BAKAR KADDARA CHAPTER 9


Sagir Kanin Jimeta shine yazo daukan su murmushi kawai Buddu take tsaki dan fuskar ta cike da fara’a ta gaida sagir daga nan airport kai tsaye gidan su Jimeta suka wuce taso kwarai sufara zuwa gidan su saidai tasan da wuya yaudin taje gidan nasu kila sai gobe,
Motar Su tana fakawa tayi saurin sanya hannu zata bude Motar Jimeta ya dakatar da ita ta hanyar ce mata,
“kin daiji abunda nafada maki ko kada nasake naji wata magana”
Hmm kawai tace sai tayi saurin ficewa daga cikin motar tayi hanyar shiga falo bakin ta dauke da sallama tashiga Mami ce kawai zaune a falon tana kallon sunnah TV tana ganin Buddu tamike tana murmushi tace,
“Barka da zuwa Buddu na” ita dai Buddu murmushi kawai take saki tana dukar dakai dan wani mugun kunyar Mamin taji tanayi abunda bata taba jiba acen baya Kodan yanzu tazama sirikar tane oho,
Rumgume ta Mami tayi tana murmushi tace MashaAllah Sannunki da hanya saita karasa da ita kan kujeran data tashi ta zaunar da ita kana itama ta zauna sai Buddun tayi saurin sauka daga kan kujeran tana murmushi kanta a duke tace,
“Mami ina wuni mun same ku lafia” bakin Mami har kunne dan takasa boye farin cikin ta dan sosai takejin kaunar Buddu a cikin ranta kuma tasan Faruqu yayi dacen mata me kunya da sanin yakamata,
Da lafia kalau ta amsa hade dace mata ta tashi tashiga ciki tayi wanka sai tayi sallah tafito taci abinci, a kunya ce Buddu tamike tawuce dakin su Zakiya kannan Jimeta kenan, bin bayan ta da kallo Mami tayi saita girgiza kai tana mamakin uban raman da Buddun tayi cikin kwanaki kadan haka amma tayi alkawarin tambayar Buddun kafin subar garin taji in akwai abunda Faruqun yake mata ne har tayi wannan uban raman haka sai kace wacce tayi kwana da kwanaki tana rashin lafia,
Bayan shiganta dakin da jimawa kadan Jimeta yashugo falon bakin shi dauke da sallama sai kace wani mutumin arziki yasamu kujera kusa da Mami ya zauna, hade da gaida ta bata wani saki fuskar taba ta amsa gaisuwa nashi sannan tafara mai tambayoyi,
“Faruqu rashin lafia Buddu tayine da tayi wannan uban raman haka ko kuma wani abun kake mata ko abinci ne baka bata”
duk lokaci guda ta jero mai wa’innan tambayoyin tana tsare shi da ido,
Rasa abunda zaice mata yayi sai yahau yan kame kame dayake yasan baida gaskiya saida ta kuma tambayar shi kana ya shararo wani uban karyan yace mata,
“Mami nifa ba abunda nakema yarinyan nan ki tambaye ta kiji kawai inaga yawan koke koken da takeyi ne kuma sannan saina matsa mata take cin abinci, idan ma baki yarda ba ki kirata ki tambaye ta”
Yakare maganar da dukar dakai dan yasan Halin Mami da saurin da’go mutum idan yayi karya,
Girgiza kai Mami tayi kana tace,
“idan ma wani abun kake mata ka daisan Komin daren dadaiwa zamu sani, kuma sannan a kullin ina kara tunatar dakai akan kaji tsoron Allah, bazan gaji da rokon kaba faruqu akan karike Amana ka kula da yarinyan nan yar uwar kace koda kuwa ita din ba matar ka bace, idan ma kana mata wani abun kayi gaggawan Rokon ta gafara tun kafin hakkin ta yakama ka”
Bawai maganar Mamin yashige shi bane Hasalima shi baiji gaba daya maganar da takeyi bah, batare data kara koda kalma daya bane tamike tace,
“idan taci abinci saika kaita gidan su ta kwana tunda dai gobe zaku tafi”
Bata jira cewar shiba tashige daki, shikam Harga Allah baiso barin ta taje gidan su ta kwana ba amma yazayyi tunda Mami tayi magana, shima mikewar yayi yawuce bangaren shi,
bayan Buddu tayi wanka tayi sallah saita saka daya daga cikin kayan da Mami ta aiko mata dasu doguwar abaya ce brown color sosai ya amshi jikin ta yayi mata wani mugun kyau,
tana shirin fitowa daga dakin Mami tashugo dakin fuskar ta dauke da murmushi saurin dukar da kanta Buddu tayi a kunya ce sannan tace,
“Mami yanzu fah nakeda niyar fitowa”
Batare da Mamin tabata amsa ba taja hannun ta suka karasa bakin gado sannan ta zauna sai Buddun itama ta zauna,
Mami tace “akwai abunda ke damun kine naga kin rame ko Hamman naki namiki wani abunne kifada mun gaskiya nasan halin ki, karya ba halin ki bane”
Idanun tane yaciko da kwalla tana so tafada abunda Hamma Faruq din yake mata amma tanajin tsoro sabida tasan inhar tafada tofah daga Mami har Ba!ah harma da kaka Sai sun dauki mummunan mataki a kanshi, sannan tasan duk akanta zai huce idan suka tsallaka suka bar kasar nan shiyasa tayi saurin maida hawayen dake neman fitowa daga cikin idanun ta batasan ta makaro bah dan tuni Mami ta kafeta da idanuwa kuma taga hawayen daya cika idon nata,
Murmushin karfin halin Buddun tasaki kana tace,
“Mami babu abun dake damuna sannan ni Hamma bayamun komai kawai dai banajin dadi ne” saita kare maganar dakara dukar da kanta dan ita kanta taji wani iri da bata fadawa Mamin gaskiya ba Tamata karya,
Mami tuni tagane akwai matsala amma sabida yanda ta karanci Buddu tsoron Jimeta gabaki daya yagama kamata ita dai fatan ta Allah yasa bawani mugun abun yake mata bah amma da mamaki ace ko sati ba’ayi ba da bikin nasuba har Buddun tayi wannan uban raman,
A siyasance Mami ta dinga bawa Buddu hakuri tana mata nasiha hade da bata shawarwari sannan tace zasuyi magana da Faruqu idan sun tafi cen Russian ya sakata a makaranta taci gaba da karantun ta tunda daman ana shirye shirye nema mata admission ne kaka ya bijiro da maganar auren ta da Hamma Faruq,
tare suka fice daga dakin Mami da kanta taje kitchen ta daukowa Buddu abinci takawo mata tana cin abinci Mami najanta da hira sabida tana son Buddun ta saki jikinta sosai kafin Jimeta yakaita gida, Tun Buddun bata son sakewa har yazo ta saki tasoma dawowa kamar dacen da takeda yawan barkwanci,
Sai cen da yamma sosai Jimeta ya aiko me aiki akan acewa Buddu tafito dayake da ita da Mami ne a zaune a falo sai tafara zazzare idanuwa dan batayi tunanin gida zai kai taba a tunanin ta bangaren Shi zataje ko kuma wani wurin zai kaita,
Mami tace kice tana fitowa yanzu, bayan tafiyar me aikin sai Mami tajuya tana kallon yanda Buddu lokaci guda ta canza tuni tagama yarda da abunda take tunani amma zata tayasu da addu’a har Allah ya daidaita tsakanin su,
Mami tace”tashi maza ki dauko mayafin ki kada yagaji da jira kinsan halin Hamman naku”
Wiki wiki da idanuwa Buddu tayi saidai takasa mutsawa Mamin sai kawai tamike tawuce ta dauko gyalen ta tafito idanun ta na ciccikowa da hawaye, Ganin Hakan da Mami tayi sai tace mata,
“Gidan su Umman ki Zai kaiki kije cen ki kwana tunda gobe zaku tafi”
Ai batasan sanda murmushi ya subuce akan fuskar taba hade dacewa, nagode Mami Allah yakara lafia da tsawoncin kwanaki”
murmushin jin dadi Mami tasaki Hankalin Buddu yana daya daga cikin abunda yake kara sawa tana jin sonta a cikin ranta, har bakin kofa Mami ta rakata hade dace mata ta gaida Umman nasu,
Tun kafin takarasa bakin motar sai taji zuciyar ta yana bugawa sai takara jin tsoron Jimetan sosai a cikin ranta dan koda takarasa bakin motar dakyar ta iya kai hannun ta tabude murfin motar tashiga ta zauna tana sunkwi dakai sai kace wacce tayi karya,
Dayake daman gate din abude yake sai kawai yaja motar da mugun gudu sukabar haraban cikin gidan har saida ta rintsa idanun ta sabida tsoro tana mamakin yawan gudun da Hamma faruq yakeyi a mota shiko tsoro bayayi,
a hankali ta daga idanun ta takalli Jimetan da gaba daya yamaida hankalin shi a tukin daya keyi, sanye yakeda kananun kaya saidai wannan Karon bakin wando ne sai T- shirt na kakin sojoji sai p-cap din daya saka sosai yayi mata kyau dan soda yawa takan zauna tana kiyasta kyau irin na Hamma Faruq saidai data tuna da halin shi ba masu kyau bane sai taji haushin kanta akan kyaun da yake mata,
Ashe abunda bata sani ba yana kallon ta, ta wutsiyar ido saida sukaje inda babu mutane sosai sannan yaja birki ya tsaya saurin dukar da kanta tayi tana wasa da zoben dake dan yatsun ta, duk da batayi tunanin ya kamata tana kallon shiba,
Kamar daga sama taji muryar shi ya daki dodon kunnan ta yace,
“Kallon da kike mun na menene ko kinada Bukata nane” Saurin girgiza mashi kai tayi tana rintsa idanun ta sabida kunya ashe dai yana kallon ta wayyo Allah na, abunda tafada a cikin zuciyar ta kenan,
Tabe baki yayi kana yakuma cewa, kinsan dai namiki warning sosai akan fadar wata magana ko”
Maimakon tabude baki tabashi amsa sai tace, Hmmm
bai damu da Hmm din da tace ba yace,
“Saura gobe kiyita bacci har nazo daukan ki 11am zanzo saiki shirya cikin shiri inko ba hakaba wallahi nazo ko baki shiryaba a haka zamu tafi dan bazan dauki iskanci bah”
Sai yatada motar sukabar wajen, ita kam tarasa gane wane irin haline da Hamma faruq mutum kullin babu abun alkhairin dazai fito daga wajen shi,
Suna karasawa bakin gate din gidan su Buddun ya danna uban horn da sauri gate man ya wangale masu gate din suka shiga,
A inda ake parking motocin gidan anan yayi parking sai yadanna Lock sannan yajuyo yana fuskan tan Buddun da har a lokacin kanta a duke yake, gyaran murya yayi kana yace,
“Dago fuskar ki ki kalle ni dakyau kada yau ki kasa bacci in dinga maki gizo naga kina son kallo na dayawa”
Turo dan karamin bakin ta tayi tana auna rainin wayo irin na Hamma faruq din yama mugun raina mata wayo wallahi meza ta kalla a shegiyar fuskar shi meson bijirowa zuciyar ta wani abun daban, kara dukar da kanta tayi,
Wani murmushin rainin wayo Jimetan yasaki sai yakuma cewa,
“Zaki dago ki kalle ni kosai nabata maki rai in banda munafurci dazu dana kamaki kina kallo na aiba sakaki nayi ba yanzu kuma dana sakaki sabida kin iya munafurci da gulma kin kasa kallon nawa, to wallahi kafin na irga biyu ki dago ki kalleni kafin namiki abunda baki tunani”
Aibai gama rufe bakin saba ta dago da fuskar ta a kunyace ta zuba mashi manya manyan idanuwan ta, da suka soma cikowa da kwalla, cikin kwayar idanuwan ta kawai yake kallo yana son ya karanci wani abu akanta amma yakasa karantar komai sai mugun tsoron shi daya gani kawai a cikin kwayar idanun nata,
Bata ankara ba saiji tayi ya janyota ya hade ta da jikin shi yana sakin wani ajiyar zuciya shifa yafara gajia meyasa baya gajia da Buddun ne baya gajia da tabata kodan ita din ta dabance a cikin mata sabida ni’imar da Allah yayi mata, Hawaye ne yafara sauka akan fuskar ta saida suka dauki mintina goma a haka sannan yasake ta yabude motar da saurin ta tafice daga cikin motar danhar tana hadawa da gudu bayanta kawai yake bida kallo ji yakeyi kamar ya janyota tadawo sabida wani mugun sha’awar ta data taso mishi a yanzu,
Saida yaga shiganta falo sannan yatada motar yabar cikin gidan kai tsaye gidan su Alamin yawuce,
Duk da tayi kewar mutanan gidan nasu bai hanata yin sallama a nutse ba sannan tashiga cikin falon gabaki daya mutanan gidan suna zaune a falo Abbu ne kadai baya nan yayi tafia,
aida gudun ta takarasa ta haye jikin Umma tana murna tana kankame ta kamar wacce zata koma ciki su Adda Rukayyah ko sai dariyar Murnan ganin yar’uwar tasu sukeyi a daren ranan kusan kwana sukayi suna hira dan daga Adda Rukayyah har Adda lauratu a daki daya suka kwana Umma ko sai cen dare tawuce dakin ta, saidai ramar da taga Buddun tayi ya tsaya mata a rai sosai,
Washe gari tunda sukayi sallan asuba sai basu koma bacci ba bayan sun gama karatu sai suka wuce kitchen kada kuso kuga yanda Buddu tasaki jikin ta, Tanata hira da yan’uwan ta ana wasa da daria karfe tara daidai suka gama hada abun breakfast sai kowa yawuce yaje yayi wanka, doguwar riga na shadda Buddu tasaka tasha aikin sirfani tun daga samar ta har kasa tayi kyau sosai, a tare suka zauna a falo sukayi breakfast suna gamawa Adda lauratu tace dole dole sai Buddu tayi kwallia kafin Hamma faruq yazo daukan ta aikuwa badan tasoba haka ta zauna Adda lauratu tamata kwallia hade da daura mata dankwali aikuwa sai takara wani kyau dan har saida Umma ta yaba sosai da irin kyaunda Buddun tayi,
Sha daya dai-dai tama Jimeta a cikin gidan su Buddu yana cikin mota ya aika me sawa flowers din gidan ruwa yakira mai ita,
Koda dan aike yaje yafada sai Umma tayi tunanin aiko bakoma Jimeta zai shugo ya gaisheta tunda ita sirikar shice amma sai bata nuna rashin jin dadin taba sai tacewa Buddun tayi sauri ta dauko gyalen ta kada yagaji da jiran ta, da kuka da komai haka Buddun ta rabu da Umma su Adda Rukayyah saida suka rakota har bakin mota hade da gaida Jimetan batare daya kalle suba ya amsa sannan yacewa Buddun,
“Zaki shugo mutafi ko nabarki kicigaba da kukan shagwban naki”
Saida ta kalli su Adda Rukayyah tayi hugging dinsu sannan tabude murfin motar tashiga tana daga masu hannu suna fita daga cikin gidan tafashe da wani matsanancin kuka, tasan zatayi kewar yan’uwan ta da Umman ta da Abbu, bai kula taba har saida suka kusa gidan Kaka sannan yafaka motar a bakin hanya hade da curo hanky a cikin aljihun wandon shi yamika mata kana yace,
“amshi kiyi maza kishare wannan hawayen sannan kiyi mun shuru kafin ranki yabaci”
batare data kalle shiba takai hannu ta amshi hanky din sannan tafara share hawayen daya bata mata fuska saita dunkule hanky din a cikin hannun ta,
Bai kara tanka taba yaja motar sukabar wajen koda sukaje gidan kaka albarka kawai yake sa masu hade dayi masu addu’a, daga gidan kaka gidan yan’uwa suka zaga sukayi masu sallama karfe hudu dai-dai suka koma gidan su Mami suna zuwa daman Mami tahada duk wani abunda zata bawa Buddun a cikin wata yar karamar jaka ko mintina ashirin basuyi ba suka fito sabida karfe shida flight dinsu zaitashi zuwa Lagos, Buddu tasha kukan rabuwa da mami sosai dan har suka shiga cikin jirgi kuka takeyi,
8:00pm daidai yamusu a Lagos tuni driver yazo daukan su koda suka isa gida kai tsaye Buddu saita wuce dakin ta da sauri sabida ciwon kan dake mugun damunta kuma tasan sabida kukan data shane shiya haddasa mata ciwon kan a daren ranan babu abunda yashiga tsakanin su da Jimeta dan kwana yayi yana aiki a cikin system dinshi, dayake flight din 4am za subi dayaga 3am Yayi sai yaje dakin Buddu ya tada ta yace tayi maza tashirya kada ta bata mai lokaci, Baccin bawani isanta yayi ba haka ta tashi tawuce bathroom tayi wankan a gurguje tana fitowa tasaka doguwar bakar jallabia cream kawai tashafa sai Perfume data feshe jikinta dashi dayake Jimeta yace kada ta dauki komi sai kawai ta dauki handbag medan girma tasaka abunda zata bukata a ciki,
Saima data zauna ta jirashi a falo yana fitowa yayi gaba sai itama tamike tabi bayan shi, dagashi har ita gidan baya suka shiga driver yaja motar suka fice daga cikin gidan suka dauki hanyar airport,
A kusan tare motar su Phendo da nasu Jimeta suka isa cikin airport din, rally itace takawo Phendo airport din, A kusan tare Buddu dasu Phendo suka fito daga cikin mota kallo kallo kawai akeyi tsakanin Phendo da Buddu,
Buddu mamaki ne yagama kamata saidai ba abun mamaki bane tayi la’akari da Phendo din karuwar Hamma faruq ce, a gaban idon ta Jimeta yakarasa Yayi hugging Phendo yayi kissing dinta ko kallon rally bayyi ba da taketa wani iyayi jan hannun phendo yayi da take sanye da wani dogon wandon jeans sai wata yar riga data dan sauko mata kadan, ganin sunyi gaba abunsu sun kyale tane yasata saurin bin bayan su,
Kowa zayyi tunanin Phendo ce matar Jimeta sabida yanda yake rike da hannun ta Buddu kuma kallon kanwar shi za’ayi mata,
4am daidai jirgin su yatashi su Uku a waje daya suka zauna saidai Jimeta da Phendo suna manne da Juna Phendo namai shagwaba irin nasu na yan dunia Buddu ko karatun qur’ani ta kunna a wayar ta sai tasanya earphone ta toshe kunnuwan ta dashi tana sauraren karatun qur’anin har bacci ya dauke ta.

11:12am flight dinsu yayi landing a Moscow Domodedovo Airport, suna sauka driver yazo ya dauke su kai tsaye masaukin su yakaisu bawani babban gida bane three bedroom ne sai parlo sai garden sai balcony ta waje gidan yayi kyau sosai sabida yanayin tsarin gidan ma abun kallo ne,
Yana rumgume da phendo har suka shiga cikin falon sai kawai Buddu taja ta tsaya tana karewa falon kallo sabida akwai abubuwan sha’awa sosai a cikin falon,
bata ankara ba sai taji an daka mata wani mugun tsawa a matukar firgice tajuyo tana kallon Jimetan dake binta dawani mugun kallo yace,
“Toh bakauyiya ga dakin kicen” sai yanata nuna dawani daki da dan yatsan shi sannan sai yaja phendo suka shige wani daki

tana shiga saita tsaya kikam duk da Hamma faruq yabata mata rai amma ganin yanayin dakin sai taji wani mugun farin ciki, sabida komai fari ne a dan gaban gadon akwai co!e chairs a hankali ta taka takarasa bakin co!e chairs din sanye take da wata katuwar jacket akan jallabiyan data saka jan kujera tayi ta zauna sai tawani kankame jikin ta sabida mugun sanyin da akwai,
Sai kuma taji tana jin yunwa sabida abincin da aka basu a jirgi bata ciba sai kawai tajanyo handbag din data sako abunda zata bukata daman akwai dambun naman da Mami tabata sai kawai ta dauki dambun naman tafara ci tana lumshe idanuwa sai cen tamike takarasa tabude fridge ta dauki bottle water takafa kai tasha sai takarasa kan gado ta kwanta saita fara tunanin abubuwan da Hamma faruq yake mata yafara isar ta sai kuma bacci yafara daukan ta sai cen tafara jiyo iface ifacen phendo da Hamma faruq muryan Phendo har yafi fitowa dan har kukan dadin data keyi saida taji, wani dogon tsaki Buddun tasaki sai kuma takara jin ihun har yafi na dazu a takaice dai sun hanata yin baccin da takeso,
Sai kawai tamike tashige bathroom tai wanka tai alwala sannan tafito a lokacin har time din sallah yayi sai takarasa wajen wardrobe tana budewa sai taci karo da hadaddun dogayen riguna da English wears masu akwai dasu burn shot dadai kaya na badala gasu nan jibge a cikin wardrobe din,
Girgiza kai tayi sai tafara tunanin yanda zata wani tsaka burn shot dinnan ta zauna haka sai kawai tajanyo wata doguwar riga pink color me irin hannun vest tasaka aiko yayi mata kyau sosai ya amshi jikin ta saita daura wani katon jacket akan rigar hade da sanya safan hannu da kuma na kafa sabida snow dake sauka a lokacin,
Sai kuma tafara tunanin abunda zata saka tayi sallah sai cen taga wani abu kamar hijab aiko tana daukowa sai taga ashe hijab ne, tayi mamaki sosai amma sai tayi tunanin ai Hamma faruq mutum ne meson addini, saida tasaka hijab din sai tafara tunanin inane alkibla cen dai ta hasasa kawai saita kalli wani wurin a matsayin gabas,
tana idarwa tacire hijab din tayi folding dinshi ta maida cikin wardrobe, tana son takira su Umman ta Amma batada sim din kasar haka ta hakura sai takoma ta kwanta hade da daukan remote ta kunna TV saidai duk yawancin channels din babu wani abun arziki saina badala sai kawai ta kashe TVn ta dauki wayar ta tafara game,
a bangaren su Jimeta saida suka gama gurzan juna sannan yayi wanka yayi sallah Phendo ko sai kawai taja blanket tarufa tafara bacci,
Yana idar da sallan sai yafito falo daman sanye yakeda kananun kaya Saidai shima yasaka katon jacket tunda ba sabawa sukayi da sanyin kasar bah dan har gwanda shi yana yawan ziyartar kasar,
Kitchen yashiga yabude fridge yadauki abunda zaici yadawo falo yazauna hade da kunna TV channel din da ake yan raye raye yasaka sai yakure Volume yana bin wakar a hankali yana sipping fresh milk,
Sosai Hayaniyar wakar ta ishe ta saita rasa inda zata tsaka ranta taji dadi sabida ita a dunia babu abunda ta tsana kamar hayaniya barin ma ace waka ce aka kure volume,
Gajia tayi da zaman dakin sai kawai tasauko daga kan gadon tafito falo, sabida tasakawa ranta daina jin tsoron Hamma faruq din itama tana son tasamu yanci kamar ko wace matar aure,
Baima san tafito falon ba hankalin shi naga kallon daya keyi saida takaraso har tsakiyan falon tasamu kujerar dake kusa dashi ta zauna cike da mamakin ta yake kallon ta itako sai tayi kamar ma bata ganshi ba dan harda wani gyara zama tayi tana kara kafe TVn da ido sai kace wacce take sauraren wakar dake tashi,
hannun ta takai kan kujerar dayake ta dauki remote din hade da rage Volume din TVn duk yana kallon ta saida ta ajiye remote din sannan yayi mata magana cikin daga murya yace,
“Uban waya saki rage mun volume ni sa’an wasan kine” Maimakon tabashi amsa sai ta kuma gyara zama duk da adan tsorace take saidai bata nuna mai hakan bah,
Saida yakara mata magana akaro na biyu sannan ta juyo takalle shi hade dawani juya idanun ta cikin muryar me kama da shagwaba shagwaba tace,
“Ayya Hamma volume dinne fah yayi yawa kuma kasan niba son yawan hayaniya nakeyi bah”
Saita kare maganar dawani cunno baki cikin irin tsigan shagwaban nan,
Sakin baki kawai yayi yana kallon dan karamin pink lips din nata bai taba tunanin Yarinyan ta iya shagwaba har haka ba, shi a ganin shima ai tafi duk matan duniya iya shagwaba ga kuma dan karamin bakin nan nata pink dashi kamar wacce take shafa lipglow, sai gaba daya sai yakasa mata magana ita kanta tayi mamakin hakan kuma tsaf takula da irin kallon dayake mata ta wutsiyar ido,
Phendo ce tafito daga daki daga ita sai yar wata yololuwar riga itako sanyin garin bataji kai tsaye saita wuce inda Jimeta yake tana bin Buddu da uban harara harta karasa ta zauna akan cinyar shi tana mai shagwaba shima sai yabiye mata hade dafara wasa da Boobs dinta mikewa tsaye Buddu tayi tana jan dan karamin tsaki a cikin zuciyar ta tace, yan iska kawai sannan takoma dakin ta tarufo kofar ta kwanta,
Jimeta tsaf yaji Tsakin data musu amma saiya shareta yaci gaba da lagudan Phendon daya gaji yace mata ta tashi taje tayi wanka tayi sallah sai takara nanike shi a jikin ta tace ai tayi sallah,
duk da yasan batayi sallan ba sai bai takura taba tunda yakula ita ko sallan ma batayi kuma ko tayi sallan ba amsuwa zayyyi ba tunda kullin hannun nan nata akwai Fixing nails sannan kanta shima tayi fixing red hair,
A haka Buddu ta wuni a cikin daki ita kadai kamar Mayya har zuwa dare saima idan tagaji da zaman ne ko kwancia sai tabude window tana kallon mutanan dake yan harkokin su a waje,
A cikin daren nanma sosai suka hanata bacci karshen ta dai karatun qur’ani tasaka ta sanya earphone ta toshe kunnan ta tana jan tsaki tana musu addu’ar shiriya tunda koba komai Hamma faruq dan’uwan tane.
A cen bangaren su Jimetan a cikin daren nan suka fara samun matsala sabida Jimeta koya fara bacci sai phendo ta tashe shi da rigimar ta tuni yagama fahimta Phendo irin matan nanne da basu gajia da da’na miji, karshen ta korar ta yayi daga dakin yamaida kofar yarufe hade da sanya key.

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE