BAKAR KADDARA CHAPTER 11


Koda yashiga daki sai yatarar da miss calls din Mami dayawa amma sai yace bazai kiraba sai yayi wanka yayi sallah, bai damu da duba Dakin da Phendo take ba yahau yin abun dake gaban shi,
Phendo bata tashi dawowa ba sai karfe shida da kusan rabi ma saiya zama na lokacin data dawo din Jimeta yana daki yana shirin tafia wajen aiki dan yau sammako zayyi kuma zai zama very busy a cikin yan kwanakin nan,
Bayan yagama shiri sai yafito falo yana jiran yaga fitowan Buddu amma sai yaji shuru sai kawai yadannawa Mami kira Bugu daya ta dauka aikuwa ta haushi da fada ta inda take shiga batanan take fita ba kuma fadan ta duk akan meyasa tunda suka tafi bai hadata da Buddu sunyi magana ba kuma shibai siyan mata layin kasar ba tunda hatta su Adda rukayya sai complain sukeyi akan hakan hakuri kawai yabata hade dayi mata alkawarin yanzun nanma zai bata sim, tana jin haka sai ta rage fadan data kemai tahau mai nasiha sosai wannan karan nasihan Mamin yafara shigan shi saidai still shifa har yanzu baigama daukan Buddun a matsayin matar shiba,
saidai yarasa gane abun dake damun Shi yanzu bini bini sai Buddun tafado mai a rai sai kawai yaga yasaki murmushi, Bayan sunyi sallama da Mamin saiya shiga dakin Buddun hade da tsayawa a bakin kofa yafara kiran sunan ta kamar dai yanda yasaba,
Cikin bacci taji ana kiran ta saita dan bude idanun ta hade da sauke su akan na Jimetan batasan sanda ta turo baki ba hade da rufe idanun ta,
Ganin hakan dayayi saiya karasa shiga dakin ya isa bakin gadon sannan yace,
“Nasan kina jina idan kin tashi daga baccin kije ki gyara mun daki sannan kiduba cikin wardrobe dina acen kasa zakiga sim ki dauka, kuma ki tabbatar kin kira Mami”
baijira cewar taba yafice daga dakin yana mein haushin kanshi da yanzu bai iya ma Buddun fada shi kanshi yasan yanzu yafara canzawa saidai har yanzu yakasa sanin dalilin fara canzawan nashi,
Saida taji alamun kulle Kofar falon sannan ta diro daga kan gadon tana murna cikin sauri tashige bathroom tayi wanka tafito yau doguwar riga tasaka saita nade gashin kanta hade da sanya wani hular sanyi mekyau,
Sai data gyara dakin ta sannan tafito falo shima ta gyara sai tawuce dakin Jimetan tsayawa kawai tayi tana kallon yanda dakin yayi wani kaca kaca dashi saidai babu datti sai tulin kaya akan gado dakan kujerun dake dakin yawancin kuma kayan singlet dinshi ne da boxer dinshi sunfi yawa,
sai data dauki wajen mintina sha biyar tana gyara dakin bayan tagama saita shiga bathroom dinshi ta wanke shi tass hade da fitowa da inners dinshi taje tasaka su acikin washing machine sannan takara komawa dakin ta dauki sim din dayace mata ta dauka,
sannan tafeshe dakin da wani turaren daki me mugun kamshi hade da kullo mai dakin, takoma nata dakin ta saka sim din a cikin wayar sannan tafito taje ta cire kayan data saka a washing machine ta dauraye ta shanya,
sannan takoms dakin ta gaba daya, bakin gado tasamu ta zauna hade da daukan wayan, Mami tafara kira suka gaisa sannan takira Umman ta sun dadai sosai suna magana kuma yawancin maganar tasu duk nasiha ce bayan sun gama saita kira Abbun ta suka gaisa shima yayi mata nasiha sosai daga nan saita kira Ba!ah shima suka gaisa bayan nan saita kira kaka aiko tasha albarka sosai,
Adda rukayya itace ta karshe da Buddun takira dayake suna tare da Adda lauratu sai Adda rukayyan tasaka loudspeaker suka fara Hiran yaushe rabo a cikin hirar tasu ne Adda rukayya take fadawa Buddu ai ansaka ranan Auren su itada Adda lauratu nanda wata daya sosai Buddu taji babu dadi sanin bazata halacci Bikin ba amma kuma ta musu murna sosai,
kafin suyi sallama Adda lauratu tacewa Buddu zata turo mata da wani littafi ta WhatsApp ta tabbatar ta karanta dan zai amfane ta sosai kuma zata qaru sosai a cikin littafin,
Bayan sunyi sallama Buddun ta katse waya sai tashiga WhatsApp aikuwa tana dubawa taga har Adda lauratun ta turo mata da littafin sai kawai tayi downloaded dinshi tace sai tayi breakfast saita fara karantawa,
Abu me sauki ta dafa na breakfast din bayan tagama saita koma dakin ta takulle ta haye kan gado tafara karanta littafin tun daga farkon littafin tafara gane yanda mace zata tafiyar da rayuwar auren ta, sosai Littafin yamata dadi dan babu abun dake tada ta Sai idan lokacin sallah yayi saita mike tayi sallah takara komawa taci gaba dayin karantun littafin, a ranan saita manta gaba daya da wata Phendo da take cikin gidan,
Dayake littafin baida wani yawa zuwa karfe shida tagama karance shi tsaf tuni tafara hango mugun kuskuren da tayi harta bari Hamma Faruq yadauko wata karuwa ya ajiye mata a cikin gida sai kawai ta dauki laifin ta daurawa kanta duk da tasan Hamma Faruq yafi karfin ta sannan tasan ba sonta yakeyi ba kamar yanda itama ba son nashi takeyi ba,
Koda tafito falo tasha mamaki sosai da bataga Phendo ba amma sai tayi tunanin tana daki ne dan haka sai tace bara ta duba dakin, saidai koda tashiga dakin saita taradda babu kowa dan hatta dakin Jimeta sai data duba amma bata ganta bs sai kawai ta tabe baki tawuce kitchen ta daura dinner,
Abu me saukin dahuwa ta daura tana gamawa ta jera komi akan trey sannan tafito dashi falo ta ajiye hade da wucewa dakin ta tayi wanka tana fitowa ta shafe jikinta da cream hade da wani body perfume me mugun kamshi,. dan ta dauri aniyar kwace Hamma faruq daga hannun ko wace ya mace kuma tana son Tadawo da Hamman nata kan Hanya madaidaiciya ya tuba yadaina aikata sabon Allah,
half gown tasaka wacce ta tsaya mata iya gwiwa kadai sai yazamana gabaki daya fararen cinyoyin ta a waje suke dan simple make-up tayi Sai taga tayi wani kyau wannan karan sai tayi parkin gashin ta bata sake shiba sai tasaka Hula sabida sanyi,
Har tayi sallan isha’i Jimetan bai dawo ba kuma itama Phendo bata dawo ba sai tayi tunanin ai suna tare da Phendon ne kawai sai taji zuciyan ta yana mata wani mugun zafin data rasa dalili tana nan zaune a falo taji alamun ana taba kofa,
Tsurawa kofar ido tayi tana jiran taga wanda zaifara shugowa tsakanin Phendo da Jimetan aikuwa sai sukayi ido Hudu da Jimeta sosai ta zuba mai idanu tana son ta karanci yanayin shi saidai babu abunda ta karanta harya karaso cikin falon ya tsaya a gaban ta sai tayi saurin dukar da kanta a kunya ce tana wasa da wani dan igiya dake jikin rigar ta,
Saida yazuba mata ido na wasu dakikai kana yayi gyaran murya hade dace mata,
“Kallon duk na menene Buddun Mami ko kinyi missing dinane”
Sai yakare maganar da daga mata gira girgiza mashi kai tayi hade da mikewa tsaye tajuya zatabar falon saurin kamo hannun ta yayi hade da dawo da ita gaban shi ya tsura mata ido,
from non where taji hawaye na sauka akan fuskar ta ita kanta baza tace ga dalilin yin hawayen nataba,
Dogon ajiyar zuciya yasaki hade dace mata,
“Namiki wani abunne kike kuka”
Saurin girgiza mashi kai tayi sai tabude bakin ta dake rawa tace,
“Hamma Yakamata ace izuwa yanzu kadaina aikata abubuwa marasa kyau kada kamanta idan har kaci gaba da aikata sabon Allah ba kayi wasu Mami da Ba!ah adalci ba, mutanan da a kullin addu’ar su baiwuci akan kagane kadawo hanya madaidaiciya ba, kada kayi tunanin kosu Mami basu san abunda kake aikatawa bane sun sani kyaleka kawai sukeyi suna binka da addu’a”
saita sanya hannun ta tashare hawayen dake gangarowa akan fuskar ta hade da dagowa ta kalle shi sannan tace,
“Hamma menenen amfanin ajiye matar da ba nakaba a cikin gidan auren ka idan har sonta kakeyi da gaske mezai hana ka aure ta, tunda tanada duk abunda kake so a jikin ya mace, nasan niba zabin ka bace kamar yanda kaima ba zabi na bane amma haka mukayi bibbiyawa iyayen mu, dan Allah Hamma idan har kana son Phendo ka aure ta akan wannan zaman da kukeyi, Hamma kaifa me ilimi ne kasan hukuncin me aikata zina meyasa kazama daya daga cikin masu aikatata bayan kasan mugun illar ta, bawai ina fada maka maganar nan bane akan wai kayi hakuri ka zauna dani ba a’a ina fada makane kawai danka gyara tsakanin ka da ubangijin ka, idan har Bakason zama dani zaka iya sauwake mun nima na huta dan bazan iya zama da mazinaci ba”
tunda tafara maganar ya kafeta da idanuwa saidai yakasa cewa komai harta juya tawuce dakin ta, saida yaji karar rufewar kofar dakin nata sannan ya motsa daga inda yake yana cije lips dinshi,
Kanwar bayan shi itache take neman dawo dashi daga hanya madaidaiciya, Kauco na Ni Faruq,
Tana shiga daki ta silale kasa hade da fashewa da kuka tabbas duk Da bata ganshi tare da Phendo ba amma tayi imanin suna tare shine dai ya rigata shugowa cikin gidan, kuka takeyi sosai data rasa dalilin yinshi
Dakin shi yawuce saiya tsinci kanshi da kasa yin komai dan hatta wankan daya keyi kullin yau kasayi yayi tunanin maganganun da Buddu tamai kawai yakeyi saidai har yanzu baya mata kallon matar shi,
A cikin daren sai yazamana daga Jimeta har Buddu babu wanda ya iya rintsawa, tun a cikin daren Buddu tama kanta alkwarin fara wasan buya da Hamma Faruq din kuma tayi alkwarin idan har bai bar aikata zina ba toh bazata kara bari ya kusance taba,
Shiyasa tun daga wannan ranan suka fara wasan buya sai yazamana ko falo Buddun ta daina zama sai yabar gidan take fitowa ta dauki abunda take bukata takara komawa daki yanzu ko takan Phendo batayi,
A bangaren shi sosai abun yafara damun shi saidai har izuwa lokacin bai bata matsayin matar shiba shidai kawai yana kallon tane a matsayin wacce yake biyan bukatar shi da ita,
Phendo da taga Jimetan yafita harkan ta itama sai tafita harkan shi tunda tanada Donald babu abunda zai dame ta.
Sun kusan fin two weeks a hakan aikuwa ranan wata laraba Buddun ta tashi da wani matsanancin rashin lafiyan daya haddasa mata amai yana falo yafara juyo kakarin aman nata da sauri yamike yakarasa bakin kofar yana bugawa yace,
“Ke Buddu kibude kofan mana koso kike wani abun yasame ki, ki hadani dasu Ba!ah”
Tana daga bathroom tana jinshi saidai aman da bata gama bane yahanata zuwa bude kofan sabida ita kanta tana bukatan a taimaka mata dan gabaki daya tagama galabaita daman gashi ita idan tafara ciwo mugun jiki take sha,
Dakyar ta iya fitowa daga bathroom din taje tabude mai kofan hade da zubewa a kasa cikin sauri yakarasa inda take hade da tallabo ta ya kwantar da ita a jikin shi yashiga tambayar ta abun dake damun ta,
Kasa cemai komai tayi in banda lumlumshe idanuwa da takeyi ganin hakan dayayi saiya tsorota kawai saiya dauketa kamar wata baby yayi waje da ita yasakata a mota kai tsaye asibiti mafi kusa yakaita,
Amsan gaggawa aka mata nandanan aka mata general check up hade da bata gado sai Dr din yace akira mai Jimeta,
Koda Jimetan yaje o!ice din doctor din sai yakosa yaji abun dake damun ta duk da a zuciyan shi yanata rokon Allah yasa ba cikine da itaba, fuskan doctor din dauke da murmushi yamikawa Jimetan hannu hade dacemai,
“Congratulation your wife she’s one month pregnant”
Kamar saukan aradu haka Jimeta yaji zancen sai yakasa bawa Dr din hannu, a zuciyar shi fadi yakeyi,
“Dole ma cikin nan yazube dan wallahi ban shirya haihuwa ba kumama da wannan yarinyan ai abun kunya ne a waje na ace nama wannan yar yarinyan ciki kai impossible dole a yau dinnan cikin nan yazube.

Sosai yashiga cikin tashin hankali saidai baisan ta yanda zaifara yiwa doctor din bayani akan a cire cikin ba sabida yasan dokar kasan amma yasan me zayyi,
Dan dole ya kakaro murmushin dole ya daura akan fuskar shi hade dayiwa Doctor din godia sai yafara kiciniyar mikewa doctor din ya dakatar dashi ta hanyar cemai,
“Ai matar tashi tana dauke da matsanancin damuwa dan haka zasu riketa a asibitin harna wa’insu kwanaki sannan yace a dinga kula da ita sosai Ana ibe mata kewa sabida tarage damuwar da take ciki”
Nodding kansa kawai Jimetan yayi sai kawai yamike yabar o!ice din yana share zufan daya keto mai akan fuskar shi, yana tafia yana magana shi kadai akan lallai lallai yazama dole a cire cikin dake jikin Buddun a haka yakarasa dakin da aka kwantar da Buddun saidai yanda yabarta haka yazo yasame ta Sai yasamu kujera ya zauna hade da sira mata ido,
shi sai a lokacin ma ya fahimci wani kyau data kara hade da cika dan sosai hip’s dinta yakara fadi boobs dinta kuma sunyi wani irin ciccikowa,
Dogon tsaki yaja shi yanzu ba wannan yadame shiba cikin dake jikin Buddun ne ya tsaya mai a rai sosai, wayar shi dake cikin aljihun wandon shi yacuro yashiga Google yafara binciken maganin dake zubda ciki a lokaci guda, bai wani sha wahala wajen samun sunan maganin ba, sosai yacika da wani mugun farin ciki dan tuni yagama tsara yanda zaibata maganin idan aka sallame ta daga asibitin batare data sani ba,
Yana nan zaune har sai data farka tana bude idanun nata da Jimetan tafara cin karo sai tayi saurin kauda fuskar ta sabida wani mugun haushin sa da taji tanaji na yauma yafi na kullin sabida haka kawai taji bata yarda dashi ba a cikin zuciyan ta a yau din,
ganin ta farka sai yayi saurin mikewa yakarasa gabda ita akan gadon marasa lafiyan ya zauna sannan yace mata,
“Ya jikin naki”
Banza tamai hade da rufe idanun ta kamar meyin bacci, yasani sarai bawani baccin data keyi ganin yagaji da zaman ne yamike yafice daga dakin sai yaje yasamu wata nurse yabata kudi akan ta dinga kula da Buddu,
Yana barin asibitin kai tsaye gida yakoma yaje yayi wanka yacanza kaya baima damu da sanin inda Phendo take ba duk da yasani sarai bata cikin gidan,
a takaice dai kullin Jimetan kafin yatafi wajen aiki zaibiya asibitin yaga Buddu amma saidai duk maganar dazai mata koh uhmm bata cemai tun abun baya damun shi har yazo yafara damun Shi sosai a cikin ranshi dan haka kawai yaji yakasa sukuni,
Yau kwanan ta biyar a asibitin kuma sosai shakuwa ta shiga tsakanin ta da Nurse din dan a bakin nurse dinma take jin tana dauke da cikin Hamma Faruq maimakon taji ta tsani cikin sai taji tana mugun kaunar abun dake cikin nata,
Dayake nurse din takira shi a waya tafada mai anbawa Buddu sallama sai daga wajen aiki kawai yabiyo asibitin ya dauke ta suka wuce gida yana parking tayi saurin bude murfin motan tafita tashige cikin gida, dafe kanshi yayi yana jin wani mugun zafi a cikin ranshi shi yarasa abun dake damun shi gaba daya rashin maganar yarinya yana neman ya zautar dashi,
A falo ta tadda Phendo tana cin abinci ko kallon ta batayi ba tawuce daki ta turo kofan da karfi hade da sanya mata key danko fuskan Hamma Faruq din bata kaunar gani,
magungunan da aka bata a asibiti ya dauka hade da sauran kayan da suka dawo dashi daga asibitin yashiga dasu cikin gida, yana bude kofan falo da Phendo yafara hada ido aikuwa tana ganin shi tayi saurin mikewa takarasa inda yake hade da hugging dinshi tana mai wani kukan shagwaba hade damai complain akan yadaina kulata sam,,
maimakon yaji ta birge shi sai yaji haushin ta yakeji kawai sai yace mata,
“Ta kyaleshi yanada abun yi sannan bata ganin Buddu batada lafia ne”
Sosai abun yabata mata rai amma sai bata nuna hakan ba saima fuskan tausayi data yi hade dace mai,, ai batasan Buddun batada lafia ba,
Banza da ita yayi hade da karasawa bakin kofar dakin Buddun saidai ya tadda kofan a rufe, girgiza kai yayi hade da kwala kiran sunan ta yace tabude kofan nan inba haka ba tabari yabude sai yabata mamaki banza dashi tayi karshe ma bathroom tawuce tayi wanka hade da dauro alwala tafito kuma har a lokacin tanajin babatun daya keyi amma sai tayi biris dashi,
Daya gaji ne yawuce dakin shi ranshi a matukar bace tuni phendo tafara hango wani abu a kwayar idon Jimetan like he has some feelings akan Buddun sai taji wani mugun kishi duk Da bata sammaci jin hakan a zuciyar taba tunda tanada Donald yanzu,
yana shiga daki yacire jacket din dake sanye a jikin shi yayi wurgi da ita hade da zama a bakin gado yadafe kanshi yana girgiza kai a hankali yace,,,
“Oh no Buddu kada muyi haka dake mana”
Sai kuma yaji wani mugun bakin ciki daya fadi hakan meke shirin faruwa dashi ne kadadai ace alhakin yarinyan nan yafara kama shine,, sai yayi saurin girgiza kanshi yace,,
“Tirr Allah ya kyauta never abunda bazai taba faruwa ba kenan ni naso wannan little rat din yarinyan da kanwar kanwar baya nane”
A ranan gaba daya Sai Jimeta yakasa sukuni dan yakasa zaune yakasa tsaye bini bini zaije bakin kofar dakin Buddun ya tsaya yana mata babatu hade da mata barazanar inya bude kofan nan Sai tasha mamakin shi karshen ta saiya gaji yabar wurin amma bazai hana anjima yasake dawowa ba haka yake tayi har zuwa cikin dare karshen tadai anan falon ya kwana,
Sai phendo tarasa yanda zatayi tafita sai da taga yayi bacci sannan tayi sadam sadam tafice daga gidan tashige gidan Donald anan take bashi labarin ai matar saurayin nata ciki ne da ita, sai Donald din yace mata kawai ta rabu dashi sabida da zarar yafara samun yara zai wulakanta tane gwanda kawai ta dawo gidan shi taci gaba da zama,,, sosai maganar Donald din tayi tasiri a cikin zuciyar Phendon daman itama tafara gajia da halin Jimetan,
A cikin daren kwana Buddun tayi tana kwarara amai amma sai bata galabaita kamar na ranan ba, amma tana jin jiki ba laifi sai idan aman ya tsaya mata ne sai tafara jin wani mugun yunwa haka zata bude fridge ta dauki Fresh milk ta kafa kai tasha, sabida jikin ta babu karfi anan tsakar dakin bacci ya dauke ta,,,
Washe gari tunda asuba yatashi kafin yaje yayi sallah saida yakara zuwa kofar dakin nata yabuga yahau mata banbani a tunanin shi ihun shi zaisa tabude kofan baisan bama ta dakin ba tun farkon fara bugun kofan dakin nata ta tashi tawuce bathroom sai daya gaji da tsayuwa sannan saiya wuce dakin shi yayi alwala yayi sallah,,,
Dayake baisamu yin wani baccin arziki ba sai yana idar da sallah yahau kan gado ya kwanta bada jimawa ba bacci yadauke shi,,,
Bashi yatashi farkawa ba sai wajen karfe goma na safe cikin sauri yatashi yawuce bathroom yayi wanka yafito yashirya cikin kananun kaya sannan yafito daga dakin baibi takan dakin Buddun ba yafice daga gidan kai tsaye wani babban pharmacy yatafi yaje ya siyo maganin dayayi googling akai,,,
Dayake tana jin sanda yafita saita samu daman fitowa cikin sauri takarasa kitchen tafara kokarin hada abunda zataci duk da batayi tunanin zaidawo dawuri ba aiko tana kitchen yashugo gidan batama sani ba Sai yaga kofan dakin nata a bude har zai shiga dakin zai yaji alamum fitowan ta daga kitchen sai kawai yaja ya tsaya hade da juyawa ya tsurawa Kofan kitchen din ido,,,
Aiko tana fitowa sukayi ido biyu da Hamma Faruq din har saida gaban ta yafadi data ganshi amma sai bata nuna hakan ba sai tafara takawa a hankali harta karasa inda Jimetan yake tsaye ya kafeta da idanuwa bata ankara ba ya sanya gabaki daya hannayen shi yariko ta yayi hanyar dakin shi da ita,,,,
Cikin muryan kuka tace,,
“Hamma kabarni ni bana so bana sonka na tsane ka bana son ganin ka”
Sosai take fadamai maganganu marasa dadi wanda inda tasan yanda zuciyar shi take kuna da bata gayamai wa’innan maganganun ba,
Saida yakaita har cikin tsakiyan dakin shi sannan yakoma yarufe kofan hade da komawa inda take ya kafeta da idanu wanshi da sukayi wani irin jajur dasu,
kuka tafashe dashi hade dabin gefen shi zata wuce ya sanya hannun shi yadawo da ita gaban shi,,
Cikin daga murya tace,,
“ka sakar mun hannu ni bana son kana tabani bana kaunar abunda zaikara hadani dakai Hamma Faruq”
Girgizata yafarayi hade da daka mata wani mugun tsawan daya sanyata nutsuwa yace,,
“Nima angaya maki son naki nakeyi ko dan kinga ina kwanciya da kene zakiyi tunanin ko sonki nakeyi toh bari kiji ban taba sonki ba kuma bazan taba sonki ba me kike dashi dazan soki wawiya kawai ko a tunanin ki kwana danayi ina buga kofar dakin ki shima zakiyi tunanin sonki nakeyi toh idan har wannan tunanin kikeyi kima daina yinshi daga yau”
Sai yanuna kanshi da dan yatsa yace,
“Ni Faruq bazan taba sonki ba bazan taba kaunar kiba amfanin ki daya ne a wajena shine inbiya bukatata a duk sanda naga dama kuma ko kinki ko kinso dole ki amince da bukatata”
Tunda yafara maganan ta tsura mai ido tana kallon shi hawaye na sauka akan kuncin ta,,, murmushin dayafi kuka ciwo tasaki kana tace,
“I hate you kuma zanci gaba da tsanar ka har karshen rayuwa ta amma ina son kasani sai kayi nadama wata rana saika zukunna a gabana kana neman yafiya na ka rubuta wannan ka ajiye”
Sai takai hannu tashare hawayen da yake sauka akan fuskar tata kana ta kuma cewa,,,
“kaine Mafarin Bakar Qaddarar ta Hamma Faruq”
Sai tabi ta gefen shi tawuce tana siyayan hawaye hade da ficewa daga dakin,,
Sosai maganar yarinyan yashige shi shi yagama yarda auren Buddu shine Bakar Qaddarar shi a rayuwa tabbas an cuce shi an zalunce shi da aka hadashi aure da Yarinyan nan,, Zubewa yayi akan gado hade da dafe kanshi yana jin wani zafi a cikin zuciyar shi,,
kai tsaye dakin ta tawuce hade da maida kofar ta sanya mata key saita zube abakin kofar hade da fashewa da matsanancin kuka meyasa tata Qaddarar tazo mata a haka kuka takeyi sosai kamar ranta zaifita.

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE