BAKAR AYAH CHAPTER 5 BY SADI-SAKHNA

BAKAR AYAH CHAPTER 5 BY SADI-SAKHNA

 

 

“Ke Madeena zoki rakani gidan Hajiya ladi,na daɗe banje ba,kullum cikin samun abin tashin hankali muke”
“Kai ummah Binciken semina fah nakeyi,maleeka ta rakaki mana”
Haɗe girar ƙasa da sama tayi,tasani sarai babu wani bincike da takeyi,dan tana jin ƙarar game ɗin candy crush a wayar tata,Kawai dai dan kar tajene su haɗu da Al’ameen a gidan,Babban ɗan Hajiya ladi wanda suke son haɗata dashi,shi yana so,amma madeena kam kwata kwata bayyi mata ba.
“Banason shashanci dallah sanjo kayanki kizo mu tafi,yara ana nuna muku abinda zai taimakeku kuna wani abun daban”
Cikin zumbura baki babu yanda zatayi ta sanjo kayan harda guntun hawayenta.
Tasan badan komai mahaifiyarta take son haɗata dashi ba,saidan yanada kuɗi,ita kuma wanda takeso bashida kuɗi,tunda ummannata taji zancen a wajen Maleekah tayiwa tufkar hanci,a cewarta ƴaƴan ta bazasu auri talakawa ba.
Tafiya suke a motar Madeenah tacika tayi fam,babu abinda ma yafi bata haushi kaman yanda yadunga yi mata izzah,dan yasan mamuƙata ake a wajensa,kawai dan yasameta mai sanyi bata mayar masa magana.
Basuyi tafiya mai nisaba suka iso gidan Hajiya Ladin,shima gidane tankatsetse naji da faɗa,kana ganin tsarin gidan kaga jiji da kan yaran gidan,kasan sunayi ne da dalili.
Wanda hakanne yasa su Madeenah jin haushin ƴaƴan aminiyar uwartasu.
Suna fitowa daga mota ,wata mata tayi musu iso zuwa ainihin falon hajiya ladin,ba wanda take tarbar mutane haka ba.
A zaune take a falon suna taɗi da ƴar ta guda ɗaya mace JAWAHEER,wanda bazata wuce sa’ar Madeenah ba,dan set ɗin su ɗaya ma,saidai ita Business Admin take karanta,irin na Jabeer.
Dukkan ahalin guda biyu babu wanda baisan yanda ake muradin haɗa jabeer da Jawaheer aure ba,saidai kash lubna tayi musu cikass,tazame musu kaɗangaren bakin tulu,har kawo yanxu babu abinda basuyi ba,amma su kansu sun tabbatar Asirin lubna yafi nasu ƙarfi,babban tsoron su kar Jabeer ya aureta a yanxu itama ta kasheta.
Sakalci take zubawa son ranta,ita kuma hajiya Ladi tana shafa mata kai,wanda yake kan cinyarta,duk da shigowar su hajiya Zeenah ma hakan bai sa ta ɗago ta kallesu ba,saima ƙarawa abinda take ƙaimi.
Hajiya ladi ce ta kalli Jawaheer tareda cewa.
“Kai mana Baby waike ko kunya bakyaji yin fitina a gaban mutane,kuma hadda maman yayannaki koh,ki tashi ki gaishesu mana,sannan ki kawo musu ruwa”
“Toh amma ruwa kam su jenifer suna nan su kawo musu mana koh momy,kinji fa nace miki jiya jikina tsami yayi dana tashi a bacci”
Ƴar dariyah hajiya zeenah tayi,tareda cewa.
“Ohhh lallai Jawaheer ɗin mama,har yanzu dai kece da cinya koh,saiki sha magani ai ki huta”
Sakin baki Madeenah tayi tana jin abinda ummanta ta faɗa,tsamin jikine zai hana mutum kawowa baƙi ruwa,kuma ji abinda suke faɗa…..anya kuwa ba asiri hajiya Ladi tayiwa uwartasu ba,inba haka ba wannan ai ya wuce ɗaukar tunani.
Harara Madeenah ta gallawa Jawaheer,wanda itama ta rama a take,kaman ba itace take sakalcin ƴan shekara biyu ba,gaisuwar da akace tayin ma batayi ba ta tashi ta tafi. Half vest ce a jikinta sai bom short,su a dole suna kwaikwayon turawa,ko mahaukaci yagani yasan abin bayyi tsari ba,amma Hajiya zeenah idonta ya rufe akan mutunin nata (kuɗi) kwata kwata bata ga hakan ba.
Har taje bakin ƙofar fita daga falon ta juyo ta kalli Madeenah.
“Ahh Madeenah zamuje ciki mana na rakaki sashen Yah Ameen”
Kallon ta Madeenah tayi babu yanda ta iya tabi bayanta,saboda kallon da Hajiya zeenah tabita shi,na gargaɗin karta musa.
Itakuwa tasani sarai ba abin arziƙi bane yasaka Jawaheer ƙiranta,dan tafi kowa sanin wacece Jawaheer ɗin.
Kaman kuwa dama jira suke,Madeenah tabin bayan Jawaheer hajiya zeenah ta matso gefen Hajiya Ladi.
Labarin abinda ya faru tafara zayyane mata na mutuwar hafsa,kasancewar basu samu tattauna hakan ba ana abin mutuwar.
Wani murmushin ciki ciki hajiya ladi tayi,koba komai taji daɗin hakan,duk da taso lubna ce ta mutu,in suka tashi hafsa bazata yimusu wahalar kawar wa ba a cikin tsarin.
“Toh naji mai kikace Zeenatu,amma ya kike ganin zamuyi yanxu toh,wanann idan muka barta bamu san wani irin barazana zatayi ta kawowa ba,sannan gaskiya bazan yadda Jawaheer tazama surukarki ba wannan matar tana gidan”
“Nasan da haka,abin da yafi mu zauna a mukawo shawara kawai,ni burina shine ta fita daga rayuwar ɗana,yazamana cewar inada iko dashi yanda naga dama”
“Plan biyu zamuyi yanzu,na farko shine ki ƙirasu dagashi har matar tasa,kafinnan ki tabbatar yasha wannan maganin a abinci tukunna.
Komin asirin dayake jikinsa to a take zai daina aiki na minti talatin,a lokacin saiki umarceshi da yayi mata saki uku,kinga koya dawo asirin dai aikin gama ya gamu.
Idan kuma wannan bayyi aiki ba,to inaga wata matar zamu aura masa,mu nuna mata muna tareda da ita,ta dunga yin duk abinda muka ce,idan tayi nasara akan Lubnah itama saimu kawar da ita,idan kuma batayi nasara ba itama ta kasheta,shikenan kinga dai ba ƴar mu bace dai abin ya faɗa kanta ba”
“Wanann aiki yayi,kai ai ƙawance dake Hajiya ladi nasara ce,da duk ban tuno haka ba…….”
Suna barin falon sashen Jawaheer suka nufa.
Part ne mai zaman kansa dukka natane,komai taga dama shi takeyi a ciki,da ƴan aikinta da komai.
Zama tayi akan kujera tana kallon Madeenah wacce take tsaye batace komai ba.
“Ki zauna mana ko sai na zaunar dake,bar ganin ina kallon inda kike,wallahi albarkacin kin haɗa jini da masoyin xuciyata kike ci,idan ba haka ba ke kin isa kiga inuwa ta ma…..gayyar tsiya kawai,kin tsaya akaina babu wani nuna ladabi,kaman ba yayan ki zan aura na”
“Ai koh yayana zaki aura?…meyasa har yanzu baki aureshin ba toh,wannan zancen har ya gunduri masu jinsa,anaso ana tsoro,in sonsa kike da gaske ki aureshi mana yanzu ƙirr,ina baki jiki a kabarinki ba,ƙaramar ƴar iska kawai.
Batun na nuna miki girma kuma,ke inban da na jefa yayanki a gwandon shara na ƙi aurensa,ai da yanzu na daɗe da zama babbar yayarki,kuma…….”
Kafin Madeenah ta cigaba da magana Jawaheer ta wanketa da wani mari mai ƙara,wanda hakan yasata yin shuru da abinda take faɗa ta dafe kumatunnata,ɗaya hannu kuma ta wanke Jawaheer itama da mari.
Faɗa suka fara da doke doke,inda Madeenah ta buga Jawaheer a akan tiles ɗin falon,daidai shigowar su Hajiya ladi kenan,ƴar aiki ta shaida musu mai yake wakana.
Da sauri hajiya ladi ta ture Madeenah akan Jawaheer tana salallami.
“Yau mai zan gani,Madeenah karya min ƴa zakiyi ki fallasheni,ji wani bugawa da kika mata wanda tunda na haifeta bata yi ba”
Jawaheer najin haka ta fashe da kuka tana yarfe hannu,kaman ba itace tafara takalal faɗan ba.
Hannu hajiya ladi tasaka a fuskar Jawaheer tana shafa inda Madeenah ta mareta,wanda yayi jajur yaji fuskar ƴar hutu.
“Mari!!!…..?”
Shine abinda Hajiya ladi ta faɗa cikin bacin rai.
Dukkansu su ukun Madeenah suka tsaya suna kallo harda Hajiya zeenah,ganin hakan yasa itama tayi saurin cewa.
“Itace tafara marina,dan kawai nace idan tanason yaya Jabeer ƙirr ta aureshin mana,shiyasa nima na ram……”
Wani marin Hajiya zeenah tasake zabga mata a ɗaya kuncin,sanann cikin bacin rai ta haɗa da cewa.
“Dan tana son yayanki shine zaki dunga yimata haka,ai tafiki tunda ana saka ta yin abu tayi,da kika bugata a ƙasa idan kika karyata fah,dallah wuce mutafi gida,batun aurenki da Aminu kuma ba fashi,ina akan hakanne kike hucewa akan ta,mai baƙin hali kawai”
Masifa Hajiya zeenah ta dunga surfawa Madeenah,yayinda ita kuma Hajiya ladi ta rungume Jawaheer tana shafa bayanta,har sanann bata daina ihu ba kamar ƴar yaye.
Hawayene yake zuba akan fuskar Madeenah,badan zafin marin da aka mata ba,saidan zafin takaicin yanda har yanzu mahaifiyar tasu ta kasa gane mai yake faruwa,idonta ya rufe kirif akan muradanta,ko ƴaƴan ta bata iya buɗe ido ta gani,bare wani abun taban.
Sallama Hajiya zeenah tayiwa Hajiya ladi tareda bata haƙurin abinda ya faru,har sanann bata wani huce ba,ciki ciki take amsawa,ita a dole an taba mata rabin rayuwarta.
Takaici in yayi dubu to ya kama Madeenah har maƙoshinta.
Suna shigowa gida Madeenah ta shige ɗakinta tareda rufo ƙofah,har wajen magriba bata fitoba,Hajiya zeenah kuwa batabi ta kanta ba,dan ita ta manta ma da ita.
Tafiya take tana zuwa tana dawowa a falon,gabaɗaya abinda aminiyar tata hajiya Ladi ta faɗa mata take tunawa na jiya. Shin zayyi aiki ko bazayyi ba bata saniba,da aika a ƙiramata shi,har yanzu bai shigoba,so take ta ƙirashi cin abincin safe yau.
Maganar Iyani ce ta dawo da ita daga kogin tunanin data tafi. Amintacciyar mai aikinta,koh su Jabeer ma tashi sukayi suka ganta a cikin gidan,komai nagidan kaff tasani,saidai ba komai take saka baki a cikiba,mijinta kuma shine masinjan Alhj Aliyu,wanda bayan ya sauƙa a kujerar CEO ma,bai yasar dashi,sai yace suzo gidan su zauna.
Abinda Hajiya zeenah bata hana na da taji zancen,saboda tanajin daɗin aikin iyani sosai,komai tagani bazaka taba jinsa a wajen wani ba.
“Hajiya angama haɗa abincin yanda kika ce”
“Okay shikenan bari su ƙariso”
Tana nan tsaye a wajen Jabeer ya shigo shida Lubna,fuskarsu ɗauke da mamaki wai Hajiya zeenah taƙirasu karin kummallo a sashenta,abinda bai taba faruwa ba kenan,har lubna tace bazata zo ba,saidai kuma komai yakamata kaje kaga menene.
Kujera suka ja kowa ya zauna bayan sun gaisheda itah,iya Jabeer ta amsawa,luban kam ko kallonta batayi ba,itama data ga haka ta yatsina fuska.
Iyahni ce ta zuba musu abincin dukka kafin ta koma gefe.
Abincin suka fara ci,har sun kuka gamawa Hajiya zeenah ta miƙawa Jabeer kunun gyaɗa a cikin jug mai sheƙi.
“Ka kunun gyaɗa anyi,kaine mai sonsa sosai,nasan kuma yanzu baka samun arziƙin shansha tun mutuwar matarka”
Kallon lubna yayi ƙasa ƙasa kafin ya ɗauki jug ɗin ya tsiyanya a kofi.
Itakuwa lubna ko uhm batace ba,dan dama tasani sarai dan aci mata mutunci aka ƙirata wajen.
Bayan sun gama karawar ne wayar Jabeer tafara ƙara,yana dubawa yaga khalil ne.
Goge bakin sa yayi zai tashi,amma maganar Hajiya zeenah daya doki kunnensa ne yasashi komawa ya zauna.
“Koma ka zauna akwai abinda zaka min”
Tana gama faɗin hakan ta ciro paper da biro ta ajiye masa a gabansa.
Kallonta yake sanann kuma yana kallon paper da alamar tambaya akan fuskarsa.
“Ummah wanann kuma fah,wani saƙo zaki aika”
“Eh saƙo zan aikawa ta kusada kai,yanzu nnan basai anjima ba inaso ka rubutawa Matarka saki uku a jikin takardarnan ka miƙa mata”
Zaro ido Jabeer yayi yana kallon Hajiya zeenah,wacce ta turbune fuska kaman a soja a fagen ya ƙi.
“Ummah saki kuma,mai yayi zafi haka”
“Ba zafi ba har ƙonewa ma yayi,yanzu nan ka rubuta kana batamin lokaci,kuma umarni ba wai shawara ba……koka rubuta mata ka bata,ko kuma na tsine maka yanzunnan…….!
Wanne ka zaba??????”

 

 

DOMIN SAMUN CI GABA DUBA 👇

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE