BARIKI NA FITO CHAPTER 33
BARIKI NA FITO
CHAPTER 33
Bariki dariya tayi, tana mamakin irin kishin Yarima Aliyu, gashi baya iya boye kishin shi, dole saiya fito dashi ……
Katse mata tunani yayi da fad’in dariya koh??
Tace a’a Yarima kawai naga kana tunanin daba haka bane …..
Yace miye ba haka bane? Tell me, tunda kika flto zaki cemin maza basu kalleki ba?? Tace Yarima yanzu fah dare ne Waye zai kalleni? lnba Kai ba.
Murmushi yayi tare da girgiza kai yace my princess your too much kin iya Kare kanki ….. Anyway yaushe kike son Ayi bikin mu?? Domin Idan Mai martaba ya turo lokaci kad’an za’a Sa
Bariki rufe fuskanta tayi cikinjin kunya tace Yarima ‘BANDA ZABI‘ sai abunda su Abba
Yarima Aliyu yace hakane but Nasan Kema kina da lokacin da kike so ayi in muka shirya basai mu fad’a ba!?
Tace hakane Yarima yace ni k0 yanzu aka bani zan taf’l dake …..
Ido ta zaro lokaci d’aya kuma ta saki dariya Sosai, tace Yarima ni nafi son yakai Nanda shekara d’aya …..
Da sauri Yarima yace what?? Amma dai you are joking koh? Ni bamma tunanin yakai nan da wata d’aya….
Bariki tace Yarima watsa d’aya yayi wuri, ni Ina tunanin nan da wata uku…. Yarima yace hakan yayi miki???
Kai ta d’aga alaman eh, domin Kafln nan ta Gama istabra’i sannan zata samu lokacin gyara kanta Sosai duk da tasan komai tayi bazata dawo budurwa ba, amma zata gwada duk wani kayan gyaran jiki danta d’an gyara kanta …..
Katse mata tunani yayi da fad’in gobe ki koma Gida Zanzo in ganki a can da rana insha Allah,
Tace Yarima gobe kuma? Yace yes ko you don’t want to see me ne?
Da sauri tace a’a kawai naga kullum sai kazo, baka zama ga amarya a gida, inaga ya kamata ka zauna ka bata hakkinta, da lokacinka
Yarima yace ok hakane, zan zauna bazan zoba har sai kin nemeni, sannan ita amarya Ai tare muke kwana da ita …..
Ganin yanda ta canza fuska yasa yayi murmushi danya Lura taji haushin magananshi ne …..
Kamo hannunta yayi tare da matse su duka biyun, yace my princess I love you so much, plz ki dinga kulan min da kanki Sosai…
Kallonshi tayi ganin shima ita yake kallo yasa tayi k’asa da kanta, cikin sanyin murya tace Yarima ……. Shuru kuma tayi tanajin nauyin abunda zata fad’a …..
Yarima Aliyu yace inajinki my princess …..
Hawaye ne ya zubo mata Mai zafl da sauri tayi k’asa da kanta dan karya gane tunda hannunta na nashi hannun ….. Cikin rawan murya tace Yarima Idan ka aureni kaji ba yanda
kake expecting ba zaka iya saki na???? Yace ban fahimta ba?? Mai kike nufl?
Tace Yarima lna nufln Bayan auren mu kaji ba yanda nake ba I mean ….. Shuru kuma tayi lokaci d’aya tasa kuka mai sauti ……..
Yarima ido ya kura mata cikin rud’ani …… Tare da tunanin mai take son fad’a mishi haka???? Ganin kukan nata na k’aruwa yasa ya fara share mata hawaye cikin tausayinta ……. Ya fara
magana kamar haka Zainab Ina son ki fad’amin abunda yake damunki ko miye I will accept you a yanda kike, ina miki so dani kaina ban taba tunanin zanyi ma d’iya mace irin wannan Son ba, tell me maike damunki???? Kasa magana tayi sai kuka da take ta faman saki cikin tashin hankali da damuwa,….
Yarima kam ido ya kura mata ganin taki magana sai kuka,… Yace Zainab kodai kina pretending ne bakya so na …….
Da sauri tace a’ah Yarima Ina Sonka, kaine rayuwa na, Ina maka son da baki bazai iya fad’anshi ba, sonda nake maka shi yasa nake tsoran fad’a maka abunda nake son fad‘ama a halin yanzu saboda ban San yanda zaka d’auki abun ba ……
Katseta yayi tare da fad’in Zainab tell me?? Fad’amin Mai yake faruwa?? ……plz Zainab tell me abunda yake damunki kin sani cikin damuwa ……
Kuka take Sosai lokaci d’aya ta fad’ajikinshi ba komai take son fad’a mishi ba sai rayuwarta wanda tsoro da fargaban abunda zai biyo baya yasa ta kasa fad’a mishi sai kuka tare da nadama
Yarima tunda ta fad‘ajikinshi ya kasa furta koda kalma d’aya ne sai Shafa mata baya da yakeyi tare da tunani Kala Kala akan Mai take son fad’a mishi?? Lallai akwai wani abu mai
muhimmanci daya danganci rayuwarta da take fargaban fad’a mishi, to miye abun???
need to knw, tunanin baya ya farayi tasha son fad’a mishl magana amma saita kasa, lallai
akwai wani abu a tare da ita toh miye wannan abun?? I have to find out ……..
D’agota yayi tare da fad’in Zainab kukan ya isa haka, what I want you to knw is dat Ina sonki I can’t live without you …… Zainab tun a mafarki Allah ya had’ani dake har na had’u dake a zahiri, ina son ki sani had’uwa na dake had‘in Allah ne, na Fara sonki tun Kafln inga Fuskanki, ina son ki sani bawai saboda kyanki ko wani abu nake sonki ba a’a kamalanki da mutunci da yanda kike suturta jikinki yasa na kara sonki koda na had’u dake …… So Zainab don’t be afraid to tell me what in ur mind ….. Zainab Abu d’aya zaki aikata in barki duk irin sonda nake miki domin bazan iya juraba dan Indai zan ganki Abun zan dinga tunawa shine ‘ZINA‘ duk da Nasan rasaki a rayuwa ta kaman baraza na ne a tare da rayuwa na, bana tunanin koda a mafarki Zaki iya aikata hakan, ina matukar kishinki Sosai harta habib da kike mu’amala dashi hakuri nakeyi badan ina so ba, tunda kince kaman dan uwanku ne,
ban son inga wani abu yazo inda kike lnba niba …….. ldo ya kura mata tare da fad’in tell me Bariki jikinta yayi matukar sanyi Sosai lallai Yarima in yasan wacece ita ya barta har abada ….. Tsayawa tayi da kukan amma hawaye na zuban Mata a ido Sosai amma yata iya tata kaddaran kenan dole ta fad’a mishi gaskiya domin hakan shine zai sa ta sami salama duk da itama ba zata iyajuran rashin Yarima Aliyu a rayuwarta ba, domin so ya mata shigar
sauri sonshi ya shigeta Sosai wanda bata san lokacin da hakan ya faru ba …….
Katse mata tunani yayi tare da fad’in Zainab tell me plz….
Shuru tayi tana kokarin yin magana amma ta kasa domin muryanta ya dashe …… Ganin haka yasa Yarima fad’in kiyi shuru kibar wannan kukan plz Kinji my princess?
Kaita d’aga mishi alaman toh
Yarima Aliyu idonshi na kanta ya tabbata akwai abunda take boye Mai, but koma miye zai
sani ….. Ganin tasa hannu a kanta alaman yana mata ciwo yasa yace my princess ciwo Kai din yake miki?
Kaita kara d’aga Mai alaman eh , bud’e kofar motar yayi ya shiga wajan driver ya kunna motar,
Da sauri ta d’ago ta kalleshi ganin yaja motar yasa ta kura mishi ido, taga Ina zashi da ita …… Karan wayanshi ne yasa ta dawo daka duniyar tunanin data fad’a
D’auka yayi tare da fad’in USMAN sorry yanzu zamu dawo, zan kaita pharmacy ne a bata magani she has a headache ….. Yana fad’in haka ya kashe tare da fad’in Ameen Yarima cikin gari suka shiga inda aka bama Zainab magani, tare da sai mata kayan fruit sannan suka kamo hanya, bayan sun karaso Bariki suka gaisa da USMAN sannan Yarima yayi mata sallama akan taje tasha magani, ta kwanta ta huta sai sunyi waya ……
Bariki gidanta take ta koma ta shiga d’akinta ta kwanta bayan tasha magani bata dad’e ba bacci yayi awon gaba da ita
Usman tun a mota yake tsokanan Yarima Aliyu, akan dole ya mutu akanta yarinyar tana da
kyau sai dai karama ce ba wata babba bace ……
Yarima dai banza da USMAN yayi domin haushin yanda yake ta fad’in Tana da kyau yakeyi,
d’an tsaki yayi cikin ranshi yace bazan kara zuwa dashi ba, tunda Kalle min Mata yake tayi…
Yarima bayan sun koma direct gefenshi ya nufa inda yayi bedroom dinshi yayi wanka, yana cikin sa jallabiya danya kwanta
Gimbiya zinatu ta shigo d’akin tare da fad’in Yarima ….. Yace ya akayi…. Tace ina son magana dakai
Baice mata komai ba sai zama da yayi akan gadon d’akin tare da d’aukan wayarshi yana dannawa …..
Kollonshi tayi cikinjin haushin rashin kulata din da baiyi ba, tace haba Yarima wai mai yasa kake haka, yau kwana na uku a gidan nan a matsayin matarka, amma baka da lokaci na, kullum inka flta sai dare, karka manta wannan baya d’aya daka cikin abunda miji ya kamata yayi ma amaryanshi, duk wani ango zama yakeyi a gida in yayi aure ya dinga kula da matarshi, yau koda bazawara ka aura ai kayi d’auki balle ni budurwa…. Yarima Aliyu kallonta yayi tare da d’an sakin murmushi yace d’auki?? Akan me? Bayan har
yanzu ban San maina aura ba …… Cikin faduwan gaba tace kaman ya Yarima ban gane ba
Idonshi na kanta domin yana son yaga yanda zatai reaction amma ga mamakinshi sai yaga batai yanda yake zato ba, kenan gimbiya budurwa ya sameta dagaske, inko hakane ya kamata ya dinga bata hakkinta duk da bawai yana jin Sonta bane a ranshi, amma tunda ta kawo budurcinta sai yaji tayi girma a idonshi, duk da Abun ya bashi mamaki, dan baiyi zaton haka dinba ……
Jin kukan gimbiya zinatu shiya sa yarima ya dawo daka duniyar tunanin da yake …… Ganin yanda take kuka yasa zuciyar Yarima tayi karaya tare da tausayinta , tashi yayi ya ka mota ya kwantar da ita akan jikinshi yana fad’in plz ki daina wannan kukan …..
Cikin kuka take fad’in haba Yarima dole inyi kuka, yanzu Yarima ace Ina amarya amma kullum saika fita, kuma inka ma fitan sai dare, her an fara magana akai na, ana fad‘in baka
d’auki na , kasan gidan sarauta akwai ya’da magana haba Yarima mai yasa baka sona?
Maina yasa …… Hannunshi yasa akan bakinta yace ya isa haka, Ganin kaman Yarima ya tausaya mata yasa taita Mai juyejuye a jiki,
Nan sha’awa ta motso ma Yarima Kafln ace Mai har an fara harka …….
Alh madu ne shida hjy babba kallon hjy babba alh madu yayi yace abunda yasa na kiraka dagaske ne bariki zatai aure ko wasa takeyi??
Hjj babba yace haka tace kuma ina ganin kaman dagaske take, dan naga gskya yanzu bata bin maza, inma tanayi Toh a boye takeyi….
Murmushi Alh madu yayi tare da fad’in ok, ina son kayi min bincike akan wa zata aura sannan a ina yake, ina nufln Ina dai son sanin Waye shi da kuma sanin daga inda ya fito …..
Hjj babba yace an gama ranka ya dad’e Kud’i alh madu yaba hjy babba, sannan ya tafi
Alh madu yace bariki Nasan bana gamsar dake, amma ni kina gamsar dani, inko dai bani zaki aura ba, shima wanda yake son canza ki dole ya rasa ki,inko na bari kinyi aure toh sai dai in zaki amince ko kinyi aure kici gaba da bina murmushi ya saki tare da fad’in zan nuna miki ni Alh madu ba’amin wargi ………