BABBAR YARINYA CHAPTER 3 Oum Aphnan
BABBAR YARINYA CHAPTER 3 Oum Aphnan
Akram zaka jawa kanka bala’i ,am not that stupid ,idiot ,Nonsense nonsensity da ka saba dating dasu bane,And so Also bari kaji yanzu watannan Islam ɗin ba irin wa’innan Rubbish ɗin Ballagazan matan bane da maza ke kallonsu a Arha ba ,Islam ce BABBAR YARINYA,Me babbar…”
“Hey ya isa ,ni nagaju da faɗanki, nasan nayi maki laifi ,amma ban damu ki haƙura ba ,ko karki haƙura wainnan ruwanki,amma abunda kawai nasan inaso a wajen ki shine ki saurare ni,kiji kalamar bakina daga nan ruwanki kimun Adalci ko akasin Hakan” A nutse yike magana hankalinsa da kallonsa sam basa inda take ,suna saitin Hanyar da yike driving .
Kallon Hadarin kaza ta fara binsa dashi ,sosai yaji a jikinsa tana kallonsa amma haka ya kanne
“Baka da laifi Akram ,Laifina ne da na bari ka raina ni…laifina ne” kawai sai muryarta ya fara rawa zata saka kuka
Daidai ya hau kan kwalta ,wani killing smile yayi na iya saman laɓɓa “Hmm yaro dai yaro ne ,Islam bari in tambayeki ,wai shekarunki nawa ne a duniyar da kike iƙirarin ke wata babba ce ? See don fa kins same ni da ajizancin ɗan adam be zamar maki damar da zaki rainani ba,Har kin manta sanda Ni nike maki wanka,wanki,da sauransu? Har kin manta sanda in banci abinci ba bazaki ci ba ? Har kin manta sanda,ki ke mun kata’in ƙaunaaa” danne kunnenta tayi da tafukan hannuwanta gamida tsaga wani irin firgitacciyar ihu kamar wacce taga irin fatal Accident ɗin nan ,wanda ya sashi sakin kanbin motar a tsorace ,sannan da sauri ya sauka akan hanyar gangara gefen hanya yayi parking ,suma motar guards ɗinta sukayi parking a bayansu da sauri suka firfito suka kewaye motar su Islam ɗin .
“Islam ” ya kira sunanta cikin sanyin murya
Ɗago idonta tayi da sika rine da ɓacin rai ,ta watsa masa a idonsa
“My baby Islam Kinson Ina sonki Baby” kamar wanda yike daɗa turara mata zuciya haka take kallonsa
“Oh no! Dont baby me ,Nafi ƙarfin ka Akram dama can kasan ba sonka nike ba shaƙuwa ne kawai irin na soyayyar jini,amma ba so na soyayya ba”
Tsaki yayi “Matsalata dake rashin ganewa nima dama nace so nike maki irin na soyayya ,kawai dai ina sonki”
Dunƙule hannu tayi ta daki gaban motar “Ohhh gosh! ,wai meyasa ka shigo mun mota ,ka shigo ne ka cemun kana sona ,ko ka shigo ne ka nuna mun yes ka riƙa manemin mata baka kunyata”
Ɗan sassanyar murmushi yayi ,ya ɗan sunkuyar dakai yina shafa ƙeya ,sosai yaji kunyar maganarta
“Akram Look up”
Ɗago narkakkun idanuwarsa yayi ya watsa a cikin idonta ,sannan ya ɗan ɗaga mata gira
“Yes Ultimatus”
Wani kasala ne taji ya shigeta,Hmm ya Akram ɗina kyakyawa ne !” ta raya a ranta ,sai dai a zahiri kautar da fuskarta tayi da sauri
“Ki yafe mun Islam ,kece rayuwata kin azabtar dani da rashinki na tsahon shekaru wallahi bazan iya rasaki a wannan karon ba ,don Allah kiyi haƙuri mu sasanta ,wlh na daina abunda kike zargina dashi ,tun ranar da kika kamamu da Usybaby” ɗan tausayinsa ne ya kamata saidai bazata taɓa nuna masa hakan ba ,don haka ,caɓe baki tayi gami da lumshe Ido
“While… Kana shiga mun cikin precious time ɗina ,sauka to naji zan tunanin maganar ka ,yanzu inaso inje gida mummy is waiting”
Kasheta da ido yayi gabaɗaya shi komai nata burgesa yike. A baya tsokanarta yanzu kuma fuzgar kanta dajin wai ita babbar yarinya ce
Haɗe giran sama da ƙasa tayi “Akram ka futa nace wai halan bakada mota ne har yanzu?”
Dariya ta bashi yanda tayi maganar baisan sanda ya tuntsure da dariya ba ,saidai da sauri ya rufe fuskarsa da tafukar hannunsa ,wai shi ne ake ma gorin mota ? Abun dariya
“Naji zan fitar maki a mota amma sai nakai momy littƙe princess gida ,yau ɗaya ai mun Alfarma in zama drivern ki,kinsan girmana ne ace gani inajan babbar yarinya kamar ki Islam”
Wani sasaanyan Ajiyar numfashi ta saki ,sannan ta koma baya tayi luuu ta kwanta tanajin kanta na fasuwa
key yayi ma motar suka bar wajen
A parking lot taso su rabu ,ganin motocin dady Alamun ya dawo gidan da mutanensa birjik ana jiran fitowarsa .
“To sai anjima ko?” kallonta yayi ,sannan ya gyara zaman rigarshi ya buɗe ya fita ya barta still a cikin motar ,saida ya rufe sannan ya leƙo ta window “Amm… Zanje mu gaisa da Dady da Momy”
zaro ido tayi da sauri ta fara kiciniyar buɗe ƙofa “No karka je ,kawai ka fita zance kana gaishesu”
Kallon Ke wacece yayi mata kafin ya kaɗa kai yayi cikin gidan ,itakuwa tsitsinan takalminta ya hanata sauri bare ta cinmasa ,a sace ya waiga ya kalleta ,yina kalloɓ yanda take ɗosana ƙafa kamar me ciwo a ƙafar,ya kuwa guntse dariya “Hmm Babbar yarinya ,lallai gayu da wuya”
Da sallamar shi ya danna kai ɗakin ,ba kowa sai Alhaji Buba dake zaune yina kallon News ,ya ajiye pot belly ɗinshi tus a gaba yina ɗan sipping juice a glass cup ,sosai girma ya ɗan kamashi ,saidai Akwai alamar tsumuwar naira a tattare dashi
Cikin yalwar fara’a ya ɗago ya kalleshi
“My son Yau kaine a gidan? Kace kun shirya da mutuniyar taka?”
Shafa ƙeya yayi
“Baba barka da rana”
Yimasa iso yayi ,a daidainan Hajiya zainab ta shigo da tray ɗauke da fruits a kai ,ta nufo wajen Alhaji Buban
Ƙasan kafet ya zauna yina ƙara gaishesu kansa a sunkuye ,kamar wasu sirikansa
Fuuu Islam tazo ta wucesu ba tareda ta ko kalle sashen da suke ba,A hankali Alhaji Buba ya ɗan murmusa ,yasan yau an taɓo ta gaban goshi,shi har yau ya kasa sanin dalilin saɓanin Akram da Islam
Gyara murya Akram yayi “Baba Nazone dama mu ɗanyi magana akan Islam indai baki da uziri a gabanku yanzu inkuma akwai sai a sakamun rana”
Cikin sauri²n maganarsa yace “Ahhhh Haba..Haba ,wlhy babu koman komai yi maganar ka”
“Dad dama na samar ma Islam Makaranta ne a UK ,Kuma nasan abunda tafison karanta tun tana yarinya shine Kula da gida (Home management) So Shine nikeso Abani dama ta tafi,Dama course ɗin da naje ban kammala ba ,sai in zauna in kula da ita acan kafin ta saba”
Shiru Alhaji Buba yayi cikin ɗan Nazari ,kafin Hajiya zainab ta yanke shirun da cewa
“Menene don kaje da ita ai yanda muke da haƙƙi akan ta haka kaima kake da haƙƙi a kanta ,don haka ba abunda zamuce maka sai Sanya Albarka ,Allah ya taimke ku ”
Murmushin ƙeta ya ɗanyi sannan ya sunkuyar dakai yina amsawa da “Amin”
Ajiyar Numfashi Alhaji Buba yayi yinajin saƙe² a ransa ,Anya ba ɓaraka a gaba kuwa? To ya ya iya dole yayi mashi fatan Alkhairi bayan ya tambayeshi lokacin tafiyan ,yace masa nan da sati biyu
Tambaya
Meye Alaƙar Akram da Islam ?
Sannan wani isuwa Akram yike dashi a shaanin Islam har ya hana Iyayenta musu mashi a tafiyarsu America?
Anya ba matsala haɗa baligi da baliga tafiya har wata uwa duniya su kaɗai? Baligin ma me shaawan tsiya irin Akram??