BARIKI NA FITO CHAPTER 32
BARIKI NA FITO
CHAPTER 32
Bariki ganin yayi rejecting kiran yasa tayi murmushi dan tasan dama inta kirashi baya d’auka sai dai ya kirata koya bari ya tsinke ya kira koya kashe ya kira, minti d‘aya minti biyu har biyar Yarima shuru bai kirata ba, d’an murmushi tayi tare da fad’in may be yana wani abune Nasan for sure zai kirani,jiran kiran Yarima tai tayi taji shuru, d’aukan wayanta tayi ta duba time din data kirashi taga wajan 44min tace Iaflya kuwa? Kar dai ace har yanzu yana fushi ne? Kai no Nasan bazaiyi fushi irin haka ba…. Kara dialing number dinshi tayi taji ance mata switch off, tace haba daman Nasan haka kawai Yarima bazaiki kirana ba, may be yasa caji ne koh yana wani Abun …… wata zuciyar tace ko kuma yana wajan amarya ba, yana zuba mata tsantsar soyayya ….. Da sauri ta girgiza kai tare da fad’in no ….. Jin ana
mata nocking yasa ta Fara fad’in Waye ne?
Muryan habib taji yana fad’in bud’e mana, ba kwarto bane da kike zunduma ihun Waye
Bud’e kofar tayi habib ya shigo ,zama yayi yana fad’in Washhhhh Na gaji, d’anzo ki
matsamin baya na Bariki tsaki tayi tare da fad’in Koba baya ba?
Habib yace eh shi nake nufl …… Ke bama wannan ba wai maiya faru tsakaninki da Yarima ne? Naga yanda yake fushi yana ta gudu dama kaman zai tashi sama, shi yasa Nayi mishi karya ya saukeni Kar yaje yajefamu kan trailer mu mutu, ban ajiye Mai min addu’a ba, ko d’an auren da mata keyi koda shiga ki flto ne ace kadai taba koshi Nayi ai babu laifi ……
Bariki tace Hmmm Allah ya kyauta, tare da fad’ama habib abunda ya faru …….
Habib yace amma da iskanci kike akan wani dalili zaki bama wani dama, ai gashi yanzu kinja ma kanki sai ki nemi mafita, ni naga kaman ma nafI son ki auri Yarima domin in Ina wajan da yake Mai kamun kai nake zama, amma ke in banda tsaban iskanci har kice zaki ga wani kuma kin San da wanda kika je wajan …..
Bariki tace ai ka tsaya ka ……. Habib dakatar da ita yayi tare da fad’in Wlh bariki ban son bura uba, akan wani dalili zaki dinga kaini jinsin daba nawaba?… Gskya banso Bariki tace kwantar da jijiyoyin cillarka ….. Tashi yayi tsaye tare da kama kugu yana fad‘in bariki sanin kanki kin San wacece habiba,
wlh banki inyi tsirara ba ni dake mu daku …… Bariki tace ah zauna kawata Ina ni Ina fad’a da babbar kawata Allah ya baki hakuri hjj habiba ikon god….
Zama habib yayi yana fad’in ah toh in banda iskanci taya zaki dinga had’ani da maza har ki maza ya karasa maganan yana dariya
ltama bariki dariyan ta saki tare da fad’in nidai Wlh na k’osa Yarima ya turo ayi bikin mu Ina gama istabra’i …..
Habib yace yauwa Ina jinki kina ban labari …..
Bariki tace Hmmm nifa Wlh nace ina son ganin mutumin ne saboda muje tare da Yarima amma Yarima yayi min mummunan tunani, yana ganin inda bai dawo ba a tunaninshi zanje wajan mutumin ne …..
Habib yace Kema maiya kaiki?? Ni Wlh ba tun yau na Lura da wannan Yarima dinba akwai shegen kishi Wlh bariki naga kaman kina wasa, samun Yarima Aliyu ba karamin Sa’a bane, inko kika bari ya kubce miki Wlh kinyi Asara, Kut Aina sha fad’a miki inda ni yace yana So Wlh da yaga yanda ake soyayya amma keda yace yana So kina iskanci, namiji har namiji wlh Yarima ya had’u so handsome …….
Bariki tace uhm, waya ce ina wasa da Yarima?? Ni kam duniyar nan banga Wanda nakejin tsoro ba tare dajin tsoran yasan koni wacece ba sai Yarima Aliyu, Kinga kawata inda bana son Yarima yaushe zan damu yasan koni wacece?
Tabe baki habib yayi tare da fad’in ai gashi yanzu kina kokarin ki nuna mishi halin naki ke gindi babu control daga Kinji ance ana son ganinki kin yarda,Allah yasa ba fushi yayi ba shi yasa ya kashe wayoyin nashi ba. Bariki tace uhm….
Habib yace kyace uhm mana tunda kin shuka tsiya …… Ni tashi muje muyi rawa ko naji sanyi kwana biyu ban girgiza duwaiya ba …..
Bariki tace wa? Rufamin asiri Aini inka ganni a lahira kaini akayi haka kawai tsautsayi ya kaini Yarima yazo a’a Wlh bada niba wai ance da tsohuwa tayi zina ……
Shewa habib ya saki tare da fad’in kunji salo nidai Kinga tunda banda tsayayye balle in takura kaina nayi gaba dan yau sai na karkad’a kayan alatu
Bariki tace ….. Lah mota ta na barta a u/kanawa Wlh Yarima ne ya caza min Kai sai yanzu na tuna,
Habib yace tsiyary’an mazan nan kenan ai shi yasa ni naki yarda Nayi aure, suna auranka suna kaika ciki ka zama nama, shi yasa nake taka tsatsan dasu a waje… Ke gaki ko ciki baki shiga ba har an fara miki duk da Kece da laifl
Bariki tace uhm bari in kira ubana na Bariki ince a kulan min da motar ni saida ta zanyi ma gobe inna flta
Habib dariya Ya saki tare da fad’in ni sai naga kaman ma kina kama da mutumin Wlh ….. Bariki dariya tayi tare da fad’in amma Allah ya isa ……
Habib fita yayi yana fad‘in sai da safe zani wajan wasa
Yana flta bariki tasa ma kofarta key ta kwanta tare da kiran babanta na Bariki ta fad’a Mai ya kula da motar, sannan ta kara da fad’a Mai Yarima zaizo jibi dan neman izinin zance …..
Tace Bari koma dai miye gobe mayi magana in nazo Abba.
,,,,,
Driver din alh madu koda ya koma abunda bariki ta fad’a haka Ya fad’ama Mai gidan nasa,.
Alh madu dariya yayi tare da fad‘in yaro man kaza, yaro yaro ne yaro bai San wuta ba saiya taka, lallai Bariki har yau baki San Waye alh madu ba, amma naga kina son in fito in nuna
miki Waye ni dan naga kanki yana rawa very soon zanyi maganin ki, sannan Indai bani zaki aura ba sai dai mu zauna muci gaba da mu’amala yanda mukeyi, dan bazaki aura kowa ba inba niba.
D’aukan wayanshi yayi ya doka ma hjj babba kira, duk da yasan ba lallai bane ya d’auka domin tun dazu yake ta kira bai d’auka ba, harya kusa tsinkewa aka d‘auka ……hjj babba ya d’auka tare da fad’in Allah ya taimaki Sanata alh madu daka majalisan dattawa sai Villa insha Allah
Alh madu yace kana ina duk inda kake kazo yanzu sannan ina son kazo min da bariki kota wani hali kafarka kafarta yau nake bukatar ganinta cikin daren nan a guest house dina ……
Hjj babba yace an gama ranka ya dad’e yanzu zaka ganmu
Bayan alh madu ya kashe wayan, hjy babba yace Toh fah hala bariki ta kara Karta Mai rashin mutunci ne Bari inje d’akinta inji y’ar bura ubar itama har mota ya bata ita da bata iya cin arziki ba inda Tana mishi yanda yake so Aida tafl karfln abunda yafi wannan motar duk da tace baida kayan aiki abu kaman ayabar yara kona jarirai ne tace ma oho ni na manta ….. Gaba yayi tare da nufa d’akin bariki data fara bacci nocking yaita mata da
Tashi tayi tare da sakin tsaki tana fad’in Waye ne?? Muryan hjy babba taji yana fad’in nice bud’e kofar
Bariki tashi tayi ta nufi kofar tana murza ido, bud’e kofar tayi taga hjy babba dinne tace lafiya cikin wannan daren???
Hjj babba yace lafiya mana, ko 12 bai karasa ba kike cewa cikin wannan daren sai kace
nazo miki da karfe biyun dare, Kinga ni bama wannan ya kawo niba, nazo ne muje wajan alh madu dake yanzu ya kirani yace yana son ganinki dan Allah shirya muje ……
Bariki tace hjyta babu inda zani domin wlh ni aure zanyi kuma istabra‘i nakeyi dan so nake inyi tsarkakken aure …..
Yace gaskiya banji dad’in wannan maganan ba Wlh Ina ke ina wani aure yanda kike da kyau da lafiya ga kuruciya, gskya banji dad‘in jikina ba wai mahaukaciya taji duka …… Gaskiya bariki ki canza shawara ai yanzu ne kike da dama kuma shi komai na duniyar nan lokaci ne gwara kici naki lokacin daka baya kyayi auren in kin daina tashe amma haka kawai tsigai Wau kina tashe ki wani cuci kanki Muma ki cucemu dan abunda muke samu saboda ke mu daina samu, ki makale waje d’aya da Sunan kinyi aure gskya raina ya baci
Bariki tace hjyta nidai bacci nakeji yanzu wlh kuma shi nakeyi kika tasheni dan Allah hjyta ki bari in koma bacci
Hjj babba yace oh yau naga ikon Allah, amma dai wlh bariki kin canza kuma Nasan yanzu bakya d’aukan maganan kowa saina Shegiyar habiba Dan naga yanda take shige miki, karki manta Nina Fara saninki Kafin habiba kuma saboda ni kike nan gidan …..
Bariki tace hakane hjyta kena Fara sani Kafin habiba, and kuma kinmin hallaci Wanda bazan manta dake ba, shi yasa har gobe nake mutuntaki hjyta
Hjj babba yace bariki Indai kina ganin mutuncina kizo muje wajan alh madu ni koda bazaki yarda dashi ba, dan Allah kizo muje Yadai ga na kawo mishi ke domin yana ganin mutuncina ko so kike ya daina, sannan inma Kinje shida kika ce ayabar tashi kaman ta yara Aiko yayi ba komai za kiji ba…. Bariki tace nifa hjyta gskya babu inda zani domin na riga na yanke hukunci kuma na fad’a ma driver dinshi sa’ko ya bashi, wato shine daya fad’a Mai shine ya Aiko ki, Toh wannan karan zaisha mamaki domin babu inda zani kuma na fad’a
Hjj babba yace oh na shiga uku an fasa aurena haka gasau kike fad’a babu inda zaki??…. Amma kam in kikai haka baki hallaci ba bariki ki duba fah har kyautar mota yayi miki …… Bariki tace Aiba ro’kansa nayi ba shiya d’auka ya bani Dan haka kuma ta bayu,.
Hjj babba yace dan Allah bariki Kar kisa nidai ya daina ganin mutuncina ki daure kizo muje koda zaginshi za kiyi nidai yasan na kawo ki, sannan in Kinje kya fad’a mishi abunda ke ranki Kinga tayu ya barki ya nemi wata ……
Jin haka yasa bariki tace muje, inji uban Mai yasa ga mata Nan a gari wanda suka flni iya zuba bariki bai nema ba sai ni, muje inji dalili Danni Wlh na gaji da wannan iskancin nashi…. D’akin ta koma tasa hijab dogo har k’asa akan rigan baccinta tare da rufe d’akin tace ma hhj babba muje …….
Bakin titi suka nufa da yake garin yau ake wasa akwai mutane birjik samun Abun hawa bai musu wuya ba, inda suka sami Mai keke napep suka shiga, direct gidan alh madu ya kaisu hjy babba ya biya kud’in sukai nocking Mai gadi ya bud’e dan yasan hjy babba da bariki, kofar falon alh madu a bud’e yake dan haka suka shiga baya falo bariki bedroom dinshi tayi
taganshi tsirara yana video call daka gani da wata mace yake, alh madu waya yake bai Masan bariki ta shigo ba saida yaga hasken wayarta alaman an d‘aukeshi hoto …… Da sauri ya tashi yaga bariki ce murmushi ya saki tare da fad’in Kaga manyan mata maganin kanana, nufanta yayi tare da janyota jikinshi Wanda babu kaya yace Bari in d’auke mu kit kit ya fara d’aukansu a wayarshi bariki kokarin Jan jikinta ta farayi tare da fad’in miye haka ne Dallah sakeni, andaiji kunya wlh kaje can ka karata da sauran y’an iskan y’an matanka badai bariki ba womanizer kawai fuuuuuu ta flta ta barshi yana kiranta ganin ta fita yasa ya fara saka kaya da sauri dan ya cin mata dan yasan Indai ta zille Mai shida ya kuma ganinta sai anjijiki tunda yanzu tazo yau yake son sanin Mai take nufl domin ya shirya Mata kota yarda ta aureshi kota fasa maganan auren da take fad’in za tayi suci gaba da cinjuna babu aure, kuma yayi alwashin cikin biyu dole ta zabi d’aya …….
Alh madu riga kawai ya iya samu yasa ya fito…..
Bariki fuuuu ta flta hjj babba ya bita yana fad’in bariki Yadai Anya lafaya kuwa? Bariki bata kulashi ba taci gaba da taflya cikin sauri
Yace bariki Wai Mai ya faru koya mutu ne Alh madun ???
Bariki tace Aidama mutuwar yayi da nafi kowa murna dan iskan tsoho tsinanne ….. Hjj babba yace oh ni amma gaskiya bariki baki da hali …..
Hango Alh madu tayi yana nufosu da sauri ta fita daka gidan….
Hjj babba ya bita yana fad’in ta tsaya mana ga Alh madu dinnan ya fito yana kiranta….
Ko kallon hjy babba batayi ba ta wuce abunta tako yi Sa’a taga wani mai mashin da sauri ta tsayar dashi tahau, tana fad’a Mai inda zai kaita, mai mashin yace dubu d’aya bata musa ba dan itama tasan dare yayi ba kowa bane zai kaita maraban jos yanzu a mashin ba ……
Hjj babba wajan Alh madu ya koma wanda shima alh madu ya koma yasa wando ya flto …… Alh madu bayan ya flto ya kalli hjy babba yace tana lna?? Hjj babba yace aita wuce ta sami Mai mashin tahau.
Kai Alh madu ya d’aga alaman yaji tare da cema hjy babba ina zuwa, bedroom ya shiga sai gashi ya flto da bandir din dubu d’aya dubu d’ari kenan yaba ma hjj babba tare da fad’in kaje zan nemeka …..
Hjj babba amsa yayi yana ma alh madu godiya tare da fita ……..
Bariki ce kwance a d’aki tana ta kiran number din Yarima ya’ki d’auka Dan tsaki taja tare da fad’in bazan kara kira ba, in kaga dama ka kirani, sa wayar tayi a silent ta fad’a toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin watajallabiya yayi mata kyau ta yafa gyalen jallabiyan ta d’auki jakarta da wayanta ta danna ko zataga miss call din Yarima amma shuru babu ma wanda ya kirata, tsaki taja sannan ta fita cikin damuwa, had’uwa sukayi da hjy babba ……
Ja yayi da baya ya kama kugu kaman wanda zaiyi dambe, yace amma ke kam bariki akwai ri’kakkiyar y’ar iska, in banda iskanci da wulakanci ki k’ekashe ido kici min mutunci, Nina rasa mai yasa kika tsani wannan mutumin yana sonki kina gudunshi kaman Kinga kashi ……
Bariki tace haba hjyta wannan jaraban fah da tujara da sassafe? Hjj babba yace aike kika so wlh bariki baki da hali, gwara ki canza wannan ba’kin halin naki tun wuri ….. Yana fad’in haka yayi gaba yana ta surfa bala’i shi’a dole bariki ta bata mishi rai gwara yayi gaba karma ya tsaya bata ma kanshi lokaci wajan magana da ita …..
Bariki ganin haka ta girgiza kai tare dayin gaba tana fad’in kaji dashi wai anyi ma mai dami sata ….. Bama Alh madu ba babu wani namiji da zai kara sanin ko ita wacece domin ta tuba abunda ta aikata baya shima tana ro‘kan gafaran uban giji akan ya yafe mata duk da itama inta zauna wani zubin takanyi mamakin irin abunda ta zuba a matsayinta na y’a mace Mai shegen kunya a da, amma lokaci d’aya ta sauya Wanda har yanzu ta kasa gane dalili, sai dai wani zubin takan kalli abun a matsayin Tana son musguna ma iyayenta ne shi yasa take hakan, duk da shima hakan bawai ya tabbatar mata a rai bane kawai inta fad’i hakan ne take ganin hakan shine silan fad‘awanta wannan mummunan harkan …..
Bariki u/kanawa tayi inda ta d‘auki motar da Alh madu ya bata ta siyar wajan y‘an motocin dake u/kanawa ta wajan NDA, bata amshi kud’in cash ba transfer tasa suka mata, sannan ta wuce gidan iyayenta na bariki,
inda abbanta na Barikiya bata shawara akan ta dawo nan da zama domin d’an gidan sarauta zata aura Karta sami matsala dan inta sami matsala suma suna ciki tunda har dasu a cikin aikin …..
Bariki tace hakane nima nayi wannan tunanin amma tashi na daka can zaiba wasu dama su Fara bincike akan abunda nake shiryawa amma zan dinga kwana a nan camma ina kwana zan dinga diban kayana da kad’an Ina kawo su nan har lokacin bikin yayi a wuce wajan,
Ranan bariki a gidan ta wuni tana tajiran kiran yarima amma shuru babu kira babu sa’ko, gaba d’aya jikinta yayi sanyi ta kasa sukuni dan tsaki taja tare da kiran Layin Yarima taji line busy alaman yana waya ….. Ajiyan zuciya ta sauke tare da fad‘in kenan da nice bazaiyi waya ba Hmmmm, babu damuwa ai gobe kace zaka zo wajan Abba zan gani in zaka zo, dan nasan baka karya alkawari saida wani dalili …… Bariki wajan 6 tabar gidan ta koma maraban jos akan cewa gobe zata 20 da sassafe insha Allah dan Yarima tana tunanin zai
Bariki koda ta koma ta kasa sukuni gaba d’aya, domin rashinjin muryan Yarima ya sata cikin wani hali, sai yanzu ta kara tabbatar ma kanta tana son Yarima Sosai, kuma zata iya aikata komai akan sonshi Indai Abun bai sabama Shari’a ba duk da tasan wannan auran da zatayi da Yarima bai dace tayi ta wannan hanyar ba, toh amma yata iya tunda haka tata kaddaran tazo Mata, yanzu inta koma Gida AI Yarima zai gane karya ta shirya mishi tun Farko, wani hawaye ne mai zafi ya silalo mata tabbas duk Wanda yabarAllah …… Allah shima ya barshi …… Ta fad’a wannan halin ne duk saboda aikata sabon Allah, gashi Allah ya jarabceta da son Yarima wanda bata son ta rasashi, saboda son da take mishi yasa tana kokarin kara jefa kanta cikin wani bala’in ta tabbata koda Yarima Aliyu ta bashi Labarin ta ya hakura ya amsheta a matsayin mata, toh iyayenshi fah? Ya zasu d’auketa da sauri ta tashi tsaye domin bata taba tunanin iyayenshi a duk cikin wannan abunda take shiryawa ba, ya iyayen Yarima zasu d’auki abun, gidan sarauta gidan Kima da daraja, gidan da babu wasa a cikinsa, kuka ta fashe dashi Mai sauti lallai ina karajefa rayuwata cikin halaka ……. Kuka take Sosai tana surutai ya iyayen Yarima zasu d’auki wannan abun, na tabbata bazasu hakura ba su, sai Sun hukunta ni akan wannan laifin da nake shirin aikatawa, bariki gidan sarauta ne gidan su Yarima ba gidan wasa bane, irin wannan auren bai kamata kiyi shi a gidan sarauta ba, lallai sarauta ba wasa bace, sarauta ba karya bane, ido ta lumshe tunawa da yanda Yarima yakeyi kana kallonshi kasan akwai jinin sarauta a tare dashi Sosai yanda yake abu …… Lallai Indai Ina son Yarima ya kamata in fad’a mishi koni wacece …… Da sauri kuma ta Fara girgiza kai tunawa da tayi yana fushi da ita akan ance ana son ganinta, jiba
yanda ya nuna kishin shi akai inaga yaji tana bin maza kuka ta kuma saki na tabba bazaka aureni ba Yarima inma ka yarda Wlh iyayenka bazasu Bari ba, dan gidan sarauta baza’a Bari ya auri karuwa ba k’asa tayi tana kuka lokaci d’aya kanta ya fara mata wani irin azababban ciwon kai ga idonta daya kad‘e yayi ja, Kun San farar mace ba wuya, in tayi kuka a gane, kwanciya tayi a k’asa tana kuka, wayarta keta kara amma ta kasa tashi ta d’auka dan bata jin zata iya tashi domin yanda takejin kanta ………. Lallai rayuwar bariki ba komai bace face kaskanci da wulakanci Wanda ta tabbata bata ga komai ba sai ranan da Yarima yasan k0 ita
wacece…. Bugun kofar da ake mata ne yasa kanta yake ta kara mata ciwo dakyar taja jiki ta tashi ta bud’e …..
Habib yaja baya yana fad’in ya ilahi Mai zan gani haka??Bariki bakidalafiya ne? Maiya sameki?
Bariki kanta ta nuna mishi da hannunta alaman kanta na ciwo
Habib cikin tausayin bariki yace sannu Allah ya baki lfya, Yarima yazo yana jiranki har yaje ya nemi izini wajan mahaiflnki na Bariki, ……
Da sauri bariki tace dagaske? amma gobe yace zai zo
Habib yace Toh gashi yazo yau, shima Nasan yayi kewarki shi yasa yazo dan haka maza kizo muje yana Bayan layi yana jiranki, yace ya kira baki d’auka ba shine ya kirani, shima abbanki na Bariki yaita kira baki d’auka ba yana son fad’a miki wai baki dad’e da tafiya ba Yarima yazo yasa akai sallama dashi …..
Bariki da sauri tayi toilet ta wanke fuska sannan ta kara feshe jikinta da turare ta yafa gyalen jallabiyan data cire sannan ta fita, suka jera Ita da habib.
Har wajan da motocin Yarima suke suka nufa, yau yazo da fadawa motoci har biyar kaman yanda Ya saba zuwa da, tun daka nesa Yarima ya gane Zainab ce ke tawo wa, amma ganin kayan jikinta jallabiya sai yasa shijin kishi domin a ganinshi bai kamata tasa jallabiya ba duk da komai nata a rufe yake, ido ya lumshe tare da fad‘in yanzu Nasan haka aketa kallon mun ita,
Usman dake zaune kusa da Yarima yace Yadai naga kana ta Jan tsaki?? Yarima yace plz bamu waje zan kiraka ku gaisa inna Gama magana da ita ….. Usman dariya yayi sannan ya fita
Koda bariki ta karaso habib ya bud’e Mata motar sannan yajuya …..
Bariki shiga tayi idonta nakan Yarima shima idonshi na kanta, bayan ta shiga ta rufe motar……
A hankali Yarima ya furta my princess maiya sameki?? Mai yasa kikai kuka tell me plz mai yake damunki? Duk a tare ya jefo mata wannan tambayoyin ….. ldonshi na kanta yana jiran amsa daka gareta ……
Ganin irin kallon da yake mata yasa ta fashe da kuka Sosai….
Yarima cikin tashin hankali ya janyota jikinshi tare da rungume ta, yana sauke ajiyan zuciya tare da shafa mata baya, a hankali ya fara magana my princess plz stop it kin San bana son kukanki, plz tell me Mai yake damunki????
Tana manne ajikinshi ta Fara magana Yarima kasan ina Sonka bazan iyajuran rashin kaba koda na awa biyu bane, yau inata kiranka kaki d’auka,jiya na kira baka d’auka ba, na kara kira naji wayarka a kashe yau tunda safe naita kira kaki d’auka… Kuka taci gaba dayi lokaci d’aya kuma taci gaba da fad’in Yarima kasan ko kad‘an Ina tare dakai bazan kula wani ba, yakamata ka yarda dani ka yarda da irin son da nake maka, yarima dan Allah karka kara fushin da inna kiraka zaka ki d’aukan min waya, koda zaka d’auka ka zageni dan Allah ka d’auka rashin jinka yana sani cikin wani hali n …… Kuka ne yaci karflnta Sosai wanda yasa dole tayi shuru
Yarima kasa magana yayi sai bayanta da yake shafa mata,jin sautin kukan nata harcikin kanshi yasa ya d’ago ta tare da kallon fuskanta da ya baci da kuka Sosai, murmushi Yarima yayi tare da fad’in Kinga kina ta zubar min da hawayenki, my princess plz ki daina i trust you shi yasa na dawo gareki and naje na sami Abba ya yarda ya bani izinin zuwa zance har mu fahimci juna manya su shiga, ya kuma nunamin yaji dad’i yanda na Fara neman izini sabanin mazan yanzu basa haka, yace ya yaba dani ya yarda da irin tarbiya na, duk da na fito gidan sarauta ban nuna iko ko sarauta ba wajan zuwa wajanshi, my princess Abba mutumin kirki ne, lallai na yarda iyayenki Sun baki tarbiya domin Abba yayi min magana na dattaku ……. My princess I really love you, Ina miki son da nida kaina ina mamaki,jiya nayi fushi dake amma gaba d’aya na kasa sukuni, saida nazo na ganki na samu nutsuwa…… Ganin ta lumshe ido yasa ya kura ma fuskanta ido,ji yake kaman ya tafi da ita, yana Mata son da bai taba tunanin Zaima kowa irinshi shiba, “
Hura mata iska yayi a fuska wanda yasa ta bud’e ido da sauri idonsu ya had’e suka fara kallonjuna, cikin ido gaba d’ayansu wani irin son junansu sukeji, Sun d’auki lokaci suna kallonjuna Kafin bariki tayi k’asa da kanta dan bazata iya juran ci gaba da kallonshi cikin ido haka ba, wannan dinma da tayi tana mamaki, ta rasa mai yasa Yarima ya banbanta da sauran maza, yana Mata wani irin kwarjini da bataji akan sauran mazan da tayi hulda Dasu
Katse mata tunani Yarima yayi tare da fad’in daka ina habib ya kiraki Ina kika je?
cikin sanyin murya tace ina gidan wata kawar innata ce, naje amso maganin ciwon kai na Hausa, Ina can habib yazo, nama barwayata a gida tana caji …..
Yarima yace ok but yaushe zaki koma Gida? I dnt knw why bana son wannan anguwar domin mutanan da nake gani a cikinta, plz ban son kina yawan zuwa my princess ya karasa maganan cikin damuwa….
Tace Yarima Karka manta y’an uwana suna nan
Yace eh I know, bawai nace ki daina zuwa bane, kawai Ina so ki rage zuwa ne plz, and my princess plz ki daina irin wannan dressing din, sai a gida na, ki dinga sa hijab dinki inso samu nema harda nikaf plz banso kowa yana ganinki
Bariki murmushi tayi tare da fad’inYarima wannan jallabiya ce babu komai ai dan nasa, shima kaman hijab ne …..
Yarima yace, Nop akwai banbanci nidai bana so ana sawa, Kinga yanda yayi miki kyau kuwa? Only god knows maza nawa kika burge da kika flto…. Shi yasa tunda yau naga Abba
Yaban izini very soon za’a turo ayi bikin kowa ya huta in kika zama tawa sai inga Wanda zai kara cewa yana son ganinki …….
Hmmmm