BAKAR KADDARATA CHAPTER 3

Da wani mugun gudu yaja motan yabar haraban cikin gidan ranshi a matukar bace tuni idanun shi suka canza launi zuwa ja,
Kuka sosai tafashe dashi hade da mikewa da gudu tabar falon tawuce dakin ta hade da sanya key takulle dakin yanda ma kosu Umma sunzo bazasu samu daman shiga dakin ba, fadawa kan gado tayi hade da fashewa dakuka me karfi a haka bacci yadauketa bata saniba.
Jimeta kam yana komawa gida yayi sashin shi yanata zagaye dakin saida yaje daidai wajan bathroom yabuga hannun shi a jikin Bangon nandanan jini yawanke wajan ko a jikin shi haka yazube akan gado yadafe kanshi jini naci gaba da zuba a hannun nashi,
tunanin abunda zayma Buddu kawai yakeyi yahuce gabaki daya takaicin shi akan ta girgiza kai yayi sai kuma yasaki wani shu’umin murmushin dashi kadai yasan ma’anar sa,
tashi yayi yawuce bathroom yadauko first aid box sannan yadawo cikin dakin yayi treating wajan da yaji ciwon sannan yabude wani loka dake gefen gado yadauki wa’insu kwayoyi ya wasa a bakin shi yakora da ruwa ba’a jima ba bacci yadauke shi,
koda yatashi da asuba sai kawai yayi alwala yawuce masallacin dake jikin gidan nasu bayan an idar da sallan sai yawuce part dinsu Mami ya gaida su
yau harda wani munafukin murmushi akan fuskar shi dashi kadai yasan muguntar da yake hadama Buddu yana fitowa daga part dinsu Mamin yashirya yawuce cikin bariki tun daga bakin gate yafara kwasan gaisuwa yau kam da fara’arshi ya amsa musu gaisuwan yana shiga o!ice din yazube akan daya daga cikin kayatattun kujerun o!ice din yana wani murmushin da tunda kaka yafada mai maganan auren shida Buddu bayyi irin taba sai yau,
Knocking akayi batare da Jimetan yasan me knocking dinba yace yashugo,
Alamin ne yashugo o!ice din da sallama sannan yasamu gu yazauna yana bin Jimetan da kallo,
murmushi a samar fuskar Shi ya amsa sallaman,
alamin yace aboki na najika shuru kadadai kacemun har yanzu baka amince da maganar auran ka da Buddu ba,
murmushi Jimeta yayi a karo naba adadi kana yace,
“ko daya aboki na ai Tuni na amince aini yanzu jina nakeyi nama rigada na zama ango” yakare maganar da kara sakin wani murmushin yana wani kada kai,
sosai abun yabawa Alamin mamaki amma sanin waye abokin nashi sai kawai ya girgiza kai yace,
“Jimeta nasan kokai wanene tare muka tashi dakai nasan halin ka tabbas ka tsani abu dakyar ka iya son abun nan daga baya tabbas akwai muguntar da kake hadawa a ranka game da yarinyan nan”
sai alamin din yakara gyara zama yace “jimeta yakamata kagane wani abu yarinyan nanfa yar’uwar kace haba kayi tunani mana duk fah iskancin mu yakamata mu dan dinga sassautawa wani lokacin”
wani mugun daria Jimetan yafashe dashi hade da cewa,
“dadi na dakai aboki na akwai saurin fahimta ni kaina nasan abunda na shirya yima yarinyan nan da kanta zata gudu tabar gidan idan an daura auren sai tagane Jimeta ta aura dan sai na koya mata hankali sai aure yafice a kanta alamin i hate dat girl bazan taba iya son kucakan yarinyan nanba kwaila da ita yar cikina kanwar baya na gaskiya ba karamin cuta na akayi ba”
girgiza kai kawai Alamin yayi hade da mikewa tsaye yace, Well wannan kuma matsalar kace nifa nan daka ganni nakusa tuba insha Allah dan gaskiya ni kaina ina bukatar auren nan and kada kamanta Auren ka yana ta matsowa kaida yar Buddun ka yakamata ka dauke ta kudan zaga gari yanda zaku saba kafin biki”
Sai yakare maganar da wani mugun dariyar shakiyanci,
Hade fuska sosai Jimeta yayi hade da cewa, please jeka tunda zuwan naka bai amfana mun da komai ba jeka dan Allah kada kabata mun rai”
tabe baki Alamim din yayi hade dakara cewa “nidai na dauki nauyin Duk wani Event daza ayi Angon Buddu’am,
Sai yayi saurin ficewa daga o!ice din yana daria dan yasan yagama batawa mutumin nashi rai,
shirye shirye sosai aka fara a bangare biyu da gidan su Buddu da kuma gidan su Jimetan Tuni Ba!ah wato mahaifin Jimeta yabada isassun kudi an hado laife hade da duk abunda za’a bukata,
yau Yakama saura kwana uku bikin kuma har yanzu babu wani jituwa tsakanin mutanan biyu,
tafia sukeyi a cikin mota babu Wanda kema wani magana kanta tajuya tana kallon motocin dake wucewa akan titi shi kuma hankalin shi naga titi saidai duk ransu a matukar bace yake saidai ita Buddu harda tsoron Jimetan daya cika mata zuciya dan jinshi takeyi kamar wani mala’ikan mutuwa,
dayake shidin rikakken dan dunia ne sai bai nuna bacin ran nashi sosai ba dan duk hakan yana cikin plan din shine kuma bakomi yasa yayi hakan ba saidan yarabu da iyayen nashi lafia dan yaga kwana biyun nan sosai suke son yin fushi dashi kuma duk a dalilin Auren nashi da Buddu
kuma daba din an tilasta mishi ba wallahi bata isa tashiga cikin motar shiba daidai wani katon saloon yayi parking sai tayi saurin kai hannun ta kan handle din murfin motan zata bude tafita,
Bata ankara ba yakai hannun shi yakama nata hannun gagam yamurde da wani mugun karfin da yasan dole dole taji wani azaba wani ihu ta fashe dashi hade dacewa, “Wayyo Hamma Kayi hakuri wallahi Allah akwai zafi”
Sai takare maganar da yarfe dayan hannun ta tana matso hawaye,
Maimakon yasakar mata hannun sai yakuma damke mata hannun sosai yanda zata kuma jin wani zafin kana yace,
“Yanzu ni nake da ikon dake koda kashe ki zanyi babu wanda ya isa yayi magana badai kin amince zaki aure niba tau ai shikenan”
Sai yasakar mata hannun hade dakara cewa” Bafa zan jira kiba tunda niba drivern ki bane”
sai yasanya hannun shi a cikin aljihun rigar shi yacuro dubu biyu yasanya mata a cikin handbag dinta ai dawani mugun sauri tabude murfin motan tafita hade da banko mai kofar sannan ta leko ta jikin window din motar tace,
“aniyarka tabika inshaAllahu baka isa ka kashe masu Umma niba”
Sannan ta ruga da gudu tashige cikin saloon din, tsaki yaja sannan yatada Motan yabar haraban wajen
yau yarage saura kwana daya biki tuni abokanan shida sukayi karatu dasu a US suka hada masu wani gagarumin Dinner a helens event center,
da kukan Buddu da komai tace babu inda zataje wallahi saida Adda Bilkisu ta rarrashe ta sannan ta amince zataje shima saida aka hadata da Umma sannan ta hakura,
ta tazauna aka fara Tsantsara mata kwalliya sai takoma kamar ba itaba sannan aka dauko wani silver material aka bata tasaka gown ne ba karamin kyau yamata ba sannan silver din head a takaice dai shigan silver color tayi kuma sosai sukayi mata kyau,
sai takoma kamar wata yar baby daman gashi Adda bilkisu tagyara ta sosai da kayan gyaran jiki na mata kala kala dan takanas tayi order dinsu daga sudan kuma kunsan kayan gyaran sudan ba daga nanba wajen kyau sheki kawai takeyi sai yazamana su Adda Rukayya da Adda Lauratu sai zuzuta kyaun da tayi sukeyi suna santin gyaran jikin da Adda Bilkisu tamata,
kowa da kowa yawuce sai yarage saura amarya da ango kawai ake jira a wajan Dinner din Jimeta ansha wani hadaddan suit black color sai yawani hakimce a bayan mota dakyar Buddu ta iya bude motar tashiga ta zauna tarakube acen gefe kamshin turaren tane yaso chazawa Jimetan tunani driver ne yatada motar sukabar haraban cikin gidan,
tunda sukabar haraban cikin gidan har suka karasa wajen dinner din babu wanda yama dan’uwan shi magana,
Sosai wajen ya kayatu danba karamin kudi aka kashe ba wajen kayata wajen ba sannan duk wani lungu da sako da mutum zai kalla a wajen Sojoji ne hakan kadai zai tabbatar maka da da cewan dinner din wani babban sojan ne,
tunda suka fito daga cikin motar sai idanun kowa yakoma kansu badan Jimetan yaso ba sai yakai hannun shi yariko na Buddun sai sukayi wani mugu mugun dacewa da Juna duk da Buddun tazama wata yar karama a kusa da Jimetan amma sosai suka birge mutane,
Sosai cikin hall din ya kayatu dan kusan mazan da suke wajen Masu uniform din soja ne shiyasa sai abun yayi mugun kayatuwa dan harda Sword crossing saida akayi abun dai sai wanda yagani dan komi cikin tsari aka yishi da kuma wayewa hade da ilimi dan gabaki daya wa’inda suke wurin yan boko ne,
sha biyu dai-dai aka tashi daga dinner din anci ansha anyi watsi da Naira abundai ba’a cewa komai,
kowa ya watse amarya da ango kawai aka bari a baya saida mutane suka watse Jimeta yasakar mata hannu hade dajan tsaki sannan yayi wurin da akayi parking motar da aka kawo su yabude yashiga hade da danna lock sannan yacema driver din yaja motar su tafi da gangan yayi hakan sabida yafara koya mata hankali tun yanzu ta kuma fara azabtuwa tun kafin akaita gidan shi,
Kafin takaiga karasawa tuni motar tabar haraban wajen batasaan sanda ta fashe da kuka ba hade da daura hannu aka sai tarasa yanda zatayi sabida babu kowa a wurin sai masu gadi sosai hankalin ta yatashi sanin bata fito da waya ba balle takira wani a gida azo a dauke ta,
Fitowa tayi daga haraban cikin wajen tafara tafia a hankali sabida Hill shoe din dake sanye a kafar ta saida tayi tafia me tsawo sosai sannan dakyar tasamu abun hawa shima saida kyar ya dauke ta dan har saida tahada maida kuka ta kuma ce koh nawa yakeso zata bashi shine ya yarda yace zai kaita
daya ke daga wajen event din zuwa NYAYKOS QUARTERS babu wani nisa mintina goma ne yakai su har bakin gate din gidan su buddun Me keke napep din yana fakawa tayi saurin fitowa tace mai Dan Allah malam bara na amso maka kudin ka bata jira cewar shiba tayi saurin karasawa cikin gidan cikin ikon Allah tana shiga suka hadu da Adda rukayya tana fitowa daga bangaren baki da alama abu takai masu,
Ganin Buddun a rikice yasanya ta saurin karasawa inda take tafara jero mata tambayoyi ba tare da Buddun ta tsaya bata amsar tambayar taba tace,
“Adda idan akwai dubu daya a hannun ki dan bani nabawa me keke napep kada yagaji da jira”
Kallon Mamaki Adda rukayyan tama Buddun hade dacewa, ina Hamma Faruq din daya barki kika hau keke napep”
Cikin muryan da mutum yakosa sosai Buddu takuma cewa, nidai Adda bani kudin kafin nafada maki abunda yafaru” maimakon adda rukayyan tabawa Buddu kudin sai kawai tayi hanyar gate tafita da kanta ta sallami me keken sannan tacewa Me gadi yarufe gate tunda kowa yadawo,
Buddun tana tsaye inda Adda rukayyan tabarta tana sharar hawaye dan sai yanzu takuma jin wani mugu mugun zafi a cikin zuciyar ta,
Adda rukayya tana karasawa takama hannun Buddun sukabi ta kofar baya suka shiga cikin gida dan tacen main parlor akwai mutane sosai,
Saida takaita har cikin dakin ta kana ta zaunar da ita a bakin gado sannan itama ta zauna hade da tsura mata ido tana karantar yanayin Buddun saidai tuni tahango tsantsan tashin hankali da kuma tsoro a cikin idanun Kanwar tata tuni taji zuciyar ta tawani tsinke tausayin yar kanwar tata ya kamata dan tasan ko tantama babu Hamma Faruq shine da laifi,
Ganin irin kallon da Adda rukayya take mata ne ya sanyata barkewa da kuka hade dacewa,
“Wallahi Adda mutuwa zanyi Hamma Faruq baida imani ko kadan a cikin zuciyar sa Adda kiduba fa kigani Hamma tafiyar shi yayi yabarni ni kadai a wajen event dinnan bai damu da halin dazan shiga ba bai damu da idan wani mugun abun yasame niba Adda ya kike tunanin rayuwa ta zata kasance idan har ya kasance daga ni sai Hamma a garin da bansan kowa ba sai shi”
A karo na biyu ta kuma fashewa da kuka itama Adda rukayya tuni tafara kukan sabida ita kanta tasan Hamma Faruq baida imani danso dayawa lokacin suna kanana sunsha cewan anya hamma Faruq yanada zuciya kuwa sabida wanda baida zuciya ne kadai zai kasance mara tausayi,
saida sukayi me isar su sannan Adda rukayyan tafara rarrashin Buddun da tuni zazzabi yafara kamata dakyar tasamu ta rage kayan dake jikin ta kana Adda rukayya tasata tayi wanka tana fitowa tamika mata rigar bacci hade da ficewa daga dakin dan zuwa nemowa Buddu abunda zataci hade da maganin zazzabi dan batason Umma tasan da wannan maganar,
koda taje kitchen bata tadda wani abunda Buddu zata iya ciba sai kawai tayi saurin hada mata tea hade da soya mata kwai sannan tawuce dakin ta tadauko maganin zazzabi kana takoma dakin buddu koda ta isa ta tarar da buddu tana sallah sai tasamu wuri ta zauna dan tace zata tafi tabarta ba lale Buddun tasha tea dinba balantana kuma maganin data taho mata dashi,
Bayan ta idar da sallan Adda rukayya ta tasata a gaba saida tashanye tea din hade da kwain data soya mata sannan tabata maganin zazzabin tasha kana tace mata tahau gado ta kwanta batare da Buddun tayi musu ba tahaye kan gado ta kwanta Adda rukayya tarufa mata wani katon bedsheet dan har yanzu tana rawan sanyi kadaan kadan duk da zazzabin yafara sauka saida bacci yadauke ta kana Adda rukayya ta kashe mata wutan dakin sannan tarufo mata kofan tawuce dakin ta,
A bangaren Jimeta koda yabar wajen event din kai tsaye sai yacewa driver din yawuce dashi guest house dinshi kawai inda cenne yasaukar da bakin shi kuma yana bukatar sukara gaisawa tunda yau din baiwani samun lokacin gaisawa dasu ba,
koda suka isa tuni ya tadda su Alamin sun hada wani gagarumin party wanda yatara mata da maza a cakude sosai suka shagala masu rawa nayi masu ba’dala nayi masu shan beer nayi abudai kala kala shiyasa sai be tsaya a haraban wurin ba yacewa driver din kawai yakai shi gida dan yana bukatar kadaicewa yana bukatar yin dogon tunani tunda gobe uwar haka sunbar garin adamawa zuwa garin Lagos,
Washe gari tuni gabaki daya gidajen biyu suka kara cika sosai da mutane dan hatta cen gidan Alhaji babba dake Dongirei cike yake makil da mutane abunku da bikin yaran manya masu fada aji a cikin Jimeta,
Zan iya cewa duk wani lungu da sako dake cikin garin adamawa da kewaye babu wanda baisan yau ake daura auren Captain Faruq Hussaini Jimeta bah,
Karfe Biyu dai-dai aka daura Auren Captain Faruq Tahir Jimeta da Amaryar sa Fatima Buddu Hassan a babban masallacin dake cikin garin Jimeta wato akga dake cikin unguwan Dongirei akan sadaki mafi karanci Naira dubu Hamsi Alhaji babba da kanshi ya biyawa Jimeta kudin sadakin,
Abbu shine yazama waliyin Ango sai kanin shi mahaifin Jimeta wato ba!a yazama waliyin Amarya,
Tuni maka’da da maroka suka fara shela tuni Jimeta yaji kanshi yafara wani tsara mashi har baisan sanda yadafe kan nashi ba hade da saurin barin cikin mutane dan tuni aka fara zagaye shi ana taya shi murna,
Gefe guda yasamu ya tsaya inda mutane bazasu ankara dashi ba saidai tuni Alamin yabi bayan shi yace,
“Wai Jimeta meye haka ne baka ganin wa’insu ta dalilinka suka zo daurin auren amma kuma zaka dawo gefe guda katsaya kuma sanin kanka ne Ba!ah yasan baka gaisa da mutanan saba sai yayi mummunan saba maka”
rintsa idanun shi yayi hade dakara dafe kan nashi yana wani jujjuya kan nashi kamar wani kadangare cikin muryan da Alamin ya dadai baiji Jimetan dashi ba yace,
“ALAMIN please kaini gida”
Sai yakare maganar da kara dafe kanshi da dukkan hannayen shi guda biyu tuni hankalin Alamin din yayi mugun tashi a matukar rikice yakama Jimetan yana tambayar shi abun dake damun shi kasa bashi amsa Jimetan yayi sai jujjuya kai kawai daya keyi hakan sai yakara tsorata Alamin har baisan sanda yadauki wayar shiba yakira daya daga cikin kannan Jimetan yayi mashi kwatancen inda suke yakuma ce yataho da mota,
Koh second biyu ba’ai sai gashi yataho da motar shi kanshi dayaga Hamman nashi saida hankalin shi yatashi dan a tsawon rayuwar shi bai taba ganin Hamman nasu a cikin mawuyacin hali irin haka ba abunda yakara tada mashi da hankali kenan,
Tuni idanun shi sukai ja dan duk da halin Hamman nasu suna matukar kaunar shi sabida duk abunda suke so a duniyar nan idan yana dashi zai basu muryar shi har rawa yakeyi wajen tambayar Alamin abunda yasamu Hamman nashi maimakon Alamin din yabashi amsa sai yace,
“sagir bude gidan baya nasaka shi mu kaishi gida”
Cikin hanzari Sagir din yabude gidan baya aka sanya Jimetan aciki sannan shima alamin yashiga gidan bayan ya zauna, sagir kuma yayi saurin shiga mazaunin driver yatada motar sukabar haraban wajen da mugun gudu,
dayake daga Dougirei zuwa mafia’s Quarters ba nisa sai basu wani jima a hanya ba suka karasa gida,
Suna parking motar Alamin ya taimaka mashi suka wuce bangaren shi hade dace ma Sagir kada yafadawa kowa yayi shuru tukunna har suga abunda Allah zayyi,
suna shiga bangaren nashi yazaunar dashi akan kujerun dake zagaye a falon kara damke kan nashi Jimeta yayi yana fidda wani irin huci me matukar zafi Alamin yana jin hakan sai hankalin shi yadan kwanta sabida ya fahimci bacin raine da kuma damuwa yasanya Jimetan shiga wannan halin,
A bangaren Buddu tana fitowa daga wanka Wata yar kanwar Umma tashugo tana murna hade da rumgume Buddun kana tace,
“MashaAllah Buddu’am tazama Matar Hamma Faruq mijin dako wace mace takeda burin samu”
Tunda Tafara maganar Buddu jinta da ganin ta suka dauke tuni jikinta ya dauki wani irin rawa dahar yasanya Ummulkhair saurin sakin ta tana kallon ta tuni hankalin ta yatashi ganin Buddun tana wani irin girgiza hade da fidda wa’insu hawaye masu matukar zafi a saman fuskar ta,
Bata ankara ba sai ganin Buddun tayi tazube a kasa a sume wani kururuwa tayi wanda yajanyo hankalin su Adda rukayya da suke gabda shugowa dakin ai da gudun su suka karasa dakin basu tsaya tambayar abunda yajanyo harta suman ba Adda lauratu tafita da gudu takira Umma,
Ita kuma Adda rukayya tana rumgume da Buddun tana kuka Koda Umma suka shugo mutuwar tsaye tayi dan duk a tunanin ta sun rasa Buddun ne saidai ganin zuciyar ta yana bugawa ne yasanya Umman yin wani hamdala hade da wucewa Bathroom ta ibo ruwa sannan tadawo ta zukunna inda Buddun take ta yayyafa mata ruwan aiko tana yayyafa mata Buddun tayi wani dogon ajiyar zuciya hade da fashewa da kuka sai kuma ta rumgume Adda rukayya da itama kukan takeyi tace,
“Shikenan Shikenan Umma yanzu nazama matar Hamma wayyo Umma shikenan Hamma zai kasheni wayyo Umma kicewa Kaka ni bana son Hamma yaraba auren nan tun kafin Hamma yakawo maku gawata”
Sai takare maganar da kara fashewa da matsanancin kukan daya sanya Umman itama fara hawaye dan ita harda kukan rabuwa da buddu takeyi,
Cikin muryan Kuka Adda lauratu tace,
“Buddu Kiyi shuru mana baki ganin kinsaka Umma kuka ne haka kikeson kibar gidan nan Umma tana kuka”
Saurin Girgiza kanta Buddu tayi hade da sakin adda rukayya ta rumgume Umman nata tana kara sakin wani sabon kukan tace,
“Umma kidaina kuka kiyi hakuri wallahi nima bazan kara kuka ba daga yau” sai takara kankame Umman nata.
Rarrashin ta Umma tafara yi hade da mata nasihan daya shiga jikin ta sosai sai tanemi kukan da takeyi tarasa saidai sosai zuciyar ta take mata zafi sosai takejin bata son Hamma Faruq kamar yanda shima yake ikirarin baya sonta.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE