BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 15
Da sauri talatu ta amsa tare da cewa hajiya timo.
“In sha Allahu hajiya za’a kiyaye da girman kujerar ki”
Ta ƙare cike da fadan ci.
“Yanzu ameerah zata nuna miki store seki duba abin da babu kiyi list insha Allah gobe seki fara zuwa tun wuri”
Da sauri talatu tace.
“A,a hajiya karki damu inda hali ma yau zata fara yi muku na dare”
Ita talatu ta faɗa mata hakane sabida kwaɗayin ta samu na daren ita kuma hassana haushin talatu taji na yadda tace zatai zaman yin na dare sabida tabar ihsan ba lafiya sannan bata bar ko sisi agidan ba.
Murmushi hajiya timo tayi a karo na farko sannan tace.
“To babu damuwa ai mana tuwon semo miyar kuɓewa ameerah kaita kicin”
Tafaɗa cike da bada umarni babu yadda hassana ta iya haka tabi bayan ameerah amman ta dawo da baya tacewa talatu ta tafi mata da wannan taliyar gida wadda matar aikin talatu ta bata tace mata takaiwa sadiya ta girka dan sadiya tafi ummul girman jiki da komai.
Hakan akai talatu taiwa hajiya timo sallama wadda ta bata 2k ta tafi tana ta godiya.
Ita kuma hassana wata kwana suka miƙa tare da shiga cikin wani katafaren kicin wanda aka zuba kayan more rayuwa cikinsa ƙofar store ɗin ciki suka buɗe suka shiga babu abin da babu na kayan abinci dan haka ameerah tana nunawa hassana ta koma.
Kimantar sanwar tayi ta ɗora ruwan tuwon da zafin nama take haɗa kayan da zatai miya da taimakon ameerah hassana ta kunna gas ta ɗora tukunya sannan ta mayar da hankali akan haɗin miya cikin ƙwarewa da iya sarrafa girki ta soma gabatar da tuwon semo ɗin miyar kubewa wadda tunma kafin ta gama kamshi ya cika gidan na daddawa da kayan ɗanɗano
Wajan magariba ta sauke tuwon ta kwashe ma mutan gidan itama ta ɗibi nata dai dai kima
Miyar kuwa seda aka idar da sallar magariba ta sauke ta sabida yadda tabar ruwan ya ƙone miyar ta haɗe jikinta waje ɗaya.
Zuzzubawa tai a kula ta soma jigilar kaiwa daining ɗin dake falon.
Seda ta gyara kicin ɗin sannan ta ɗauki nata abinci taiwa ameerah sallama ta wuce gida domin bata ga ƙeyar mutan gidan ba.
Allah Allah take takai gida har tana tuntuɓe hankalinta yana kan yaranta
Lokacin data kai ƙofar gida malam habu na dawowa daga masallaci kirjinta ne ya buga amman seta nuna ko in kula ta cigaba da yunƙurin shiga cikin gidan.
Bata ko kalle shiba.
Sallama ɗauke a bakin ta sadiya wadda take jan ruwa a rijiya takwa saki gugan ya faɗa rijiyar duk akan murnar ganin mahaifiyar su ta amshi kayan kan bamu takai ɗaki tana ta mata sannu.
Wannan guga data faɗa rijiya ita ta haddasa masifa a gidan sabida basira ƴar hadixa zata ɗibi ruwa ta tarar da sadiya ta jefa guga nan ta hau cin mutunci har hadiza ta fito ta amshe har tana cewa bamu bata san daga inda ta fito ba kota fara yawon maula ne.
Toshe kunnen hassana tayi bama zakace akwai mutum agidan ba.
Alwala tai ta soma sallah sannan ta zaunar da yaranta tana tambayar su yaya suka wuni.
Sosai ummul take bata labarin irin yunwar da sukaji amman da kausar taje wajan babansu akan ya basu kuɗi su sai gari seya korota
Rufe kausar bamu tai da faɗa tana cewa bata yarda ta ƙara zuwa wajan babansu karɓar kuɗi ba tunda tasan baze basu ba
Suna idar da sallar isha’i suka ci tuwon su suka ƙoshi wannan 3k ɗin da matar aikin talatu ta bata ita ta ƙulle ta saka yaran agaba ta kaisu makarantar islamiyya ta dare gaba ɗaya a aji ɗaya aka sanya su sabida rashin ilimin da tun farko basu dashi aikwa nan ƴan aji suka fara yi masu dariya daya ke sadiya ba ƙyalle bace yasa tai musu tass nan yaran suka lafa musu.
Koda aka tashi daga makaranta suka kamo hanyar gida kuma a daren sukaita bitar karatun su, hadiza kuwa seta sami na yada habaici a tsakar gida lallai kishi kishine yana ƙoƙon zuci domin wannan ɗan sauyin da hassana ta samu se hadiza kuma ta kwana tana zubda magana a tsakar gida.
Haka garin Allah ya waye hassana ta jera yaranta agaba zuwa wata makarantar gwamnati dake can ƙasansu tunda duk sun isa zuwa hatta ihsan mai shekara bakwai.
Wajan shugaban makarantar taje tai masa bayani akan cewar zata sanya ƴaƴanta a makaranta amman yayi mata haƙurin uniform se ƙarshen wata.
Da tausayawa yace ai babu damar ɗalibi yazo makaranta babu uniform dan haka karta damu akwai daman uniform ɗin da wata ƙungiyar tallafawa marayu take aiko musu dashi duk ze basu godiya tai masa sosai a wannan rana su ummul suka shiga aji wanda ita aka kaita uku sadiya biyu kausar da ihsan ɗaya kuma babu laifi sun ɗan taɓa karatu tunda suna ji daman wajan su sakina suna biyawa a gadarance.
Daga makarantar yaran gidan aikinta ta wuce koda taje taɗan makara anan ta gamu da wata tsagerar yarinya mai suna mima
Sosai ta tsare hassana tana mata masifa akan ta shanyasu batai musu break fast da wuri ba wadda yarinyar a haife bata fi sa’ar sadiya ba.
Tuno gargadin hajjiya timo yasanya ta ƙasƙantar da kanta tana bawa ƴar cikin nata haƙuri wadda take kamar ana tunzurata.
Dama wasu ƴaƴan masu kuɗin suna da haka suna jin feeling iyayen su nada shi zazu taka kowa bare su da aka ɗaure musu gindi.
Da rawar jiki hassana ta ƙarasa kicin agaggauce tai musu abin kari sedai koda taje kai musu, watso mata wani saurayi yayi a fuska yana taɓe baki tare da cewa ya bata minti goma ta sako masa da wanda ya gaya mata a lokacin.
Cikin ɗumbin mamakin rashin kunya da tarbiyar yaran hassana ta juya zata koma dan tai mai abin da yace ɗin
Tsawa ya daka mata akan tazo ta kwashe wanda ta zubda haka ta rissunawa ƴaƴan agabansu ta kwashe ta nufi kicin.
Ranar dai hassana wunin sauke ɗora tai kuma dan iskanci baifi suyi loma biyu ba zasu ce tazo ta ɗauke kwanikan ameerah ce tace ta samu katuwar kula tana juyewa ta tafi dashi gida in ba haka bama ashara za,a zubar.
Ranar ma hassana bata koma gida ba se bayan magariba
Koda taje yaranta sunyi girkin su da wannan taliyar sunci sun wuce islamiyya ga kayan bokon sunan a ninke tsaf.
Ɗaga hannu tai tana kwarara yabo da godiya ga sarki Allah abisa canjin daya kawo musu ko a haka ma tana godiya gare shi ta fita ta dawo ta tarar da ƴaƴanta sun tafi makaranta kuma sun sami abin taɓawa lallai taji daɗin wannan canji data samu.
Alwala ta fita tayo itama ta tayar da sallah se lokacin ta sami nutsuwar cin abincin ta.
*Uwa kenan! innah uwa mafi uba koda uban yayi sarki ina miƙa gaisuwa ta ga duk wata macen data amsa suna na uwa mai tarbiya da sadaukar wa domin inganta rayuwar ƴaƴan ta* 😭😭😭😭