BA SONTA NAKE BA TAUSAYI CHAPTER 34

“Abba akwai wata”
Seyay shuru yana faman jan gemunsa yana murmushi yaƙi cigaba da sauran maganar.
Tsira masa ido Abba yayi cike da ganɗokin son yaji me zece masa sedai shikam Aliyu yayi gum ya kasa ƙarasa abin da ze faɗi ɗin.
“Muna jinka wannan wani irin haline Baffa tayaya zaka tsaida mu? muna magana dakai kaja baki kayi gum”
Ammi ta faɗa tana kallonsa.
Dariya ya saki kaɗan yana ƙoƙarin miƙewa ammi ta jefo masa filon kujera tace.
“Karka tashi baffa Allah ka tashi ranka zeyi mugun ɓaci”
Ammi ta faɗa tana kallonshi.
Harara ya ɓallawa su hassana waɗanda suka zuba mashi ido ganin kallon dayay musu yasa sukai wuff suka bar falon sukai cikin ɗakunan su.
Komawa yayi ya zauna kansa a ƙasa har yanzu ya kuma kasa magana kasancewar sa namiji mai tsananin alkunya.
Da zurfin ciki duk abin da kaga ya buɗi baki yayi magana akansa tofa abun mahimmi ne Aliyu akwai tsabar zurfin ciki da kunyar tsiya.
Gyaran Murya! Abba yayi cike da dattako cikin zuciyar shi kuma murna ce fal na yadda ubangiji ya amsa musu addu’arsu ya karkato musu da hankalin ɗan nasu.
Sannan Abba yace.
“Muna jinka Baffa faɗa min gani ga Ammi ko ta samu ne?”
Abba ya faɗa da barkwancin shi wanda yakewa dukkan yaranshi sabida Abba idan yana wa ƴaƴansa magana bakace mahaifinsu bane sabida yadda yake sakewa dasu sosai yake basu mahimmancin su wasa da dariya mai tsafta wanda babu raini acikinsa haka zalika Ammi waɗanda suka mayarta kamar kakarsu dan tsabar yadda take jansu ajiki.
Wannan ɗabi’a ta su Ammi da Abba tajanyo shaƙuwa mai yawa a tsakaninsu da ƴaƴansu wadda takai gaba ɗayansu basa iya ɓoyewa mahaifan nasu komai kuma duk abin da ya faru zasu masu addu’a ko shawara hatta su anty jidda da sarat dake aure a katsina suna jin ɓurin zasu kira abba ko ammi su gayawa ɗabi’ar jan ɗa ajiki ba ƙaramin alfanu take janyo wa ba domin sosai su Ammi suke da fahimta mai kyau a tsakanin su da ƴaƴan su.

Dai dai ta nutsuwar sa yayi tare da kallon ƙasan carfet yana wasa da azurfar hannun shi cikin nutsuwa yace.
“Akwai wata yarinya anan maƙotan hajja sunanta ummi khairy but abba ina jin tausayinta sosai sabida ƙaddarar data sameta…………………….”
Ya kwashe labarin ummul ya shaidawa mahaifan shi sedai me? ya tsinci bakinsa da rufawa ummul asirin cewar A hotel ya ganta da kuma cewar a gidan karuwai ta zauna bayan korar da mahaifinta yayi mata sam ya kasa bayyanawa mahaifansa wannan maganar dama kuma ya kwaɓi hajja.

Sannan ya cigaba.
“Tana zaune a wajan hajja fa har zuwa wannan lokaci Abba ban taɓa ganin uba irin nata ba wai daman akwai mahaifa irin su? duk girman ƙaddarar yarinyar ya kasa amsa sema korar ta dayay daga gidan yanzu bada ban hajja ba da ina zata wace rayuwa zata faɗa?”
Yafaɗa idanunshi jajir cike da ɓacin rai.
Tagumi Ammi tayi tsigar jikinta na miƙewa duk da bata da labarin yarinyar a wajan hajja kuma bata santa ba kasancewar bata yawan zuwa gidan hajja ɗin in tana son ganinta Aliyu ke zuwa kano ya ɗaukota ko a tura draver ya ɗaukota.
Tai kwanakin ta ta koma Amman wannan labari ya girgiza Ammi a matsayinta na cikakkiyar uwa! kawai ayyanawa take yaya mahaifiyar yarinyar zataji ƴarka tun tana shekara goma sha biyar ai mata fyaɗe kuma baka da kuɗin da zakaja shari’a da waɗanda sukai matan saboda suna da hannu da shuni.

Muryar Abba ce ta katse mata tunanin inda yake ta jan salati murya cike da ɓacin rai matiƙa yake furta.
“Ka tambayi Baban shin ɗan uban waye daze mata haka( daya ke sunan da yake gayawa hajja kenan baba) ka tambaya min sunan ubansa a kano na rantse da Allah ko dukiyata zata ƙare sena makasu a kotu kuma kai zaka tsaya mata ka karɓa mata hakkinta ina son wannan ya zama darasi ga masu halin akuyoyi irinsu ai in baka da kuɗi ba yana nufin baka da rayuwa ba! Abu na gaba kuma kai Aliyu zakaje ka nemi auren ta wannan babban jahadi ne sabida a rage mata zugi da zafin tunanin ƙaddarar data sameta tunda har baba ta ɗauketa ta riƙeta na tabbata mai tarbiya ce ƙaddara ce ta faɗa mata sabida haka ni zan tura iyayenka wajan sakaran ubanta sune maka auren ta ina son na inganta mata rayuwarta yadda zata zama fitila ga Baƙin mahaifinta wanda ko a tarihi ban taɓa ganin mutum kamar shi ba marar imani da tausayi”!!!

Tunda Abba ya ambaci ya aureta jikinsa yayi sanyi gumi ya wanke mai fuskar sa sabida ko a lissafi bai kawo wannan ba shiyasa ma ya kauce da maganar ya soko musu tarihinta sabida yana da tabbacin Abba ze magantu akan lamarin.
A nufinsa dama ko Abba zece ya ɗaukota ta dawo gaban Ammi idan yaso shize ɗauki nauyin karatunta da komanta harta kammala ta sami miji tai aure.
Domin shi a lissafin sa babu auren ta yadai gayawa hajja ze auren ne domin su rabu lafiya ita kanta yana binta ne dato harya samu ya kammala da fahimtar dasu abba domin yasan ya gaya mata baze aureta ba tabbas guduwa zatai daga gaban hajja.

“Ai kam seya AURE TA! Nima ina goyon bayan hakan ɗa ai na kowa ne tunda har hajja ta riƙe ƴar nan nasan tagari ce bani da hofi Allah ya tabbatar da Alheri kuma wannan maganar ta tsaya dagamu sekai ko ƴan uwanka bance ka gayawa ba”
Ammi ta faɗa cike da murna.

A karo na barkatai ya goge zufar dake karyo mai kafin murya a shaƙe yace.
“Nifa Abba Ammi wallahi BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE!”
Sannan ya ƙarasa da cewa.
“Tausayi ne yasa na sheda muku don Allah karku ce na aure ta danni bana sonta tausayin ta nake yi”
Yafaɗa kamar zeyi hauka dan takaici.
Dana sani fall a zuciyarsa na faɗawar da yayiwa mahaifan nasa dama ya sani yaja bakin sa yayi shuru.

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE