BABBAR YARINYA CHAPTER 6 Oum Aphnan
BABBAR YARINYA CHAPTER 6 Oum Aphnan
Razana yayi da yanke Hukunci Alhaji Buba ,take ya soma bashi haƙury don yasan idan har aka haɗa auren shi da Islam ba abunda zai gadar sai rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali,ƙarshenta a rabu kuma zumunci ya lalace.
“Abba ai ma Islam Haƙuri a bata lokaci ta fudda wanda takeso!” tsaki yaja gamida gyara zaman sa sosai
“Ai ba na faɗi magana don Ace mun sorry bane in haƙura ,dakai da islam ɗin duk avun hukunci na ne ,kuma na zartar da hukunci saidai in baka son jinina ne to sai ka faɗa mun inji”
Sunkuyar dakai yayi yina bashi haƙuri amma haka yayi ɓarin iska dashi,ba arziƙi ya ɗauki waya ya fara kiran Inna Lami
Saida suka gaisa kana ya miƙa masa wayar ,Gaisuwar mutumci sukayi kafin ya faɗa mata gundarin dalilin kiran nasa
Ɗauke wuta tayi na ƴan sakonni ,saboda tasan akwai tiƙeƙen aiki in akayi gigin haɗa auren Islam da Akram,Inama zai yiwu ,matar da ta tsanesu take allah wadai da talaka ,har take iƙirarin wanda ya talauce baƙin halinshi Allah ya duba ya barshi a talaka!
“Ya naji kinyi shiru ,ko akwai damuwa ne? Naso a kira shi malam ɗinne to yaƙi yarda ya riƙe salulan zamanin nan gashi nasan yanzu yina gona”
“Alhaji dama wato ina jinjina lamarin ne ,ita Islamiyyan tace ta yarda ne?”
“Nine mahaifin Islamiyya ,nine nike kuma da ikon zaɓa mata mijin aure da zai kula da ita a musulunce don haka na rigada na yanke hukunci ,gobe da safe zan aiko da mota akwashi ƴan ɗaurin aure ,ana idar da sallar jumu’a za’a ɗaura aure Inshaallah ,hajiya zainab ko bana numfashi a gobe ku cikamun wannan shine burina na ƙarshe”
Tsiri² sukayi da ido ,har yayi sallama da inna ,sannan ya juyo ya kallesu cikin ƙufula
“A tashi a bani waje”
A hankali Akram yaja ƙafa ya fice ,aikuwa Da gudu Islam ta wuce ɗakinta ,tana zuwa ta faɗa kan bed ta ɗaura hannu akanta sannan ta daddage ta kurma gigitaccen Ihu,wanda saida ilahirin gidan ya amsa,shiru ta ɗanyi tana rarraba idanuwa a tunaninta ko iyayen nata zasi shigo da gudu su rarrasheta saidai wayam ba karan da ya leƙo ,shikam Alhaji buba kiraye kirayen wayansa ya cigaba dayi yina shaida ma mutanensa ɗaurin auren tilon ƴarsa gobe bayan An sauka masallaci
****
Tun tanajin kamar kuka shine mata mafita ,har dai taɗanyi la’asar taje gaban mirror tayi zuru tana ƙarewa kanta kallo,Nikam me Allah ya tawayeni dashi,wanda kuɗi bai bani ba? Haba Ace duk kashe kuɗin da nikewa jikina don kawai in auri rantsatstsen mai kuɗi sai in rasa wanda zan ƙare mawa sai Akram da ko keken hawan kansa ya gaxa mallaka saboda sun riga sun ƙulla abota da tsiya?
Shiru tayi tana tuno rayuwar da suka gudanar acan baya ,da irin tsiraɗin Talaucin da ta ƙetare ,anya zata yarda ta koma wannan ritsitsin Matsalar??
Takaicine ya ƙara ƙular da ita ,yanzu fa da ace ɗaya daga cikin masu mun rawar ƙafa na samu na tsaida ɗaya in aura ai da duk haka bai faru ba .
“Allah sarki ne ” ta faɗa a zahiri sanda ta tuno da Prince Adam,Yaro nagartacce Abun nemar kowata ƴa mace .
Ranar wata jumu’a da safe ,Prince Adam ƙarƙashin masarautansu ya aiko da takardan neman izinin ganawa Da Islam in iyayen ta sun yarda. Zo kaga fara’a wajen Hajiya zainab cikin gaggawa ta tura masu da accepting letter .
washenkari Asabar da yamma kuwa ,ya shiryo cikin tsadajjen shigarsa da magoya bayansa da babbar Amininsa suka taho gidan Alhaji Buba.
Shigarsu babu daɗewa akayi masu iso falon manyan baƙi na musamman
Hajiya zainab da kanta taje ta ɗauko ma islam kaya masi daraja ta kawo mata tareda kwakwkwafanta ,acewarta dama Islam jin kanta da fafanta ,tafi dacewa da gidan sarautan aje can dai zai fi.
Cikin rawan jiki da lallaɓawa Hajiya zainab kema Islam Nasiha ,tana daɗa kimtsata tana rataya mata wani faskeken gold a wuya tamkar ita ɗin queen ce da kanta.
Caɓe baki Islam tayi “Momy wa ya zo wajena ?”
“Ɗiyata namijin da yayi daidai da tsarin rayuwarki ,prince Adam nasan kin sanshi ,kuma tabbas inkin natsu kuka zanta zaki soshi”
Wani Siririyar Ajiyar ziciya ta aje a hankali ,kafin ta basar ta shiga da shiryawa
Tana fitowa,sukuma suna tunkaro ƙofar ɗakin ,da tawagarsa ɗuuu ,masu malunmalun da fadawa sai zabga masa kirari sukeyi ,wani soyuwa ne taji ranta yayi ,yanzu ji ta zeronta ba masu dafe mata baya amma jishi yuuuu kamar wani Hamshaƙin sarkine yike tafe?
Ƙiran guards ɗin ta tayi a waya sai gasu da sauri su huɗu sun dafe mata baya cikin suit ɗinsu .
Tunkaron juna sukayi sosai ,kowa na kallon ɗan uwansa ,Adam miskiline na ƙarshe don haka ya ɗaure fuska dukda a ransa kallonta kaɗai da yayi ya samu natsuwa.
Aikuwa kamar mai majnunan Aljannu take taji ta tsanesa ,a cewarta ai baayi namijin da zai kalleta ya kauda kai ba just like that! maimakon ta kulashi kawai sai ta ɗan ɗaga ƙafa tana neman raɓeshi ta nufi wajen parking lot.
cikin sauri yace “Ahmmmmmm…” ya ɗaga mata hannu saidai rashin sabo da magana yasa muryar ta cije a maƙoshi taki fita
wani kallon up and down tayi masa ,bilhaƙƙi take neman ƙaƙalo masa muninsa ,sannaɓ ta coge a ƙafafunta ,gamida riƙe ƙugu.
“My princess am here for you ina zaki?”
wani fitinannen tsaki taja da saida tsikar jikinsa ya tashi,a duniyarsa ya tsani tsaki
“Ni ka faɗa mun zuwanka? To bansan da zuwanka ba,don haka bazaka shiga cikin tsadajjen lokacina with your silly things ,so plz can excuse me ,Ynz Akwai super market ɗinda suke jirana”
Shanya baki yayi yina kallon tsiya mai ɗaukeda madarar Isuwa
Haiƙam yaga zafa ta tafi ta barsa in eeadiness ta kunyatashi cikin mutanensa
Ɗan ɗaga murya yayi “My princess!” kuma ya isa gabanta da sauri
“Y nah?”
ɗaga masa hannu tayi da sauri “Uhm hmmm karka dameni,rather zan rejecting duk wani Appointments da zai biyo ta wajenka…..(Ɗan kallon gefenta tayi ,and she calls) Guards!!?”
Da sauri suka nufi bakin ƙofar motarta suka buɗe mata ta faɗa gaban driver
……Wani zazzafan ajiyar zuciya ta ajiye ,cikin ɗan ƙaramin nadama “Oh Allah! Da na sani da ban wulaƙanta shiba gashi tun daga ranar bai ƙara zuwa ba ,bai kiraba,ynz gashu zata ƙare da auran talaka dan mitsiyata da sam basu gaji Arziƙi ta kowani suffa ba!”
*****
Asalin Labarin Tushen komai.
Littafin Nan ba wanda xai ganeshi sosai sai wanda ya bini a *AUREN SHA’AWA* don Haka bari muɗan ƙetara mu dawo cigaban labarim Auren Sha’awan
Kafin nan mu dakata ! Kin shirya biyan kuɗinki?? To ₦200 ne regular ,inkuma vip ne ₦500 ,sai kuma masu son special ₦1000 duk ta nan bank ɗin 7782217014 ,Mohammed Hassana ,fcmb
Ko kuma katin MTN ta wannan Number 09065990265