BARIKI NA FITO CHAPTER 34

BARIKI NA FITO
CHAPTER 34
Bariki bata farka ba sai da asuba,jin kiraye kirayen sallah shine yasa ta farka, kuma bata tashi da ciwon kai dinba, tashi tayi ta fad’a toilet, alwala tayi tazo tayi sallah, tare da ro’kan Allah akan ya shiga lamarinta …… Koda ta idar kasa komawa bacci tayi sai kayanta na sawa data fara sawa cikin karamin akwatinta domin zuwa wajan iyayenta na bariki danta d’an Fara kwana a can, gashi yarima yace ta koma yau dinma. 
Bayan ta d’iba kayanta na kwana biyartasa cikin akwati ta rufe tare da ajiye akwatin a gefe, kwanciya ta koma amma ta kasa bacci domin ba komai take ba sai tunani, a duk lokacin da taso ta fad’ama Yarima gaskiya saita kasa, sai kuka yazo mata in tayi kokarin ta daure ta fad’a mishi saiya kashe mata Giwa da fad’in bazai auri mazinaciya ba… Wani hawaye ne ya zubo mata Mai zafi, Tana son Yarima bata son rasa shi, lallai Indai tana son samun Yarima a matsayin miji shine ta boye mishi labarinta har abada ….. Da sauri ta girgiza kai tare da fad’in labari na bazai taba boyuwa ba domin komin daran dad’ewa sai gaskiya ya fito, lallai fad’ama Yarima gaskiya shine mafita amma sai bayan na aureshi, zanyi kokarin in fad’a mishi gaskiya ranan daya aureni Nasan May be yayi min uzuri, tunda ba haka nake ba, kaddara ce ta 
fad’amin wanda nida kaina bazan iya cewa ga 
abunda ya faru ba, koda za’a samun wuka a wuya ban San yanda Abun ya faru ba …… ****** 
Haulat ce takejan akwatinta daga gani tafiya za tayi…. 
Hjj habiba tana bayanta tana fad’in yanzu sai yaushe kuma? Haulat tace mum sai dai munyi waya, kawai 
Farhan ne ya fito tare da fad’in muje in kaiki train station ….. 
Hjj habiba tace farhan ka Bari driver ya kaita mana, Yace no mum Bari in sauketa 
Babu yanda hjy habiba ta iya, dole farhan da haulat suka fita. 
Haulat na gaba farhan na mazaunin driver, ta kalli farhan tace plz mu biya ta gidan hjj Umaima zan amsa sa’ko ……. 
Farhan yace 0k, amma zaki missing train din 8, sai na 10 zaki hau, Tace babu damuwa Juya motar yayi sukai gidan hjj Umaima, haulat ce kad’ai ta shiga ….. Ta d’an jima Sosai ban San mai suka tattauna ba sai gata ta fito ta shiga motarta kalli farhan tana y’ar murmushi wanda shima din ita yake kallo tace muje ….. 
Mai makon suje din saiya kama hannun Haulat yana fad’in haulat dagaske aure za kiyi???? Tace aure kuma? A’a 
D’an shuru yayi yana nazari, toh tace a’a Bayan mum dinshi tace aure za’a Mata ….. 
Katse Mai tunani haulat tayi da fad’in, farhan zanyi aure Indai na samu Mai sona kuma wanda nake so, da an taba son had’ani da wani Wanda bana so ….. Wanda shine silan 
fad’awa ta cikin k …… Da sauri tayi shuru domin taso tayi baran barama. 
Farhan yace inaji haulat Tace andai fasa auren nawa Wani irin ajiyan zuciya farhan ya sauke, tare da kallonta cikin idonta yace haulat zaki aureni??? 
Da sauri ta kura Mai ido, tare dajin bugun zuciya, lallai farhan ya had’u ba tun yau take sonshi ba, tunda ta Fara ganinshi, domin yanda yake nuna mata kulawa, wanda ko wace mace tana son taga ana nuna mata caring ….. Sau da yawa rashin nuna halin ko in kula da maza suke nuna ma matansu suke sa su Fara neman mata y’an uwansu, misali namiji ya fita office, ko kasuwa, kodai wajan da yake Sana’a, bazai kiraki ba, may be in kin kirashi bazai d’auka ba, namiji inya auri mace babu kalaman love duk sai ya daina, in baki da lafiya babu sannu koya jiki, inya biya kud’in magani shikenan, maza kuma kuna da laifi Sosai wajan fadawan wasu matan h mace tana son Mai kula da ita Sosai, yau koda auren dole akama mace bata son miji….. Indai yana kyautata mata wlh sai kuga ta Fara sonshi ….. Amma kai miji babu kyautatawa daga tayi abu sai hantara …… ldan tana da k’awa taga tana kyautata mata in bata da lafiya, bini bini ta kirata tana yajiki kaza da kaza, in kawar Tana bin mata haka zatai tajanta ajiki in aka samu Mai raunin imani ganin yanda kawar tata take mata inta fito mata da kudirinta saita yarda ta amince Mata …… wlh maza kuma kuna da laifi Sosai, damme bazaka dunga nuna ma matarka soyayya da kulawa ba,bayan aure shikenan daka anyi aure sai a fara d’aure fuska haba haba maza ya kuke haka, sannan saika gama d’aure fuska in dare yayi ka lallabo kana Kai hannu ko kunya babu O …….. 
Farhan ne ya Katse ma haulat tunani da fad’in…. Haulat why r you silent and stare at me lyk this???? Murmushi tayi tare da fad‘in nothing, kawai Ina mamakin abunda kace ne …… 
Farhan yace mamaki kuma? Kodai bazan samu karbuwa bane? Haulat tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki, Wlh haulat so nake na aureki inhar kin amince Kece mace ta farko dana Faraji ina burin in aura ……. 
Haulat wani irin murmushi ta saki tare da fad’in farhan zanyi tunani akai, yanzu dai muje train station Kar in makara ….. 
Tada motar yayi suka wuce kabuwa station, koda sukaje saida suka zauna bayan yasai mata ticket, zama sukayi suna jiran lokaci, 
Haulat ba komai take tunani ba, sai abunda suke aikatawa da hjy habiba, Uwar farhan gashi d’anta yau yace yana Sonta, in kuma tace bata son farhan tayi karya, tashin hankali uwa da d’a ……. ldo ta lumshe tare da fad’in Anya wannan abun zaiyi kuwa? Maganan farhan bai kamata in daukeshi da muhimmanci ba, domin ba Abu bane mai yihuwa naga tsiraicin mum dinshi na cita ….. Yanzu kuma sai kawai inzo in auri d’anta Kai no way ……. 
Farhan ne ya Katseta tare da fad’in when zaki dawo? Koni inzo kaduna? Dariya tayi tare da fad‘in mudai yi waya kawai ….. Dai dai lokacin aka fara fad’in su tashi 
train yazo ….. Tashi haulat tayi tana kallon farhan tare da fad’in sai munyi waya Kai ya d’aga alaman ok tare da bata Wani karamin Leda daya ciro cikin aljihun shi, 
Amsa tayi tana fad’in ngd tare da tafiya ….. Koda haulat ta shiga jirgi tunanin farhan tai tayi wanda ta rasa dalili …….. Bud’e ledan daya bata tayi taga wani kwali karami anyi raping dinshi bud’ewa tayi taga wani zoban zinari Mai shegen kyau, bata san lokacin data saki murmushi ba …….. 
,,,,,,,,,,,
Yarima Aliyu ne zaune gaban iyayenshi yana mi’ka musu gaisuwa, mai martaba yace yaushe zaka Fara aiki a asibitin ka? Yarima Aliyu yace Abba duk sanda ka bani umarni Niko yau zan iya Fara aiki…. 
Mai martaba yayi murmushi domin duk cikin yaranshi babu wanda yake so kaman Aliyu bawai dan yana d’a namiji ba kawai, a’ah harda irin biyayyan da yake mishi… Mai martaba yace saika shirya cikin satin nan ka Fara sannan akwai wani fili da nake dashi a u/sarki saika Fara ginawa tunda a can zaka Fara aiki, Nasan wata rana iyalanka zasu bika can din in 
aiki yayi yawa ……. 
Mum din Yarima tace Kai Masha Allah, ina taya Yarima godiya Mai martaba murmushi yayi tare da fad’in kin ara bakinshi kenan kinci Mai Albasa Yarima yace Abba na gode Sosai Allah ya kara girma, Allah ya biya da gidan Aljanna 
Mai martaba ya amsa da Ameen tare da fad’in waziri zai baka takardun fllin sannan zai nuna maka filin, Mum dinshi tace sai ka Fara ginin mata biyu koh? 
Yarima kasa magana yayi, sai mai martaba da yace ginin mata biyu kuma? Aure yace miki zai K’ara?….. 
Mum tace eh gashi nan ya fad’a maka da bakinshi…. 
Mai martaba ya kalli Yarima Aliyu tare da fad’in ina jinka?? Yarima ya fara magana da fad’in Abba dama dama akwai dama…. 
Murmushi mai martaba yayi tare da fad’in dama me? Gaba d’aya ka kasa magana, mai martaba yaci gaba da fad’in Aliyu inaso ka sani bazan hanaka k’arin aure ba, amma sai dai Ina Mai baka shawara kayi hakuri nan gaba domin baka dad’e dayin aure ba ko sati d’aya bakayi dayin aure ba, inaso kayi hakuri nan gaba kad’an sai a taso da maganan auren da kake son yi, amma fah shawara ce ba umarni ba ….. 
Yarima Aliyu yace Abba umarni ko shawara duk abunda kace min a matsayin umarni yake a wajena…. Abba kayi hakuri a kullum nafl son kaban umarni domin Ina Mai biyayya ga duk wani abunda kacemin 
Mai martaba yace Allah yayi maka albarka, kaima Allah ya baka masu yi maka biyayya Yarima ya amsa da Ameen Abba, 
Mai martaba yace yarinyar y’ar inace???? 
Yace Abba a cikin kaduna suke, a u/kanawa ,sannan Abba mahaifinta bamai karfi bane… Mai martaba yace babu damuwa, ya tarbiyan gidan yake?? 
Yace Abba Alhmdlh gidan akwai tarbiya domin yarinyaryar  kwana hud’u da suka wuce ta sauke AL’QUR’ANI Mai girma kuma hadda…. Mai martaba yace Alhmdlh, lallai gidan akwai tarbiya, Allah yasa na tsoran Allah ne sannan duk Wanda yake da ilimin addini yaji dad’in duniya da lahira zai iya zama da kowa, dukiya ko mukami bashi bane Abun dubawa tarbiya itace Abun dubawa, kaje zansa Ayi bincike 
akan gidansu …… 
Yarima tashi yayi yana mai yima mahaifin nashi godiya sannan ya fita cikin murna yana K’ara godema Allah da har mahaifinshi ya yarda yanzu tunda Mai martaba ya amince toh ya Gama samun Zainab insha Allah, lallai Allah Abun godiya bai taba tunanin zai samu amincewan mahaifin nashi cikin sauri haka ba …… Gefenshi ya nufa , koda ya shiga rufewa yayi tare da nufa bedroom dinshi ya fara kallon hotunan Zainab din, Wanda ya zana, tunani ya farayi Mai Zainab take son fad’a mishi wanda take tsoron fad’a??? Kodai in tambayi habib?? Nop bai kamata ba ita ya kamata ta fad’amin koma miye, and  d way yanda take kuka yana nunamin abunda take son fad’a Kaman ya shafi rayuwanta? Toh mai take son fad’amin ido ya lumshe yana tunani ….. Na farko dai bata da wani aibu balle yace ga abunda take kokarin fad’amai, to Mai Zainab take boyemai??……. Kai ban tunanin abun serious ne inda serious ne data fad’amin._.. Wata zuciyartace mishi kaika sani ko nauyin Abunne yasa ta kasa fad’ama? And kuma Inba serious bane mai yasa take kuka haka in tayi kokarin fad’a Mai? Ganin duk iya tunanin da yayi ya kasa gano komai yasa ya cire abun a ranshi tare da fad’in koma miye Indai Mai muhimmanci ne zai sani, yanzu dai ya kamata in mata surprise inje in ganta…. 
Bariki na kwance taji ana mata nocking, tashi tayi ta bud’e kofar da sauri ta saki kara tare da rungume haulat Tana fad’in mutanan abuja sai yau, ko waya babu ….. 
Dariya haulat tayi tare da fad’in kiyi hakuri bariki Wlh wayata ce ta fad’i bani da number d’inki yanzu, sai yasa ina dira kaduna Wajanki na fara zuwa Kinga ko d’akina banje na ajiye akwati ba nazo Wajanki ….. Bariki tace shigo mana 
Haulat shiga tayi tare da zama tana fad’in Kai nasha abuja Bariki tace gashi kin kara kyau da k’iba kaman bake ba, kai zama waje d’aya yayi Murmushi Haulat tayi tare da fad’in dan bani wayarki in tura hotuna na tare da number 
d’inki, banda pic dina dake ko d’aya a phone dina Bariki mi’ka mata wayar tayi tare da fad’in yunwa nakeji wlh Bari in duba habib 
Haulat tace ok, haulat ta d’auki abunda take so cikin wayar bariki, sannan tayi murna da abunda ta samu a game da bariki din …… 
Bariki bata dad’e Sosai ba ta dawo, cikin d’akin tare da fad‘in habib ya cika yawo kaman yaci kafan Kare…. D’aukan iPhone dinta tayi ta Fara kiran habib harya tsinke bai d’auka 
Haulat tace ashe kinyi iPhone ga Samsung ga iPhone gskiya bariki kinajin dad’i…. Tashi haulat tayi tare da mi’ka ma bariki wayarta Tana fad’in Bari inje inyi wanka in huta anjima 
nazo Bariki tace ok but nima zanyi tafiya sai dai munyi waya Haulat tace ok tana murmushi ta fita Bariki ganin data dinta a bud’e yasa ta shiga whatsapp da message keta faman shigowa ganin Alh madu ya mata message yasa ta bud’e nashi ganin hotunan daya d’aukesu tayi, tsaki taja tare da shiga gallery ta goge dan in an turo Mata hoto shida kanshi yake bud’ewa bata rufe ba, harda na Hon salis duk ta goge su Wanda ya tura mata kwanaki, duk wani hoto data d’auka wanda bai dace ba ta goge a cikin wayarta …… Kiran Alh madu ne ya shigo cikin wayarta kaman Karta d’auka saita tuna da hotunan daya turo Mata Wanda hakan ya tabbatar mata yana son Mata wani tuggu sai yasa ta d’auka tare da fad’in lafiya? Dariya yayi tare da fad’in hotunan sun d’auku da kyau koh? 
Tace tir da hali irin naka 
Yace na baki awa biyu kizo inda nake ko yanzu ki ganki a internet ansa hotunan da mukayi kuma da fuskan wani ba nawa ba danna biya kud‘i anyi min aikin , babu wanda zai gane an canza fuskan domin kwararru sukamin aikin kuma ba y’an kasar nan bane 
Bariki k’asa tayi tana hawaye wayar ta sulale a hannunta 
Kuka take Sosai tare da nadaman fadawarta bariki, wanda Ita da kanta tana mamakin yanda harta fad’a wannan mummunan harkan, yanzu kenan kowa zai iyayi mata barazana kenan? Duk yanda taso ta kimtsa kanta sai an gwadayi mata barazana? …… Share hawayenta tayi lokaci d’aya ta saki murmushi tare da shiga tallet tayi wanka tasa dogon wando da hijab, sannan ta d’auki akwatinta ta flta, u/kanawa ta Fara zuwa ta ajiye, bata sami abbanta na Bariki ba Sai ummanta na banki dan haka tace mata bari taje ta dawo. Bariki direct gidan Alh madu ta nufa, bayan ta karasa ta sallami mai keke sannan ta shiga cikin gidan Kai tsaye…. 
A falo taga Alh madu 
Ganin bariki ta shigo yasa ya tashi yana fad’in dama Nasan zaki zo, nasan dole kizo ….. Bariki ta dakatar dashi tare da fad’in Zanzo for sure, gani nazo Mai kake bukata?? Yace ke nake bukata tare da d’aga mata gira. 
