BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 35
“Idan banda Abin ka Baffa ai So Da Tausayi aciki shiya ke zama so! idan har baka son yarinyar nan wallahi bazakaji tausayin taba, Yara nawa irin hakan ta sama wasu ma yafi hakan amman bakai tunanin yi musu taimako kamar wannan ba? sabida haka ni zanyi maka gatan da gaba zaka gode min ko bayan raina kai min addu’a da samun mace tagari kamar ta sabida haka zanyi wa su yaya usman magana su samu ko zuwa next week aje can wajan mahaifin nata a nema maka auren ta, Nikam na hutarka komai ni zanyi duk abin da ake buƙata na aure kai kawai mata za’a kawo maka nan, ammi kira min yayarsu a waya maza gobe idan tana da lokaci tazo zan bata order dubai a haɗo kayan lefe”
Abba ya kai maganar fuskarsa ɗauke da maɗaukakin murmushi wanda yajima bai yishi ba.
Idanun shi jajir har wani ruwa ne ya taru acikinsu wani irin haushin ummul yakeji acan ƙasan ranshi tunaninsa ma yanzu ya rabu zuwa gida barkatai yana raya cewar maza nawa tai hulɗa dasu lokacin da take zaune a gidan karuwai hatta ganinsa na farko da ita a hotel bai ɗauka tana jin hausa ba sabida shigar daya gani a tare da ita duk da yayi rayuwar ƙasar turai lokacin daze kammala karatunsa da kuma wani course daya kaishi can har na tsayin shekara tabbas yay cuɗanya da turawa yasan wannan shigar ba wani abu bace ba awajansu sedai mu anan a al’adar hausa fulani ya zama abin kunya ga ɗiyar musulmi kuma cikakkiyar bahaushiya tai wannan shigar sedai yawanci masu yinta su kasance ƙabilu, idan kwa a yaren hausa fulanine to tabbas sedai ɗan duniya duba da addini da al’adarmu bata bamu damar yin shigar da zata bayyana mana tsiraicin mu ba.
Muryar shi can ciki sabida ɓacin rai ya furta.
“Nifa Abba wallahi Allah ban taɓa jin soyayyar yarinyar nan acikin zuciya taba, kuma abin da zanyi mata zanyi ne for the sake of God, ba domin komai ba Abba a duba nifa mata ɗayar ma da yaya bare mata har biyu Abba bani da lokacin kula dasu kasan yanayin aikina aikine daya ke da takura idan na fita office tun 8:00am se 8:00pm nake yin off”
Ya ƙarashe maganar tashi acikin nutsuwa.
Murmushi Abba yayi tare da cewa.
“Haba jarumina haba Ali mazan fama Ali ƙusar yaƙi Ali jijiya ba tsoka ba wallahi duk Ali ba rago Ali jarumi ne agida jarumine a dagar yaƙi ni kaina bada ban ina ɗan tsoron tashin hankali ba dase na cika huɗu bare kai yaro mai jini da lafiya tare da wadata mai ze firgita ka ga auren mace biyu kaida Allah ya bawa damar auran huɗu idan da halima harda ƙwarƙwara”
Dariya Aliyu ya sauke kaɗan yana kallon Ammi data ɗauke wuta tunda taji abba ya kamo wata tashar daban wai shima bada ban tsoro ba daya cike har huɗu.
Sannan ya ɗauke duban shi gareta ya dubi agogon farar azirfar dake ɗaure bisa tsintsiyar hannunsa har 11 tayi kawar da kanshi yayi tare da kallon Abban nashi kana yace.
“Nifa Abba duk ba wannan ba, Ina da halin aure ina da lafiyar riƙe su kawai dai ni Abba……
Abba bai bari Aliyu ya ƙarasa ya tare shi da cewar.
“Na gama magana tashi kaje idan an kawota ka sakata amai kaita suya”
Murmushi Aliyu yayi yana duban Abban nashi tare da cewa.
“Amman Abba zata zauna anan ne harna sama mata inda zata zauna dan gaskiya bazan haɗata da matata ba”
Caraf Ammi ta karɓe zancen tare da cewa.
“Wallahi ban lamunce ka ware mata gida kaita cutar da ita ba, Akan waccan tsilar matar taka baza ka gasa yarinyar da bana tunanin takai sa’ar su ƴam biyu ba sabida haka koda zata zauna a wajanmu na sati biyu ne kacal ka gyara mata ɗakin da zata zauna agidanka da kanka zakazo ka ɗauketa ka mayar da ita ɗakinta kuma idan ka tauye mata haƙƙinta Allah baze taɓa barin ka ba, sakarai kawai wanda bai san me duniya take ciki ba”
Ammi ta karasa tana jefa mashi harara.
Tsabar takaici bai bar Aliyu ya ƙara magana Ba, baƙin cikin wannan aure shiya tokare masa ƙahon zuciyarsa tunda yake da Ammi bata taɓa gaya masa magana mai zafi ba amman akanta gashi har tana kiran matar sa tsila shi kuma sakarai.
Abba ne ya ɗan girgizawa Ammi kanshi kaɗan yana mai gargaɗinta akan karta sake yiwa Aliyu faɗa akan wannan aure gudun karya birkice musu kafin ya dubi Aliyu murya a tausashe yace masa.
“Tashi kaje ɗan albarka alfaharin iyayensa uba ga ƙannensa,insha Allahu wannan aure alkairine sekai dariya ina mai baka tabbaci wannan yarinya zata sama maka tagwaye irin su hassana kaidai kaje kaita shirin biki ka gyara mata ɗakin dake kusa dana matarka ka saka aranka aure bautar Allah ne sunnar Annabi ( s.a.w) ne ka cire komai a ranka zata zauna anan tai sati biyu kafin nan ka gama gyara mata ɗakin nata”
Abba ya ƙarasa yana murmushi.
Miƙewa yayi tare da ɗaukar wayar shi murya a daƙile yayi musu sallama ya fice Ammi ta bishi da harara.
Bayan Fitar Aliyu Abba ya dubi Ammi data gama ɗaukar zafin Aliyu kana yace mata.
“Hafsa sefa kin ɗanyi haƙuri da yaron nan domin har yanzu akwai ragowar sihirin matarsa ajikinsa to mu lallaɓashi har ya auri yarinyar nan ina ji ajikina itace alkairinsa sannan itace mai rabon sama masa yaran daya ƙwallafa ranshi akan su kinsan abu mai alkairi yana zuwar wa bawa a jinkiri ko a ɗan samun matsala kaɗan”
Abba ya gayawa Ammi hakan wadda duk abin duniya ya taru yayi mata yawa.
Tagumi ta rafka tare da cewa.
“Jina ke kamar a ɗaura auren yau wallahi Abbansu bana ƙaunar matar baffa ko kaɗan, wannan yarinya Allah ya gaggauta kawo mana ƙarshenta kuma aure ne babu fashi ai ko baka ɗauki nauyin lefe ba sena yi da kuɗina Allah de yasa ai a nasara da sa’a amin”
Waya Ammi ta ɗauka a gefenta ta kira ya jidda tai mata bayanin auren Aliyu ya jidda harda taka rawa tana cewa ammi tana nan bisa hanya zata shigo ai shawara tunawa da fyaɗan da aka ma ummul yasa Ammi tacewa ya jidda tazo mata da kayan gyaran jiki masu kyau dan a sati biyun data ɗiba ma ummul Agabanta gyarata zatai ciki da waje yadda babu yadda za’ai Aliyu ya kawo mata raini.
Shidai Abba dariya yake taiwa Ammi na yadda take rawar jiki akan surukar tata wadda ko fuskarta bata taɓa gani ba amman ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗora mata.
Ran Ammi fari ƙal haka taita kiran ƴan uwa tana sheda musu auren Aliyu na biyu duk da Abba yace babu wata bidia da za’ai ɗaurin aure kawai zasuje suyo a taho da yarinyar.
Shima Abba ɗakinsa ya wuce ya shiga kiran yayyansa yana sheda musu lamarin.
Lokacin daya gayawa Kawu Abubakar babban yayansu kabbara kawu ya saki yana hamdala tare da cewa Abba.
“Kagani ko Ali amfanin addu’a kenan Allah ya sani muma nan bamu zauna ba kowa addu’a yakewa baba Ali Allah ya kawo masa mace tagari ba irin tashi ba ita kuma tashin ya shiryata idan mai shiryuwa ce sabida haka ga sakamakon addu’armu nan Allah ya nuna dan haka daga nan zan saka ƴan uwana ranar juma’a mai kamawa zamuje kano ɗin baba karami ze kaimu tunda kace nan gidan hajja take ɗiyar ko? shikuma mahaifinta a kusa da gidan hajjar ko?”
Abba yace.
“I”
Sannan kawu ya cigaba da cewa.
“To masha Allah zamuje da kuɗin auren mu idan da hali ma ranar sati zamu koma a ɗaura aure”
Murmushi Abba ya saki tare da jin dadin yadda ƴan uwanshi suke kula da lamarin shi kana yace.
“To yaya babu damuwa ni zan turo da akwatunan lefe zuwa wani satin wanda za’a tafi dasu ranar ɗaurin aure”
Sosai kawu yakewa ABBA godiya a madadin Aliyu kana sukai sallama.
Kiran jidda Abba yayi tana ɗauka ta fara masa kirari cike da wasa da dariya tana furta.
“Allah dai yaja kwanan abban mu”
Dariya ya saki dama shi baya mata alkunyar ɗiyar fari wannan se ammi wadda ko sunanta bata faɗa.
“Zan turo miki da kuɗi sabida ina son nan da kwana ki uku ki sami vixa ta dubai zaki haɗo kayan lefen ƙanin ki”
Maganganu sukai sosai kana yayi mata transper ɗin kuɗin komai sukai sallama wanda tace masa ita kam daga ta dawo ma daga dubai ɗin gida zata wuto har se anyi biki zata koma.
Bayan sun gama wayar ya jidda ta ƙara kiran ammi ta sheda mata bazata sami damar zuwa nan da kwana biyun data ce ba sabida aiken Abba amman zata aiko da kayan ta tasha wanda za’aiwa amaryar gyaran jikin dasu sallama sukai wayar sarat ta shigo harda kukan daɗi dan murna kafin wani lokaci suma su ƴan biyu sun kunna kiɗa a falo suna rawar murnar auren yayansu musamman da ammi tace sa’arsu ce nanfa wata murnar ta ɓalle ranar hatta ma’aikatan gidan ALHAJI ALI DIKKO sun sheda ahalin gidan na cikin murna dan rabon kuɗi Abba ya dinga yi musu tare da kayan abinci.
Wannan ya kuma bani tabbacin lallai Aliyu ɗan so ne kuma ɗan gata wajan ƴan uwansa da iyayensa, Tabbas ina zaton ummul zata sami gata wajan iyayen mijin nata wanda ta rasashi a wajan nata mahaifan duba da yadda Bamu take marar abin hannu shi kuma malam habu jarababbe tabbas ummul ta taso cikin rashin jin daɗin rayuwa ga kuma makauniyar ƙaddarar data gifta mata amman da yake Allah mai rahma da jin ƙai ne, seya ƙaddara kawota inda kukan ta ze gushe hawayenta ya ƙafe sabida kasantuwa da iyayen miji nagartattu waɗanda tunma kafin a kawota suke ɗaukinta fata de Allah yasa ta zama ta gari a agare su amin.
Shikuwa Aliyu……….
Bai koma gidan saba se ƙarfe sha biyu na rana koda ya buɗe ƙofar falon shi ya shiga gidan tsit tamkar babu ɗan adam acikinsa.
Kasance war jiya ya dawo yasan daman yau basmah bazata fita aiki ba abin ya bashi mamaki daya leƙa kiching yaga komai a yadda yake tun jiya bai sauya ba.
Da ɗunbin mamaki ya nufi hanyar bedroom ɗinta ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga ciki sassanyan ƙamshin turaren ɗaki ya doki hancin sa ga wani azababban sanyin AC mai kama da raɓa ya ratsa mai jikinsa.
Kwance ya hangi basmah a tsakiyar gado rufe da blanket da alamu ma da ƙyar idan tayi sallar asubahi duba da yadda take ta zuba numfashi.
Da sassarfa ya nufi gaban gadon ya ɗora ƙafarsa guda a saman gadon kana ya sanya hannu ya yaye blanket ɗin data rufe jikin nata dashi.
Tsila tsilan cinyoyinta da suka yaye ta cikin riga suka bayyana masu kama dana fara! Kauda kansa yayi tare da ƙwanƙwasa katakon gadon yana cewa.
“Basmah Basmah!!”
Muryarsa ke tashi a nutse.
Sannu a hankali takejin sautin muryarsa acikin kunnenta A hankali take wara ƙananun idanunta harta buɗesu akansa tarwai.
Tana wani yauƙi ta miƙe zaune bakinta cike da miyan bacci ta tashi soƙai soƙai kamar kyauro ta nufi bathroom ta tofar da yawun kana ta dawo gabanshi ta tsaya mai sangam gam aka.
Wani irin takaici ne ya kamashi daman ga bakin cikin auren shi da tsawa yayi mata magana.
“Ke wai wacce irin marar hankali da tunani ce yanzu inba rashin hankali ba tayaya ƙarfe har 12 da mintuna kina baccin asara baki sallar safe ba?”
Tsananin mamakin furucinsa ya sanyata zare idanunta masu kama dana zomo, Ta dube shi da kyau cike da ɗunbin mamaki tare da shakkar sa data ɗarsar mata aranta tace.
“Da kyau Aliyu nice marar hankali? kuma marar tunani?”
Ai jin wannan furucin ya ƙara tunzura zuciyarsa yayo mata ka kamar ze duke ta yana furucin.
“Duk wanda baze tsaida sallar saba sunan shi mahaukaci tayaya kina kwance a gado kina baccin asara har lokacin sallar farillah ya wuceki babu sallah bare gyaran gida bare akai ga ɗora abinci sarai kuma kinsan ina gari”
Yafaɗa tare da ware mata girman idanunsa da suka sauya launi ya koma mata Aliyun da sak wanda ta sanshi marar wasa da sakin fuska sabida gudun raini.
Jikinta ne yayi sanyi ta koma da baya ragwab ta zube saman gado tana zubar da hawaye ko a mafarki batai zaton Aliyu ze ɗaga mata murya irin haka ba shin meke faruwa da itane daga jiya zuwa yau?
“Wallahi idan na dawo baki sallah ba sena saɓa kamannin ki wawiya kawai aikin gida baki tsaya kinyi ba saboda tsabar bakin halin ki kin hana a ɗauko miki mai aiki se gandar tsiya”
Yaja tsaki yabar ɗakin.
Basmah ta mike zuwa toilet tana tsiyayar hawaye! Sosai lamarin ya firgitata ahaka tayo alwala babu ko kunyar mahaliccinta ta soma yin sallar safiya tana idarwa babu ko addu’a ta miƙe tayi gaban mirrow ta ɗauko wayarta tana kuka tana shedawa hajiyarta abinda yake faruwa da mafarkin data yi.
Wani ashar! hajiya binta ta saki tare da cewa.
“Ni zan nuna wa Aliyu banufiyar usul ce dani yake zancen share hawayen ki amman dole kema ki dage wajan shawo kansa ta hanyar kirsa da kisisina tamu ta mata maza tashi ki wanka ki haɗa masa break ki kai masa ki kuma bashi haƙuri akan zaki gyara”
Cikin zare idanu tace.
“Hajiya nifa tsoro nakeji wallahi bakiga ba ɗazu kamar ze duke ni wallahi iyayen Aliyu sun rusa mana aikin mu damuka sha kuɗi akan sa bakiga yadd ya koma min kamar kumurcin zaki bafa”
Cikin ɓacin rai da tarin damuwa hajiya binta tace.
“Bari nai masa waya amman de ki daure kije wajan nashi”
Kana ta katse wayar.
Miƙewa basmah tai jiki babu ƙarfi tai wanka ta tsuke cikin riga da wando wanda ya bata samfir mai kama da muciya da zani, Ta goga turare kana ta fice zuwa kicin tea ta ɗora masa tare da wainar ƙwai daman ba wani girki ta iya ba ita dai barta da dauriyar sex wannan kobe nema ba a miƙa masa bataƙi ta kwana ana haƙar taba.
Rai ɓace yabar ɗakin zuwa nashi room ɗin zama yayi a bakin gado ya tube rigarshi ya sakarwa kanshi A’C gaba ɗaya baya jin dadin yanayin nashi wanda yake zaton wannan auren ne ya janyo masa hakan.
Ya jima a zaune kafin wayar shi ta ɗauki ringing ganin sunan hajiya binta maman basmah yasa yaɗan gyara nutsuwar shi kana ya ɗauki wayar wanda ada sedai ya katse ya kirata da kanshi.
A nutse yayi mata sallama takwa amshe cike da tsantsar bariki take gaishe shi.
Cikin jin nauyin gaisuwar yake amsawa tare da cewa.
“Ai hajiya dakin bari na fara gaisar dake tunda kece gaba dani”
Sautin dariya ta sauke kaɗan tare daa cewa.
“Ai yanzu kaine babba Aliyu yadda kake hidima da ni da marainiyar Allah sedai Allah ya biyaka, Dama naji shirmen da wannan yarinyar tai makane shiyasa na kiraka na baka haƙuri kuma har gida zanzo na zaneta tayaya zata dinga sakaci da ibada ni ai data gayamin zageta nai tas nace har kiyiwa mijinki laifi kizo kina gaya min sabida haka kayi haƙuri Aliyu basma yarinya ce ƙarama tsayin ƙafane kawai amman zata gyara”
Tafaɗa tana ƙasa da murya.
Murmushi ya sauke tare da cewa.
“Babu komai hajiya ya wuce”
Ta kwa amshe tare da cewa.
“Kasan abinka da farin shiga, Tunda kukai aure shekara biyar bata taɓa kawon laifin kaba haka kaima baka taɓa kawon nata ba shiyasa yanzu da kuka sami saɓani tai saurin gayamin akan na baka haƙuri”
Hajiya binta ta faɗi hakan dan kar yayi zargin basmah ta kawo mata ƙarar sane.
Murmushin ya kumayi a karo na biyu tare da cewa.
“Ba komi hajiya nagode”
Sallama sukai ya aje wayar yana ƙoƙarin kwanciya sabida yau babu inda zeje.
Basmah ta turo ƙofar tare da sallama a hankali.
Babu yabo babu fallasa ya amsa mata kuma bai fasa kwanciyar tashi ba.
A ƙasa ta dire tray ɗin abincin data kawo masa.
Tare da cewa.
“Dan Allah my sweet man kayi haƙuri insha Allah bazan kuma ba”
Tafaɗa tana mai kamo ƙafafunshi.
Kuka ta sanya masa sosai tana magiyar basa haƙuri.
Ahankali take karya masa zuciyarsa kasancewar sa mutum mai tsananin jin tausayin mace musamman idan tana kuka sabida yace mata masu raunine.
Tashi yayi tare da kamota ya haɗeta da jikinsa ya saka bayan hannunsa yana share mata hawayenta.
Sannu a hankali ya matse ƙugunta tai ƴar ƙara kaɗan ta shigar da kanta kirjinsa tana jin duk duniya babu wadda takaita dacen miji kuma duk duniya babu wanda yakaita son Aliyu domin bata haɗa soyayyarshi data kowa ba.
A hankali ya fara wasa da ƴan ƙuli ƙulin nonuwanta marasa fasali masu kama da shafi milera se wani noƙewa take tana shigewa jikinsa sannu ahankali ya kwantar da ita asaman gadon yaja musu blanket a hankali ya soma gwada mata yadda yayi missing ɗinta na kwanaki ukun dayay basa tare.