BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 36

Cewar hajja dake tsaye akan ummul cikin faɗa take wannan furucin.

A karo na barkatai ummul ta share hawayen dake faman zubo mata kamar famfo jikinta duk yayi sanyi kamar marar lafiya.
Ta dubi Hajja a raunane tare da ce mata.
“Hajja rabona da shi tun jiya fa yace mini baya jin daɗi kar na kirasa amman shi ze dinga kirana”
Tafaɗa murya can ƙasa.
Neman guri hajja tayi ta zauna tana mai fuskan tar ta.
Cikin nutsuwa hajja tace.
“Ummi karki zarme akan soyayyar Aliko ita mace da jan aji aka santa dan Allah kina jan aji irin na mata wai nikam mai Aliko yafi sauran maza ne da kike masa wannan soyayya haka babu koda jan aji cikin ta?”
Hajja ta faɗa cikin ɗaga murya sama.

Lumshe ido ummul tai tana mai hasko girman cikar zatin kyawunshi tare da kamewar shi uwa uba nutsuwa da kamala tare da haiba kana ta waresu tar wai a kan fuskar Hajja cikin kalar tausayi tace.
“Hajja bari kede ni bance Ali yafi kowa ba amman a zuciyata yafi kowani namiji haka nan Allah ya ɗauki son shi da tausayin shi ya ɗora min acikin raina”
Tafaɗa tana mai danne saitin zuciyarta da hannunta wanda yin hakan ya bawa hajja tabbacin kome ta faɗa iya gaskiyarta ta faɗi.

Cikin tausaya mata hajja tace.
“To ki dinga addu’a ko abinci fa baki ciba shi ƙila ma yana manne da matar sa a wannan lokacin suna soyayyar su amman ke kin zauna kina haƙilon iska”
Hajja ta faɗa mata hakan tana hara rarta.
Tura kanta tayi tsakiyar cinyoyinta a hankali take rera kuka mai fitar sauti murya cikin kuka take cewa.
“Allah bani na ɗorawa kaina soyayyar bawan kaba ya Allah kaine ka ɗoran ya Allah kasa ta ficen a raina kona huta”
Taɓe baki hajja tayi tare da tashi tabar mata wajan.
Yinin ranar ummul ta kasa kai komi cikin bakinta bini bini zata ɗauki wayar hajja taga koya kirata amman shuru har wajan yamma lokacin su sadiya ƙannenta suka shigo gidan hajja murnar ganin su yasa raguwar damuwar rashin kiransa taɗan sauka zama sukai suna taɓa hirar abubuwan da suka faru a bayan tafiyarta.
“Anty ummi ina gaya miki har yau gida fa na nan yadda kika sanshi sema abin da yayi gaba”
Cewar kausar mai bin sadiya tana kallon ummul wadda duk rabin hankalinta baya kansu.
Idanunta kaɗai ze baka shedar bata cikin hayyacinta amman su sabida yara ne yasa basu fahimci hakan ba.

Sadiya ce ta dube ta tare da cewa.
“Ai bayan tafiyarki munsha kuka munsha takaici mutane sahu sahu suka dinga zuwa yiwa bamu jaje wanda rabi munafurci ke kawosu shiko baba seda ya dena fita sabida kowa zaginshi yake a unguwar nan ana cewa yaƙi ɗaukar ƙaddarar data sami ƴarshi domin ashe kowa yasan halin da muke ciki shiyasa babu wanda yabi bayan shi”
Murmushi ummul tayi mai ciwo tare da cewa.
“Dama ai Allah mai rahma da jin ƙai ne ya ɗauka duk abin da yake mutane basa lura”
Sadiya ta ƙara tarar numfashin ta da cewa.
“Ai bayan kin tafi bamu ta dena aiki ga jariri abinda zamuci se hajja ke kawo mana aikwa ba shiri bamu ta tattara ƴan kuɗinta ta saro man ja dana gyaɗa wallahi Allah ya saka musu albarka a yanzu haka dashi muke komai domin tana ciniki sosai”

Ƙwallace ta tarar wa ummul ta share tare da cewa.
“Hmm sadiya shiyasa naso nai karatu kodan na tallafi bamu amman dayake shirina daban dana Allah se Allah ya rusa nawa shirin ina kwa gidan hajiya timo sun nemi bamu?”

Haɗe rai sadiya tayi tare da cewa.
“Basu nemi kowa ba, ai nake gaya miki talatu har gida tazo tana kuka tana bawa bamu haƙuri akan inda tasan haka abin ze zama da bazatai hanya ba,koda uwar ɗakin talatu tajewa hajiya timo da maganarki seta koreta tai mata fata fata anan abotarsu ta watse”
Kuka ummul ta saki tana furta.
“Sadiya meye amfanin talauci wai ace sameer yana garin nan mahaifan shi suna nan amman nakasa karɓan hakkina sabida ina talaka? sabida bani da gatan wanda ze bimin hakkina ko kwanaki na ganshi a wani hotel da budurwa sun shiga?”
Tafaɗa tana share hawayenta.

“Dena kuka ummi ni jikina yana bani sameer baici bulus ba Allah ze kawo mai taimakon mu tunda mu bamu dashi Amman insha Allah se zina tai wa sameer sanadin ajalinsa”
Sadiya ta faɗa itama kamar zatayi kukan sannan ta ɗora.
“Ai ina gaya miki se umma tahau habaici a tsakar gida tare dasu ya basira suna mana waƙa Bamu tace karmu kula su haka muka share su bama kula kowa hatta baba seda muka dena gaida shi, Kwatsam in gaya miki rannan munzo zamu shigo gida muka gamu da baba a zaure yana ƙoƙarin haska fitilarsa ze shiga soro se muka bi bayan sa sabida daga makarantar dare muke kawai baba na haska fitila sega nonon ya basira nan cimu cimu a bakin wani saurayi suna iskanci, sabida rawar jiki ihu muka saka wanda shiya janyo hankalin mutan gidan namu umma da bamu suna ta rawar jiki suka shigo soron hmm ai ummah tana ganin haka seta koma da baya cikin kunya tana susar kai bamu kuwa taja hannun mu muka koma gida, shiko baba kasa magana yayi”

Taɗan nisa kana ta cigaba.
“Har washe gari gidanmu tsit bakajin hirarsu da habaicin su sabida anyi abin kunya, Hmm ashe in gaya miki kowa a unguwa yasan mai suke idan uwarsu ta aikesu shaguna taɓe su ake a basu kuɗi koda baba ya taramu yace duk su fito da miji buɗar bakin samarin se sukace ai abinda suke nema idan sun aure su ai sun samu a waje, wannan maganganu sune suka saka baba harda kwanciya jinya yanzu de ataƙaice babu mai zuwa wajan su ya basira kullum suna gida kuma daga ranar uwarsu bata sake mana gorin kin bar gida ba wanda ada wallahi tun safe idan ta dasa yi mana habaici har a kwanta bacci”
Sadiya takai maganar tana murmushi.
Ummul cikin takaicin halin da ƴan uwanta suka shiga tace.
“Ai baba yanzu ya fara ganin bala’i tunda baida zuciyar nema ya bawa ƴaƴansa sedai ƙarfin kwanciya da mace to yaya ake son suyi? ataimako de baza’a tai makesu ba sukuma basuda tsarka kakkiyar zuciyar kare kansu nasan ba komai ze sakasu bin shaguna ana taɓesu ana basu kuɗi ba face rashi! inda akwai da bazasu yi hakan ba se kuma uwa uba kwaɗayi da zulama tare da hangen abin da na sama yake dashi, Allah ya kyauta wannan darasi ne Allah ya nunawa hadiza ranar da baba ya koreni ina kallo tana sheƙa dariya ashe itama tata ranar na tafe oh! ni ummal kairi inda ranka zaka sha kallo”

Dariya sadiya ta saki tare da cewa.
“Amman su ai bai kore suba wallahi baba bai maki adalci ba”
Tafaɗa cike da jin haushi.
Murmushi mai ciwo ummul tai tare da cewa.
“Barni dashi lokaci na nan tafe shiyasa jiya daya ganni yawani tsaya zemin magana na share shi”
Dariya sadiya ta saki sannan tace.
“Ai baba yayi laushi har yanzu baya cas baya as amman de babu masifar nan sabida yana nema ajikin matansa kowacce idan tai girki zata bashi sedai baya wannan faɗan Allah de ya kawowa baba mafita yabar wannan zaman rashin abinyi ɗin”
Da amin ta amsa wa sadiya ahaka sukai magariba suka wuce.

Bayan ta idar da sallar magariba tagumi ta sanya tana kurɓan shayi da ƙyar wanda hajja ta tilas ta mata akan seta shashi.

ABUJA.
Sosai ya more jikin basma bai sarara mata ba se wajan rana sannan ya mirgina ya ɗagata ya shiga wanka koda ya dawo ya tarar itama ta fice harta sauya mai bedshirt zama yayi yana tsane kanshi sannan ya sauya kaya tare da nufar toilet ya ɗauro alwala ya wuce masallaci.
Daga nan wani mutumi yayi masa waya akan yana son ganinsa sabida wata shari’a daze tsaya masa a kotu sabida haka daga masallaci nan cikin mai tama ya wuce wajan mutumin agidan mutumin yayi har magariba saboda tattauna war mai tsayi ce a tsakanin su.

Tafe yake akan titi yana draving hadarine ya haɗo sosai yana gab da zubda ruwa titin tsit sabida kasantuwar haɗowar hadarin ya saka mutane suketa raguwa.
Sannu Ahankali yakai hannunshi saman wayar shi dake faman ringing! lumshe kyawawan idanunshi yayi ganin number hajja a karo na barkatai.
Shafo kanshi yayi da ɗayan hannun shi har wayar ta katse bai ɗaga ba seya danna dialing ɗinta.
Ringing biyu Ummul dake zaune ta cure a saman sallaya tana kuka ta ɗauka muryarta a dakushe tayi masa sallama.
Jiyay tsigar jikinsa ta miƙe jin tattausar muryarta da yayi a yanzun.
“Ya salam bade kuka kike ba? mai aka maki me ke damun ki?”
Duk ya jera mata tambayar batare daya san hakan ta faru ba.
Wannan tambayar renin hankalin daya yi mata wadda yasan ai sabida shi take kukan ita ta fusata zuciyarta wadda ta bata damar baje baki ta dinga rera masa kuka kamar ance mata bamu ta rasu!
Da sauri ya dafe sitiyarin motar babu shiri ya kasheta ya dafe kanshi yana sauraran kukan nata.
Seda tai mai isarta bai hana taba sannan ta soma sakar mai ajiyar zuciya akai akai mai ƙarfi.
Cikin cool voice yace.
“Shiiiiit ya isa kukan mana ummiy khairy idan kika ƙarar da hawayen babu ruwana please me aka maki kike ta kuka ko hannun ne?”
Ita tama mance da wani hannu ai, amman dan karya kawo mata raini yace sabida shi take kuka seta basar tunawa da huɗu bar hajja ta ɗazu data ce ta dinga ja masa aji hakan yasa ta ƙaƙalo ƙarya ta shirga masa.
“Ni tunda na tashi hannuna yaƙi motsi nayi nayi yaƙi yi kuma hajja tace bata san kan maganin ba shine naketa kiran ka kagaya min nawa zan sha baka ɗauka ba?”
Tafaɗa a sakarce.
“Kuma shine ake kukan?”
Yafaɗa murya kamar mai raɗa.
Numfashi ta fesar tare da cewa.
“Zafi fa yake min”
Lumshe idanunsa yayi yana jin wani kalar yanayi ajikinsa wannan shagwaɓa tana kashe shi.
A hankali ya furta.
“Ki sami man zafi ki goga a wajan hajja ta saka maki ruwan ɗumi a gasa amman dai adena wannan kuka hakan nan ya isa”
Yafaɗa mata hakan cikin kwantacciyar murya.
Wani irin kuka ta cigaba dayi mai kama dana yara idan suna son abu aka hanasu tana ce masa.
“Nide ka dinga ɗaukar wayata sabida irin wannan idan ba haka ba sedai ka dawo kano ka tarar bana nan”

Harga Allah wannan shagwaɓa ta birkita bawan Allah idan har ta cigaba dayi zeyi abin kunya don shi shagwaɓa tana sanyawa ya kasa controlling kanshi.
“Shiiii dena kukan pls kiyi bacci take care bye”
Yafaɗa muryar shi na wani irin karkarwa.
Kamar mai jin sanyi haka ya yarda wayar jagwab ya koma yaja seat ɗin kujera ya kwantar da kanshi yana mai lumshe kyawawan idanunshi da suka sauya kala zuwa jajir………..

Ya Salam, Ya Allah”
Ya faɗa a gajiye yana mai shafo gashin sajen dake kwance a saman fuskar shi ya sanya haƙoranshi yana cizon ƙasan laɓɓanshi.
Ya kai mintuna talati a zaune seda aka soma yayyafi sannan ya tada motar yabar wajan tafiya yake a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa aciki har Allah ya kaishi gida.

A parking space ya aje motar tare da kasheta ya fito waje yana ɗan gudu kaɗan sabida gudun kada ruwa ya taɓashi.
Seda yaje bakin ƙofar falo sannan ya dai daita nutsuwar sa.

Ya kama handle ɗin ƙofar falon ya murɗa ya buɗe ya shiga ciki farin hasken ƙwan falon ya haske falon ga wani irin haɗaɗɗan ƙamshi da sanyin AC da suka bugi hancin sa.

Sallama maƙale a bakinshi ya shiga ciki babu kowa a falon se Uban ƙarar tv dake tashi.
Ya ƙarasa gaban tv ya kashe ta sannan ya wuce ɗakin shi.
Yana tsaye a gaban mirrow yana cire botir ɗin rigar shi basma tayo sallama ta shigo.
Ba yabo ba fallasa ya amsa mata a hankali ta ƙaraso gaban sa sanye take da riga da skirt na marun ɗin leshi sedai ɗaurin zahra buhari wanda shigar tai matiƙar yi mata kyau.
Hannu ta saka tana taimaka masa wajan cire botiran.
Seda ta taimaka masa ya cire kayan jikinsa sannan ta wuce bathroom ta haɗa masa ruwan wanka.

Bayan ya shiga ta kuma ƙara gyara masa ɗakin kafin ya fito har turaren wuta ta kawo.
Lokacin data ke turara mashi ɗakin shikuma ya fito jikinsa ɗaure da tawul agaban mirrow ya tsaya ya kintsa kanshi ya shirya cikin farar jallabiya turare ya fesa sannan ya shinfiɗa darduma a ƙasan tiles ya tada sallar isha’i.

Zama tayi a gefen gado tana kallon yadda yake sallah a nutse ya jima hannunshi a sama bayan ya idar da sallar yana roƙon Allah, Kafin ya shafa ya miƙe tare da ninke abin sallar.
Ya ƙaraso wajanta ya zauna daf da ita har ƙamshin turarenta yana dakar mai hanci ya lumshe idanunshi.

Tare da cewa.
“Sannu da hidima Allah yayi miki albarka kinyi matiƙar kyau”
Fari tayi da idanunta tare da ware hannunta taɗan sakosu a gefen kafaɗunshi tare da furta.
“Nagode mijina ga abincin ka can a falo na jiran ka”
Lumshe idanu yayi tare da cewa.
“Kinyi sallah de ko?”
Murmushin dake fuskarta bai gushe ba har yanzu tace masa.
“Eh nayi tun ma ɗazu”
Ta tashi tsaye ta kamo hannunshi suka fita falo.
Kujera ta ja masa ya zauna ta shiga serving ɗinshi.
Farar shinkafa ce da miyar ganda se lemon data zuba mai a cup ta ɗora spoon cikin shinkafar ta tura masa gabanshi.
Kashe mata ido ɗaya yayi tare da cewa.
“Ke kinci?”
Shagwaɓe fuska tayi tare da gyaɗa masa kai alamar “eh”!

Bisimillah yayi tare da ɗaukar spoon ya fara juya abincin.
Lomar farko yaɗan yatsina fuska sabida mugun yaji da gishirin daya yi yawa acikin abincin.
Aje spoon ɗin yayi tare da kallon ta.

Sannan a hankali ya ɗauki cup ya tsiyayi ruwa yasha tare da miƙewa yabar daining ɗin.
Sororo tayi tana bin bayan shi da kallo harya ƙarasa cikin falo ya zauna a one seater ya ɗauki remote yana serching chanel.
Ƙarasowa tayi gabanshi ta zauna a ƙasa tana bin fuskar shi da kallo tasan idan batai mashi magana ba idan zasu kwana a haka shi baze mata ba sabida rashin maganar shi.
“My Sweet man”
Tai amfani da ƙaramar murya wajan kiran sunan nashi.
Bai amsa ba, itama bata jira cewar shiba tace.
“Naga bakaci abincin ba kama taso baka kulani ba?”
Tafaɗa kamar zatayi kuka!

Seda ya ɗauki manyan lokuta bai ce mata ƙala ba sannan daga baya yace mata.
“Basmah wai akan girki munta samun matsala dake kenan? babu yadda za’ai ki girki naci a kwanciyar hankali? yanzu shi wancan yajin da kika lafta a miya ai seya kasheni, Gaskiya bazan juri rashin iya girki ba dan nagaji da siyan na restuarant shekara biyar da aure amman kusan koda yaushe sena fita sayan abinci kona ci agidan ammi, Sabida kinfi bawa aikin ki mihimmanci akan zama ki girki mai kyau ki kula da mijinki koma kina gidan idan kinyi girkin baya daɗi why basmah nagaji gaskiya”
Ya ƙarasa maganar da ɓacin rai.

Tunda ya soma maganar take bin fuskarshi da kallo wato daga jiya zuwa yau Aliyu ya sauya hali kenan jiya yayi mata cin mutunci yau ma kuma yazo yana mata idan yasan irin manyan lokutan data ɓata wajan haɗa mai wannan girkin da baze mata haka ba.
Cikin takaici tace.
“To naji nagode bazan kuma ba”
Zata miƙe yace.
“Dakata ni zaki bawa wannan amsar kamar wani sa’anki? look basma bafa zan ɗauki renin hankalin kiba, Idan har baki sauya ba wallahi zan baki mamaki and kuma daga yau na soke fita aiki ki zauna a gida kema kamar sauran mata”
Yana gama faɗin haka ya miƙe ze tashi tayi saurin riƙo rigarshi cikin kuka tace.
“Dan Allah karka min haka please ina son aikina yadda ban taɓa haihuwa ba wannan fitar ita take ɗebe min kewar yara”
Yadda take kuka kamar ranta ze fita yasa jikinsa yayi sanyi ture hannunta yayi tare da cewa.
“Naji amman daga yau babu wata fita aiki harse kin min girki kin gyaran gida nan da two weeks zan kawo mai aiki dan bazan iya zuba ido gidana kamar kango ba”
Wata zabura tai kamar mahaukaciy tayo kanshi da wani ihu! take cewa.
“Ni wallahi bana son mai aiki babu wata macen da zaka kawon gidana ko tsohuwa ko yarinya”
Wani banzan kallo ya jefa mata ya wuce bedroom ɗinsa ya datso ƙofar waya yayi dasu Ammi sannan yayi nafila yayi kwanciyar shi.

Washe gari tun wajan 7:00am ya shirya cikin black suite yayi matiƙar kyau ya fice office.
A ranar bai samu kanshi ba se dare sabida ayyukan da suka tarar masa.
Daga nan gidan Ammi ya wuce suka gaisa yayi gida.
Kusan kwana uku Aliyu ya ɗauka yana busy sabida tarin ayyukan dake gabanshi dazarar kuma ya tashi daga office seya wuce wajan Ammi yana dawowa gida seya kulle kanshi a ɗaki yana aiki akan shari’ar da zasu fara gabatarwa on monday.
Gaba ɗaya basma ta fita a hayyacinta sabida rashin kulawar da Aliyu baya bata duk ta susuce kullum seta yiwa mahaifiyarta waya tana kuka ita kuma hajiya kwana biyu ciwon ƙafa ya hanata fita wajan malaman nasu bare taji meke faruwa.

Yau kimanin kwanaki biyar da dawowar Aliyu sedai tun washe garin ranar daya dawo basu ƙara waya da Ummul ba har yanzu.

Gaba ɗaya ummul ta koma wata iri ko doguwar hira batayi koda yaushe tana tunanin Aliyu kuma tayi alƙawarin bazata kuma kiranshi ba itama zata ja ajinta irin na mata.
Amman duk da wannan ƙudirin na zuciyarta kullum setai kuka idan ta kwanta bacci tun hajja na faɗa harta zuba mata idanu.
Kusan koda yaushe ƙannenta na gidan hajja suna hira wannan ke ɗauke mata kewa itama kuma ameerah tana yawan zuwa ziyartar ta.
Har zazzaɓi seda ta kwanta na kewar Aliyu ta riga ta saka acikin ranta son Aliyu ajininta yake.

Shima kuma daga ɓangaren shi ayyuka ne sukai mashi yawa sun fara gudanar da wata shari’a ne mai zafi shiyasa ma ko a gidan shi yana ɗaki a kulle yana bincike.
Tuni Basma tayi kwanto ta bashi haƙuri ya barta ta koma wajan aikinta sedai babu wannan sakin fuskar yanzu wani irin shakkar shi take sabida yadda baya sakar mata fuska koda yaushe fuskar shi a ɗaure.

Yau ta kama friday kimanin sati guda kenan da dawowar Aliyu.
Tun wajan 8:00pm yaje gidan ammi zaune yake yana cin tuwon semo shigowar abba yasa yaɗan dakata suka gaisa.
Seda ya kammala cin sannan Abba ya dube shi tare da cewa.

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE