BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 32 BY AUTAR MANYA

Bai farka ba se da asubah bakinshi ɗauke da salati, tare da addu’ar farkawa daga bacci, ya sauke santala santalan ƙafafunshi Aƙasa yana jinsa saka yau duk babu wannan gajiyar ta jiya data kashe masa jikinsa.
Kai tsaye bathroom ɗinsa dake manne a cikin ɗakin ya shiga bayan ya kammala uzirin gabanshi ya ɗauro alwala jikinsa ɗaure da faffaɗan tawul se kanshi dake ɗigar da ruwa.
Ƙaramin tawul ya ɗauka ajikin ƙofa yana tsane ruwan kanshi ya ƙarasa gaban ƙaton madubin dake ɗakin ya ɗauki turare ya fesa ajikinsa kana ya nufi wadrobe ya ɗauki wani farin lallausan yadin kufta mai ɗinkin half body ya sanya ajikinsa.
Agurguje ya tayar da raka’atul fijir sannan ya fice a ɗakin ya nufi ɗakin basma ya buga mata bai jira tashin taba ya fita waje tare da mai gadinsa suka wuce cikin masallacin dake bakin layin.

Tunda tabar bakin ƙofar ɗakin Aliyu take rangaji Allah ne ya kaita ɗakinta lafiya kwalaban turaren dake shaƙe a saman madubin ta take watsar wa duk sun farfashe sun fasa mata ƙafafunta amman bata damu da jini da zafin dake zubo mata ba face ware gashin kanta datai wanda yaci uban saloon ta tsaya a gaban madubin tana maganganu ita ɗaya.
“Why Aliyu me nai maka da zakai min wannan horon tabbas jikina yana bani akwai abin da ze faru dani marar kyau sedai ko meye nasan bokana ze tare mini shi” ( wa’iyazubillahi )
Tafaɗa tana bubbuga kanta da madubin kamar zararra haka ta wanzu a wannan dare tana sumbatu gashi tana ta kiran layin hajiya mahaifiyarta yaƙi tafiya.
Haka ta koma ƙasan tiles tai zaman dirshan tana kuka kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa seda taji kanta ya fara ciwo sannan ta haƙura ta faɗa gado tai rubda ciki tana kukan dai wanda ahaka tayi bacci.
Cikin baccinta tai wani mafarki wanda ya sakata tashin dole acikin mafarkin taga wata farar mace mai tsaho amman ba can ba sedai ta saka mayafin daya rufe fuskarta wanda bata sheda kowa ce ba, seta ga matar tana nufota sedai koda tazo wajanta seta tarar da ita zaune da Aliyu gadan gadan matar wajan Aliyu ta nufa tana miƙa masa hannu da wani irin murmushi ya miƙa mata shima hannunsa ya rungumeta a zafafe basmah tai nufin shiga tsakanin su sedai wani ƙaton rami mai macizai aciki yay mata shamaki dasu domin datai yunƙurin binsu seta faɗa cikin wannan ramin wata irin ƙara ta saka wadda ita ta farkar da ita agigice duk ta haɗa uwar zufa.

Idan banda rawa babu abin da jikinta yake idanunta sunyi jajir ta sauka daga saman gadon wayar ta dake yashe a ƙasa ta ɗauka numbern sabon bokansu ta kira alokacin wajan ƙarfe uku da rabin dare, Duk da bokan bai taɓa ganin basma ba amman suna waya sosai da ita saƙone dai mamanta ke amso mata.

Ringing biyu ya ɗauka daga ɓarinsa maganganu ne da alamun aiki yake.
“Hajiya basmah sarkin kishi kece da wannan tsohon dare?”
Dayake sunan da yake gaya mata kenan sabida bata da wata buƙata a wajansa seta kar mijinta yayi mata kishiya kar mijinta yaje wajan iyayen sa ( mata aji tsoron Allah! )
“Uban ɗakina ba kanta ba wannan ba……..”
Tas ta kwashe labarin mafarkin nata ta gaya masa daga karshe ta kece da kuka tana cewa.
“Dana ga ranar da Aliyu ze min kishiya gwara naga ranar mutuwar mahaifiyata” ( wa’iyazu billahi)
Taja fasali tare da ɗorawa.
“Kai min bincike wallahi idan mafarkina ya zama gaskiya sena kashe duk wadda take ƙoƙarin shiga gonata”
Tafaɗa tana jan majina.
Kecewa da dariya yayi tare da ɗaga ƙaton kaskon dake gabanshi yayi zanen sunan Aliyu wanda ada daga ya zana yake ganin hoton Aliyu muraran da halin da yake ciki sedai wannan lokacin ya zana yafi sau biyar baiga komai ba sedai yaga wani irin haske ya cika kaskon wanda har kashe masa ido hasken yake yi dan tsabar yadda ya haske shi.
Gumi ya yarfe ya kuma zaro duƙu-duƙun idanunsa hankali tashe yacewa basma.
“Nakasa ganin komai sema wani haske dake ƙoƙarin kashen idanuna, wanda nake tunanin addu’a ce wannan hasken duk yadda akai a yanzu mijin ki baya sakaci kamar da a wannan karon da wuya aiki mai ƙarfi ya shige shi a bincike ma ze kai kusan shekaru arba’in aiki bai taɓa shiba! sedai mu juya bala’in ga duk wadda tai gigin shiga rayuwarku semun salwantar semun zubda jini semun ɓatar!!!!”
Yafaɗa yana kecewa da wata jahilar dariya mai abin tsoro!.
Gaban basmah ne ya faɗi ta wani firfito da idanunta waje cikin firgici tace.
“Kana da tabbacin akwai yuwuwar ya ƙara aure?”
Tafaɗa cikin bugun zuciya!
Dariyar da yake ya taƙaita tare da ce mata.
“Ai in kinga mijin ki ya ƙara aure to sedai a ƙiyama domin mun masa aiki da mukulli wannan na gaya miki ne kawai amman banga yuwuwar auren shiba ki yarda dani domin bana ƙarya”
(Astagfirullahi)
Cikin yarda da maganar bokan nata tare da bashi gaskiya tace.
“Kana nufin mafarki ne kenan baze tabbata ba?”
Dariya yayi mai sauti.
“Baze taba aure ba! Baze taɓa Aure ba!!!
Yafaɗa yana mai katse wayar yabarta da baki sake.
Sedai maganganun daya gaya mata tare da bata tabbacin baze ƙara aure ba yasa hankalinta ya kwanta harta samu ta tattare kwalaban data yasar ta koma baccinta wanda bugun ƙofar shine ya tashe ta amai makon ta mike tai sallar.
Seta ƙara jan bargo ta rufa ta cigaba da baccinta…….

Aliyu koda ya idar da sallar asubahin zaman shi yayi cikin masallacin wanda ya cigaba da azkar da karatun alkur’ani mai girma.
Har fiddowar rana ya tashi ya bada sallar walha sannan ya fito lokacin ƙarfe wajan taran safiya.
Gidan mahaifanshi ya wuce da ƙafafunshi ya taka har can gidan a bakin gate suka gaisa da mai gadi sannan ya wuce.
Ammi tsaye tana jere kayan abinci a daining yayi sallama ya shiga cikin falon.

Fuskarta cike da annuri ta waigo tana kallon sa kafin ta amsa masa sallamar har ƙasa ya tsugunna yana gaisheta da murmushi ta amsa masa kana ta juya da sauri ta shiga wata kwana wadda ɗakunansu ke ciki mintuna biyu ta dawo hannunta ɗauke da wannan jarkar ta jiya.
Ruwan ciki ta tittulo a cup ta miƙa masa tace masa.
“Maza jeka zauna saman seater kai bisimillah kashan ye ka shafe kanka da fuskar ka”
Tura baki yayi kamar ƙaramin yaro, ya wani langwaɓar da kansa gefe tare da cewa.
“Wai nikam Ammi tun jiya ake bani tofi na minene?”
Yafaɗa kamar wani ƙaramin yaro.
Murmushi ta sauke tare da cewa.
“nidai kasha kabani cup bana son wannan tambayar taka ta lauya”
Dariya ya saki yana mai ƙarasawa saman kujerar ya zauna tare da bin umarninta dama can Ali baya musu garesu sharrin mace ne Allah ya haɗa shi da shi.
Sosai Abba yaji daɗin ganin ɗan nashi rukumi sukai wajan yin break cikin soda ƙauna.
Bayan sun kammala Suka koma falo suka zauna suna kallo.
Aliyu na sunne kai ƙasa ya dubi Abba yace masa…………

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE