BAKAR KADDARA CHAPTER 2

Alamin daya gaji da zautukan da Jimetan yakeyi sai yamike yakarasa inda yake yace,
*Jimeta wai meye haka ne kada fah kamanta a cikin gidan ku kake ba’a garin lagos bah daka saba shan giyar ka kana hauka kuma sanin kanka ne idan har Ba!a yasan kana shan beer zai iya mummunan fushi a kanka ciki ko harda cire ka daga cikin jerin ya’yan sa daya Haifa dan haka kabi komai a sannu kagane ko”
A matukar haukace jimetan yajuyo yana fuskan ta Alamin din sai kuma yafashe da wani irin mahaukacin daria hade da nuna kansa da dan yatsa yace,
“so what idan Wancen tsohon yacire ni daga cikin ya’yan sa who care’s kai nifa cikin hankali na nake sanin kanka ne beer baya haukatar dani so relax badai sunce saina auri Buddu ba OK babu damuwa I will definitely get married to her tunda abunda suke so kenan,
Amma fa ka’kaf Ahalin Jimeta sai sunyi dasun sanin wannan auren dan sai na dandana masu abunda suka dandana mun saina shayar dasu dacin da suka shayar dani wannan alkwari ne”
A hankali tafara bude manya manyan idanuwan ta tasauke su akan na Umman ta dake zaune a gefen ta ta tsura mata ido,
Tuni wa’insu hawaye masu zafi suka suma gangarowa akan fuskar ta saidai takasa cewa komi illa kallon Umman ta da take tayi,
Kara matsawa gabda ita Umma tayi hade dakai hannun ta takamo na Buddun Kana tace,
“Buddu na nifa yawan kuke kuken nanne bana so kuma kinsani sarai shine musabbabin wannan ciwon naki kuma kukan nan bazai hana Alhaji babba abunda yayi niya bah dan haka ina son ki kwantar da hankalin ki kicire duk wata damuwa a cikin ranki kin daiji abunda abbun ki yace maki ko”
Nodding kanta kawai ta iyayi hade da hadiye kukan da take shirin yi,
Shafa sumar kanta Umma tayi hade da sakar mata murmushi sannan tace,
“Ina ji a jikina ke alkhairi ce a rayuwar Faruqu kece zaki zama silar shiryuwan shi dan haka ina son ki dage sosai da addu’a InshaAllahu babu abunda yafi karfin Allah”
Sannan tamike tsaye tace “bara nasa su rukayya su kawo maki Abinci”
bata jira cewar taba tafice daga dakin tana kara jin tausayin Buddun a cikin ranta,
A babban falo ta tadda su adda rukayya suna kara tattaunawa akan auren Buddun, suna ganin ta kowa yaja bakin shi yayi shuru dan tuni taja masu kunne akan kushe auren,
kallon gefen da Adda rukayya take tayi hade dace mata, “Ki kaiwa Buddu abinci ta farka kuma ki tabbatar taci sannan bana son kuje kuna kara tada mata da hankali” daga haka tashige daki,
Sanin Buddun ba iyacin wani abu me nauyi za tayi ba yasa Adda rukayya hada mata tea takai mata saida tayi dakyar sannan buddun ta iya shanye tean adda lauratu ta ballo magani tabata shima saida akayi daru dan har saida adda Rukayya tace bari taje ta gayawa abbu sannan buddun tasha maganin tana wani yamutse fuska,
bata dadai ba bacci me mugun nauyi yayi awon gaba da ita, saida suka tabbatar baccin yayi nisa sannan ko wacce ta wuce dakin ta,
A daren ranan Bacci gagaran idon Jimeta yayi daga karshe nema yasamu daman dauro alwala yafara nafilfilu sabida duk iskanci shi yana matukar son ibada baya yarda yayi wasa da ibada hakan kuma yasamo asali ne tun daga kan tarbiyan daya samu a gidan nasu,
Cikin ikon Allah yana idar da sallan bacci yafara daukan shi saidai daya tuno da Auren da akeson lakaba mashi da yar cikin shi sai baccin ya gagari idon shi,
Washe gari lafia lau buddu ta tashi saidai rashin karfin jiki kawai da bata dashi,
Tunda tayi sallan asuba sai bata koma bacci ba sabida daman hakan yariga daya bi mata jiki bama ita kadai ba gabaki daya yan gidan hakan yazame musu jiki sabida soda yawa a babban falo suke haduwa ayi tilawar Qur’ani yau ma hakan ne ta kasance dan har basuyi tunanin buddun zata fito ba sai kuma su kaga tafito saidai da yan kalle ta za’a san bawani karfi ne a jikin nata ba karfin hali ne kawai irin nata,
tana karasowa tasamu gu kusa da Umman ta ta zauna hade da gaisar da ita sannan takai duban ta gunda abbun ta yake tace,
Abbu ina kwana antashi lafia”
Saida ya murmusa kana yace,
“lafia lau buddun abbun ta ya karfin jikin naki”
“Cike dajin dadi ta amsa da lafia lau abbu” sannan ta gaida su adda rukayya suma suka mata sannu da jiki sannan suka fara tilawar qur’anin,
Karfe bakwai dai-dai suka kammala sannan kowa yamike abbu yawuce dakin shi tare da autan shi me suna Musa,
Su kuma su Umma suka wuce kitchen sabida haka al’adar gidan yake suna gama tilawar qur’ani zasu wuce kitchen sufara kokarin hada abunda za’ayi breakfast dashi,
Buddu sabida karfin hali harda binsu kitchen din saidai kuma sai rabe rabe takeyi dan tasan dawuya Umma ta barta ta zauna a kitchen din tunda batada lafia,
Adda rukayya cema takula da ita tace,
“Buddu baza kiwuce ki kwanta bawai kodai har jikin naki ya warware ne”
Nodding kanta kawai buddun tayi hade da turo baki,
Girgiza kai Umma tayi hade da cewa,
“Buddu na ki koma daki ki kwanta yau kam ki huta kinji ko”
Murya a shagwabai tace, Umma nidai A’a ina son na zauna a kitchen dinne nafa ji sauki”
Takare maganar da langwabe kai babu yanda Umma ta iya da ita dole tabarta ta zauna a kitchen din tana kallon su tunda babu aikin da zata iyayi,
A bangaren Jimeta tunda yayi sallan asuba daya koma bai tashi ba sai lokacin da yaji ana mai knocking wuraren sha biyun rana kenan,
Dakyar ya iya saukowa daga kan gadon yafito daga bedroom din yafito falo,
Cikin daga murya yace “uban waye”
Daga waje wata yar yarinya da bata wuci shekara sha bakwai ba tace, Hamma Niche Mami ce ta aiko ni”
Wani dogon tsaki yaja hade da bude kofan yana mata wani Mugun kallo tuni jikin ta yadauki rawa tace,
“Hamma kayi hakuri mami ce tace wai kazo tana kiran ka yanzu kuma wai mu taho tare”
Sai takare maganar da sunkyu da kanta tanaja da baya dan tasan ba karamin aikin shi bane yajanyo ta yahau bugu,
cikin daga murya yace, dan uban ki ni sa’an kine dasai kin tasani a gaba common gerrout kafin naci uban ki”
Aida gudu tabar wajen ta koma cikin gida dan tasan tana cewa zata kara wani magana tofa dukane zai biyo baya shiyasa ta shafawa kanta lafia ta gudu,
Maida kofan yayi yarufe hade da juyawa yakoma bedroom kai tsaye sai yawuce bathroom saidai yadauki mintina kamar sha biyar acikin bayin kana yafito wajen shiryawa ko saida yakusan mintina talatin sannan yagama shiryawan,
shigan kananun kaya yayi kuma sosai sukai mashi kyau dan jimeta ba baya ba wajen kyau da haduwa shiyasa mata suke yawan kawo mai hari barin ma matan kabilun nan da suke garin Lagos dan anan yola koda sunce suna son shi ba cika kulasu yakeyi ba sabida baicika son harka da yaran hausa fulani ba a cewar shi basuda sirri kuma basu iya sarrafa da’na Miji ba basu san yanda zasuyi kwanciyar gado ba shi kuma a rayuwar shi na dunia yana mugun son macen data iya kwanciyar gado ma’ana wacce zata iya sarrafa shi,
Yana niyar barin Sashin nashi wayar shi dake cikin aljihun wandon shi tafara kara ko dabai sani ba yasan Mamin shice murmushi kawai yasaki hade da sanya hannun shi yacuro wayar hade da amsawa ya kafata a kunnan shi,
Tun kafin yace wani abu, mami daga cen tace,
“Dan uban ka so kake ni nataso nazo tunda kai kafi karfin kazo a daidai lokacin da ake kiran ka”
Murmushi yakuma saki a karo na biyu kana yace, Ayya Mami na gani nan zuwa kiyi hakuri ki yafewa Danki”
Daga haka sai ya katse wayan yafara takawa da dan sauri sauri zuwa ainihin cikin gidan nasu,
ta kofar baya yashiga sabida tanan ne zai kaishi falon Mamin da sauri yana shiga suna hada ido ta banka mai harara tace
” isashe sai yanzu kaga daman zuwa”
Saida yasamu daya daga cikin kujerun falon ya zauna sannan yace,
“Mami kiyi hakuri tunda gani dai nazo yanzu”
Harararshi ta kumayi a karo na biyu kana tace
“daman bawani abu zaka munba shiryawa zakayi zuwa da yamma kaje gidan Ba!an ka ku fara fahimtar juna da kanwar taka tunda dai kaga kwata-kwata sati biyu Alhaji babba yasaka Lokacin bikin naku sannan yakamata tun yanzu kafara shiri dan tunda safe addan ka ta turawa ba!an ka list din komai da komai”
Yamutse fuskar shi yayi kana yace”nifa Mami babu wani shiri da zanyi kuma inaga ai basai naje ba”
yakare maganar dason mikewa tsaye,
Cikin daga murya Mami tace”umarni nake baka ba neman shawara nake da kaiba ka Tabbatar yauda yamma kaje inko naji labarin ba kaje ba wallahi saina mugun bata maka rai tunda kai bakajin maganar kowa”
Ranshi a matukar bace yafice daga falon tayaya za’ace yaje zance wajen yar cikin shi tauma idan yaje mezai cemata yarinyan da batada kunya wallahi tana mun wani hauka zanci uban ta.Sai bayan magrib sannan yashirya zuwa gidan su Buddu kananun kaya yasaka white T-shirt sai black din trouser sai P-cap din daya sanya a kanshi sosai yayi wani mugun kyau naban mamaki duk da jimeta ba fari bane kuma ba baki bane ma’ana shidin ruwan tarwada ne a turance ana kiran masu kalar fatan jikin shida Chocolate color or black beauty,
soda yawa idan yafita kasashe ketare abroad kenan sai ayi tamai kallon black america sabida sosai yake kama dasu kuma sai shigar daya keyi da yanayin yanda yake dabi’un sa sai akara tunanin shidin usulin black america ne,
Dan akwai lokacin daya taba zuwa America yin wani course na wata daya dayake shi kadai yatafi sai zaman gida ya gundure shi haka zai shirya yatafi night club tofah achen zai hadu da matan turawan nan dama black america’s suyi ta shishshige mai dan a tunanin su dan uwan sune sabida kwata-kwata babu wani alama daza agani ache shidin musulmi ne kuma dan Nigeria,
Dan tun daga secondary school dinshi har ya kammala digri dinshi na biyu anan america yayi fannin farkon a digiri dinshi saiya tafi wata babbar jami’a dake nan cikin kasar American ya karanci Mechanical Engineering tau bayan ya kammala ne yakara yin digri dinsa na biyu,
Bayan ya kammala ne saiya koma gida Nigeria yayi short service na navy sabida shi tun yana yaro karami yake matukar son zama soja, shiyasa koda yafito da first class achen America suka so daukan shi aiki sai yaki yagudo Nigeria duk da suma American sun so sosai su dauke shi yazama US army saidai shi sam yaki yarda yace kasar shi yake son yiwa aiki,
Dan hatta Ba!an shi yaso ya mika mai ragamai companyn dinshi dayake Asia sai yaki yarda amma still yakan laika jefi jefi duk da har yanzu bai maida hankali ba,
Sabida baiwani jima ba sai aka Kara mai girma yakai captain sabida gwazon shi da kuma yanda yakeda mugun kokari sosai yakeda wani kwarjini wannan kenan,
Tun a hanyan zuwa gidan su Buddun yafara tunanin abunda zaice idan yaje gidan danshi a ganin shi abun kunya ne yace yazo wajen yar cikin shi zance,
Da wannan tunanin yakarasa har gidan su Buddun a bakin gate ya tsaya yadanna wani uban horn me karfi wanda saida gate man din hanjin cikin shi suka ka’da dan yasan mutum daya ne yake dan iskan horn haka,
Ana bude mashi gate din yacusa kan Benz dinshi cikin gidan,
a inda aka tanada danyin parking yafaka motar nashi saidai yajima sosai yana tunanin yanda zayyi yashiga cikin gidan dan shikam ko matar gidan bazai iya gaisar waba dakyar yasamu karfin gwiwan fitowa daga cikin motan yana wani kalar tafia irin ta isassu harya karasa bakin shiga babban falon gidan,
Cikin Ikon Allah saiya tadda Kofar falon a bude saidai hayaniyar daya dan jine yasanya shi kara hade fuska sosai hade dayin sallama ciki ciki,
Su kansu su Umma da suke zaune a falon basu san yayi sallamar ba balle susan da zuwan nashi sai kawai ganin mutum sukayi yasamu kujera ya zauna yadaura kafa daya kan daya yana latsa Waya,
dayake daga Umma sai su adda lauratu a falon da adda rukayya sai sukayi saurin mikewa tsaye adda Rukayya tafara gaida shi kana adda lauratu,
Basu jira ya amsa ba sukayi saurin barin falon, sai yarage daga Umma sai shi mamakin shine sosai yacika mata zuciya duk da tasan ba wannan bane karo na farko daya fara shugowa cikin gidan nasu kai tsaye batare dayayi sallama ba koya gaishe da wanin suba,
Sun kusan mintina sha biyar a haka kana yabude bakin shi dakyar shima yayi maganar ne sabida ganin ana neman bata mashi lokaci yace,
“Barka dai” bai jira jinme Umman zata ceba a gadarance yakuma cewa,
“Buddu za’a kira mun” sai yaci gaba da latsa wayar shi kamar bashi neba yayi maganar
abun yawa Umma zafi sosai saidai babu yanda zatayi tunda shidin yanzu surukin tane sannan koba haka ba kamar da yake a wajen ta,
Kala bata cemai ba tamike tabar falon tana mamakin hali irin na Faruqu lallai akwai aiki babba a gaban Buddun ta tabbas Buddu sai tayi yaki sosai da zuciyar ta inba haka bako akwai matsala babba.
Kai tsaye dakin Buddun tawuce ta sameta tana karanta wani littafi na wata shahararriyar marubuciya yar america ta kwarai sosai wajen wallafa littafi da kuma tsara shi,
Tana ganin Umman nata ta ajiye littafin akan gado tace, “Umma”
Samun waje Umma tayi a kusa da Buddun ta zauna kana tafara magana cikin rarrashi da kuma kwantar da hankali tace,
“Buddu Kinyi bako kiyi hakuri da duk abunda zai maki InshaAllahu komi zaizo yawuce ki tashi kishirya kije kada yagaji da jira kinji Buddu na”
Hawaye ne suka cika Idon Buddun saidai bata bari sun sauko ba tayi saurin shanye su dan a halin da ake ciki a yanzu ta fahimci ganin hawayen ta shine tashin hankalin iyayen nata,
Saidai cikin murya tausayi da kuma tsantsan yarinta tace,
“Umma Hamma Faruq neko Tau Umma ni mezance mashi Umma ai bansan yanda ake hira ba kuma mani Umma tsoron Hamma faruq nakeyi Umma kifada mun abunda idan naje zance mashi kinsan abu kadan ake mashi yace mutum yamai laifi barin nima dayafi tsana kaf cikin dangi”
Murmushin karfin hali kawai Umma tayi hade da kuma cewa “Buddu na kenan nidai tashi kishirya kada yagaji da jira yayi tafiyar shi”
Badan taso ba tamike takarasa wajen wardrobe dinta ta janyo wani katon hijabi wanda ya saukar mata har kasa tasaka
binta da kallo kawai Umman ta takeyi tana jin wani mugu mugun tausayin yar tata,
Kallon Umman nata tayi sai kuma tadan saki murmushi a karo na farko dan tun sanda aka fara zancen auren ta da Hamma Faruq rabon da aga murmushi akan fuskar ta,
cikin muryar ta me matukar sanyi tace,
Umma kidaina damuwa ni kaina izuwa yanzu na yarda da Qaddara kema ina son Umma na ki yarda da Qaddara,
Daga haka sai tayi saurin ficewa daga dakin dan kuka take sonyi dan koda tafita saida ta tsaya a wani dan corridor tayi kuka sannan ta goge fuskar ta tawuce falon,
bakin ta dauke da sallama tashiga falon saidai ko daga fuskar shi bayyi ba balantana tasa ran yaji sallaman nata amma tabbas tasan yaji dan da dan karfi tayi,
Samun waje tayi a daya daga cikin kujerun falon ta zauna hade da dukar da kanta tana wasa da zuben dake sanye a daya daga cikin yatsun hannun ta na dama,
muryar ta na rawa tace, “ham.. ma ina wu..ni
Sai tayi saurin jan bakin ta tayi shuru tana jiran taji ya duro mata wani uban asharia amma sai taji shuru hakan sai yayi matukar bata mamaki,
Saida suka kusan Mintina ashirin babu wanda yace mawani kala,
Sai cen batare daya kalle inda take ba yace,
“Kina son naci uban kiii”
jikinta har rawa yakeyi wajen amsa mashi dacewa, “A’ah Hamma kayi hakuri”
Sai tafara kuka kadan kadan dan har hannun ta tasaka tana toshe bakin ta dashi sabida kada hamma faruq din yajita,
Saidai tuni yajuyo sautin kukan nata,
Kamar saukar aradu taji ya daka mata wani uban tsawa,
“Kukan uban ki kike mun”
kamar yana kallon ta tayi saurin Girgiza kai tana kara fashewa dawani sabon kukan,
Kamar daga sama ta tsinci mutum a gaban ta ai batasan sanda tasaki ihu ba
“na tuba wallahi Hamma natuba kayi hakuri wallahi Allah nabar kukan kuma ni bance ina son na aure k….
Bai bari takarasa bai yabige bakin da mugun karfin daya sanya ta kusan sakin fitsari a wando yace,
“Shut up kafin na tattaka ki anan wajen na kuma jin pin sai naci uban ki wallahi ai bakiga komi ba tukunna kidai bari a daura auren sai kin gwammaci mutuwar ki akan aurena”
Sannan yadire mata kudin dani kaina bansan adadin suba a gaban ta,
Batare daya kara koda kalma daya bane yafice daga falon,
Saida ta tabbatar yafice daga gidan gaba daya sannan tafasa wani uban ihun daya rikita su Umma.

 

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE