BAƘIN DARE CHAPTER 6

BAƘIN DARE 
CHAPTER 6
Batare da bata lokaci ba yaje ya nemo wani boka dayake cewa kansa Mallami akan ya ringa musu aiki kafin su fita operation sabida yanayin aikin nasu akwai Hatsari Mai gida ake cewa Mallamin inda yayi fice sosai akan tsubbuce tsubbuce ba iya barayi yake yiwa aiki ba harda matsafa da kidnappers Kafin su fita operation sai sun fara zuwa wajensa ya duba musu akwai sa’a afitar tasu ko babu kamar kuwa mai gani amadubi dan duka yanda operation din nasu zai kasance Mai gida sai ya gaya musu har wani zobe ya bawa Alhaji Bala akan yasa Atsakiyar yatsan shi na hagu indai da akwai danger a duk inda suke ko kuma ana nemansu zaiji zoben hannunsa na mishi zugi
Da wanan d’aurin gindin da Alhaji Bala ya samu awajen Maigida yasa ya rufe ido yake farautar dukiyoyin jama’a da rayukansu babu d’igon imani ko kad’an a zuciyarsa tamkar yanda zaka kashe Sauro kana daga cikin d’aki haka yake kashe mutumin da ya nemi ya mishi gardama ko kuma ya hana shi kud’i ga fyade da bai d’auke shi a bakin komai ba dan in dai zai fita operation indai yayi tozali da mace wala mai Aure ko buduruwa to fa sai ya mata fyad’e dan yana cikin sharad’un mai gida ya ringa yiwa mata fyad’e 
Tuni Alhaji Bala ya zama kungurmin dan fashi Dan yanzu ba iya matafiya yake tarewa ba har manyan gidaje yake zuwa fashi idan kuwa yaje fashi tsautsayi yasa babu kud’i a gidan to fa aranar sunanku gawa Dan bazai fito batare da ya d’auki rai ba 
Adaya bangaren kuwa Mahaukatan kudi kawai yake Samu Dan bai fiye sakarma su lion kudi ba sosai he is very selfish ga wayon masifa duk abinda su lion zasuyi idonsa na Kansu dan bayaso suyi betraying dinshi kamar yanda yayi betraying d’in Oganshi Chris 
Acikin kanensa babu Wanda bai Mallakawa gida ba banda Mahaifiyarsa da ya tamfatsawa wani katon gida da masu aiki 
Albarka Saude kawai ke sa mishi Dan duk a tunaninta aikin da Alhaji Bala keyi ne Allah yasa mishi Albarka 
Yan cikin garin kuwa irin kud’in da suka ga Alhaji Bala na samu ne cikin kankanin lokaci yasa suka fara tunanin ko dai yana yankan kai ne 
Abinka da Kauye tuni kananan maganganun da yan garin ke yi ya koma kunen Mahaifiyar Alhaji Bala data tashi daga mai dan wake zuwa Hajiya Saude sabida duk shekara Sai Alhaji Bala ya biya mata Umara da Hajji Hankalinta ne ya tashi data ji abinda yan kauyen ke cewa inda ta nemi Alhaji Bala da yazo da gaggawa tana so taganshi aikuwa babu b’ata lokaci yaje ya sameta 
Murmushi yayi a lokacin da Hajiya Saude ta gaya mishi zargin da ake mishi agari inda ya musanta zargin da ake mishi yace aikin mai yake yi kuma kowa yasan aikin mai na kawo kud’i A take Hajiya Saude ta samu relief a zuciyarta ta shawarce shi akan ya ringa taimakawa ‘yan garin nasu tunda yana da kud’i kuma ba laifi akwai Mabuk’ata da yawa agarin Alhaji Bala shawararta ya nema akan ta fad’a mishi wane irin Abu sukafi bukata a Kauyen 
Anan Hajiya Saude ta zayyano mishi abubuwan da suke bukata 
Aikuwa kafin shekara d’aya da Maganar Alhaji Bala ya tamfatsa wani k’aton makaranta asibiti da wani katon massallaci tuni ya siye zuciyar mutanen Kauyen duk lnda ka zaga kyawawan halayenshi ake Fad’i Dan kowani dan siyasan bai isa yayi kwatan abinda Alhaji Bala ke yi ba a cikin kankanin lokaci mutane suna fara Sanin Alhaji Bala da irin taimakon da yake yi dan indai kaje ka samu mahaifiyarsa ka fad’a mata matsalarka to kamar angama yi maka ne Dan tana bashi list D’in masu Neman taimako zai bata 
Tuni kowa yasan da labarin Alhaji bala ba iya ‘yan garin ba dan har daga wasu jihohin ake zuwa garinsu Alhaji Bala Neman Taimako ahaka manya Manyan mutane suka San shi amma basu San ainihin Sana’ar da yake ba Alhaji Bala ganin mutane sun sanshi da yawa ciki kuwa harda manyan mutane yasa ya fara tunanin badda kama sabida kar wayanda yake yiwa fashi su gane shi Anan ya fita can kasarwaje yaje ya samu Mask mai irin fatar mutum sak aka mishi bak’in fenti ya koma yake Sawa idan zai fita fashi acikin irin wanan yanayin ya had’u da wata lubna ‘yar Ethiopia suka kula soyayya acikin kankanin lokaci ya Aureta abunka da akwai masu gidan rana Shekararsu biyu da Aure ta haifo mishi wata tsalleliyar ‘ya mai mugun kama da ita dan tama fi Mahaifiyarta kyau nesa ba kusa ba kai kana ganinta tunani zakayi ta hadajinsi da larabawa gashi 
Alhajj Bala tunda yake bai tab’a San wani Abu arayuwarsa ba sama da ‘yarsa Naila yana bala’in ji da ita Wanda yake ganin ko ruhinsa zai iya cirewa ya bata gatan da yakewa Naila ya wuce tunanin mai tunani Dan dai dai da makaranta daya saka ta sai da yaja wa masu makarantar warning sosai akan ta ko kuda baya so ya tabata ballantana akai ga duka 
musamman ya samu Nanny da bata da aikin da ya wuce ta ringa kula da ita harsu taso 
Kowane lungu da sak’o na gidan shi mak’ale yake da hoton Naila sai data shekara bakwai ya daina kwana da ita burinsa bai wuce yaga duk abinda yagani ya siyo mata ba abunda dai ake cewa gata Naila ta same shi 
Mahaifiyarta kuwa tunda ta haifi Naila bata k’ara b’atan wata ba hakan kuwa ba karamin damunta yake ba Alhaji Bala ke kwantar mata da hankali akan karta damu Naila kawai ma ta ishesu rayuwa 
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Alhaji Bala yake k’ara samun dabaru da kwarewa na fashi sosai Dan har ‘yan siyasa yake robbing abun shi abun yana ciwa mutane tuwo a kwarya amma an rasa Wanda yake wanan aika aikan Watarana Alhaji Bala yaje gidan wani attajiri shi da yaransa Dan suyi fashi bayan sun gama kwashe uban kudade da gwala gwalai anan yace zai keta haddin matar Attajirin ai fa nan gizo ke sak’ar dan Attajirin fur yaki yarda a taba mishi mata yace sai dai idan bayan ranshi 
Da yake doka Mai gida ya basu akan idan zasuyi wa mace fyad’e karsu sake su kashe mutum sai sun gama biyan bukatarsu agaban kowa sanan idan zasu kashe mutum sai su kashe 
