya Nafeesa dasu Saiam magana ya farayi yana 
“Akram meyesa baka ceci rayuwar matan nan ba meyesa bakayi wani Abu dan kar Alhaji Bala ya harbeta ba tunda nake ganin abubuwa ban taba ganin abun tausayi irin wanan ba matan nan tabani tausayi fiye da tunanin mai tunani Alhaji Bala ya Dade yana abubuwa amma this time around his cup is full bama bukatar wani prove k0 evidence wayanda muke dasu kawai sun ishemu enough is enough Iokaci yayi daya kamata mutane su San waye Alhaji Bala lokaci yayi daya kamaka ace mutane suSan irin sana’ar da yake yi” Rawa jikin shi keyi sosai Idonsa jajawur Akram kuwa  magana ya kasa yi dan shi kadai yasan halin da yake Ciki 
Ni kam waye wanan Alhaji Balan ne toh bari muji waye shi 
Alhaji Bala haifaffen dan jigawa a kauyen kafin Hausa su hudu iyayensu suka Haifa duka maza sun taso ne a cikin tsananin talauci dakyar suke cin abinci sau biyu arana tunda Bala ya taso ya taso da masifar San kudi dan idan ya zauna da mahaifiyarsa Saude haka zai ta bata labarin irin kudin da zaiyi Idan ya girma da abubuwan da zai mata da kanensa sabida mahaifinsu ya Dade da rasuwa ahaka Alhaji Bala ya taso da mugun San kudi duk da mahaifiyarsu Saude na matukar kokari dan taga ta sama musu ingantaciyar rayuwa 
Alhaji Bala na da shekara goma sha biyu ya fara buga buga shine noma shine aikin gini sharar kwalta duk wani Abu daya San zai shigo masa da kudi yinshi kawai yake ahaka rayuwa tayi ta tafiya dakyar ya gama primary sch a kauyensu inda daga nan ya tara karatun ya watsar ya cigaba da Neman kudi yana kula da mahaifiyarsa da kannensa uku Saidu Abubakarda zaldu ahaka Alhaji Bala ya ringa Tara kudin da yake buga buga inda ya Tara wajen dubu biyar a lokacin kudine masu daraja da yawa shawara yayi da mahaifiyarsa Saude data tsufa tukuf wanda a zahiri ba Bufan tayi ba tsabagen talauci ya tsufar da ita Shawara ta bashi akan yaje birni ya saro shaddodi da atamfuna masu kyau na manya da yara yanda basai aringa wahalar zuwa birni siya ba aikuwa take yabi shawararta dan babu inda ake siyarwa a kauyen Aikuwa cikin sa’a ya saro kayan dan kayan basa sati ake siyesu har da masu kawo mishi kudi ya hada masu lefe awanan lokacin Watarana yaje birni zai sari kayan an gama loda mishi kayan a mota kenan zai hau yaji ana ta mishi horn abayansa Juyawa yayi yaga wata hadaddiyar mota ya hadiyi wani irin yawu dan sai ka isa zaka iya siyan motar kafin ya gama karewa motar kallo aka bude kofar motar aka fito buhun hannunsa ya wurgar ya tafi da gudu ya mngume abokinsa Ukasha! da sukayi primary sch tare Sai da ukasha ya kalleshi daga sama har kasa kafin yace ya yaganshi haka 
shi dai Alhaji Bala baki a sake kawai yake bin ukashat da kallo da kayan jikinsa da motarsa Horn mai motar ya ringa yiwa Alhaji Bala dan yazo su tafi Ukashat kuwa yace yaje ya hau zai biyosu abaya Aikuwa haka akayi har kofar gidansu Alhaji Bala Ukashat ya bisu sai da aka gama sauke kayan gabadaya Sanan Alhaji Bala ya nufi wajen ukashat dake hakimce a cikin motarsa yana yatsina fuska kamar Wanda yaga kashi daya barin Alhaji Bala ya bude ya shiga ya zubawa ukasha ido yana mamakin yanda akayi yayi kudi acikin shekara takwas kawai da sukayi da rabuwa abunda burinsa kenan arayuwa 
Agurguje Ukasha ya gayawa Alhaji Bala silar samun kudinsa ta hanyar arm robery ne inda wani ya mishi hanya shima anan shima yace idan Alhaji Bala yana so yayi bankwana da talauci to shima yazo yayi jonning dinsu da farko Alhaji Bala ki yayi amma da Ukasha ya kwadaita mishi irin kudin da ake samu make ya amince 
Kaninsa Saidu ya dora akan kayansa akan yaci gaba siyarwa ya shirgawa Mahaifiyarsa karya akan ya samu aiki a birni adduoi Saude ta bishi dashi ba tare da bata lokaci ba yabi Ukasha suka tafi 
Dayake masu aiki irin nasu Ukasha partner in crime kawai suke nema da hannu bibbiyu suka karbi Alhaji Bala aka hau yi mishi training din yanda ake sata da magana da hannu ido da yanda ake Harbin bindiga ogansu gabadaya a lokacin wani ne inyamuri anace mishi Chris Bala duk da yadan sha wahala kafin ya saba ya ajiye tsoro a gefe hakan bai hana shi iya training din da suka mishi ba Inda bayan sati uku da joining dinsu suka fita operation daddare suka tare wasu matafiya masu tafiya PortHarcourt aranar zallar rashin imani suka yiwa matafiyan Dan dama ogan nasu ba musulmi bane ballantana yayi imani 
Bayan sun kwace musu kaya da dukiyoyi sai da suka yi raping din matan dake cikin motar gabadaya acikin su takwas sai da suka samu mata bibbiyu Ciki kuwa har da Alhaji bala da bai taba sanin mace ba Ogansu na tsaye akansa yayi raping wata yar shekara takwas da mahaifiyarta sai kuka suke banda wayanda suka susuma Wata ce mata dage tana musu gardama sosai taki yarda da ogansu Chris sai Ihu take 
A fusace Chris yajanyo hannun Alhaji bala ya damka masa bindiga yace yana so ya fasa kwakwalwar matar data Goya jaririn da bai wuce wata biyu ba tunda taki yarda ta bashi hadin kai Jikin Bala ne ya hau rawa sabida bai taba kisan kai ba yacewa Chris ba zai iya ba aikuwa a fusace Chris ya buga mishi gindin bindiga akan ya harbeta k0 shi harbeshi 
Alhaji Bala yana rawarjiki ya harbi matar dake ta sallati da yaronta abaya Tundaga lokacin alhaji Bala shima ya Faso gari suke fita garuruwa fashi idan sunyi fashi ma sai sunyi wa mace fyade Tuni yayi kudi yayi ginin bullo a kauyensu ya Gina wani katon shago ya zuba kaya kanensa suke kula da shagon Saude Albarka kawai take sa mishi Watarana kuwa sun fita fashi da yamma a lokacin basu fiye zuwa gidajen jama’a ba sai dai su tare matafiya akan hanya su kwace musu dukiyoyinsu da kudinsu 
A hanyar Abuja suka yi fashin inda ogansu Chris ke tsaye yana basu umarnin chaje matafiyan suga ko akwai inda suka boye kudi cikin zafin nama Ukasha da Alhaji Bala suka ringa chaje matafiyan 
Matan da suka sunkuyarda kansu akwance suna rawarjiki ahankali wata dattijuwa ta dago sakamakon jin kamar muryar tilon danta 
Arazane ta Mlke tana nuna Ukasha dana ‘Ukasha dama kai Dan fashi ne’ Ukasha wani irin fitsari ne ya kubce mishi ya gwallo Ido yana kallon mahaifiyarsa dake mishi wa’azi kusan kullum akan ya guji haram ya kusanci Halal yaji tsoron Allah a duk inda yake 
Hannu ya dora akai ya zube akan gwiwarsa yana kallon mahalfiyarsa da hawaye ke gudu akan fuskarta 
A take ogansu Chris ya gane mai ke faruwa wani mugun tsawa ya dakawa Ukasha yana “who is she to you”? 
Cikin rawar jlki Ukasha yace mishi ” she’s my mother am dead she never knew am arm robber” Wani irin dariya ogansu Chris ya kwashe dashi yace “who ever knows our secret must die before counting of 3 shoot her she must die” 
Wani mugun ihu Ukasha ya fasa yace ” no boss don’t do this to me all am doing is because of her I can’t kIll her she’s my mother how can l kill her” 
Wani Dariyar ya kwashe dashi yace ” Ukasha i Said shoot her if not am going to shoot d both of you Ukasha girgiza kansa yayi yace ‘I can’t kill my mother pls kill me and leave her am begging you boss don’t kill her pls” 
Ogansu Chris counting ya fara yi take ukasha ya juya ya kalli Mahaifiyarsa data kura mishi ido hawaye kamar an bude famfo da sauri yafara cewa “Ummina Dan Allah ki yafemin nayi miki ba daidai ba bana so na ringa ganin irin wahalar da kike sha akanmu bana San aikatau dinnan da kike yi shiyasa na zabi wanan sana’ar Dan babu hanyar da zan samu kudi sai shi Ummi ki yafemin kasheni zasuyi Dan Allah ki yafemin” 
Adai dai lokacin da ogansu Chris ya kusa gama counting 10 a guje mahaifiyarsa faje ta tsaya agabansa ta hade hannayenta tana mugun kuka tafara magana tana “Dan Allah kar ka harbe Min da ka harbeni na rokeka dan girman Allah karka harbeshi agabana kayi hakuri” 
Maganar da bata karasa ba kenan Oga Chris ya sakar mata bullet akai ya sakarwa Ukasha 
sau biyu Wani irin ihu Alhaji bala yayi yaje wajen Ukasha yana jijjiga shi ogansu bakin bindiga ya buga mishi aka yaja shi kamar tsumma ya jefa shi a cikin mota Alhaji Bala sai kuka yake yana kallon gawan Ukasha da mahalfiyarsa ahaka suka tafi suka bar wajen 
Mutuwar Ukasha ba karamin girgiza Bala yayi ba atake yaji shima idan ba kashe oga Chris dinan yayi ba hankalinsa bazai taba kwanciya ba Aikuwa daddare bayan sun kasafta kudin Ogansu Chris ya aika a siyo mishi giya Dan idan dai suka fita operation suka dawo sai yasha giya ta kusa kwalba goma 
Sai da yasha yayi mankas ko hannunsa baya iya dagawa Alhaji Bala ya dauki bindigarsa ya bude mishi wuta kamin sauran suyi wani yunkurin dauko bindigarsu ya harbe su duka sai huci yake Dan shima yanda yakejin zuciyarsa babu Wanda bazai iya kashewa ba 
Hade kan kudaden yayi yayi nashi gurin tunda daga lokacin ya zama ogan kansa inda ya 
samo wasu sabbin yaran sune su lion dasu killer…….. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE