BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 31 BY AUTAR MANYA
Tamkar yana kallon ta, Kuma har lokacin bata da niyyar yi mashi magana.
“To kiji ni da kyau wannan shine first and last dazan kuma ji kince zaki bar gidan hajja wallahi in ba haka ba…….”
Yaja ƙwafa kamar tana gaban shi.
“Toba kaine kace baka sona ba tausayina kake kuma koka aure ni jingine ni zakai gidan ku, Sannan kuma bana son ganin babanmu gwara nai nesa”
Maganarta yake ji mai cike da tarin ƙuruciya lumshe idanu yayi cike da kasala sannan ya kuma cewa.
“To duk ki bari na dawo semuyi magana a nutse kinga yanzu na sauka ko gida ban je ba kuma sannan ina jin yunwa ga zazzaɓi yana damuna pls karki tafi ko ina kimin alƙawari kinji?”
Yafaɗa muryar shi a tausashe.
“Nayi maka amman yaushe zaka zo?”
Rintse idanu yayi tare da cewa.
“Any time zaki iya ganina”
Yana gama gaya mata hakan ya datse kiran yana jin wani irin yanayi atare dashi.
Itama daga nata ɓarin tsalle ta doka tare da yarda wayar ta faɗa katifar hajja tana rungume pillow.
ABUJA.
Sannu a hankali yake draving harya ƙaraso ƙofar gidan ammi lokacin wajan ƙarfe bakwai na dare a hankali yayi parking motar a ƙofar gate ɗin gidan tare da kasheta kana ya fito daga cikin motar shi ilahirin jikinsa na buƙatar hutu sabida uwar tafiyar daya ciyo daga Kano zuwa abuja wadda bai taɓa yin irinta ba kasancewar yawan ci irin wannan tafiyar yafi yinta a jirgi.
Seda ya tsaya suka gaisa da mai gadi sannan ya nufi shiga ciki.
Da sallama a bakin sa cikin babban falon daya sha kayan alatun more rayuwa babu abin da ke tashi se sautin ƙira’ar sheik Abdurrahaman sudais a tashar saudi arabi’a dake cikin ƙatuwar Plasma tv’n dake manne da bangon falon.
Macece mai kimanin shekaru hamsin aduniya fara jajir mai cike da kamala tare da haiba zaune a saman darduma hannunta ɗauke da littafin hisunul musulim tana bitar addu’oin cikinsa dakatawa tayi da karatun tare da amsa masa sallamar shi kana ta mayar da hankalinta kan littafin hannunta seda yakai kusan mintuna biyar a zaune kafin ta shafa addu’oin sannan ta dube shi fuskarta cike da annurin murmushi wanda ya ƙi ɓoyuwa acikinta.
Sada kanshi yayi a ƙasa tare da kamo ƙafafunta yana matsa mata su kamar yadda yake mata ada.
Murya can ƙasa kamar zeyi mata kuka yace.
“Afuwan ammina dan Allah karki ce komai yau gani agaban ki a kuma shirye nake da ɗaukar dukkan hukuncin ki da kika yanken domin ina da tarin laifuka agare ki”
Yafaɗa cikin ladabi.
Murmushi ta sauke aranta tana hamdala ga sarki Allah sannan tace.
“Babu wani laifi dakai min kullum cikin albarkar mahaifa kake baffa Allah ya tsare min kai Allah ya gani kai kaɗai Allah ya bamu namiji muna buƙatar ka a kusa damu sedai…..”
Muryarta ta fara rawa.
A gigice ya ƙarasa daf da ita kamar ze koma cikinta sannan yace.
“Dan girman Allah ammi karki min kuka! abin zemin yawa na kasa gane a wace duniya nake ada kamar ina ta baccine mai tarin mafarkai marasa kan gado Don Allah ammi karki zubar min da hawayen ki masifa ne agareni”
Yafaɗa jikinsa yana rawa.
“Bazan maka kuka ba baffa nina kasance uwa mai afuwa ga ƴaƴanta sedai fa ka sani duk mai tikitin raba ɗa da mahaifi ya tanadi makomar shi”
Tafaɗa tana ƙoƙarin miƙewa da sauri ya kamo hannunta yana langwaɓar da kanshi gareta.
Shafa kanshi tai tare da cewa.
“Ina zuwa”
Mintuna kusan biyar segata ta dawo falon bayanta ma’aikatan tane mata ɗauke da kulolin abinci masu azababban kyau agaban shi sukaita jerewa suna zubewa suna gaishe shi ammi kuma wata ƙatuwar jarkar ruwa ta aje wadda ruwan tofin addu’oin Ayatul rahman ne acikinsu.
Cup ta ɗauko na glass tare da buɗe jarkar ta cukota da wannan ruwa ta miƙa masa babu musu ya amsa ya shanye tas ta kuma tuttula ta miko masa seda ya sha har sau uku sannan ta tsiyaya ta shafa mai saman kanshi har zuwa fuskar shi tana sakar masa murmushinta mai tsada.
Kular abincin ta janyo wadda tai masa tuwan shinkafa da miyar agushi data ji bushshen kifi mai yawa acikinta.
Ta ɗauko plate ta zuba mai dai dai cikinsa ta tura masa gabanshi.
Cup ta ɗauko ta zuba mai ruwan kunun ayar data yi mai tun yamma wanda yaji madara da kayan haɗi na musamman Aliyu har wani girgiza kai yake sabida santin girkin Ammin sa daya jima baici shiba.
“Ammi wallahi zaki sa cikina ya fashe”
Yafaɗa yana dariya.
Murmushi tayi kafin tai magana ƴan biyu sun shigo falon ganin su yasa yaɗan haɗe rai kaɗan kasancewar baya sakar musu fuska gudun raini.
Da murna tare da mamakin yaushe rabon daya zo musu suka zube a ƙasan carfet suna gaishe shi babu yabo ba fallasa yake amsa musu yana cigaba da kurɓar lemon ayar dake hannunshi.
Cikin haka shafa’atu tayo sallama falon hannunta ɗauke da jakarta jikinta kuma sanye da uniform daga ganin daga office take se yanzu tayi off ganinshi yasa taɗan zo da sauri bakinta ɗauke da farin ciki take furta.
“Wow suprise Big bro saukar yaushe? muda mukaji tafiyar ka wajan Yaya baba?”
Tafaɗa tana zama gefen shi.
Dayake suna shiri sosai da shafa’atu acewar sa yana jin tausayinta na yadda har yanzu batai aure ba gata kuma da haƙuri sosai akaf ƴan uwan shi yafi sakewa da ita.
“Ɗazun nan na sauka shi baba ƙaramin yake ce muku nai tafiya?”
Yafaɗa yana tsareta da girman idanuwan sa.
Dariya tai tare da kama ɗayan spoon ɗin ta saka cikin tuwon sa tahau ci cikin basar da zancen tace.
“Dama yaya kamar kasan yunwa nakeji”
Bai ce mata ƙalaba ya cigaba da shan kunun ayarshi.
Har suka kammala cin abinci kowa ya dubi familyn yasan yau ranar ta musammance musamman fuskar Ammi dataƙi ɓoyuwa da farin ciki.
Wajan ƙarfe taran dare Abbah ya shigo daya ke jiya ya dawo daga tafiya sosai suka gaisa a hankali abba yake masa nasiha tare da nuna masa mahimmancin iyaye da ƴan uwa har wajan goman dare kafin ya umarce shi akan ya tafi jikinsa duk yayi sanyi haka ya ɗauki keyn motar shi da phone ɗin ya nufi hanyar fita bayan yayi musu sallama.
Harya shiga mota yana jingina maganganun Abba har wata ƙwallar tausayin mahaifan nashi ce ta tarar masa duba yadda suke farin ciki da ganinsa.
Yana gab da shiga layinshi wayar sa ta ɗauki ringing duk ya ɗauka basmah ce wadda take ta zubo masa waya tare da uban message.
Sedai ganin numbern hajja yasa yay rejecting call ɗin duk a zaton shi itace seya kirata.
Wata sassanyar ajiyar zuciya ummul ta sauke ta kuma raɓewa ajikin pilow idanunta lumshe taƙi magana se uban saukar masa da ajiyar zuciya data ke acikin kunnen shi.
“Idan baki da abin cewa zan kashe nazo gidana kuma karki sake kirana domin matata tana da kishi……..
Da sauri ta katse shi ta hanyar ce masa.
“Dama cewa zanyi yaya jikin naka?”
Muryarta tana ɗan rawa kaɗan.
Gira yaɗan ɗage guda tare da cewa.
“Me kike yi har yanzu baki yi bacci ba salon ki makara a sallan asubahi”
Ya tsinci bakinshi da faɗa mata hakan.
“Tunanin ka nake ai sabida kace baka jin daɗi kona kwanta ma bazan iya baccin ba dan Allah karkace na dame ka yaya jikin naka”
Tafaɗa cikin wata kalar murya mai kama data mai shirin yin kuka!
Wani irin mugun tausayin tane ya tsirga masa batare daya shirya ba yace mata.
“Naji sauƙi daman na missing ɗin su Ammi ne kuma ina sauka ta gidan na wuce yanzu haka daga can nake zan tafi gidana”
Wani farin cikine ya kama ummul wanda harta ɗan saki dariyar data kasa ɓuya tare da ce masa.
“Kai masha Allah naji daɗin hakan yaya su ammin kayi musu zan cen mu?”
Wani irin killer smile ya sauke tare da cewa.
“See you marar kunya, Ni karki lalatani bye”
Yana faɗin haka ya katse kiran yana sauke murmushi adai dai nan kuma ya ƙarasa bakin gate ɗinshi da sauri mai gadi ya fito daga cikin ɗakinshi ya wangale masa ƙaton gate ɗin cikin nutsuwa ya cinna hancin motar cikin harabar gidan ahankali ya kashe motar kana ya fito yana miƙa da hannun shi sannan ya waiga ya dubi mai gadi dake rissune yana masa barka da shigowa cikin sanin darajar ɗan adam suka gaisa kafin ya nufi cikin gidan nashi……….
Tun daga farkon falon shi yake jin wani irin sassanyan ƙamshin turaren wuta lumtsuma ƙafafun shi yayi acikin ƙaton lallausan carfet ɗin dake shinfiɗe a falon kana ya tattaka ya nufi tsakiyar falon ya zube a saman three seater yana mai lumshe kyawawan idanunshi masu matiƙar girma da kyau.
“Ya subuhanallah”
Yafaɗa yana maida kansa ƙasa cike da gajiya yake fiddo wayar shi daga cikin aljihun wandon shi numbern basmah ya shiga kira sedai harta katse bata ɗauka ba still sake dialing yayi a wannan karon ta ɗauka muryarta a shaƙe alamun taci kuka ta ƙoshi take masa magana.
“Ki fito ina falo”
Abin da ya faɗi kenan gami da katse wayar shi.
Jim kusan mintuna biyar ta fito zuwa falon.
Siririyar mace ce marar fasali suffarta a bushe take kirjin nan se ƴan Mitsi-mitsin nonuwa masu kama da bindin ɓera doguwa ce sosai harta so ta kere shi a tsaho sabida rashin fasalinta yasa ka tsayin nata yayi mugun fitowa fuskar nan tasha mai hannayen ta suma ɗar kwai da mai sedai sunyi dabbare dabbare na alamun man bai ratsa su yadda ake buƙata ba.
Bakin nan yayi duhu sedai ta shafa masa man leɓe se maiƙo yakeyi sanye take cikin wata matsiyaciyar doguwar riga iya gwiwarta wadda ta bawa ƙwaurinta damar bayyana cilai cilai kamar na sauro haka ta taho soƙai soƙai tana baza ƙamshi da ƙaurin hayaƙin magani.
A hankali take ƙare masa kallon soda ƙauna tasan bada ban Allah yayi Aliyu mijinta bane ko a farce yayi mata zarra nesa ba kusa ba se yanzu take kuma ƙarewa baiwar kyawunsa duba wani irin so take masa wanda bata jin zata iya barin wata ɗiya mace ta raɓe shi tabbas duk wadda tai gigin raɓarshi zata iya rabata da rayuwarta
Cikin yauƙi da gwalli ta ƙaraso gabansa a ƙasa ta zube tare da zube hannayenta akan takalmin ƙafafunsa ta shiga zare masa igiyar cikin takalmin bayan ta cire ta saka hannu tana share masa ƙafafun kafin ta ɗago soƙai soƙai ta nufi frig taje ta ɗauko masa gorar faro tare da glass cup ruwa mai sanyi ta tsiyayo ta nufi bakinsa dashi.
Sau ɗaya tak ya kurɓa ya kauda kanshi.
Alamar ya ƙoshi.
Har ƙasa ta duƙa muryarta shaƙe take furta.
“My swt man barka da dawowa dafa tan kaje lafiya ka dawo lafiya ina maka fatan nasara mai tarin yawa ina fatan wata ƴar hau ɗin batai gigin koda kallonka ba?”
Tafaɗa tana sakin murmushi kana ta miƙe tare da zama a kusa dashi
Ɗage gira guda yayi yana mata kallon ƙasan ido kafin yace.
“Matsala ta dake zafin kishi meye kuma wata ƴar hau wannan maganar bata layin tarbiya sam sam! to idan ma na kula wata ko wata ta kulani niba mijin mace huɗu bane?”
Yafaɗa muryar shi a dake babu alamar wasa bare ta kawo masa wargi.
A dabarance taɗan saci kallonsa fuskarnan murtuk seya koma mata kamar Aliyun data sani ada can kafin ya aureta ya zama mai wasa da dariya.
Gabanta ne taji ya faɗi sabida idan ada ne wasa ze farayi yana ɗagata sama yana cillawa yana cewa daga ita babu ƙari amman yanzu jiba amsar daya bata
Sanin halinsa yasa tace.
“Soyayyace ta saka hakan kuma kaga dole nai kishin mijina”
Tafaɗa tana kai hannunta saman gemunsa haɗi da sajensa tana shafawa
Zare hannun nata yayi tare da miƙewa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa.
Jimm tai tana bin bayansa da kallo tana nazarin sauyawar sa sedai ta watsar da tunanin tana zaton ko gajiya ce ke damunsa hakan yasa ta miƙe tabi bayanshi.
Taimaka masa tai ya haɗa ruwan wanka tana son ta taimaka masa wajan tayashi wankan ya dakatar da ita wajan faɗin.
“Please basmah fita waje i’m not a good mood”
Yafaɗa batare daya bari taga jikinshi ba jiki babu ƙwari tajanyo masa ƙofar bathroom ɗin ta fita waje ta ɗauko masa kayansa a wadrobe na shan iska ta aje a gefen bed ita kuma ta fice zuwa ɗakinta agigice ta shiga kiran wayar mamanta.
Cikin kuka take mata bayani kamar haka.
“Hajiya ba kanta Aliyu ya dawo amman kamar a hargitse kodai ya biya ta gidan waɗancan tsinannun( gidan iyayensa fa kenan)”
Daga ɓarin hajiya binta zamewa tai daga gefen gadonta dan tsananin tsoron abin da basmah tace mata da sauri ta furta.
“Me,me, kika ce?”
Share hawaye basmah tai tare da cewa.
“Hajiya tunda ya shigo babu wannan rawar kan koda nai masa magana ma a hantare ya ɗauka sannan na bisa ɗakinsa zan masa wanka ya dakatar dani yau ni Aliyu yake ɓoyewa al’aurar sa hajiya kamar ba matar sa ta sunna ba”
Tafaɗa babu kodaa jin nauyin mahaifiyar tata.
“Ki kwantar da hankalin ki bana son ki saka damuwa aranki insha Allahu gobe zan tafi sule ja wajan wannan sabon malamin seyay mana bincike akan lamarin amman yanzu ki koma ki kula dashi nafi zargin ko gajiya ce sami wannan turaren sihirin manta uwar ki shafa ki haɗa masa abinci da wannan ruwan maganin ki tabbatar yaci pls karki min asarar kuɗi dan ubansa zuwa gobe yayi laushi”
Hajiya binta ta faɗa mata hakan tare da bata tabbaci.
“Allah de ya biya uwata wallahi kinfi kowace uwa a wajena yanzu zanyi insha Allah uwata aminiyata seda ke mamata Allah ja zamanin ki mutuwa ba yanzu ba”
Basmah ta faɗa tana sakin dariya kamar ba ita ta gama kuka yanzu ba bayan sunyi sallama da mahaifiyarta wadrobe ɗin kayanta ta buɗe ta ɗauko wata ƙaramar kwalba mai azababban ƙamshi wanda ya cika ɗakin tunma kafin ta buɗe ta buɗe murfin ta tsiyaya ta zuba a tsakiyar kirjinta tare da saman goshinta da kurmin idanunta.
Sannan ta mayar dashi ma’ajinsa ta nufi hanyar waje.
Kicin ta shiga a daddafe ta ɗora masa ruwan coffee tare da ɗan dankalin turawan data soya ta zuba ruwan maganin cikin ruwan coffee ɗin ta haɗesu a babban tray ta nufi hanyar bedroom ɗinsa.
Sedai me tana murɗa handle ɗin zata shiga taji ƙofa a garƙame.
Taja taja abin yaci tura ta buɗu ga ƙofar irin masu tsadar nan ne koka buga baza’ajiba.
Gashi babu spay key a hannunta zubewa tai a ƙasa har coffeen na ƙonata ta saka marayan kuka na baƙin cikin asarar juye maganinta datayi aciki ta jima tana kukan takaici kafin ta ɗauke kayan a zuciye tabar wajan tana jan ƙwafa aranta tana ayyana kodai ya fara dawowa hayyacin sane da alamun sesun sake upgrated na asirin su.
Ya jima yana watsawa fatar jikinsa ruwan ɗumin dayay masa daɗi sosai yaji gajiyar duk ta sake shi.
Bayan ya kammala wankan yayi brush ya fito tare da nufar wajan ƙofa ya murza key dan haka kurum yaji baya son hayaniya a wannan time ɗin,
Alwala ya ɗauro ya sanya jallabiya fara ƙal ya tayar da sallar isha’in dayay missing.
Bayan ya idar ya nufi wajan coffee machine ɗinsa ya haɗa iya wanda yake buƙata ya dawo saman sopa ya zauna yana kurɓa da zafi zafinsa gefen shi ya duba wayar shi nata ringing!
Duba yakai ga ƙaton agogon dake manne a bangon ɗakin kusan sha ɗayan dare tayi a wannan lokacin.
Duba yakai ga screen ɗin wayar hajja ɓaro ɓaro yagani nata yawo.
“Mayya ta”
Ya faɗa cike da ƙosawa a wannan karon ma bai ɗauki wayar ba harta katse sabida yana tunanin da kuɗin hajja take amfani wanda shike zuba mata duk sati cikin wayarta.
Ƙoƙarin tashi yake wani kiran ya ƙara shigowa.
Tsaki yaja kaɗan ya ƙi ɗagawa har seda ya aje cup ɗin dake hannunsa saman ɗan ƙaramin frij ɗin dake ɗakin ya komo ya kashe ƙwan ɗakin sannan ya ɗauki wayar ya ajeta saman gado.
Ya cire jallabiyan jikinsa yayi saura daga shi se singel faffaɗan kirjinshi na cikakkun maza ya bayyana kwance da baƙin gashi.
A nutse ya kwanta a saman gadon ya matse pillow a gefen shi ya tada kai da hannunshi na dama hannunshi na hagu kuma yake lalubar numbern hajja dashi.
Daga ɓangaren ummul wadda taketa juyi a saman gadon hajja ta kasa bacci hajja se mita take akan ta dameta da sukur sukur harta gaji tai bacci ta rabu da ita.
Wayar hajja ta ɗauko ta shiga kiransa har sau uku bai ɗaga ba wurgi tai da wayar tana turo bakinta gaba.
Wata zuciyar na ce mata ai yana can manne da matar sa a kirji wannan tunani seya hadda sa mata jin zazzafan kishin daya sanya ta kuka ta kife saman pillow tana faman kukan takaici.
Jin wayar na ringing! yasa ta goge hawayen ta ɗauka amman batai magana ba
“Assalamu Alaikum”
Dakakkiyar muryarshi mai cike da Amo!
Ta ratsa cikin dodon kunnenta.
Muryarta a dashe da alamun tai kuka tace.
“Amin wa’alaikassa salam”
Jimm shuru babu wanda yayi magana cikinsu tsayin daƙiƙu biyar kafin yace.
“Fisabilillahi nikam yau bazaki barni na huta ba ummi? kira de kira de wallahi kin hanani bacci me kike ke baki baccin ba?”
Yafaɗa daɗan daɗa kaɗan.
A wannan karon kuka ta saki na rashin dalili.
Shafo kwantacciyar sumar kirjinshi yayi tare da lumshe idanu yana jaddada rigimarta.
“To daman dan ki ɗagamin hankali yasa kika kirani da tsohon daren nan me akai maki kuma?”
Jin wannan furucin yasa taɗan rage sautin kukan tace masa.
“Wallahi bazaka sami kwanciyar hankali ba harse ka ɗaukeni anan in ba haka ba nikam zan ƙara gaba dan bazan zauna kusa da gidanmu ba kamaji da wai ehe”
Tafaɗa cike da rashin kunya.
“To naji ki bani nan da kwana uku sakarai”
Yafaɗa yana jimanta wautar yarinyar wani ƙululun baƙin cikin raping ɗin da wancan ɗan iskan yaron yayi mata yaji ya naushi zuciyarsa in banda rashin tausayi wannan ƴar yarinyar meta isa.
Tausayinta yaji ya kamashi cikin kwantar da murya yace.
“Kiyi addu’a ki kwanta dan Allah ba danni ba karki je ko ina ki bari har na dawo amman ki dena kirana ni zan dinga kiranki muna gaisawa”
Yafaɗa da ƙaramin sauti.
Cikin sakarcin ta na shagwaɓar data zama ado agareta tace masa.
“Amman inna jika shuru zan kira bye asuba tagari”
Tafaɗa tare da kashe wayar.
Murmushi ya sanya mai sauti tare da aje wayar agefen sa anya ma kwa a ƙuruciyar yarinyar nan tasan soyayya kodai shirmen tane