Aifa nan Alhaji Bala yafara kokawa da Attajirin da yak’i bari yaje kusa da matarshi duk gindin bindigar da ya ringa buga mishi akai jini na wanke masa fuska hakan bai sa ya hakura ya bashi hanya ba kokawa suke sosai inda Attajirin ya kai hannunsa fuskar Alhaji Bala dan ya yak’uso mishi fuska aikuwa sai gashi ya Ciro mask din fuskarshi anan yayi tozali da fuskar Alhaji Bala Ya gwallo ido cikin kidima yana nuna shi da hannu dan shima kansa Yasan Alhaji Bala awajen taimakon talakawa 
Alhaji Bala kuwa k’arasa cire Mask din fuskarshi yayi ya ce ya daina mamaki shine nan anan ya hau gaya mishi mugayen halayenshi da Sana‘arsa inda a k’arshe ya sa su Lion suka 
rike mishi Attajirin ya ketawa matarsa haddi agabanshi 
Ya harbe matarsa ya harbe mutumin sau biyu daga nan suka saka kai suka fice 
Suna fita mak’ota suka shiga gidan dan duk abunda ke faruwa sunaji har ‘yan sanda sun kira amma shiru basu karaso ba har b’arayin suka tafi Abunka da babban mutum tuni aka kaisu asibiti acikin daren duk da basu da tabbacin suna rayye Suna zuwa aka karbesu Matarsa kuwa dama ta Dade da rasuwa Mijin ne dai ake ganin da alamaryana numfashi A lokacin da likitoci suka dukufa akan shi dan ceto ransa bude idonsa yayi a cikin mayuwacin hali ya yafito d’aya daga cikinsu 
Yana isa inda yake yayi Sauri yace ya kira mishi d’aya daga cikin ‘yan sanda dake waje 
Da sauri suka kira daya daga cikin ‘yan sandan yana zuwa Attajirin yace da karfi “ba kowane ke robbering mutane ba sama da “ ALHAJI BALA MAI KUDI WANDA KE TAIMAKON TALAKAWAN NAN SHINE YAZO YAMIN FASHI YAYI WA MATATA FYAD’E YA HARBETA YA HARBENI” 
cikin sauri sauri Attajirin ya gaya musu yanda sukayi da Alhaji Bala inda mamaki ya hana dan sandan motsawa yana kokarin ya tambayeshi ko dai mai kama dashi ne rai yayi halinsa Tofa anan yan sanda suka fara bincike a b’oye dan su San sana’arda Alhaji Bala keyi inda suka saka mishi ido sosai a lokacin suna zaune a garin kano 
Mai gida ne yafara gaya mishi yayi taka tsantsan an fara sa mishi ido asirinsa ya kusa tonuwa idan da hali ya bar garin kano Aikuwa a cikin kankanin lokaci Alhaji Bala ya koma port Harcourt da zama shi da iyalansa Inda ‘yan sandan suka tabbatar da zargin da suke mishi anan suka samo Akram dan ya kware a binciko sirrin mutum dan har pretending ya taba yi akan shi mahaukacine sabida kawai su kamo wani dan yankan kai 
Tuni Akram shima ya koma portharcourt da zama ya samu wani dan benci ya baza sweet alewa hardasu sigari yafara siyarwa a opposite gidan Alhaji Bala yana ganin duk wani shige da ficen Alhaji Bala da iyalinshi har da ‘yar tilon ‘yarsa dayake bala’in ji da ita kamar ransa Sai da ya samu wata shidda yana lura da duk wani movement din Alhaji Bala inda watarana da yamma Bayan akram ya gama had’a wani plan Alhaji Bala na dawowa gida tunda ga nesa Alhaji Bala yaga antaru a opposite d’in gidansa ana alamar akwai abunda ke faruwa 
Parking yayi ya nufi wajen da saurinsa dakyarya kukutsa cikin mutane anan yaga Akram na dambe da wani akan sai ya biyashi kud’insa daya siyi sigari da sweet Akram har dasu kuka yasaka yagaggun kaya 
Tsawa ya daka musu suka rabu da juna suna sauke ajiyar zuciya Akram kuwa har da guntun hawayensa da majina 
Anan Alhaji Bala ya tambayesu mai ke faruwa suka fad‘a mishi yayi wani tsaki ya Ciro sabbabin Dari bibiyu masu yawa ya mikawa Akram 
Akram kuwa ya tsuguna har kasa ya fara yiwa Alhaji Bala godiya K0 tsayawa bai yi ba ya nufi wajen motarsa 
Daddare bayan su Alhaji Bala sun gama cin abinci haka kawai Akram ya ringa fad’o mishi a zuciya haka kawai yaji yaron ya kwanta mishi bai tsaya wani dogon tunani ba ya mike yayi waje 
Direct wajen Akram ya nufa daya buga tagumi yana kallon waje daya har ya zauna agefenshi Akram bai sani ba sai daya dafashi 
Ya juyo a Firgice suna had’a ido yayi sauri ya sauka daga kan bencin zai tsuguna Alhaji Bala yayi sauri ya maidashi ya zauna 
Alhaji Bala sai da ya gama kare mishi kallo yace “kabani takaitaccen tarihinka” 
Wani irin farinciki ne ya rufe Akram amma a zahiri kuwa kwalla suka hau zubo mishi 
Anan Akram ya karkata kai ya fara zuba mishi mugun karyar irin talaucin da suke ciki shi da iyayensa shine babba a familynsu su wajen goma sha biyu babansa makaho ne haka ma mamansa sanadiyar accident da sukayi yanzu shine komai nasu 
Wani irin tausayin Akram ne ya rufe Alhaji Bala ya tambayeshi yana so yayi bankwana da talauci da sauri Akram ya zube a kasa yace mishi ee Alhaji Bala k’ara tambayarshi yayi kowane irin aikine zai iya? 
Bud’ar bakin Akram sai yace koda yankan kai ne zai iya 
Wani irin murmushi Alhaji Bala yayi yace kar ya damu zasu had’u gobe ya shirya zasuje wani wajen 
Aranar Akram kwanan farinciki yayi ya kira manyansa akan su taya shi da add’ua su kuma sa ayi mishi sauk’ar Qurani akan Allah ya kareshi daga wani mugun Abu 
Washegari da sassafe Alhaji Bala ya d’auki Akram suka d’auki hanyar Maiduguri inda Mai gida yake sai daddare suka isa wajen Mai gida idan banda adduoi babu abunda Akram keyi 
a zuciyarsa 
Abun mamaki mai gida shima yana ganin Akram yaji San shi hara zuciyarsa 
Anan Alhaji Bala ya gabatar mishi da Akram akan yanaso ya zama yaronsa shima ya duba akwai alheri atattare da Akram ko dai babu 
Abun mamaki Har Mai gida ya gama dube dubensa haske da alheri kawai yake hangowa attatare da Akram 
Cikin farinciki mai gida ya fara gayawa Alhaji Bala irin Al khairan dake tattare da Akram akan zai ringa samun mahaukatan kud’i dan haka ya ringa lallaba Akram ya ringa binshi a hankali karya ringa matsa mishi akan yayi Abu 
Take Alhaji Bala ya amince bakinsa har kunne anan suka kwana mai gida ya ringa musu tsubuce tsubuce Akram kuwa ya ringa zuba addu’a a zuciyarsa 
Washegari suka koma port Harcourt da Akram da shirin shima next operation dashi zasu tafi Duk abunda ke faruwa Akram na sanar da manyansa halin da ake ciki 
Ahaka suka fara fita first operation inda suka nufl garin bauchi sukayi wa wani hamshakin mai kud’i sata sukayi wa yaransa biyu fyade’ duk abunda ake yi Akram na makale da secret camera dinshi a lokacin babu yanda Alhaji Bala bai yi da akram akan shima yayi wa d’aya daga cikin ‘yan matan fyade ba yaki next operation ma ya kuma yiwa Alhaji Bala gardama akan shi zai ringa rakasu amma bazai iya kashe mutum ba bakuma zai iya yiwa kowa fyad’e ba tun a lokacin Alhaji Bala yaso ya fasa kwakwalwar Akram amma mai gida na hana shi 
Wanan shine takaitaccen tarihin Alhaji Bala Cigaban labarin 
Alhaji Bala sai da yayi wa Naila yar shekara goma sha hudu uban siyayya na wajen dubu d’ari hud’u sanan ya karasa gida 
lnda yana isa gida Naila ta fara tsalle tana mishi oyoyo 
Duk girmanta kuwa sai daya d’aga ta sama ya yi juyi da ita kafin ya sauketa kasa yana tambayarta ya gida Hajiya Lubna kuwa tana daga gefe tana ta murmushi tanajinjina irin soyayyarda Alhaji Bala ke nunawa Naila 
3hrs ltr 
Bayan Alhaji Bala yaci abincin dare ya huta suna ta hira da Naila tana bashi labarin School shi kuwa sai biye mata yake yana kyalkyala dariya Hajiya Lubna kuwa ganin alamun gajiya a tattare da Alhaji Bala amma yaki zuwa ya kwanta yasa tacewa Naila ta hakura gobe sai ta cigaba da bashi labari amma a yanzu Daddynta ya gaji Alhaji Bala da sauri da ya mike dan dama ya gaji hanya yake nema 
D’akinsa ya nufa direct ya shiga wanka yana fitowa ya fad’a kan gado ko towel d’in jikinsa bai cire ba dan wani mugun bacci yakeji ga gajiya ko minti biyu bai yi da kwanciya ba bacci yayi awon gaba dashi 
Kafin Hajiya lubna tayi shafe shafenta tazo wajen shi har yayi nisa a bacci 
Girgiza kanta tayi ta gyara mishi kwanciya ta kashe fltilar dakin ta bardakin ta koma Palo dan akwai film d’in da takeso ta kalla. 
12:30 am dai dai Alhaji Bala yayi wani irin juyi dan ya gyara kwanciyarsa kamarcewa akayi ya bude idonsa ya kalli bakin kofa aikuwa ya hango Hajiya Nafeesa a tsaye rigarta gabad’aya ajike dajini har diga jinin keyi ta zuba mishi ido tana kallonshi hawaye sai zuba suke a idonta 
Wani irin razananan Ihu Alhaji Bala yayi take fitsari mai zafin gaske ya kubce mishi ihu yake sosai da iya karfinsa 
Hajiya Lubna da Naila ta Dade da bacci a cinyarta a guje ta mike Naila tabi bayanta 
Suna shiga d’akin sukaga Alhaji Bala ya rufe idonsa da karfi yana “dan Allah kiyi hakuri ki rabu dani” Karar bude kofar d’akin ne yasa ya bud’e idonsa da sauri ya duro daga kan gadon jikinsa na wani irin kyarma duk yabi ya jike da gumi sai sauke nannauyan ajiyar zuciya yake kamar Wanda yayi gudu ….. 
Bangaren su Saiam kuwa a lokacin da suka isa asibiti tana hada ido da Alhaji Nazifl Hawaye ya hau zubo mata dan yabi yafita daga hayyacinsa kamar ba shi ba hawaye kuwa sai zubo wa suke a fuskarshi 
A hankali ta kalli gefen gadonshi ta hango Samha itama a kwance idonta a rufe itama hawaye nata zubo mata ahankali ta karasa gadon da Samha ke kwance ta rik’o hannayenta adai dai lokacin da Samha ta budeb jajayen idonta babu k0 digon fari ahankali ta fara magana cikin rawar murya tana ” Aunty Saiam yanzu Mummy ta tafi ta barmu kenan muma yanzu mun zama marayu bazata sake dawo wa ba”? 
Saiam kuka ta fashe dashi ta jawo Samha ta rungumeta tana rarrashinta 
Alhaji Nazifl dake kwance a gefe kuwa ya fashe da wani irin kuka ……… 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE