BA SONTA BAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 10 BY AUTAR MANYA

Kwanci tashi asarar mai rai tafiya na tafiya shekaru suna ja.
Yanzu haka ummul takai shekaru goma a duniya sadiya tara kausar takwas ihsan mai bakwai.
Abubuwan rayuwa sun ƙara kacamewa sabida yanayin da ake fama dashi na tsadar rayuwa, Yanzu gyaɗa Bamu take kasama ummul a bakin layi ta saida to kuma kusan koda yaushe ta kasa mata gyaɗar ita keda asara sabida ummul irin yaran nan ne masu shegen sanyi tana kai gyaɗar yaran layin ke mata wayo su cinye wani bin sadiya ke ƙwatar ta ga hajja na masifar son ta amman tsabar ƙulaƙucin uwa ya hanata zaman gidan hajja kullum tana manne da mahaifiyarta.
Ranar wata talata da daddare wata maƙociyar su mai suna talatu ta shigo gidan siyan awara wadda ummah keyi da daddare zuwanta keda wuya ta tarar da baba ya dasa kujera yana danna cin mutunci wa ummah wadda ta sunkuyar da kanta tana kuka.
Seda ya ƙare cin zarafin sa sannan ya kaɗa rigarsa ya tafi.
Daya ke shi haka yake muddin yana faɗa wa iyalansa ko baƙo ne ze shigo gidan bafa ze fasa tashin hankalin daya ke ba haka ze gama ya tashi ya barka da jin kunya.
Kallon ummah talatu tayi tare da cewa.
“Wai daman hadiza har yanzu malam habu bai dena wannan faɗan nashi ba?”
Share hawaye ummah tayi tare da cewa.
“Kedai bari talatu wallahi kullum halin malam sake ƙaruwa yake, masifar yau da ban ta gobe daban yanzu ma akan yace na bashi rancen naira ɗari ne dan na hanashi yake min wannan cin zarafin to adashi ne rancen malam wanda ba’a ɗauka ɗari hamsin nidai ya ranta yafi sau a ƙirga”
Tafaɗa cikin takaici.
Muskutawa talatu tayi tare da cewa.
“Ai mutane ke ɗorawa kansu masifar rayuwa tun farko malam habu bai da ƙarfi amman yasan ya masifar ƙara aure azuciyarsa wannan ma ya zama cutar da kai da kuma mugunta kai baka iya riƙe kan kaba ina ga mata har biyu ga yara yanzu kaf unguwa yi ake dashi ga masifa yayita zagin ƴaƴan mutane ya koma kamar taɓaɓɓe kai naka yaran babu arabi bare boko”
Talatu ta faɗa tare da ɓallo goro ta garza.
“Kedai bari kawai talatu, ai duk wanda baiji bari ba yaji hoho! inji bahaushe ada ai na ɗaga hankalina daya auro ta amman dana gane idan tazo ma ƴar gusau zata ci yasa na saki raina ai seda wadata kake kishi talatu a kullum na kwanta tunani na ɗaya a abun da zamuci da yaran nan ita kuwa haka zakiji cikin dare yaran na kukan yunwa idan tace babu se suce abasu babun suci waccan tsohuwar ke taimakon ta yau da gobe se Allah itama yanzu ba koda yau sheba”
Hadiza takai maganar da ƙarfi abinka da bebe.
Gyara zama talatu tayi cike da tausayawa tace.
“Amman hadiza kema da laifin ki tayaya naki ƴaƴan zasu ci su sha na kishiyarki suna kukan yunwa har kina bada labari cike da nishaɗi”
Talatu ta faɗa cike da rashin jin daɗi.
“Kinga talatu daya tashi ƙara auren nina ce ya ƙaro? jaraba dai irin ta namiji yawanci talakawan maza sunfi masu kuɗi jarabar son ƙara aure kana tare da matarka ɗaya ta rufin asiri ka tashi ka ƙaƙabo auren da baka da yadda zakai dashi”
Ummah ta faɗa tare da miƙewa dan ƙara zuba awarar ta a kasko.

“Haka ne hadiza sedai idan anduba ƙaddara da rabo sune lin zamin komai auren malam habu ƙaddara ce daga Allah kuma ina za’a kai waɗannan kyawawan ƴaƴan data haifa?”
Aifa jin wannan furuci yasa ummah ta fara zazzagawa talatu masifa abin ka dama da kurma ganin tana neman tara mata mutane yasa talatu tayi saurin tashi ta nufi ƙofar ɗakin hassana.
Lokacin hassana tana bawa ihsan koko wadda take ta kukan zazzaɓin daya kamata sedai rashi yasa ba’a sayo mata magani ba.

Sadiya da kausar da ummul sukuma suna cin tuwo wanda nan ma dambe suke har sadiya ta danne ummul tana ƙwaƙwular na hannunta daya ke tafita ƙarfi.
Cikin tausayawa talatu ta dubi hassana tare da cewa.
“Sannu maman kausar Allah ya kawo muku ɗauki”
Share hawaye hassana tayi tare da sakin murmushi taɗan dafe cikinta bata ce komai ba sabida yunwar data keji amman sabida yaranta basu ciba yasa ita ta haƙura ta tura musu guntun tuwon ranar da akai agidan wanda ya samu da ƙyar ya kawo rabin kwanon gari.
“Bata jin daɗi ne naga tana ta nishi?”
Talatu ta faɗa tare da taɓa jikin ihsan.
“Eh bata jin daɗi wallahi zazzaɓi ke damun ta”
Cewar hassana tare da janyo ihsan jikinta sosai.
“Zo nan ummi zokije shagon sabo ki sayo maku garin kwaki da sugar sekije wajan wancan mai allurar ki siyo mata maganin zazzaɓi”
Talatu ta faɗa tare da zaro ɗari biyu daga haɓar zaninta.
“A,a sedai sadiya ummi sanyin ta yayi yawa”
Cewar hassana tana sakin murmushi.
Tura baki ummul tayi sega hawaye yana zubo mata, Amman sabida rashin maganar ta setai shuru.
Godiya hassana tayiwa talatu kamar zata ari baki har seda talatu taji nauyi.
Bayan fitar sadiya talatu ta dubi hassana tare da cewa.
“Hassana yanzu rayuwa ta sauya munafurci yayiwa mutane yawa su bazasu taimaka maka da ƙwandala ba amman zasuyi cinikin gulmarka na dubu, Ni kin ganni nan bana jin kunyar nema kuma bana munafurcin wani abayan idanun sa kowa gulmarki yake a unguwar nan na yadda kika saki ƴaƴanki ba arabi ba boko dai dai da ummi bata saka pant sabida talauci, kuma su bazasu taso su gaya miki gaskiya ba sabida tsoron masifar bebiyar kishiyar ki”
Kuka hassana ta sanya tare da cewa.
“To talatu yaya zanyi tunda nazo garin nan bani da kowa bana hulɗa da kowa sabida gudun zuciya, Waccan tsohuwar hajja ke taimakona nikam har na gaji da hidimarta garemu,Mijina babu ta sanya shi ya zama mafaɗacin ƙarfi da yaji iyayena babu rai bare su taimaka min hussainata iyali sun mata yawa ga rasuwar mijinta to yaya zanyi da raina ƴar gyaɗar idan na soya babansu ya rance kuɗin nayi magana ya zageni tass”
Tafaɗa tare da fashewa da kuka!
Da sauri ummul ta zo ta rungumeta tana share mata hawayen ta cikin ƙuruciya take cewa.
“Ki dena kuka bamu inna girma zan siya miki mota na kaiki makka amman bani bawa baba mai miki faɗa”
( hattara iyaye maza masu cin mutunci uwa a gaban ƴaƴanta wallahi ku sani komai kayi yaro yana ƙullace da abin aran shi )
Tsananin tausayin su ya sanya talatu hawaye!
Cikin damuwa talatu tacewa hassana………

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE