BAƘIN DARE CHAPTER 9
CHAPTER 9
Alhaji Bala ba karamin farinciki yayi ba a lokacin da yaga ya kwana biyu Hajiya Nafeesa
bata zo mishi a amafarki ko a zahiri ba
Tuni yafara dawowa dai-dai hankalinsa ya fara kwanciya sai a lokacin yaje ya samu Naila har cikin dakinta sabida ta daina fitowa gabadaya sabida tsoronsa da takeji Hajiya Lubna kuwa ido kawai ta zuba mishi bata kara bi ta Kansa ba tunda taga alamar baya so ya fada mata abinda yake damun shi
Naila da sauri ta mike a lokacin da taga ya shigo
Alhaji Bala ya sakar mata murmushi yana “zo nan babyna kar dai kice gudun daddynki kike”? Naila itama murmushin ta sakar masa da ta Ganshi a nutse ta tafi da gudu ta rungume shi tana “Daddy what happened to you” Murmushi Alhaji Bala yayi a lokacin dayake kwantar mata da dogon gashinta San tilon ‘yarsa na ratsa mishi zuciya yanda yakejin San Naila he can do anything bcos of her
Zame ta yayi daga jikinsa ya rike hannyenta ya nufl dogon kujerar dake d’akin ya zaunar da ita ya zauna a gefen ta tare da kuma rike hannayenta yace ” am so sorry dear Some thing came up that Daddy could not handle but now am fine u should not be scared again”
Naila murmushin farinciki ta saki tace “Daddy yanzu ka warke babu abinda yake damunka” Alhaji Bala cikin farinciki ya gyada mata kai
Naila kuwa ta tashi ta fara tsallen murna kamar wata yarinya dama yarinyar ce ma tunda she is 14yrs
Alhaji Bala mikewa yayi yace ta shirya anjima zasu tafi shopping ta zabi duk abinda take so
Naila wani tsallen murnarta karayi tare da rungumeshi tana “I love u daddy you are d best dad eva ” “I love you to Darling” Alhaji Bala yace adai dai lokacin da yake barin dakin fuskarsa dauke da tsantsar farincikin yayewar matsalarsa
Dakin hajiya Lubna ya nufa dan ya rarrasota dan yasan fushi take dashi Bai sha wahala wajen rarrashinta ba abunka da mata da miji sai gashi sun bige da soyayya dan dama tunda ya dawo basu had’u ba sabida rashin kwanciyar hankali sai da komai ya
wakana Hajiya Lubna ta hau bashi shawarwari akan ya daina wasa da Sallah dan ita tasan
aljanu ne suka ringa tsorata shi sabida babu wani kariya a jikinshi
Murmushi kawai Alhaji Bala yayi yace mata to zai gyara daga haka ya mike ya fada bandaki Siyayya yayi wa Naila na fitar hankali Hajiya Lubna sakin baki kawai tayi tana kallon shi dan siyayyar ma har Dana banza bata kuma isa ta hana shi ba idan ma tayi magana cewa zai yi ita kadai ce dashi gwara ya kashe mata
Sai da magriba suka dawo gida bayan ya kaisu wajen shakatawa aka ringa jido musu
siyayyarda sukayi ana shiga dashi cikin gida
Alhaji Bala yana tsaye aka gama shiga da kayayyakin Hajiya Lubna da Naila kuwa dama sun Dade da shiga ciki
Wajen motarsa ya koma ya shige ciki tare dasa lock
Wayarsa dayake communicating dasu killer ya dauko daga bayan seat din motarsa dan baya shiga da wayar cikin gida sabida tsaro Bai yi mamakin ganin miss call dinsu ba dan yasan Dole dama su neme shi
Layin Killer ya fara kira bugu daya ya d’auka Yana amsa gaisuwar da Killer ya mishi yace “karku damu all is fine na dan shiga rububi ne hope duk kuna villa sunan da yake cewa gidansu dake daji kenan
Killer ce mishi yayi ” eee oga duka muna nan AKram ne kawai har yanzu bai zoba
sakamakon mom dinsa bata da lafiya yama ce zai kiraka ya fada maka” “Zancen banza zancen wofi ina ruwanmu da wani Mom dinsa bata da lafia who even cares ko mutuwa tayi dole ya dawo bakin aikinsa bansan mai yasa yake so ya ringa take umarnina ba amma babu komai zanyi wa tufkar hanci tunda mai hanani is gone let me call the fool”
Bai bari Killer yayi magana ba ya kashe wayar yana huci tare da dialling number Akram
Adai-dai lokacin da Akram ke kan Sallaya yana Jan carbi idonsa a lumshe fuskar Samha nata mishi yawo a ido dan kwanaki nan shi kad’ai yasan mai yake ji akan Samha duk fitar numfashinsa sai ya tuna ta bai taba jin San ‘ya mace a zuciyarsa kamar yanda yakejin San Samha duk da Sau d’aya ya taba ganinta Ringing din wayarsa ne yasa ya bud’e idonsa tare da daukar wayar ganin mai Kiran ne yasa ya mike da sauri tare da gyara zamansa ya daga wayar
Alhaji Bala fada ya rufeshi dashi yana “wai meyesa kake so kaga kana bijirewa umarni nane? Yanzu kawai Dan uwarka bata da lafiya shiyasa Baka koma Villa ba tuntuni yo ko mutuwa tayi na baka umarni kaki bi Akram abubuwan da kake min ya isa haka not any more yanzu ba zanyi tolerating wanan nonsense din naka ba idan muka fita operation dole ka ringa participating idan na saka doka dole kuma kabi baka isa kuma ka bar cikin mu ba Dan idan kayi joining dinmu ba fita idan kuwa ka dage zaka fita sai na kasheka na kashe family dinka gudun tonuwar asirinmu yanzu ba anjima ba ka shirya ka tafi Villa jibi muna da operation and kai zakayi leading dinmu ranar kaji mai nace ko bakaji”
Da kyar Akram ya iya cewa naji sabida tsananin mamakin Yanda Alhaji Bala ya canza take ya fara tunanin ko dai Mai gida ya fara ganowa shi dan lekan asiri ne
Jikinsa na rawa yafara Neman oganshi Abdullahi dan ya gaya mishi halin da ake ciki
Shima mamaki ne ya rufe shi daya gama jin abinda Akram yace ajiyar zuciya ya sauke yacewa Akram “tabbas Alhaji Bala is up to some thing tunda kaji yace yanzu kai ma dole ka ringa participating idan ya fita operation” Akram hankali a tashe yace “oga yanzu ya za’ayi nifa bazan taba iya wani Abu ba idan ya fita rashin imaninsa har fyad’e fa yake sawa ayiwa yaran mutane da matan su ni aganina kawai tunda mun Riga da mun samu evidences kawai gobe aje har gida ayi arresting d’in shi”
Da Sauri Ogan shi yace “aa Akram ai inaga yanzu ya fara gano kane so shi yasa yake so ya tabbatar ko kai dan lekan asirine yanzu abinda za’ayi idan yasan wata ai bai San wata ba
ka shlrya kaje ayau din kamar yanda ya bukata inyaso kafin Ku fita operation din ka ringa kokari kana sanin wanda za’aje ayiwa operation din idan yaso sai ka sanar damu ko ta text message ne mu kuma zamuyi sauri mu sanar dasu akan su bar gidan da dukiyarsu kar su kwana a gidan kai kuma u would pretend ka jagorance su aranar kai ma irin no mercy dinnan kaga idan kukaje kukaga babu Wanda zaku samu mun Riga da mun ruguje mishi plan bai Sani ba haka zamu ringa mishi a duk lokacin da zaku fita kai dai kawai ka ringa sanar damu gidan da za’aje kaga ahaka zamu kama shi red handed dan inaso aranar da za’a kama shi har video covering da yan jarida zamu taso inaso kafin muyi arresting d’in shi yafara samun failure a duk fitar da zakuyi” Wani irin murmushi Akram ya saki yace “hakan yayi oga dama fargabana ace nima zan
aikata wani Abu da hanuna da sunan investigation amma tunda zaa ringa rushe mishi plan fine ni kuma zan ringa updating d’inku inda za‘aje operation Dan yana fada mana so I have to get going Dan yanzu yace na tashi na tafi wanan dajin”
Girgiza kai Ogan shi yayi game da jinjina kokarin Akram akan aikinsa yace “Allah ya tsareka ya kare ka da karewarsa addu’ar mu na tare dakai”
Murmushinjin dadi Akram yayi yace “Ameen oga ngd bari na kira Mahaifiyata itama tayi min addu’a” ahaka sukayi Sallama
Akram ya kira mahaifiyar shi itama ta raka shi da addu’a
Alhaji Bala kuwa yana gama waya da Akram ya fito daga motar ransa a bace yana tunanin bai San mai Akram ya dauki kansa ba dama mai gida ke hana shi yaci ubansa yanzu kuwa Tunda Mai gida ya ware dole ya budewa Akram wuta operation da zasu fita next sai Akram yayi kisa ya kuma yi fyade wanan ya zama dole idan yaki kuwa ya harbeshi
A Daren ranar Alhaji Bala Sam bai yi bacci ba yana ta bincike akan Alhaji Buba mai gwala gwalai hamshakin mai kudin dake zaune a garin kano duk wani information da yake so ya samu akan shi ya samu Abu daya kawai ya rage mishi yasan yanayin gidan wayarsa ya dauka ya kira wani sharon da bashi da aikin da ya wuce ya ringa mishi bincike akan yanayin gidan dazasu je operation Dan Sharon ya kware ta wanan fanin yana gama gaya mishi Sharon yace an gama shi dai yaji alert gobe zaiji cikakken bayani akan description din gidan Washegari kuwa ya turawa Sharon kudi
Karfe Hudu na yamma Sharon ya mishi sending description na gidan Alhaji Buba mai gwala gwalai Murmushin nassara Alhaji Bala yayi ya dauki wayarsa ya kira Killer
A lokacin duk suna zaune awanan katon palon har da Akram dake zaune acan gefe yana Dane Dane akan karamar wayarsa amma duk abinda su Killer suke yana kallonsu jin da Alhaji Bala suke waya yasa ya nutsu tare da baza kunnunwansa dan yaji mai yake cewa dan
kaf a cikinsu da Killer kawai Alhaji Bala yafi yin waya
Bayan minti Biyar Killer ya katse wayar yana murmushi ya kalli su lion da hankalinsu gabadaya yake kanshi ciki kuwa har da Akram yace musu
“Oga ne ya kirani yace gobe mu shirya da sassafe mu tafi kano mu sauka a gidansa na can dan karfe dayan dare zamu tafi operation gidan Alhaji Buba mai gwalagwalai yace akwai shegun idan ba’ayi wasa ba dukan mu sai mun samu one one million dan 3 gobe yake kai kudin cinkinsa gida kafin ya kai banki” Wani ihu su Lion suka saka Akram shima ya wayance yana ihun murna
Nan da nan kowa ya hau Iissafin abinda zai yi idan million d”aya ta shigo hannunsa ciki kuwa har da Akram dake lissafi awayar shi na karya nan kuwa text message ya turawa Ogan shi akan gidan da zasu je operation gobe Ogan shi kuwa yana recieving din text message d’in Akram ya tashi ya hada kan yaransa guda biyu suka dauki hanyar gidan Alhaji Buba mai gwala gwalai dan sananne ne
Suna parking d’in motarsu motar Alhaji Buba mai gwala gwalai na shawo kwana da wani mota a biye dashi abayansa da excort d’in motar ‘yan sanda sabida kud’in da suka d’auko A lokacin da Abdullahi yayi wa Alhaji buba mai gwala gwalai bayani jikinsa ne ya hau rawa zufa suka hau keto mishi
Kwantar mishi da hankali sukayi suka ce su dai bukatarsu ya d”ebi iyalinsa da dukiyarsa su bar gidan duk wani Abu da yasan mai Mahimmanci ne ya kwashe yabar komai a hanunsu
Jikin Alhaji Buba mai gwala gwalai na rawa yace musu ko dai subar garin Abdullahi yace aaa ya dai samu wani wajen ba sai ya bar garin ba kar ya damu he is save A takaice a Daren Alhaji Buba mai Gwala gwalai suka bar gidan da iyalinsa da dukiyoyinsa
suka koma wani gidansa dake can wajen gari har da ‘yan sanda biyu masu gadin shi Babu komai a gidan daya wuce furnitures da kayan kallo
Alhaji Bala kuwa Allah Allah yake gari ya waye ya d’auki hanyar kano dan yasan account
dinsa zai cika da kud’i kuma Alhaji Buba mai gwala gwalai yana da lafiyayyun abinci masu
numfashi da zaici ya koshi
Tunda Asuba Alhaji Bala ya dau hanyar kano A lokaci guda suka isa kano dasu Killer
Sai da suka ci suka sha suka huta ya kalli Akram fuska a daure yafara magana yana “Akram a yau kai zaka zama oga awajen operation din da zamuyi ayau sai kaci abinci dole duk Wanda yayi mana gardama inaso ka sheka shi har lahira abaya nayi tolerating din ka not any more yanzu Dole ka ringa participating idan muka fita operation kaji ko baka ji ba” Akram da sauri ya gyada masa kai yana “insha Allah”
Alhaji Bala kuwa yayi tsaki ya kwanta yana hararo yanda zai huta ajikin ‘yayan Alhaji Buba
mai gwala gwalai Karfe dayan dare dot suka dira cikin gidan kasancewar Alhaji Bala yasan description din gidan shine agaba yana leading dinsu Akram kuma yana biye dashi da wani dogon bindiga
a hanun shi sai zare ido yake alamar no mercy Majestically Alhaji Bala ya zauna akan dirka dirkan kujerun dake girke a palon ya dora kafa daya akan daya yana girgizawa tare da karewa palon kallo su lion kuwa tuni suka raba
Kansu dan su taso mutanen gidan ciki kuwa har da Akram dake ta Abu azafafe kamar
Hmm