Bariki tace ni kake bukata??…. Wani irin dariya ta saki lokaci d’aya kuma ta gimtse fuska tare da fad’in amma wasa kakeyi koh?? Ina tunanin ka manta wacece bariki shi yasa kake kokarin Sani abunda Banyi niya ba…. Kasan Mai yasa nazo???…. Kai a tunaninka saboda ina tsoran ka tura hotona a internet yasa nazo? Never…. Karka manta bariki ake kirana miye danka watsa hotona a internet?? Miye a Ciki? Kai a tunaninka dan kasa hotona a internet zanji wani abu?? Dariya ta saki tare da fad’ln u r wrong duk yarinyar data baro gidan iyayenta ta flto tana zaman kanta kai a tunaninka dan kasa hotanta da namiji tsirara zata damu??? Aini ldan kasa aka watsa a internet plz kasa a had’a da number dua May be in sami Mai babban ayaba ba irin naka ba na Wasan yara, SANATA ALH MADU ….. kana son buga wasa dani tunda ka Fara sai mun buga ….. Karka manta bariki ba y’ar Siyasa bace, bariki ba Sanata bace bariki bamai mukami bace ….. Face karuwa Mai zaman kanta wacce take aikata komai dan ta sami duniya ….. Yau Idan ka d’aura hotona a internet koda ace nice banda kaya a jlklna suna zaka samamin zaka sa in sami yawan masoya masu son sex dani, Kaga may be Turai ma su kirani susa inyi blue film a Biyani ….. But amma abunda nake 
tsoro shine inkai ka rasa kujeranka na Sanata …….. 
Da sauri yace enough don‘t you dare say something like that in your life again in front of Me
Dariya tayi tace why?? I thought mulkin farar hula muke kowa Nada y‘anci koka manta ne??? Ba nazo wani dogon surutu bane ko turanci ba ….. Am hare to warning you, ka fita harka na ,nasha k0 d’an Siyasa kaman distinguish senator yana da tunani da basira, ashe ba haka bane ….. 0h na tuna abun ya had’e da tsufa dariya ta saki mai sauti sannan tace ga kuma son duniya…. Wlh harna tausaya ma al’umar da kake wakilta basu San tsohon banza 
suka tura …… Tas ya wanke fuskanta da Mari tare da Jefata kan kujeran falon 
Bariki tace u slap me?? Kara mata wani Marin yayi…. Yazo zai kara mata wani tayi wuf ta ri‘ke hannun amma karfln mace dana miji ba d’aya ba ya kwace hannunshi tare daja mata hannu yayi bedroom dinshi da ita, yana shiga ya Jefata kan gadon d’akin ….. Sannan ya kalleta yana wani huci kaman wanda yayi aikin karfi ….. Yace zan nuna miki ni tsohon banza ne, zan ajiyeki a nan har karshen rayuwarki inyi ta cinki sai dai ki mutu y’ar iska 
Dariyan da bariki ta saki ne, shine yasa ya kura mata ido, tace amma kayi hauka koh?? Ina tunanin Bayan tsufa da toshewan basira ka Fara tabuwa, Bari kaji Kafin inzo inda kake saida na shirya ma, ka d’auka haka kawai Zanzo ba tare da wani shiri ba???? Toh inma haka kake tunani Toh ka daina…… Karka manta dazu ka kirani duk abunda ka fad’a nayi recording, sannan ka turamin ainiyin hotan da ka d’aukemu nida kai, Kaga in kasa an canza wancan zan karyata ta hanyar tura Wanda ka turamin wanda fuskanka ne akai tare da tura recording din da nayi kake ta surutai akan kasa a canza fuska …… D’an shuru tayi tare da kallonshi ganin yanda ya d’an tsorata yasa taci gaba da fad’in Kaga in nasa nawa Nima kimarka da siyasan ka ya zube …… Madu ina son ka sani bana son bata maka suna amma kana ingizani, are you not are shame, nace na daina harka da maza aure zanyi amma kana son dole saina ci gaba dayi, inaso ka sani daga yau shine rana ta karshe da zaka sake yunkurin shiga al’amari na, zan iya fasa auran da zanyi kaifa zaka iya yarda ka rasa kujeranka???….. Ganin Alh madu ya kasa cewa komai yasa ta Fara kokarin flta har takai bakin kofa ta tsaya tare da waigowa tace ina maka fatan shlriya domin mutuwa ci take kaman rana, a shekarunka yanzu babu abunda ya dace dakai sai istigfari domin neman gafaran Allah dan an bata y’ay’an mutane da dama, kaima ka jira Kaga abunda za’ayi ma naka da yardan Allah …… Fuuuuu ta flta tabar gidan, taflya take tana kuka a kafa tare da takaicin tsintar kanta da tayi cikin wannan kazamar harkan, amma ta d’anji dad‘i tunda yanzu ta tabbata Alh madu bazai K’ara Mata barazana ba akan rayuwarta dama shine matsalanta….. Yanzu Abu d’aya zan fuskanta shine ldan Yarima yasan gaskiya shima zanyi komal yanda ya dace ta hanyar fad’amai da fahimtar dashi komai… 
Bayan fltan bariki Alh madu murmushi yayi wanda nidai ban gane na miye ba. na mamaki ne? kona nadama ne? kona shirin wani tuggu ne? oho …… Koma dai miye zamu gani in yaji gargadin bariki ko kuma zai sake bibiyarta 
Bariki tana zuwa kofar gidansu na u/kanawa ta hango motar yarima a fake, wanda shi d’aya yazo….. Mamaki abun ya bata Toh Mai yasa bai kirata ba. kuma wayarta na hannunta, tace may be yanzu yazo …… Gaba tayi tazo zata wuce cikin gidan tayi kaman bata ganshi ba, shima yana kallonta baice mata komai ba harta shige Cikin gidan ….. Murmushi Yarima 
yayi tare da d’aukan wayarshi ya tura mata message kamar haka …… K0 in tafl ne??? 
Bariki ganin message dinshi yasa tayi dariya tare da komawa waje ta sameshi inda yake bud’e 
motar tayi ta shiga Kallonta yayi tare da fad’in kina ganina kika wuce Tace Yarima yaushe na ganka?? 
Murmushi yayi tare da fad’in my princess inafa kallonki, harda wani kawar dakai Kalan baki ganni ba 
Tace Yarima nidai naga mota amma ban San Waye a aki ba, ko kana son inyita kallon maza ne ?? Bai san lokacin da yayi dariya ba, tare da fad’in koda yaushe kin San hanyar da zaki Kare kanki… 
Shuru tayi tana tunanin i wish Yarima yasan gaskiya ya fara sona, hawaye ne ya gangaro mata a ido da sauri tasa hannu ta gage dan karya gani tare da d’ago kanta taga koya gani…. Kurtaga yana kallonta …… Da sauri tayi k‘asa da kanta 
Yarima Aliyu yace Zainab a kullum nazo Wajanki kina Sani fargaba, Wai Mai kike boyemin ne?? Kina sani tunani Kala Kala plz tell me Mai yake damunki banso ki barni cikin duhu …..  
Kuka ta farayi tare da fad’in Yarima tunda nake ban tabajin son kowa ba sai Kai, inajin tsoran abunda zai faru in kasan gaskiyan al‘amarin da nake boye maka ……. Karan wayan Yarima ne ya Katseta 
D’aukan wayan Yarima yayi ganin Sunan waziri ne, ii nayi Yarima yana fad’in 0k gani nan zuwa, har kun karaso?…. Kashe wayan yayi tare da kallon zainab yace Bari inje in dawo yanzu. Hannunta ya ri’ketare da fad‘in haka zaki ma Fuskanki yana hawaye??….. Janyoka yayi jikinsa tare da gage mata hawayen fuskanta yace plz my princess kibar wannan kukan yanzu zan dawo sai muyi magana Kinji? Kaita d’aga Mai alaman eh. 
Murmushi yayi tare da fad’in den my girl, inna dawo zan fad’a miki albishir Murmushi tayi tare da fad‘in saika dawo sannan Yarima direct u/sarki ya nufa inda Zai had‘u dasu waziri a nuna mishi filin da Mai martaba ya bashi sannan suje asibitin shi y’anjarida su d‘auka domin a tallata asibitin duk da Yarima baiso hakan ba, amma waziri yace ayi tunda yace zai Fara aiki na wata uku kyauta akan matsalolin mata tunda shi likitan mata ne, ta gidan tv da radio mutane suji marasa karfl su zo….. Asibitin ba Yarima kadai bane zaiyi aiki a cikinsa ba harda wasu likitoci na fanni daban daban…… 
Bariki bayan ta shiga cikin gida, ummanta tace Zainab Yadai har Yarima din ya tafl? 
Tace eh amma zai dawo…. Wai har yanzu habib bai zoba? Tun dazu yake cemin yana 
Sallaman habib dinne yasa tayi shuru ya shigo yana gafaran ku dai masu gida Shiga d‘akin dasu bariki suke yayi yana fad’in In shigo k0 in jira a kimtsa…. 
Bariki tsaki taja Tana fad‘in Asara, bayan ka shigo din kake tambaya koka shig …… 
Waige ya farayi yana duba dawa bariki take magana, yaga babu wani namiji a wajan yace ke Dawa kuma?? Naga banga ko wani namiji a nan ba Bariki tace dakai nake mana… Yace Wlh bariki zan miki rashin mutunci miye wani ka? Mai yakai mace jinsin maza, gsky banso yana maganan yana hura hanci Kalan ranshi ya baci….. 
Umman bariki ta Karya babu abunda take sai dariya, tace Zainab gskya bakya kyautawa taya zaki dinga kiranta dana miji Bayan kin San macece y’ar uwarmu…. 
Habib yace fad’a mata dai Bariki dariya tayi tare da fad’in ni bama wannan ba kawata kina ji?? Habib yace kunne aikeji 
Bariki bashi Labarin yanda sukayi da Yarima tayi Kafin yace zaije ya dawo, taci gaba da 
fad’in Wlh Ina son fad’a mishi gaskiya Kinga sai muyi aurenmu laflya ba tare da matsala Ba
Habib gyara zama yayi yace lallai Bariki, ban taba sanin baki da wayau ba sai yau. Ke kina tunanin in kika fad’ama yarima gaskiya zai aureki?? Kin bashi iyayen karya tare da Labarin karya ke kina ‘tunanin duk son da yake miki zai yarda ya aureki? Karki manta kina fad’amin yanda yake kyaman mace mazinaciya, sannan kike gigin son fad’a Mai gskya? Toh inma shi Yariman ya yarda ya aureki kina tunanin iyayenshi zasu yarda??? Bariki kin San Gidan sarauta kuwa?? Shawaran da zan baki shine kiyi shuru da bakinki kiyi yanda kika tsara in an d’aura aure kya fad’a mishi gaskiya tunda naga kina mishi son tsakani da Allah kuma naga kina son zaman auren, kuma nasan bazai sakeki ba tunda ya aureki kuma don basa saki ….. Yau inda bakya sonshi Kinje gidan da wani manufa ne sai kice mai fyad’e aka miki, 
amma tunda son gaskiya kike Mai saiki fad’a mishi gaskiyan koke wacece. 
Mahaiflyar bariki ta Karya, tace bariki gaskiyan habiba ne, dan Indai kika fad‘a mishi gaskiya zaki iya rasashi kuma na har abada, gidan sarauta zasu ‘Iya yarda su rasa d’ansu akan ace ya auro musu karuwa domin abun kunya ne, ki duba kiga su ko aure kayi a gidan sarauta sai Anga jini shine kin Kai budurci… Bayan bako wace mace kejini ba kuma budurwa ce 
Habib ya tabe baki tare da fad’in nidai Allah yasa ina d’aya daka cikin mata masu zubar da jinin, Kar lnsha gorin miji Dan mazan nan ba mutunci garesu ba ….. Bariki tace toh kuna ganin inna aureshi na fad’a mishi zai hakura dani? 
Habib yace insha Allah, dole ma ya zauna dake tunda bada gardi ya kamaki ba, ai yanda kikaji dad’i al’adan gidan basa saki, sai an kamaka da gardi kuma kince kin tuba ….. kuma na tabbata koda yayi fushi zai sauko tunda ya aureki zaki san hanyar da zaki janyo hankalinsa ma dole ya sauko, domin ya sami. santaleliyan yarinya son kowa kin Wanda ya rasa…… Toh Bari dai mu gani bariki zata fad’ama yarima inya dawo koko ta d’auki shawaran habib au Anty habiba ….. 
Hmmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE