BARIKI NA FITO CHAPTER 16
BARIKI NA FITO
CHAPTER 16
Habib kallonta yayi yace bariki Wlh son Yarima kike.
Bariki hararan shi tayi tare da fad‘in ni na fad’a haka koh? Kawai daka had’uwa na dashi sai in fara sonshi.
Habib tabe baki yayi tare da fad’in, oh mai yasa kike cewa zaki gujeshi saboda kin kasa fad’a Mai gaskiya?
Bariki shuru tayi t‘ana nazari….
Habib ya Katseta tare da fad’in in bakya sonshi Mai yasa kike tsoran fad’a mishi gaskiya? Saboda kina tsoran ki rasa shi koh?
Da saurita kalli habib
Murmushi habib yayi tare da fad‘in Kinji na fad’a miki abunda ke ranki koh? Toh Bari kiji gwara da baki fad’a mishi koke wacece ba, domin na tabbata dan gidan sarauta bazai auri karuwa ba, balle ke da kikai suna cikin wannan anguwan
Bariki tace nace miki auranshi zanyi ko cewa nayi ina sonshi? Dan Allah tashi ni mubar wannan gidan in koma d’aki na Ina bukatan in huta.
Habib dariya yayi tare da d’aukan Mata ledan da Yarima ya bat‘a. yace duk dai boye boyen mai ciki dole wata rana ya fitowa, yayi tabi bayanshi har d’akinta habib yakai mata kayan sannan ya fita tare da fad’in ina da ba’ko zanje in Kai mishi yarinya sai na dawo nazo mu tattauna.
Bariki t‘ace toh tare da rufe kofarta..
Habib yace bariki ki gama Munafurcin ki, Danni tuni na baro jirgin soyayya ta kama ki, yana tafiya yana maganar t‘are da bokare duwawu Wai shi a dole yana rangwada.
Bariki kwanciya tayi tare da lumshe ido duk abunda ya faru ita da Yarima Aliyu yake dawo mata, da sauri ta bud’e ido tare da tashi d’auko card din daya bata tayi ta bud’e wanda yake ta faman kamshi Fara karantawa tayi kaman haka ……..
I have liked many but loved very few. no-one has been as sweet as U. I would stand and wait in the worlds longest queue. Just for the pleasure to a moment with U.
Ido ta lumshe Bayan ta gama karantawa a hankali ta furta so romantic, ledan daya bama habib ya bata, ta Fara bud’ewa, kwalin waya ta farayin karo dashi iPhone Xmas, sai su turare masu tsadan gaske kuma duk Arabian perfumes ne, a kalla sun Kai Kala goma sha biyar, banda su body spray, murmushi tayi domin a duniya tana son kamshi, d’aukan kwalin wayan tayi ta bud’e tare da sawa a caji, ba karamin jin dad’in kyautartayi ba, wannan ne karo na farko da namiji ya bata kyauta harta yaba kuma taji dad’i Sosai, d’aukan wayanta tayi tare da shiga wajan message ta Fara rubutu kaman haka….
Naga sako nagode Sosai ban San wani irin godiya zanyi ba, Allah ya biyaka da gidan
Aljanna, amma wannan kayan kaman sun min yawa Yarima na.
Tunani tayi ta tura mai ko Karta tura, tayi wajan minti biyar tana tunani sannan ta tu ra mai.
Harga Allah ansha yi mata kyauta Kala Kala,toh mai yasa bata jin dad’i irin haka sai wanda Yarima ya Mata? ido ta lumshe tare da fad’in kodan shi ba irin sauran samari na bane? Kai ta d’aga alaman hakane shine wanda ya fara min kyauta tunda na fito bariki ba tare daya nuna yana son wani abu daka gareni ba. Murmushi take tayi tuna firanta dashi ga kamshin turarenshi da har yanzu yana hancinta yaki tafiya, lokaci d’aya kuma ta dan gimtse fuska data tuna yace Mata auranshi rana ita yau, tabbas ya kamata inyi gaggawan rabuwa dashi tun Kafin ya zaman min matsala a cikin rayuwa na, tashi tayi ta d‘auki wayanta tare da
dannawa taga har yayi mata reply da cewa….
My princessl really miss you, komai na baki u deserve it, so ban son daka yau ki karamin
godiya, love you so much, I will call you when arrived home, take care.
Ido ta lumshe lokaci d’aya kuma ta bud‘e idon tare da kashe wayanta…. Tace Yarima bazan cuceka ba,nasan da kyakyawan zuciya kazo min, rayuwa ta abun kyamace ga dukwani namiji mai kishin kanshi, na tabbata rabuwa dakai shine Alheri a tare dani, domin bazan iya fad’a maka wacece ni ba, infact ma babu tsarin aure a rayuwa na, Indai harzanyi tunanin haka burina bazai cika ba, bazan so hakan ba kuma wani hawaye mai zafI ya zubo mata, lokaci d‘aya tasa hannu ta goge tare da fad‘in Yarima na Barka daka yau bazan kara
sauraranka ba, dan had’uwa na dakai na rana d‘aya yana kokarin canza min tunani …..
Yarima Aliyu ya karasa gida gab da magrib, bai shiga ciki ba, masallaci ya shiga inda yayi alwala dan yana jira a kira sallah sai ya shiga gaba d’aya, har sai da akayi sallah isha’i sannan ya shiga gida, direct gefen shi ya shiga ya fad’a toilet, shower ya saki ya dad’e ruwa yana dukanshi ba komai yake tunani ba saina gimbiyarsa ya dad’e a haka Kafin ya fitO, jallabiya ya saka, dan shirin kwanciya, falo ya nufa inda yaga anjera Mai abincin dinnera table, zama yayi kuyangi har biyar suka zo domin zuba mai abinci, zuba mai abinci sukayi suka gama, sannan sukai dan nesa dashi, bai wani ci da yawa ba ya tashi yabarwajan
domin yana bukatarjin muryan princess dinshi ….. Yana shiga d’aki ya doka Mata kira, amma sai me?
Yaji ance number din a kashe, abun mamaki ya bashi dan haka ya kara kira amma switch off, d’an shuru yayi alaman damuwa, tare da fad‘in maiya sami wayanta? Kiran Layin habib
yayi Habib d’auka yayi tare da fad‘in Allah ya taimaki Yarima.
Yarima Aliyu amsawa yayi da ngd, maiya sami wayan zainab I try her line but switch off.
Habib yace Wlh Yarima na fita ,amma anjima kad’an zan koma, I’na tunanin babu wuta ne,
hala bata da caji. Yarima yace ok bari in kira a kawo muku yana fad’in haka ya kashe wayan.
Habib tashi yayi daka inda yake domin ya koma yaga lafiya bariki ta kashe waya dan yasan haka kawai ta kashe badan bata da caji ba, sallama yayi ma mutumin da yakai ma mata har biyu zai kwanta dasu, d’aukar kudi yayi yaba habib sannan yayi gaba.
Yarima Aliyu shugaban Nepa na kaduna state ya kira, bayan ya d‘auka sun gaisa da Yarima
Aliyu, yarima yace Ina son a kaina maraban jos wuta, yanzu akwai ….. Sai kuma yayi shiru
Shugaban Nepa yace ranka ya dad‘e ai suna da wuta, banyi ko minti biyarda gama waya da
wani dan uwana dake Jaji ba, kuma duk hanyar su d’aya tun daka Barakallahu birnin yaro har zuwa jaji.
Yarima Aliyu yace ok nagode tare da kashe wayan, dan shuru yayi cikin mugun damuwa, maiya sami wayanta‘! Kara kiran layin habib yayi.
Habibya d’auka tare da fad’in Allah ya taimaki yarima, ina hanya na kusa zuwa Gida.
yarima yace ok am worried Sosai na kira ance akwai wuta, na damu da naji wayanta a kashe.
Habibyace lna zuwa zan kira in bata.
Amsawa yarima yayi da fad’in 0K tare da kashe wayan.
Yarima Aliyu shuru yayi yana tunani wai yau shine yake kira akan mace, dan kawai ya jita shuru, ido ya lumshe, yana tuna yanda take magana cikin nutsuwa, tunawa yayi sanda tace mishi Yarima na. Bai san lokacin daya saki murmushi ba …….
Habib Bayan ya karasa gida, direct d’akin bariki yayi, nocking ya fara mata
Bud‘e kofar tayi daka ita sai rigan bacci dai dai cinyarta tace wannan bugun kofar kaman ana bina bashi.
Habib yace kyaji dashi dai, in banda iskanci kya tashi ki kashe waya Bayan kin San sarai za’a nemeki
Bariki tsaki tayi tare da fad’in ai duk mai nema na sun San inda nake, kai baga shi kazo
Dakata habib ya Katseta ke dawa? Naji kina kai Waye Kai a nan? Wlh bariki sarai kin San banda mutunci akan me zaki dinga danganta ni da maza? Gskya bana so wlh, sannan da kike maganan masu nemanki sun san inda kike aishi yarima bai San inda kike ba….
Tace kaman ya?
Labarin yanda sukai da Yarima ya bata tare da fad’in yanzu ki kunna waya domin Wlh lndai baiji muryanki ba yanda ya damu zaki iya ganinshi yanzu.
Bariki tace na shiga uku na had’u da bala’i, gskya nifa ban son takura
Habib yace Mai kike nufl? Toh Wlh bari kiji wannan daman ba kowa ke samu ba, ki kalli mutum kaman Yarima Yaro Mai Kyau ga sarauta ga kud’i da iko haryace yana sonki ki dinga gudu, kalli dukwannan Abun nashi baki ga yanda yaita kirana ba.
Bariki tace kawata ba gudunsa nake ba, nasan duk ranan da yasan wacece ni, zai barni, ban son sama kaina abunda zai daman, Nasan Yarima yafl karfina rayuwa na da nashi ba iri d’aya bane.
Habibyace ke har kina tunanin zai gano gaskiya? Toh ta ina zai gano gaskiyan? Bari kiji kawai kiyi abunda nace miki Wlh Indai kikayi yanda nace Yarima zai zama naki sannan
naza: taba sanin gaskiya ba. Bariki tace taya hakan zai faru gaskiya bazan iya ba. Habib yace Toh ko ayabarsa karama ce?
Bariki duka takai ma habib tare da fad’in uhm ni inama na Lura baki ga yanda ya cika min ido ba ban ma sami daman Lura ba, amma ai duk Wanda yaga Yarima yasan jarumin namiji ne dan yana yinshi kawai ya isa ya gamsar da mutum.
Habib dariya yayi tare da cewa ahayye nanaye Bariki tace harda waya Yaban kin ganta iPhone Xs mas
Habib sakan baki yayi tare da fad’in Kinga harkan arziki? Oh wannan yariman ko dan arziki ke bariki arziki na kiran ki kina gudu,jiba dubu d‘ari biyu yaban ba ‘tare da nayi mishi aikin komai ba, wlh Idan kika bari Yarima ya kubuce miki saina tsine miki.
Bariki dariya ta kwashe dashi,tare da fad’ln sannu uwata wacce ta kawo ni duniya.
Habibyace Aini haihuwarki ne kawai Banyi ba, amma ina baki shawaran arziki, wlh bariki ki
kunna waya yanzu tun Kafin ya diro cikin daren nan.
D’auko wayanta tayi tare da kunnawa tana fad’in oh ni bariki ina ganin abu ni Wlh ban son harka da mutane masu kokarin canza min tunani, aiko tana kunnawa saiga kiran yarima ya shigo, nuna ma habib tayi
Habib yace ce dan halak. D’auka tayi tare da sawa a kunnenta sallama tayi
Amsawa yayi tare da fad’in my princess maiya faru kika kashe waya, kin san yanda na damu kuwa? I thought wani abune ya faru.
Tace na kashe ne nasa a caji, sai bacci ya daukeni, yanzu habibyazo yasa aka tashe ni, shine na kunna Ina son kiranka sai gashi ka kira.
Yarima yace eyya sorry my princess nasa an tashe ki .
Murmushi tayi tare da fad’in ya hanya da fatan ka koma lafiya?
Yace Alhmdlh sai dai gskya I really miss you, Anya zan iya jira jibi kuwa?
Murmushi tayi tace ai kaman yau ne Yarima yaufa kazo muka had’u kuma ka ganni
Yace hakane amma ban gaji da ganinki baA… D‘an shuru yayi Kafin yace Zainab za’a iya bani auranki a wata biyu?.
Daram taji gabanta ya fad’i amma da yake y‘ar duniya ce saita wayince tace haba Yarima Wlh har kaban dariya.
Yace am serious Zainab, ina son insha Allah nan da wata biyu in aureki inda so samu nema da nan da wata d’aya zan ce, so plz ina son ki bari inga iyayenki nayi miki alkawarin Indai na gansu suka bani izini Indai bamu dai daita ba zan hakura, bazan bari ayi miki dole ba.
Kasa magana tayi, domin bata san mai zata cemai ba.
Yace Zainab nasan yanzu ba Abu bane mai sauki ki yarda dani lokaci d’aya be, but Ina son kiyi trusting dina bazan ‘aba cutanki ba, so plz ki bari inga iyayenki
Tace shikenan zaka ga iyayena amma sai bayan bikin ka, Kafin nan ka sami nutsuwa.
Murmushi yayi tare da fad’in dukyanda kika ce haka za’ayi, bari in barki ki huta sai munyi magana gobe.
Tace Allah ya kaimu.
Ya amsa da Ameen tare da fad’in I love you
Murmushi tayi tare da fad’in nagode.
Yace Nop ba haka zaki ceba, amsa nake bukata nace I love you sai kiban amsa. Tace shine nace nagode ai
Murmushi yayi tare da fad’in in baki bani amsa ba in nazo sai nasa kin ban Tace uhm tare da fad’in I love you too, tana fad’in haka ta kashe wayan.
Yarima wani irin nishad’i yakeji, tare da mamakin kansa Wai yau shine yake fira da mace haka ikon Allah.
Habib ganin bariki ta kashe waya yace Wlh bariki keba karamar yar duniya bace,jiba yanda kike waya da Yarima kaman wata baiwar Allah.
Bariki tace eh naji din, kin san mai yace kawata? Wai aurena zaiyi nan da wata biyu yake son muyi aure.
Habib yace an gama, inma wata d‘aya yace ke k0 gobe yace Wlh zamu aurar dake. Bariki tace taya?
Habib yace kaman yanda mukaje gidan mutane kika flta a matsayin nan ne gidan y’an uwanku haka ma za’a ai auran iyayen bariki zamu samo …..
Bariki tace iyayen bariki kina ganin babu matsala? Habib yace koh d’aya kawai kiyi yanda nace
Bariki murmushi tayi domin wannan ne kadai hanyarda take ganin ya dace ….. Kai Anya zan iya kuwa? Babu tsarin aure a rayuwa na. Murmushi kuma ta kuma saki tunawa da tayi yace in basu dai daita ba bazai Mata dole ba ……