BAKIN DARE CHAPTER 13

BAƘIN DARE 
CHAPTER 13
Dakyar aka kamo Alhaji Bala Dan sam ba a hayyacinsa yake ba 
Hajiya Lubna kuwa tunda ta farka ta zubawa gawan Naila ido tana ta zubar da hawaye dan gani take kamar a mafarki wai Naila ta rasu kuka ta fashe dashi sosai tana kiran sunan Naila 
a lokacin da taje ta yaye mayafin Da aka rufe Naila dashi ta kankameta tana kuka 
Dakyar Nurses suka janyeta 
Alhaji Bala kamarya haukace a lokacin da aka saka gawan Naila a ambulance aka nufi 
gidansa Dan ayi mata sutura akai ta gidanta na gaskiya 
Sai rirrikeshi akeyi yana tirjewa Hajiya Lubna kuwa wani irin dauriya ne yazo mata ta ringa addu’oi aranta 
Kafin kace me mutane sunji Labarin mutuwar Naila ‘ya daya tilo ga Alhaji Bala kasancewarsa sananne mai taimakawa talakawa kowane gidan radio da television labarin 
kawai ake yi Akram da ogansa Abdullahi na zaune a lokacin da suke kallon labaran a tashar NTA 
Akram kabbara yayi a lokacin da yaji sanadin mutuwar Naila Dan Alhaji Bala tamkar mahaukaci duk wanda ya gani sai yace mishi agaban idonsa akayiwa ‘yarsa fyade har ta mutu dan haka bazai yarda ba sai inda karfinsa ya kare 
Akram girgiza kansa yayi yacewa Ogansa “Allahu Akbar Allah da girma yake abinda Alhaji Bala yakewa yaran mutane da matan mutane gashi yajuyo kansa tun ba’aje ko ina ba wlh baka ga yanda yakeji da yarinya nan ba idan kana so kaga fara’arsa da dariyarsa ka kira shi da Daddyn Naila wlh naji tausayin yarinyar laifin mahaifinta ya shafeta” 
“Eee da tausayi dan tausayi kam dan batayi sa,an uba ba Sam to yanzu da aka mishi 
mutuwa zai yiwu muyi arresting dinshi a gobe kuwa”? Abdullahi yace yana kallon Akram 
Akram shiru yayi na ‘yan mintuna kafin yace ” ina ganin mu kara gwada Alhaji Bala mugani ko ya dan rusuna sabida abinda akayi wa ‘yarsa mu bashi zuwa nan da sati biyu mugani ko ya kira k0 bai kira ba zamuje muyi arresting dinshi kawai abinda zamuyi a kara tsare 
yaransa sosai sabida kar ya gano shirin da ake akansa” 
Da haka sukayi ta tattaunawa ta hanyoyi da zasu bullowa Alhaji Bala 
Alhaji Bala kuwa rikeshi akayi tayi lokacin da aka zo fita da gawan Naila sai ihu yake yana kiran sunanta Hajiya Lubna kuwa daurewa tayi sosai tayiwa ‘yarta addu’ar rahamar Allah har aka tafi kaita gidanta na gaskiya 
A haka idan kaga Alhaji Bala sai ya masifar baka tausayi dan mutane sun San irin San da yake wa Naila sai surutu yake shi kadai yana sai ya nemo barayin da suka kashe mishi ‘ya wasu ma sun dauka k0 tabin hankali ya samu,,
Manyan mutane ne suka ringa zuwa mishi gaisuwa sabida sun San yanda yake hidimantawa talakawa ciki kuwa har da wasu ‘yan siyasa 
A cikin masu zuwa kalilan din mutane ne kawai Alhaji Bala bai yiwa fashi ba wani Alhaji Ghali hamshakin mai kudi dake tashen Naira shima ya biyo wani abokinsa dan suyi wa Alhaji Bala gaisuwa 
Duk da Alhaji Bala baya iya amsa gaisuwar da ake mishi amma yana sane da duk wayanda suke zuwan mishi gaisuwa tunda Alhaji Ghali ya zauna Alhaji Bala ke satar kallonsa dan k0 iya suturar dake jikinsa da agogon dake sakale a hannun shi idan ka kalla kasan ba 
karamin kudi aka kashe wajen siyansu ba Su kuwa tattaunawa kawai suke akan yanda barayi suka addabi Mutane bayan sun maka sata ma bazasu barka haka ba ko suyi kissan kai ko suyi raping din iyalanka mata Alhaji Ghali kuwa shima sai tofa albarkacin bakinsa yake yana cewa A Nigeria babu matakan tsaro sosai shi yasa barayi ke abinda suka ga dama dan babu kasar da ake yin haka sama da Nigeria dan haka yana gama ginin gidansa a Cairo zai kwashe iyalinsa su koma can dan duka yaransa ma can suke karatu Hutu kawai ke kawo su nan shima yana kasuwancinsa acan sosai 
Duk hirar da suke Alhaji Bala ya baje kunnuwansa yana jinsu a zuciyarsa yana tunanin Alhaji Ghali shine next target dinsa dan abinda su Steven suka mishi yasa ya kara jin babu ko digon imani azuciyarsa 
A cikin hirar da suke yi Alhaji Bala ya ringa samun information akan Alhaji Ghali da irin sana’ar da yake yi kansa a sunkuye yana wani Jan carbi kamar bai San hirar da suke ba mikewa sukayi suna kara yiwa Alhaji Bala gaisuwa tare da bashi shawaran ya saka yan sanda su binciko wayanda suka mishi wanan aika aikan
Alhaji Bala godiya kawai yake musu yana share hawayen dake zubo mishi su kuwa tausayin 
Alhajl Bala ya ringa rufesu dan sun San irin kaunar da yakewa tilon ‘yarsa Har bakin mota Alhaji Bala ya rakasu yana kara nazarin Alhaji Ghali inda harya rike lambar motar Alhaji Ghali har sai da suka tafl ya juya ya koma yana sake sake aransa Bayan kwana bakwai da rasuwar Naila Alhaji Bala yana zaune a dakinsa shi kadai ya saka hoton Naila a gaba yana kallo sai hawaye ke zuba a idonsa da ace zai iya ganinsu Steven da babu abinda zai hana ya kashesu ya yankasu ya kona su 
Hajiya Lubna kuwa tafi Alhaji Bala tawakalli dan tasan Allah daya basu Naila yafi su San ta har mamakin rashin tawakkalin Alhaji Bala take 
A yanzu ma zuwa tayi ta tarar da shi yasa ka hoton Naila agaban yana kuka 
girgiza kanta tayi ta nufi inda yake ta zauna a gefensa tare da dora hannunta akan kafadarsa 
Wani irin zabura Alhaji Bala yayi kamar an dora mishi wuta yabi Hajiya lubna da wani mugun kallo 
Hajiya Lubna sakin baki tayi tana kallon shi cikin tsananin mamaki daurewa tayi tace “Alhaji Lafiya mai yafaru”? 
Wani Mugun kallon ya kara binta dashi yace ” ki fitar min daga daki bana San ganinki babu matar dana tsana sama dake wlh naso ace ke kika mutu ba Naila ba yar iska kawai mara mutunci” 
Jikin Hajiya Lubna ne ya hau rawa sabida girgiza da tayi da maganarsa hawaye kuwa suka hau wanke mata fuska cikin in ina tace “Mai na maka haka Alhaji”? 
” dalla ki bace min da gani har ni zaki ringa tambaya mai kika min sabida ke tantiriyar ‘yar iska ce agaban idona maza bakwai sukayi layi akanki suna saduwa dake tsabagen kinajin dadin abinda suke miki ko tari bakiyi ba ballantana naji ihunki ballantana akai ga kiyi kokawa dasu akan kar su sadu dake lumshe idonki kawai kikayi kina jin dadi Lubna Ashe ke yar iska ce bansani ba wlh na masifar tsanarki bazan iya cigaba da zama dake ba kyankyaminki ma nakeyi” 
Hajiya Lubna zubewa tayi a kasa kirjinta ya fado kasa ta ringa nanata “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun” kallon Alhaji Bala kawai take dayake binta da wani irin kallon tsana cikin matsanacin kukan da ta fashe dashi tace “Bala nice yar iskar azo har cikin gida ayi mana fyade nida ‘yata bakayi wani yunkuri dan ka hanasu keta mana haddi ba har na rasa ‘yata amma kace min ‘yar iska kai da kake namiji ma sunfi karfinka sai ni danake mace zanyi kokawa dasu” Wani mugun tsawa Alhaji Bala ya daka mata yana “dalla rufe min baki yar iska sa‘oinki da ake zuwa yi musu fashi a nemi a keta musu haddin kinsan irin kokawar da muke yi dasu dan kawai kar a keta musu haddi akwai matar ma da sai data gwammace ta rasa ranta da a keta mata haddi Dana ‘ya‘yanta amma tsabagen ke ‘yar iska ce kwanciyarki kawai kikayi suka ringa hawanki suna sauka” 
Alhaji Bala Sam bai San ya saki layi ba Hajiya Lubna kuwa kalmarsa kawai ke amsa kuwaaa a kunenta ” _Kinsan irin kokawar da mukeyi dasu dan kawai kar a keta musu haddi_ 
Kanta taji ya mata nauyi a hankali ta mike ta fara ja da baya tana nuna Alhaji Bala cikin rawar murya da jiki tana “Bala Bala dama kai dan fashi ne har matan mutane kake ketawa haddi”? 
Sai a lokacin Alhaji Bala yasan kwabar da yayi fuska a daure yace “dama bakisani ba ni cikakken dan fashi ne da kudin fashi kike watayawa da kudin fashi kike abinda ranki keso da kudin fashi kike walwalawa na kashe rayuka sunfi dubu na ketawa matan aure da yan mata haddi sunfi Dari da ace banida kudi bazaki taba yarda ki Aureni ba,, Da nazo Neman Aurenki babu Wanda ya gwada tambayata wane irin Sana’a nake sabida tsabar danginki makwadaita ne su dai kawai tunda sun samu mai kudi shikenan dan haka Lubna ni Armrobber ne ni killer ne tunda kinringa da Kinsan waye ni I would not spare you kema kasheki zanyi kawai” Hajiya Lubna aguje ta fice daga dakin Alhaji Bala ya bita a guje Cikin zafin nama ya damkota Hajiya Lubna ta saki wani irin ihu tana rokonsa akan ya kyalleta 
Janta kawai yake yi a kasa har sai da yaja ta wajen bayan gidansa da rijiya yake ya damkota da hannu biyu yace “kin Riga da Kinsan sirrina kasheki shi zai fiyemin alheri idan na barki zaki tona min asiri mutane su San wayeni dan haka zanjefaki a cikin rijiyar nan idan yaso zancewa mutane na nemeki na rasa” 
Hajiya Lubna cikin rawar murya tace “Bala wlh bazan tona maka asiri ba dan Allah kar ka kasheni ka tuba mu gina ingantaciyar rayuwa tunda kaga ishara akan tilon ‘yarmu Naila abinda kayiwa ‘ya’yan wasu akayi mata har sai da ya kaita ga rasa ranta wlh babu Wanda zan gaya wa dan Allah kar ka kasheni” 
Alhaji Bala girgiza kansa yayi yace “Kasheki shi zai fimin alheri Lubna dan babu digon kaunarki araina bazan iya cigaba da zama dake amatsayin matata ba bayan maza bakwai sun shiga inda nake shiga” 
Daga haka ya bude murfin rijiyar yana kokarin Danna Hajiya Lubna a ciki sai ihu take Ji yayi an fisge Hajiya Lubna daga hannunsa ya waiga da sauri dan yaga Wanda ya fisgeta Na Maliya yagani asaman ruwa fuskarsa a daure 
Alhaji Bala k0 tsorata baiyi ba shima ya daure fuska yace “mai kake nema kuma awajena 
naga wacce kake so na kawo maka ta Riga da ta mutu” 
“Nasan da haka shi yasa nazo na tafi da uwarta ta maye gurbinta kai kuma kana kokarin ka kasheta” 
Alhaji Bala murmushin mugunta yayi ya kalli inda Hajiya Lubna ke zube tana rawar dari gumi yabi ya wanke mata fuska ta kalli Na maliya ta dawo da kallonta kan Alhaji Bala 
“Zaka iya tafiya da ita na bar maka ita duniya da lahira Aljaninka dan saurayi yayi ta hutawa 
da ita har karshen rayuwarsa” 
Na Maliya kara daura fuska yayi yace “naga alamar farinciki kake ka rabu da ita sabida ba kaunarta kake ba tunda hakane bazan mata komai ba taimakonta zanyi zan maidata garinsu sabida karka kasheta idan yaso kai kuma sai na dauki fansa akanka kai da kwanciyar hankali sai dai a lahira ayanzu zaka gwammaci mutuwarka da rayuwarka a yanzu zaka girbi abinda ka shuka” 
Alhaji Bala tabe baki yayi yana harararsa Na Maliya ya fashe da dariya ya bace Da sauri Alhaji Bala ya juya yaga itama Hajiya Lubna ta bace daga wajen 
Kara tabe baki yayi ya nufi cikin gidan dan yana ganin Na Maliya ya rage mishi aiki tunda ya tafi da Hajiya Lubna 
Waje yayi direct ya nufi cikin motarsa dan ya dauko wayarsa ya kira su Killer dan tunda 
yazo garin ya kashe wayarsa 
A kashe yaji wayar Killer ya kira na Lion 
A lokacin wayoyin suna gaban table din Akram da sauri ya d’auki wayar daya ga Alhaji Bala ke kiransa ya nufi wajen da aka kullesu a guje dan ya dade yana expecting din kiranshi 
Su Lion dake zazzaune duk sun bi sun fita daga hayyacinsu sabida azabar da ake gana musu 
Akram da sauri ya mika mishi wayar tare da dora bindiga akansa akan kar ya kwapsa dan ya Riga da ya gaya musu irin had’in kan dayake so su bashi dan su chapke Alhaji Bala cikin sauki 
Lion sai da ya daidaita kansa da muryarsa kafin ya daga wayar yasaka a hands free 
Kifta mishi ido Akram yayi yayi sauri yace “Oga muna ta gwada wayarka akashe dan mu maka gaisuwar rashin da aka maka da zamu zo black yace kar muzo tunda baka mana izini ba” 
“Gwara da Baku zo ba dan ana ganinku ansan ba mutanen arziki bane rashi kam anyi min shi sai na dauki fansa akan masu shekarun Nailata har sai na aika su Lahira kamar yanda aka aikata Lahira ina sauran suke”? 
Da sauri Akram ga kifta mishi ido yana mishi magana da hannu Lion yace ” dukanmu muna nan a villa dake Abuja” “Dats good dan anan zamu yi operation jibi ina Akram yake”?  gashi nan oga” 
Akram da sauri ya karba wayar Killer dake gefe kamar ya fusge wayar daga hannunsa yace mishi Akram Ss ne suna nan a kulle 
Akram gaishe shi yayi yana ce mishi ya hakuri 
Alhaji Bala ko amsa gaisuwar baiyi ba yace “kai jibi zamuje operation kuma kai zaka mana jagora wlh any slight mistake consider your self dead” 
Da Sauri Akram yace “to Oga ina zamuje operation din”? 
” Babu ruwanka da inda zamuje operation Ku dai zama ready kawai bawa Killer wayar danna kirashi wayarsa a kashe” 
Akram wani irin harara ya wurgawa Killer yana mika mishi wayar dan Killer na da taurin kai sai da Akram ya dauko iron din da ake gana musu azaba dashi Killer ya daidaita nutsuwarsa yace 
“Oga ina gaisuwa ya hakuri” Alhaji Bala tsaki yayi yace “mai yasamu wayarka a kashe” “Wlh oga wayana babu chaji ne” 
“OK jibi ina nan shigowa zamuje gidan Alhaji Ghali dan chanji zamuyi operation dinda ba’a tab’a yin irinsa ba dan sai na dau fansar kissar da akayiwa Nailata” 
“Allah ya kai mu oga sai kazo” 
Akram fusge wayar yayi daga hannunsa fuskarsa d’auke da murmushi dan dama burinsa ya San wa zasuje suyiwa operation din 
Hajiya Lubna kuwa bata tsinci kanta a k0 ina ba sai a kofar gidansu 
Da sauri ta mike ta shige jikinta na rawa …….. 
Hmm Alhaj bala fa bai saduda ba kome zai faru????????

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE