BAƘIN DARE CHAPTER 7

BAƘIN DARE 
CHAPTER 7
Saiam da Sauri ta Saki Samha dake sheshek’ar kuka ta nufl wajen Alhaji Nazifi dake kuka 
kamar karamin yaro 
A gefen gadon ta zauna tare da Ruk’o hannun Alhaji NaziFI ta saka d’aya hannun nata ta gage hawayen dake ta zubo mata tace muryarta na rawa 
“Daddy dan Allah kayi hakuri ka daina kuka haka Allahn da ya bamu ita shi ya karbeta Dan yafi mu Santa hakuri ,zamuyi mu ringa mata addu’a Mummy tace kar mu sake zubar mata da hawaye addu’ar mu kawai take bukata Daddy a matsayinka na Mijinta addu’a kawai ya kamata ka ringa binta dashi idan kai kana kuka mu mai zamuyi Daddy Dan Allah Daddy kayi hakuri ka share hawayenka kukanka na k’ara tunzura Samha kukanka na kara karya mata zuciya kai ya kamata ace ka rarrasheta” 
Alhaji Nazifi kamar k’aramin yaro ya ringa gyad’a kai da sauri yana goge hawayen da suke kara tultulowa 
A hankali yafara magana cikin rawar murya 
“ALLAH YA JIKANKI NAFEESA ALLAH YA KAI HASKE KABARINKI TUNDA NA AUREKI BAKI TAB’A YARDA NA KWANA DA FUSHINKI BA BAKIDA BURIN DA WUCE KI FARANTA MIN RAI KINYI MIN BIYAYYA NAFEESA KIN BINI SAU DA K’AFA KIN BAWA YARANA TARBIYYA INGANTACIYA K0 DAN WANAN INSHA ALLAHU ALJANA CE MAKOMARKI BAZAN TAB’A SAMUN MACE IRIN KI BA NAFEESA NAYI RASHIN DA HAR NA KOMA GA MAHALLICINA BAZAN SAMU WACCE ZATA MAYE GURBINKI BA ALLAH SARKI NAFEESA INA MA ACE NASAN DAREN JIYA ZAKI TAFI Kl BARNI INA MA ACE NASAN GANIN K’ARSHE NAKE MIKI DA WLH BAN KWANTA BA DA NA ZAUNA NA NEMI YAFIYARKI NAFEESA ALLAH YA JIKANKI NAFEESA” 
Duk inda Alhaji Nazifl yakai Dan ya danne kukan daya taho mishi kasawa yayi sai daya kwace mishi Saiam da Samha kuwa mutuwarta ya dawo musu sabo fil aransu suka hau kuka Kamar Wanda aka mitsina suka ga Alhaji Nazifi ya mik’e yana “Saiam an binneta ne”? Saiam kanta kawai ta iya gyad’awa 
Alhaji Nazifi kuwa yayi sauri ya tuge Karin ruwan da ake mishi a hannun bai damu da jinin dake zuba a hannun shi ba 
Yayi hanyar kofa da sauri 
Saiam da sauri itama tabi bayan shi tare da shan gabansa tana ” Daddy ina zakaje ahaka ?kagajinin da ke ta zuba a hannunka bane? 
Alhaji Nazifl da sauri yace ” Saiam zanje kabarinta nayi mata addu’a tunda badani aka 
binneta ba tana bukatar addu’ata” Daga haka ya ratsa ta gefen Saiam yayi waje da Sauri Samha itama Saukowa tayi daga kan gadon tacewa Saiam itama zata tafi gida zaman asibitin ya isheta haka 
Babu yanda Saiam ba tayi da Samha akan ta bari ruwan da aka sa mata ya kare ba fir taki 
akan dole Saiam ta kira likita ya Sallamesu Naila da sauri ta juya tayi waje sakamakon ganin towel din da Alhaji Bala ke d’aure dashi a 
kugunsa ya fado kasa 
Alhaji Bala sabida tashin hankali da tsoratar da yayi bai ma San a tsirara yake ba 
Hajiya Lubna kuwa itama cikin rawarjiki ta nufi wajen Alhaji Balan daya jike da gumi ta 
dauki towel dinsa dake k’asa tace “Alhaji lafia kuwa mai ya firgita ka haka da har towel d’inka ya barjikinka Baka sani ba”? 
Alhaji Bala sai a lokacin yasan a tsirara yake hannuwansa na rawa ya karbi towel d’in daga hannun Hajiya Lubna ya d’aura tare da zama a gefen gado still yana hango Hajiya Nafeesa a tsaye a idonsa 
Numfashinsa sai fita yake da Sauri sauri 
Hajiya lubna itama zama tayi agefensa Dan tunda take dashi bata taba ganinsa acikin irin 
wanan halin ba A hankali tace “Alhaji Lafiya mai ya tsorata ka haka ko dai mafarki kayi”? 
Alhaji Bala bai ce mata komai ba har lokacinjikinsa bai bar rawa ba Magana Hajiya Lubna ta kara yi Alhaji Bala ya daka mata wani mugun tsawa yana “dalla ki rabu dani Wai meyesa bakida hankaline dolene saina gaya miki abinda yake damuna”? 
Hajiya Lubna da sauri ta mik’e tayi waje ba tare da ta tsaya bashi hakuri k0 taji mai zai cigaba da cewa ba 
dan haka take idan taga ransa a bace bata tsayawa a wajen barin gurin shi zai fiye mata alheri dan itama akwai zuciya 
Naila data yi jingum a Palo tana ganin Hajiya Lubna ta fito ta tareta da sauri tare da 
tambayarta abinda ya samu Abbanta 
Hajiya Lubna da itama ranta ya baci bata cewa da Naila komai ba illa ma hannunta data rike 
sukayi hanyar dakinta 
Naila kuwa ganin babu fuska yasa bata kara tambayarta ba ta kwanta kamaryanda Hajiya 
Lubna ta kwanta 
Alhaji Bala aranar kwanan zaune yayi a tsorace gani yake ko yaya ya runtse idonsa Zai iya ganin Hajiya Nafeesa 
Rayuka nawa ya kashe amma babu wacce ta taba masa fatalwa sai Hajiya Nafeesa tunda yake ko mafarkin wayanda ya kakashe bai taba yi ba sai Hajiya Nafeesa me hakan ke nuf agaskiya bai ga ta zama ba dole da asuba ya d’au hanyar Maiduguri yaje ya nemi taimakon mai gida 
Allah Allah kawai yake gari ya waye 
Wajen k’arfe 3:40 yafara gyangyadi a zaune sai baccin ya kusa sace shi sai yayi firgigit ya zauna ahaka ya ringayi har sai da baccin yaci karfin idonsa ya kwanta bacci yayi awon gaba dashi 
Mafarki ya fara yi da Hajiya Nafeesa tana ta kuka ga kirjinta na ta zubar dajini sai binshi take da gudu shima yana ta gudu da iya karfinsa sai ihu yake yana azo a taimaka mishi amma ina gani yake kamar ba gudu yake ba sabida Hajiya Nafeesa tana dab da karasowa inda yake Hannu ta mika da niyyar damko shi ya mike a firgice yana ihu sabida ba ilimin islama ballantana yayi sallati Yana zama ya kuma hango hajiya Nafeesa abakin kofa atsaye kamar dai yanda ya ganta a mafarki 
Wani razannan ihu ya saki da iya karfinsa Hajiya Lubna da Naila suka kwasa aguje sukayi dakin Suna bude kofa Hajiya Nafeesa ta bace 
Alhaji Bala kuwa ya ringa wani irin kyarma kamar mai jin sanyi ga wani uban gumi kamar Wanda aka kwarawa ruwa “Naila a bakin kofa ta tsaya dan towel d’insa ya kuma yin wani wajen 
Hajiya Lubna kuwa fuska a d’aure ta nufi wajensa tana “Alhaji wai me hakane mai yake damunka kake ta mana ihu ka fadamin kaki ka fad’amin abinda yake furgita ka wai mai haka ne dan Allah dan annabi”? 
Hajiya Lubna tace tana jefa mishi towel dinsa daya yi gefe 
Alhaji Bala ajiyar zuciya Kawai yake yana kalle kalle sai zare ido yake 
Hajiya Lubna wadrobe ta nufa ta d’auko mishi wani dogon jallabiya da gajeran wando Ta cilla mishi adai dai lokacin da Naila ta bardakin 
Hajiya Lubna kuwa tace ” ga kaya nan ka sa tunda abinda yake firgita ka saka yake kayi tsirara agaban ‘yarka” 
Alhaji Bala da sauri ya zura jallabiyar da gajeran wandon yabi bayan Hajiya Lubna data yi hanyar waje da sauri dan bayajin zai Iya zama a d’akin shi kad’ai 
A palo suka zauna gaba d’aya Naila ta haujerawa Alhaji Bala dajikinsa ke rawa Sannu 
Alhaji Bala shi dai kansa a sunkuye yana hango yanda yaga Hajiya Nafeesa a mafarki da zahiri a hankali ya d’aga kai ya kalli agogon dake bangon palon yaga hud’u da minti Arbain an fara ma kiraye kirayen Sallahr asuba 
Hajiya Lubna tagumi kawai tayi tana kallon shi aranta tana ta mamakin abinda yake tsorata shi ya fita daga hayyacinsa haka Alhaji Bala kuwa yana ganin biyartayi ya mik’e ya d’auko mukullin motarsa a daki saijuye juye yake dan duk a tsorace yake 
Ko salla bai tsaya yi ba dan dama ba damunsa yayi ba sai yaga dama yake yi 
Ko kallon Hajiya Lubna dake ta tambayarshi ina za shi bai yi ba ya fice da sauri dan burinsa bai wuce ya gan shi agaban Mai gida ba 
Bangaren Akram kuwa aranar Sam bai runtsa ba da tunaninsu Saiam ya kwana ko yaya ya juya sai ya hango Samha a idonsa tana ta kuka 
Wajen k’arfe uku bacci yayi awon gaba dashi atake ya hau mafarki da Hajiya Nafeesa tana ta kuka tana ce mishi ya kular mata da yaranta kar wani Abu ya same su sai kuka take a mafarkin tana hade hannyenta alamar roko 
Da Sallati Akram ya farka daga baccin da yake yana ta mamakin Mafarkin da yayi 
A hankali ya sauko da kafarsa daga kan gado ya nufi bandaki dan ya d’aura alwala 
Alhaji Bala a zaune yake agaban mai gida yabi ya had’a gumi yana ta kallon K’asan da mai gida yake bugawa shima sai hada gumi sai daya samu minti Ashirin yana buga kasa yana gogewa yana kuma zana k’asa sai girgiza kai yake alaman Al amarin babba ne 
Alhaji Bala kuwa dukya matsu ya gaya mishi abinda yake faruwa 
A hankali Mai gida ya d’ago tare da sharce gumin dake tsatsafo mishi a goshi ya kalli Alhaji Balan da jikinsa ke rawa dan shi kansa tunda yake bai taba ganin mai gida a irin wanan yanayin ba 
Mai gida magana ya fara yi yana “Kura akwai matsala matsalar ma kuwa gagaruma dan wanan fada ne tsakanin matacce da rayayye matar nan daka kashe spirit d’inta na da karfi sosai wlh haka zata tayi ta bibiyarka har sai ka zamto kamar mahaukaci ka fito duniya ka fadi hallayenka da kanka da irin sana’ar da kake yi kafin ta rabu dakai kayi kuskure daka bari jininta ya tabaka” 
Hankali a tashe Alhaji Bala yace “mai gida kamar ya jininta ya tab’ani kana nufin babu abinda zaka iya yi akai”? 
emana jininta ya tabaka ai sabida hular kanta ta cire ta saka a kirjinta sai da yajike dajini ta jefo ma a fuska koba ayi haka ba”? Da sauri Alhaji Bala yace “anyi haka wlh na dauka taurin zuciya yasa tajefo min hularta ni kuwa na karasa kasheta na shiga uku na lalace mai gida yanzu maiye abun yi dan Allah ka taimaka min dan ni Dana San matar nan haka take wlh da ban soma ma kasheta ba da iya shegun zan debo na fito” Alhaji Bala yace cikin rawar murya 
Mai gida ajiyar zuciya ya sauke yace “Abu biyu zaka iya yi ta rabu dakai na d’aya ka koma gidan ka d’auko wanan hular nata ka kona shi na biyu kaje gidan ka durk’usa agaban mijinta da yaranta kace su yafe maka idan sun yafe maka to zata rabu dakai amma idan kuwa acikin biyun nan ba’ayi d’aya ba to ni kam babu abinda zan iya yi akai kuma Abubuwa na dab da jagule maka ga rashin kwanciyar hankali da zakayi ta fama dashi” Hankalin Alhaji Bala idan yayi dubu ya kai kololuwa wajen tashi a Firgice ya mik’e yana “mai gida kasan mai kake cewa kuwa ta ina zan iya samo hular da ta cire?ta yaya zan koma gidan a matsayina na Wanda ya kasheta haba maigida ya zaka fad’i abinda ba zai yiwu ba” Mai gida ce mishi yayi to “iya abinda na duba kenan Wanda zaka yi ta rabu dakai amma bayan shi babu abinda zaka iya yi akai amma dai zan baka wasu Abubuwa idan ka dace ba zata ringa zuwar maka ba” 
Da sauri Alhaji Bala ya zauna yana “dan Allah ka taimakeni matar nan ta firgitani har tsirara nayi agaban ‘yata bansani ba” Mai gida wani kwarya ya dauko Wanda ya aka nannade da jajayen kyalaye ya mika mishi yana  idan ka tashi ka warware wanan Jan kyallen ka daura akan goshinka da kafarka akwai wani kullin magani guda biyu a ciki bakin jikawa zaka yi ka shafa ajikinka gabad’aya wari ne dashi kamar kashi amma haka zaka d’aure idan gari ya waye sai ka wanke 
Dayan kuma turara d’akinka zaka yi dashi kafin ka kwanta bacci” 
Hannu yasa ya dauko Wasu jajjayen candles ya kuma mik’a mishi yana ” ka kashe wutan d’akinka sai ka kunna candles d’in idan dai kaga tazo maka bayan kayi abubuwan nan to babu abinda zan iya yi akai face dai zabin farkon Dana baka” 
Alhaji Bala da Sauri yace “insha Allahu ma ba zata kuma zuwar min ba indai nayi yanda 
kace” Mai gida girgiza kansa kawai yayi bai ce komai ba ahaka Alhaji Bala ya ajiye mishi makudan kud’i ya tafi ……….. . .
Hmm kome zai faru

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE