BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 18 BY AUTAR MANYA

Alhaji Ali Dikko…………..
Haifaffen Jahar katsina ɗane a wajan malam muhammad Asalin dikkon da yake amfani da ita laƙanine na jaharsa.
Alhaji Ali shine ɗa na huɗu kuma ƙarami a wajan mahaifin shi malam muhammad da mahaifiyar shi saratu akwai Yayyinsa, Abubakar se usman se umar se shi Ali.
Allah bai sa saratu mahaifiyar su ta taɓa haihuwar mace ba sun taso cikin rufin asirin Allah amman dai baza’ace musu masu kuɗi ba sedai agidan malam muhammad akwai cida sha da suttura.
Sunyi karatun Arabic dana boko sedai na boko bamai zurfiba ne iyakacin su abubakar diploma se suka, koma kasuwa wajan mahaifin su wanda yake kasuwar dabbobi yana saida wa.
Shikuma Ali ya sami damar haɗa digree ɗinsa, sedai halin da rayuwar tamu ke ciki da kuma yadda ƙasar tamu ta zama na se kana da wane kasan wane zaka sami aiki yasa Ali Ya Faɗa harkar gine gine shi bai je kasuwa ba kwangila yake amsa ta gini idan ya kammala sedai ya baka makullin gidan ka, Da wannan sana’a ya samu ɗaukaka sosai sunan shi yakai inda bai tunani ba yana karɓar ginin shaguna tafi tafi har makarantu duk yana ginawa wanda ya sami hanyar amsar ginin makarantun gwamnati daga wajan wani abokinsa daga haka arziki da sauyin rayuwa ya fara zuwar musu

Lokaci Ɗaya Abubakar da usman da umar sukai aure kuma a shekarar da sukai aure Allah yayiwa mahaifin su rasuwa.
Sosai ahalin suka shiga halin jimamin rashin.
Komai yana tafiya yadda ya kamata dan su kansu su Abubakar suna samu sosai da harkokin su haka zalika shima Ali yana samu atashi sana’ar lokacin dayakai minzalin aure mahaifiyar shi ta takura akan seya fidda matar aure koda a dangin sune sedai kawai yayi murmushi batare daya bawa maganar mahimmanci ba, Ahaka Allah ya cillashi kano yin wani ginin kamfani wanda ya sami kwangilar shi anan Allah ya haɗashi da Hafsatu ɗiyar hajja yabawa da halinta na kirki da nutsuwa da tarbiya yasa yay sha’awar auren ta hafsatu ita kaɗai ce wajan mahaifiyarta da mahaifinta wanda tun tana karama ma mahaifin nata ya rasu,Ali bai bar kano ba seda yaje wajan kanin mahaifin hafsatu lokacin yana raye yayi tambaya akan yana son auren ta babu wata matsala kanin mahaifin hafsatu ya aminta da Ali wanda shikuma bayan ya gama aikin daya kawoshi ya koma katsina anan yake shaidawa mahaifiyar shi ya sami macen aure babu jimawa su Abubakar sukaje kano nemawa ƙaninsu auren hafsatu wanda ba’a wani saka lokaci mai tsahoba akasha biki hafsat ta tare gidan mijinta anan kusa da yayinsa inda mahaifinsu ya saya musu ƙaton fili yace kowa inze aure ya yanka ya gina domin baya son su rabu da junansu.
Zaman hafsatu da matan yayin ta se son barka domin kansu ya haɗu babu gulma bar munafurci sannan yaransu na xuwa gidan hafsatu su wuni dayake ko wanne ya haifi ɗa ɗaya a lokacin kuma maza ne .
Rayuwar zuri’ar gwanin shawa’a sabida haɗin kai gakuma ilimi da iyayensu suka tsaya musu akai.
Sannu Ahankali Ali ya soma fita aiki abuja na wasu gidaje da gwamnatin taraiya take ginawa na ma’aikata duba ƙwazo da nagartar aikinsa yasa gwamnatin dake ci a wannan lokacin take yawan bashi gayyatar gine gine ahankali Alhaji Ali dikko ya tattara ya koma abuja da zama shida hafsa mai tsohon ciki a gidan haya ya soma zama kafin komai ya dai daita masa.

Ba jimawa hafsatu ta haihu inda ta sami ƴa mace aka sanya mata sunan hajja hauwa’u ( jidda) farin ciki a wannan family kamar me wanda jidda nada kwanaki 40 hafsat tazo ganin ƴan uwa Allah yayiwa maman Ali rasuwa mutuwar data girgiza wannan Alhali.
Sannu Ahankali Ali ya fara rushe gidajen yayinsa ya haɗe dana mahaifiyarsa dana sa ya soma gina musu ƙaton gida mai sassa da dama domin iyalansu daga can abujan ma harya buɗe office ya zuba ma’aikata sabida masu zuwa neman yayi musu aiki sannan a hankali ya fara ginin gidansa anan wata anguwa mai suna gwarinfa.
Gida mai kyau ya gina wadatacce, Daga ɓangaren nasu ma ya gina musu katon gida mai uban girma harda B.q domin ƴaƴa yensu sannan akwai ɓangaren maza sannu ahankali rayuwa na tafiya matan su abubakar na haihuwa inda ayanzu ko wannen su yana da ƴaƴa 2 mata da maza lokacin Allah ya kuma bawa hafsat ciki bayan wata tara ta haifi ɗanta ƙato kyakykyawan gaske ranar suna Ali ya mayar da sunan shi Aliyu wanda ake ce masa baffa.
Kusan a tare hafsa suka haihu da matar Kawu usman yayan Abban Aliyu Sedai Matar kawu usman ta bawa hafsa kwana uku kuma ita namiji ta haifa wanda yaci sunan muhammad amman ana ce masa baba karami.
Sannu ahankali rayuwa na tafiya shekaru na tafiya an saka Aliyu da jidda makaranta anan abuja in akai hutu Abba ya turo su katsina har ammi anan ɓangaren su zasuyi hutu su koma Aliyu bai da wani Aboki se Baba Karami, ɗan wajan kawu usman wanda suka taso kusan a tare ragowar kuma sun girmesu shiyasa su biyun suka kulle suka xama kamar uwa ɗaya uba ɗaya.

Seda Aliyu yayi kusan shekaru goma aduniya sannan ammi ta sake haifar wata macen Sarat daga sarat ta haifi shafa daga shafa ta haifi ƴan biyu hassana da hussaina waɗan da daga kansu kuma bata kara haihuwa ba ƴaƴanta shidda namiji ɗaya mata biyar, lokacin rayuwa ta sauya Tuni Alhaji Ali ya zama mai kuɗin gaske yasan manya sosai, Zuri’a kuwa tana ta ƙaruwa, ƴaƴan kawu abubakar 12 ƴaƴan kawu usman 9 ƴaƴan kawu umar 13 ƴaƴan abba ne shidda sune marasa yawa sabida shi ne bai kara aure ba amman su kowanne ya ƙara aure matan su bib biyu.

Wannan tasa wannan zuri’ar take ɗan ƙullah auren zumunci sedai su basu hana AUREN BARE ba in kana da taka a waje ka auro in kuma kana son ta gida ka aura yanzu haka jidda yayar Aliyu tana auren ɗan gidan kawu Abubakar mai suna yaya Hamza haka auratayyar take kulluwa.
Suma sauran yawanci suna auren junansu ne.
Shima baba karami ya sami aikin banki tuni bayan ya gama karatun sa inda ya auri sarat kanwar Aliyu wanda shi har wannan lokutan baida niyyar aure har seda Kawu usman yace ko rokiya za’ayi masa sedai yanayin karatunsa yasa suka hakura domin karatu yake mai matikar wahala na low.
Ya sami karatun addini mai zurfi dana boko Ali yana ɗaya daga cikin mutane masu ƙwaƙwalwa ko laifi kayi daga kwayar idanunka ze fahimta yana da sanyin hali ma’ana hali mai kyau yana da son mahaifan sa tare dayi musu biyayya bai da magana sosai yana da miskilanci yana da yawan ibada sannan yana da son ƙwallon ƙafa.
Ya kammala karatunsa na digree da master tare da phd ɗinsa duk a harkan low inda ya fito a ƙwararren lauya mai zaman kansa barrister Aliyu Ali dikko,ya soma aiki da wani alkali anan cikin garin abuja wanda seda ya sami gogewa ta tsayin shekara sannan ya sami damar buɗe nasa katafaren office ɗin sabida kowa yasan lauya mai zaman kansa bai da haɗi da gwamnati shi aiki yake da ƙashin kansa wanda in kana da wani case zaka iya ɗaukar sa amman case ɗin da bai shafi under criminal case ba domin kowa yasan criminal case yana under lauyoyin gwamnati ne sedai inma lauya mai zaman kansa ze ɗauki ragamar criminal case tofa dole seyaje wajan antomy general na hight coaut yay taking wannan case to kansa sannan ƙarar zata dawo hannunsa su yawanci lauyoyi masu zaman kansu daman sunfi tsayawa masu kuɗi case ko kamfanin nika da sauran su.

Lauyoyin gwamnati kuma suna tsaya wa akan criminal case misali kisan kai.
To duk wanda aka kashewa ɗan uwa toba case ɗin sa bane na gwamnati ne don gwamnati ce zatai taking case ɗin to coart sannan ta ɗauki lauya daga cikin lauyoyinta.
Wannan kenan

Zuri’ar su Aliyu ƴan boko ne domin ko wanne yana da rufin asirin sa sedai babu wanda ya gaji mahaifin shi don duk suna aikin gwamnati ne kama daga nurse’s bankers lawyers police t.c.e dan hatta shafa kanwar Ali mai bin sarat likita ce kuma tana aiki anan abuja sedai har wannan lokacin batai aure ba kannen sa kuma ƴan biyu sune ke secondry school ya jidda yayarsa tana aiki anan wata babbar secondry a cirancin katsina tunda anan mijinta yayi mata gida, sarat matar baba karami tana aiki nan ministry of agriculture Dake Local government ɗinsu.

Tuni Abba yakai ƴan uwan sa maka yakai ammi shima kansa Aliyu yaje saudi yafi sau a ƙirga haka nan ammi ta siyawa hajja gida anan tunga ta gine mata shine na kakar su ummul data rasu baban su ummul ya sayar. babu abin da hajja ta nema ta rasa komai ammi na mata ita da jikokinta.

Office ɗinsa sun je ita da mamanta akan suna buƙatar ya tsaya musu akan ƙarar da zasu shigar ta Ƙanin mahaifin basmah wanda yayi babakere da dukiyar mahaifinta sabida yana gadarar basmah kaɗai ya haifa suma suna da gado to ita maman basmah ba wannan ne ya dameta ba, Yadda ya riƙe dukiyar baki ɗaya yaƙi basu koda ƙwandala na daga cikin gadon shiya fi damun su sabida a lokacin ma bada ban aikin da basmah take na banki ba, Da basu da yadda zasuyi su samu koda abin da zasu cine.
Lokacin da sukaje office ɗinsa babu abin da basmah take se kuka! sabida yadda rayuwar ta isheta komai ya tsaya musu cak kamar ba mahaifinta ne ada mai shagwaɓata da bata kulawa ba yanzu an wayi gari babu shi aduniya hatta gidan da suke ciki ya soma mutuwa sabida rashin wadata.
Sosai Aliyu ya tausaya musu harga Allah ya tsaya musu ne ba domin su biyashi ba domin basu da kuɗin da zasu iya ɗaukar shi a wannan lokacin ataƙaice maman basmah ta yi mai bayani akan tarihin su.

Mu ƴan asalin garin naija ne aiki ya kawo mijina nan abuja muna zaune anan gwarinfa( kusa dasu Aliyu ma kenan)mijina yana sona kamar yadda nake son shi muna zaune lafiya cikin soda kaunar juna sedai Allah baisa na haihu ba hakan tasa ƙanin mijina dake nan kusa damu shima yana aiki a wani kamfani ya takura mini har yake haɗani da sauran ƴan uwan shi akan se lallai Abban basmah ya ƙara aure kwatsam se Allah ya bani ciki na haifi yarinyata gata nan basmah  munyi farin ciki matika haka na zage ina bata kulawa har takai mun sakata a makaranta bayan tai candy taje kano gidan kanwata ta shiga university ta nan bayero bayan ta kammala ta dawo gida mahaifinta ya sama mata aiki a bankin dayayi ritaya fara aikinta da wata biyu Allah yayi masa rasuwa muka tarkata naija anan aka masa suttura bayan bakwai muka dawo gida dayake duk kaddarar sa,Baya neman shawarata akai se shawarar ƙaninsa yasa ka ƙanin nashi yaƙi bamu hakkin mu hatta abin da zamuci se basmah tai albashi take siyo mana.
Tafaɗa tana gursheƙen kuka.
Sosai zuciyar Aliyu ta karye ya dinga bata haƙuri tare dayi mata alkawarin zeyi iya yinsa wajan ƙwatar mata hakkinta dana ƴarta.
Yayi ƴan rubuce rubuce ya ce musu suje ze nemi mutumin.
Bayan kwana biyu Aliyu ya kammala shari’ar dake gaban sa yabi adireshin gidan ƙanin mahaifin basmah mamaki sosai Aliyu yayi na yadda yaga mutumin dattijo mai kirki da dattako a kunyace suka gaisa mutumin ya kawo kujera fara ta roba suka gaisa.
Rasa yadda zeyi yayi masa magana yayi sabida kwarjinin da mutumin yayi masa.
A dake ya ɗauko farar takarda tare da Id card na shaidar cikakken lauya mai zaman kansa ya nuna wa kawun basmah tare da cewa.
“Cikin kwana ki biyu da suka wuce matar ɗan uwanka marigayi Alhaji Muktar ta kawo ƙarar ka akan tana son na shigar da ƙarar ka kotu na kacinye musu dukiya ita da ƴarta shin haka ne?”
Aliyu ya faɗa cikin sigar tambaya irin ta lauyoyi.
Murmushi dattijon ya saki babu wata fargaba yace.
“Au ta nan kuma hajiya binta ta ɓullo mini to samari ban hanaka kai ƙarata ba amman bara kaji wata magana hajiya binta matar ɗan uwana ce amman ko a ƙiyama bana fatan Allah ya haɗa mutum da mace irinta mace ce mai muguwar kirsa seda ta rabashi da iyayen sa hatta mahaifiyar mu ranar da zata rasu kuka take tana akira mata muktar amman bai zoba, A takaice binta seda ta sanya muktar ya rubuta sunanta dana ƴarta akan dukkan kaddararsa wallahi dai dai da farcen susa bai bari da sunan mu ƴan uwansa mu gada ba se wannan gidan dana ke ciki wanda shiya bani da kansa amman matar nan kullum idanunta akan gidan nan yake wanda hakan yasa take min barazana akan seta makani hukuma an basu saboda malamai da ƴan tsubbu sun cinye mata dukkan kaddarar data ke da ita a yanzu haka basu da komai se gidan su hajiya binta macen kirsa sunan ta kafi asiri illa data haɗa da asirin kuma tafi bom bala’i”
Dattijon ya faɗa cike da takaici.
“Burinta kullum na tashi daga wannan gida wanda shedu suka shaida muktar ya bani shi duniya da lahira na tashi na bar musu sabida bata ƙaunar kowa a ƴan uwan muntari hatta ƴarta bata nuna mata dangin mahaifinta ba”
Sosai jikin Aliyu yayi sanyi amman bai nuna wa wannan dattijon ba sema basa hannu daya yi sukai musabaha ya tashi ya tafi ko agida tunanin lamarin yake ya kasa tan tance mai gaskiya acikinsu musamman yadda matar take kuka sedai fuskar dattijo mai haiba da kamala batai masa kama.data makaryaci ba.

Bayan kwana biyu suka sake komawa office ɗin Aliyu kamar yadda yace yana buƙatar hakan wannan karon basma tai kwalliya ta baɗa turare mai masifar ƙamshi domin tunda ta koma gida take kuka akan tana son Aliyu bare data ga tsantsar kyawun da Allah ya bashi nan fa hajjiya binta aka nausa kauyen sileja wajan malaminta ta karbowa ƴarta sa’a domin itama tace ta hango hutu alherine ya kaisu office ɗinsa malamin daya bawa hajiya binta tabbacin da zarar Aliyu ya shaki kamshin angama magana wannan yasa hajja binta bawa ƴar turaren takwa makashi gaba ɗaya ya game jikinta.

Zaune suke saman banci wanda masu tsaron office ɗin suka tanadawa masu son ganin Aliyu wajan karfe goma ya ƙaraso da sauri ɗaya daga cikin ma’aikatan ya je da sauri ya amshi jakar hannunsa seda ya kammala shirinsa sannan ya umarci da a shigo dasu ciki.
Yau sabida sauri ko azkar ɗin asubahi baiyi ba wata shari’a ya gabatar har guda biyu da sassafen nan yanzu haka sauri yake yaɗan yi abin da zeyi Yayi break fast ya koma gida to kuma se wannan matar ta shigo office ɗin nasa.
Zaman su keda wuya yaji gaban sa yayi mummunar faɗuwa…………..

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE