BABBAR YARINYA CHAPTER 4 Oum Aphnan
BABBAR YARINYA CHAPTER 4 Oum Aphnan
_Wasu Na cewa wai Anya Oum Aphnan ɗin nan Musulma ce kuwa? … To Tambayarku ta dawo gareni,saidai banda Amsarku A ynz ,Amma in kuna jin tantama zaku iya ɗabbaƙa mun kalma Asshahada sai kuga in zan karɓa._
Da ƙyar Islam ta yarda ta fito dinner ,bayan kiran da suka dinga mata a waya a cewarta tayi fushi dasu ,tinda suka bar Akram ya zauna basu hanashi ba to tabbas sun daina sonta.
A dinning wani shan kunu tayi tana cusa abincin kamar magani, taƙi haɗa ido da kowa ,saidai Hajiya zainab ɗin da Alhaji buban su kalli juna su guntse dariya.
“Baby” Alhaji buba ya kira sunanta a hankali ,kumburo kumatu tayi amma ta kasa magana
“Baby Girl” Hajiya zainab ta sake kiranta
Murya can ƙasan maƙoshi ta amsa da “Um” sannan ta caki Fried plantain taɗan gutsura tana taunawa
“Baki tambaye mu me ya kawo yayanki Akram ba?”
Saida ta juya ƙeya ta kalli ɓangare ɗaya ta babballara harara gamida murguɗa baki kafin tace “So who cares me ya kawoshi,sai yayi ta zuwa in yaso ya shekara anan…ni inma cemun akayi un bar masa gidan bari zanyi tunda kun daina sona” Ƙwalla da ya soma taruwa mata a ido yasata shanyewa gamida yin shiru
Kannewa Hajiya zainab tayi “Oh yeag mu mun isa muce Ki bar gidan nan ke da yike mallakinki mufa dik zamanki muke ,Saidai shi Alkhairi da cigaba yake yunƙurin kawo ma rayuwar ki ,don zuwansa ma yace ya samar maki Admission a UK zakije ki karanta Home managements abun daɗin ma tare zaku tafi…”
Islam data kai glass cup baki ta kurɓi lemo kenan ta furzo shi waje
“What??” ta tambaya gamida zaro ido
Kafin suyi wani yunƙuri ta ɗaura da bala’i kamar wacce ta tasa ƴaƴanta a gaba
“Ni?…Ni dai Islam nine zan bi Akram UK da sunan wai karatu,kuma ma in rasa a abunda zan ƙare sai a mai koyan dafa abinci! Wannan shine abinda bazai taɓa yiwuwa ba ” tana kai aya ta ture kujeran da take kai baya ta miƙe ta bar masu wajen gabaɗaya
Waigowa Alhaji Buba yayi ya kalli Hajiya zainab
“Ko zaki ki ɗan rarrasota? Nifa dama shiyasa ban goyi da bayan tafiyar nan ba”
“Haba Sweet haba don Allah ,wannan fa abun na Islam yina neman yawa ,kar mutane suzo suga yanda take maltreating ɗin mu a fita da ita a baki da sunan bata girmamu muji kunya”
“To ai laifin kine ,ke kika sangarta ta”
“Haba Alhaji ni ko kai?” take suka fara musu ,kowa yina zargin ɗan uwansa da bada gudunmawa wajen lalacewar tarbiyyan Islam…Ƙarshe dai Hajiya zainab ne ta janye maganar ta miƙe tai masa saida safe ,yasan tayi fushi ne amma kawai sai yayi burus da ita shima yayi hanyar samansa .
*****
Akram kam tun kafin ya bar gidan ya kira wayar drivern Office ɗinsa ya kwatanta masa Gidansu Islam yazo ya ɗauke shi.
A back seat ya zauna cikin motarshi GMC ,lumshe ido yayi ,yina tuno sanda Islam ta wani ɗaure rai gamida haɗe giran sama da ƙasa ,tana tambayarsa wai Anya har yanzu ma ka mallaki motar kanka?
Dariya ya sake fashewa dashi ,yina tuna yanda ta wani yi balance cikin fasuwan kai ala dole ga ita Babbar yarinya
Wayarsa ne ya fara ɓurari ,Kallar wayar yayi yaga baƙuwar number ce ke kira a kuma personal phone ɗinsa ba na wajen Aiki ba
Kamar zai ƙyale wayar sai kuma ya ɗaga tunda yasan duk wanda zai kira tanan tabbas family member ɗinsa ne.
Ɗauka yayi ya kanga a kunne
Ta ɗayan sashen akace “Hello” Gwale ido yayi cikin mamakin muryar mace
“Assalamu Alaik,waccece?”
“Sorry durling dama na kira ne in tabbatar in numberne ashe kuwa shine ,Affa?”
Tsaki yaja cike da ƙuluwa “Wai wanene plz”
“Oh Mr. Man calm down na aza ko cikin muryoyin mata dubu zaka iya cankar muryata? Hmm karka damu to Khairy ce your cleaner”
Wani mitsiyacin tsaki yaja kawai ya kashe wayar yina jin ransa na tafasa ,shikam wa ya bata numbersa ? number ma na gida ba na wajen aiki ba?
****
Next day Evening
Islam kwance take akan bangajejen gadon royals ɗinta sai juyi take cikin barci mai ɗauke da mafarki mai tsayuwa a rai ,Dirkuwar motocine ,ya isheta a barci da ɗan hayaniyar mutane haka daga can tsakar gidan.
Cikin fushi ta miƙe ta kwaye cikinta daga cikin blanket ɗin ,ta sako ƙafarta ƙasa daga ita sai ɓingilar riga armless da ya ɗan gota gwuiwarta da kaɗan.
Zuwa tayi gaban windown ɗakinta dazayi hango mata tsakar gidan ta leƙa ,Wani Tsaki ta saki me cike da ƙuluwa ,Ɗaga murya tayi ta ƙwalla ma guard ɗinta kira
“Amaka!!”
Guards ɗinta da suke zaune akan plastic chairs a ƙofar ɗakinta , suna hiransu cike da fara’a da Nishaɗi ,ga alama dai sunajin daɗin zuwan wa’innan Baƙin ,A furgice wanda aka kira da amaka ya miƙe “Yes Ma!”
Ya Shiga ɗakin saidai a bakin ƙofar ya tsaya
“Barka da yamma”
Ɗan yamutse fuska tayi
“Hayaniyar me nike ji? ,A waje?”
“Eh to ,dama Yaron Gomna ne Ishaq maga ,wannan babbar lawyan dake da kotuna a ƙasan Ingila ne yazo neman Aurenki shine kike jin jiniya!”
Wani tsawa ta daka masa “Oh sharraf!”
Da sauri ya ɗinke bakinsa
“Go and tell them to turn that blurdy Noisy Idiot off”
Zaro ido yayi jikinsa na ɗan rawa “Ehem hajiya?”
Ranta ƙara ɓaci yayi “Bakaji da kyau ne? Wuce kaje kace su kashemun banzan jiniyarsu inason inyi barci ,this is just 5:00pm “
Da sauri ya juya ya fita daidai nan ya haɗe da hajiya zainab ta nufi ɗakin Alhaji Buba da sauri ,shima ko bayanta yabi don ya faɗa mata abunda Islam ta aikesa yayi tunda gaskiya shi bazai iya zuwa ya faɗa ba.
Saidai yana soma kiranta ta dakatar dashi da hannu
“kaga ina zuwa ,munyi baƙi dakace ni kaɗan” tana maganar tana hayewa ɗakinsa
****
Jin An kwashe a ƙalla mintuna Biyar baa ɗauke ƙaran jiniyar ba ya sata harzuƙa ,a yanda take ta suri Room slippers ta fice a zafafen ƙarshe ,tana ƙwallawa su Amaka kira saidai bataga kowa ba ,hakan ya sata wucewa tsakar gidan , ta sa a dakatar da kanta amma a ranta tana kimtsa rashin mutuncin da zatayiwa su amaka ƙilan ma yau ɗin nan zata dakatar dasu a bakin aikin su ,don basu da amfani kasancewarsu guards ɗinta
Harabar gidan ta fito Sosai daidai Sojoji sun rufo masa baya cikin isa da shiga ta Alfarma
Wani haɗe rai tayi tamkar me jin amai,tana masa kallon raink wani lukuti dashi,shikam sai ɗan murmushi yike mata dukda ,daka kalli fuskarsa ba ma’abocin fara’ar bane ara yayi kawai ya yafa
Riƙe ƙugu tayi a bakin ƙofar da zasu shiga ma’ana inda akayi masu iso
Ƙyar yike kallon suranta cikin lafaffen cotton ɗin rigar jikinta ,sosai ya yaba halittarta saidai baiji daɗin fitowarta a haka cikin mutanensa ba ,sam ba girmansa bane ,amma zaiyi mata uzurin yarinta ne da ya aureta zai gyara abinsa
Cikin tsawa da bala’i ta kallesu “Ashe ban aiko a kashe mun wannan lousy Noise ɗin ba ,kun gallaze ni ina barci wannan wani irin zaluncine ?”
Jikinsa rawa ya somayi ,da sauri ya matsa gabanta ,cikin sassauƙar murya irin na wanda basu saba ɗaukan kwaram ɗin jama’a ba yace “My love”
Tsawa ta daka masa gamida ɗaga masa hannu tana faman hura hanci “Oh shut that your dirty mouth up !…ka kawo mun Wa’innan Irresponsible Nonentities ɗin cikin gida saboda selfishness ɗinka duk sun hargitsa mana gida this evening an katse mun barci who dare you ,Da zakasa a kawo mun wannan Good for Nonthing Fools ɗin ehem?”
Ta ƙare tana ɗaga jijiyar wuya kamar ta samu ɗan cikinta
A hankali ya tako gabanta yina ɗan ware hannu ,yanda zai mata magana cikin sulhu
“Haba ke kuwan,karki kunyata ni cikin mutane na mu shiga ciki sai kiyi mun magana a tsanake,tunda kinga ko banza dai abun arziƙi ta kawoni da nufin mu ƙulla soyayya mai tsafta cikin ƴan ƙalilan kwanaki mu angonce…”
Ras ! Taji gabanta ya faɗi ,take taji gabaɗaya ya koma mata baƙi wuluk a idonta ,rasama me zatayi masa tayi ,kawai Ɗaga hannu tayi bai aune ba saidai yaji ɗauuuuu!! Ta dalle sa da mari wanda ya sashi razana gamida sakin baki shaye da tsananin mamaki ,a take lafiyayyun yatsunta biyar suka bayyana a kuncinsa
Asheƙeƙe ta kallesa tana jin yanda ƙirjinta ke kaiwa da komowa a zafafe,sannan cikin gatsali ta ɗaura da masa magana
“An faɗa maka ni ,Islam Kwantai nayi da zaka kawo mun wasu sillallun ƙafarka nan wai…(Ta shiga kwaikwayan yanda yayi magana) Abun Arziƙi ya kawoni da nufin ƙulla soyayya me tsafta dani dake fa !!” Haɗe rai ta kuma yi “Oh gerrout ,tsami kawai
Cikin zafin nama ta danno ƙofan sai ji kake kararaf ta kulle ƙofar ,ta barshi anan tsaye dafe da kunci kunyar duniya ya gama shansa ,ko motsi ya kasa yi bare har kuma ya iya ɗaga ido ya kalli guards dinsa da suke ganin kimarsa.