BARIKI NA FITO CHAPTER 39

BARIKI NA FITO
CHAPTER 39
 Sosal, bariki kuka ta Fara Tana tad’ln Yarima Mai yake damunka?? Tare da tabashl tana son d’ago Shi ,hannunshi da yasa a baki yana tari ya cire ya fara kokarin tureta alaman tabar tabashi, amma jikinshi babu kwari ya kasa tureta din …… Wani irin tari yayi tare da yunkurin yin amai saigajini nan ….. Wani irin ihu ta saki mai ban tsoro tare da kiran nashiga 
uku Yarima maiya sameka?? 
Ganin jinin a bakinshi yana fita yasa ta fita da gudu,  taga fadawa tace dan Allah kuzo Yarima zai mutu, tana maganan tana kuka da ihu, kuzo mu kaishi asibiti ….. Da sauri suka shiga wasu kuma suka je fad’ama iyayenshi, koda fadawa suka shiga ganin Yarima sukayi a kwance yana wani irin nishi gajini na zubar mai a baki, da sauri suka D’aukeshi suka fita dashi, suna cikin sashi a mota mum dinshi tazo, ganin halin da d’an nata yake ciki yasa ta Fara fad’in Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, Yarima maiya sameka, lokaci d’aya kuma tasa kuka, shiga motar tayi da sauri suka nufi asibiti …… Bariki Kafin ta karaso har Sun wuce dan haka ta Fara cewa sauran fadawan muje ku kaini dan Allah inda suka je ….. Ganin kanta ko dankwali babu yasa wasu kuyangi dake tsaye wajan suka karaso suna fad’in Allah ya 
taimaki gimbiya, ki koma ki saka mayafi sai a kaiki,. 
Sai a sannan bariki tasan a halinda take da gudu tayi ciki, inda ta d’auko mayafinta tana kokarin fita wayar Yarima dake d’akin ya fara K‘ara dole yasa ta koma ta d’auki wayar babu suna number ne ke kiranshi harya tsinke bata d’auka ba ….. Fita tazo yi lokaci d’aya kuma ta tsaya cak domin tunawa da abunda ya faru da Yarima, wanda tunda aka kirashi ta rasa gane kanshi,har wannan abun ya sameshi, danna wayan tayi da nufin ta shiga taga Mai aka turo mishi, gani tayi akwai password, shuru tayi tana nazari Mai Yarima ya gani?? Kodai wani ya fad’a mishi koni wacece?? Gabanta taji ya fara fad’i tunawa da kalaman daya Fara Mata Kafin ya fad’i …… Wani irin kuka ta saki mai ban tausayi, tare da fad’in shikenan sunyi nasara Sun fad’ama Yarima koni wacece kuka take Sosai, lokaci d’aya kuma ta fita da gudu inda taga mota na jiranta shiga tayi domin a kaita asibiti da yake fadawa sun San asibitin da suke zuwa nan aka nufa da ita dan suna da tabbacin can aka Kai Yarima, tana mota tana kuka …… 
Kafin kace Mai har labari ya bazu cikin masarauta, Yarima Aliyu bashi da lafiya rai a hannun Allah, har wasu na cewa jini ke fita a bakinshi hala amaryanshi ba budurwa bace, wasu kuma suce kodai wani abu tayi mishi?? Haka dai ake ta jita jita, koda kuyangin gimbiya zinatu suka fad’a mata cikin tashin hankali itama tayi asibitin ….. 
Yarima Aliyu ko Kafin akai asibiti, ya daina koda motsi, ana zuwa akai emergency dashi
likitoci sukai kanshi aka fara dubashi, tare da bashi taimakon gaggawa…. 
mum ta kasa zama sai kuka takeyi ga fadawa a wajan da yawa, kowa ya shiga Cikin damuwa. 
basu dad’e ba saiga bariki ta karaso Tana kuka, tare da fad‘in mum Ina Yarima?? Ina Yarima?? Mum din ri’keta tayi tare da rungumeta, ta kasa ko magana sai shafa ma bariki baya takeyi alaman tayi shuru …… 
Suna cikin haka saiga Zinatu tazo cikin Tashin hankali ganin Bariki wajan mum ko ba’a fad’a mata ba tasan itace amaryan da Yarima ya auro, da sauri ta nufi bariki ta fincikota tare da watsa mata Mari Tana fad’in mai kika ma Yarima?? Mai kika mishi?? Kuka ta saki Zinatu 
tare daci gaba da fad’in Wlh Idan wani abu ya sameshi saina kasheki W ……. ‘ 
Mum sai yanzu ta iya magana, tace Zinatu kina da hankali kuwa?? A gabana kike wannan abun?? Shi Yarima dinne yace miki ita ta mishi wani abu?? Cikin kuka tace mum, daka ita sai shi, Nasan wani abu tayi mishi …… Mum tace ya isa haka, plz ki barni inji da abunda yake damuna ban son rigima…. Bariki kam tunda zinatu ta mareta take ri’ke da wajan Tana kuka, ko bata tambaya ba tasan itace Uwar gidan Yarima Aliyu …… Bariki tasan lallai k0 ba’a fad’a ba dole kowa yayi zarginta, abunda Zinatu ta fad’a gaskiya ne ….. Kuka tayi k‘asa tanayi tare da fargaban Kar 
wani abu ya sami Yarima dan bazata iyajura ba ….. Kowa na cikin Tashin hankali, ga doctors haryanzu basu fito ba …… Suna nan zaune saiga 
Mai martaba shida Hafsat Sun zo cikin Tashin hankali. Mum ganin Mai martaba yasa ta tashi ta nufeshi tana kuka, tare da fad’in inajin tsoro Kar Yarima ya mutu Aman jini yakeyi Ina tsor ….. Toshe mata baki Mai martaba yayi, tare da fad’in ki daina fad’in haka, Hafsat itama kuka ta Fara cikin Tashin hankali ….. 
Duka kowa shuru yayi babu Mai rarrashin wani, suna nan tsaye d’aya daka Cikin doctors din ya fito, suna ganinshi suka nufeshi tare da fad’in Dr ya ake ciki, ganin Mai martaba yasa 
yace ranka ya dad’e wacece Zainab a cikin nan?? 
Da sauri mum tace ga tanan tare da nuna bariki, yace ok tare da kallon Bariki yace taso 
Da sauri ta tashi tabi Dr, kowa da abunda yake sakawa, Zinatu ta Fara fad‘in mum kin gani ko kin gani wlh itace tayi mishi wani abu ….. 
Kowa shuru yayi ya kasa cewa koda uffam…. Suna jira suga ikon Allah …… 
Koda Bariki suka shiga oxygen din da akasa ma Yarima yana k’asa alaman yana son d’aukewa, kuma yana saka zero shikenan mutum ya mutu, da sauri Dr yace plz ki mishi 
magana sunanki yake ta kira pls say something karku rasa shi ……. Da sauri ta ri’ke Mai hannu tana kuka tare da fad’in Yarima karka bari wani abu ya sameka ….. You know that I can’t live without you, plz Yarima ka tashi kasan ina Sonka kaine rayuwa na, wlh bazan iya juran inga wani abu ya faru dakai ba …… Lokaci d’aya oxygen din ya fara k’aruwa alaman numfashin shi yana son dai daituwa…. 
Likitocin ganin haka yasa suka fara kallonjuna alamanjin dad’i an fara nasara ….. Bariki kuka take Sosai tana fad’in karya mutu ya barta…. Idonshi dake rufe ya fara zubar da hawaye …… Lokaci d’aya numfashin shi ya dai daita …… D’aya daka cikin doctors din yace ma Bariki yauwa komai yayi dai dai mu jira muga kuma yanda Abun zai kasance amma muna bukatar ki zauna har muga farkawanshi, muna nufin Kar kibar asibitin nan har sai munga ya farka 
Cikin kuka tace babu inda zani Ina nan tare dashi Dr din fita sukayi, inda suna fita Mai martaba yace ya akayi?? Mai yake faruwa dashi?? D’aya daka cikin Dr din yace ya samu bugawan zuciya ne, ina tunanin yaga abunda ya bashi tsoro ko mamaki, kuma daga duka alamu abunda ya gani ko yaji yana d’aya daka cikin abu masu muhimmanci a rayuwanshi, hakan yana faruwa wasu ma rasa ransu suke, a gskya masu rasa ransu ma sunfi yawa amma shi yayi Sa’a k0 ince mun samu mun ceco rayuwanshi tare da taimakon Allah da kuma wannan baiwar Allah dake ciki, magananta da yaji shine yasa zuciyarshi ta Fara harbawa, inda badan ita ba toh gaskiya dasai dai kuji mummunan labari , dan haka dole ta zauna dashi muga yanda Allah zaiyi ….. Mai martaba godiya yayi ma Dr din tare da fad’in zamu iya ganinshi?? Sannan kana ganin zai tashi babu wani matsala?? Dr yace zaku iya ganinshi amma plz Kar kuyi magana, sannan zai tashi insha Allah Indai yarinyar na kusa dashi kuma yana jin magananta a kusa dashi ….. 
Mai martaba yayi ma Dr godiya, sannan suka shiga d’akin, ganin Bariki sukayi a zaune kusa dashi hannunta na ri’ke da nashi tana kuka ….. 
Kowa tsayawa yayi yana mamakin irin wannan Abun musamman mum damai martaba, ita dama zinatu bata shigo ba domin maganan Dr yasa taji wani iri tare da takaici ….. Mum ce ‘a k’arasa kusa da inda Yarima din inda  yake tare da kamo d’ayan hannunshi, fuskanshi tayi fayau ga hawaye a idonshi na zuba ….. Mum itama hawayen ne yake zuba daka idonta, kowa dake wajan ya tausaya mishi …… Mai martaba ganin mum nason kuka mai sauti yasa ya kamota sukai waje, Hafsat da Bariki suka zauna a d’akin Zinatu ce ta shigo d’akin ganin Zinatu yasa bariki tashi tabar d’akin domin irin kallon da taga zinatu din nayi mata, kuma ko babu komai ya kamata ta dan bata waje ta gana da mijinta duk da bai farka ba ….. Fita Bariki tayi tana fita, Mai martaba yace Zainab ya kika fito?? Ko wani abu kike bukata?? Tace a’a Abba cikin jin kunya, na d’an basu waje ne ….. Mai martaba ya gane ta flto ne saboda Zinatu ……. Mum tace Zainab bai kamata ki ‘fito ba ai, maza ki koma Kinji ….. 
Tace toh mum jiki a sanyaye Bariki ta shiga, abubuwa sun mata yawa, na farko Tana zullumin Mai aka fad’ama Yarima a waya, sannan maiya gani, dukwannan Abun suke ta faman Mata yawo a Kai ….. Koda Bariki ta shiga zinatu fta tayi 
Bariki zama tayi kusa da Yarima tare da kurama fuskanshi ido, har yanzu yana hawaye, 
gaba d‘aya zuciyarta ta tsinke, shidai haryanzu bai farka ba, toh wannan hawayen fah????….. Kiran Hafsat akayi a waya ta tashi tabar d’akin Tana fita kaman ance Yarima ya bud’e ido , a hankali ya bud’e idonshi ya sauka akan na Zainab wacce itama shi take kallo tana murna tare dason yin magana murna ya hanata…… Murmushi ya sakar mata, tare da kamo hannunta ya ri’ke tare da matse su ….. A hankali tace Yarima Ina Sonka I can’t live without you, tana maganan tana kuka, tace l was scare with your conditionl …… Hannunshi yasa ya rufe Mata baki yana kokarin yin magana ya tsaya alaman ya tuna da wani abu ……. Lokaci d’aya ya sake mata hannu tare da fad’in leave from hare I hate to see 
your face …….. Cikin kuka tace Yarima zainab din’ka ce Yarima nice maina …… 
Ya daka mata tsawa tare da ri’ke kirjinshi yace I said leave from here ……. Su mum dake waje Suka shigo harda su zinatu, ganin Bariki na kuka Yarima shima hawaye ne ke zuba a Mai martaba yace Aliyu matarka ce kake koranta?? Maita maka??…… Yace Abba plz tell her to leave I don’t want to see her face…. Why am I still alive…. Dai dai lokacin doctor yazo yace kowa yabar d’akin …….. Bariki da sauri ta Flta Tana kuka lallai ta tabbatar an fad‘ama Yarima ko ita wacece kuka take Sosai tare da barin asibitin ba tare da sanin kowa ba …… 
Bariki kuka take Sosai tana tafiya a kafa, tafiya take bata san inda take wurga kafarta ba, ba komai bane a ranta sai yanda Yarima yake nuna tsanan ganinta, ta tabbata abunda take boyewa take burin in sunyi aure ta fad’ama Mai, wanda take burin Sanar Mai an samu wani ya fad’a Mai ….. Zama tayi a k’asa gefen titi Tana kuka cikin Tashin hankali, bata taba tunanin abubuwa zasu cabe Mata haka ba, tunda take shirya wannan abun bata taba tunanin Idan ta fad’ama Yarima gaskiya dole iyayenshi Suma su san gaskiya tunda tayi amfani da iyayen bariki, gaba d’aya dana sani takeyi Wanda hausawa ke cewa k‘eya ce, da yake dare ne Sosai babu mutane sai motoci dake Faman wucewa, suma motocin jifa jifa suke wucewa ba Sosai ba …… Bayan iyayen Yarima sun fito dasu Zinatu, kowa da abunda yakesa’kawa cikin ranshi game da wannan al’amarin ….. 
Zinatu kam dad’i ya cikata Sosai, tare da aiyana ma ranta lallai Yarima ba virgin ya sami matarshi ba, tunda har Ya nuna baya son ganinta, yake nuna mata tsana k’arara, ji take Kaman tai ihu dan murna, tare da fad’in da Gimbiya Amina batai bacci ba dana kirata na bata wannan kyakyawan labarin, amma Allah ya kaimu gobe …… 
Sunyi wajan 20min 3 wajan, sannan mai martaba yace Ina Zainab?? Nan mum ta kalli Hafsat tace ina tayi?? Hafsat tace nima ban sani ba mum, Nan mum ta tambayi fadawan dake wajan ko sunga inda tayi?? 
D’aya daka cikin fadawan yace ta fita, daka ganin alama kuma waje tayi dan yanda ta fita da sauri tana kuka …… ‘ 
Nan mum tayi hanyar waje fadawa suka bita, itama hafsat bayan mum tabi…. 
Fita sukayi suna nemanta amma basu ganta ba, fadawa sukayi gaba suna dubata, wani daka cikin fadawan ya dawo da sauri yana fad’ama mum ga tacan a zaune a k’asa Tana kuka Da sauri mum suka nufa inda take, tana nan zaune a k’asa Tana kuka mai cin rai ….. Mum d’agota tayi tare da fad’in Zainab lafiyanki kuwa zaki fito bakin titi ki zauna kina kuka?? Zainab bata ce mata komai ba, domin haryanzu kukan take ….. 
Mum tace maza kuzo a kaiku gida, kuje ku huta tare da kamo hannunta sukai asibitin ….. Suna k’okarin shiga sai ga Mai martaba shima yana fitowa, ganinshi yasa suka tsaya harya karaso inda suke …..Mum tace Dr din ya fito ne?? 
Yace a’a nazo inga ko kun ganta Ashe ga tanan, suzo a kaisu gida dare yayi …… 
Mum tace Zainab kiyi hakuri kuje gida gobe da safe sai kuzo Kinji?? 
Kai ta d’aga amma badan taso ba, sai dai dan bazata iya musu da mum ba, haka suka tafi gida ita da Hafsat da Gimbiya zinatu damai martaba domin mum ce zata kwana dashi ….. Duk da sun so suji maike faruwa in Dr Ya fito amma mum tace suje babu wani matsala tunda aiya farka …… 
Koda kowa ya fita, Yarima Aliyu ido ya lumshe tare da kwanciya yana Mai jin zafln abunda ya gani…. Dr ne ya mishi y’an dube dube sannan yace haba Aliyu, kana son sama kanka damuwa plz ka kwantar da hankalinka an fad’amin you r a doctor so nasan Idan na fad’a maka ka sami bugawan zuciya zaka San abunda ya kamata kayi wajan cire ma ranka abunda ya razana ka …… Yarima baiko Kalli Dr ba balle ya kulashi sarautar ta motsa ….. Dr yaci gaba da fad’in Yarima ka gode ma Allah, amma kana son Zainab dinnan da yawa, Allah Yarima Aliyu ya Katse Dr da fad’in ina son a sallameni …… Dr yace sallama? Yarima Aliyu yace yes yanzu 
Dr yace a’ah ka Bari ka K’ara samun sauki, domin haryanzu baka dawo Normal ba ….. 
Yarima Aliyu tashi yayi dakyar ya zauna tare da fad’in Dr i am a Dr too I knw how to handle myself, and kace na samu buguwar zuciya?? So zamana a nan baida amfani dole inje gida a nan zan samu nutsuwa… 
Dr shuru yayi yana nazari, maganan Yarima Aliyu gaskiya ne, Idan mutum ya sami buguwar zuciya irin haka, is either an fad’a Mai wani abu ko ya gani, so inya duba yaga abun is not true a hankali zai Fara samun lfya domin ya samu nutsuwa ……. Yarima Aliyu tashi yayi jiki babu kwari, kaman zai fad’i yayi sauri ya ri’ke hannun Dr din ……. Doctor din yace kayi a hankali, ka zauna let me call your parent su ri’ke ka, taimaka ma Yarima yayi ya zauna yana cije baki alaman yanajin jiki ….. Yarima Aliyu ba komai bane yasa yace a sallameshi sai dan yayi magana da Zainab bariki, akan yaudaran da ta mishi and bayajin zaiyi accepting d’inta a matsayin mata, matar data gama watsewa a duniya ko wani namiji ya santa……..Bud’e kofar da akayi yasa ya d’aga ido da yake zubar da hawaye, ganin mum da fadawa yayi, nan Dr yace su taimaka sukai Yarima Mota, kamashi sukayi suka fita, mum kallon d’an nata take cikin tausayawa.. Bayan an fltar da Yarima mum ta kalli Dr tace nidai banso ka yarda ya koma Gida ba, inajin tsoran Karwani abu ya sake samunshi ……. Dr yace karki damu, a gidan zaifi samun nutsuwa, Idan mutum yayi irin haka kika ga yace yana son tafiya akwai abunda yake son tabbatar wane, wanda shine yasa ya fad‘a irin wannan matsalan, sannan komai ya faru call me ….. Mum godiya tama Dr sannan ta fita. 
Bariki bayan sun karasa gida gefenta da aka kaita nan ta shiga, bedroom tayi Kai tsaye, ta zauna a k’asa tana kuka kaman ranta zai fita, wayan Yarima dake hannunta tayi k’ara 
alaman an turo Mai sa’ko. alive wayartavi a gefe …… Tabbas tasan wannan ba komai bane. tunda tun Farko ta zabi sabama Allah, dole taga bacin rai, dama duk Wanda ya kauce hanyar Allah kuma yasan yabar hanya Mai Kyau dole ya had’u da ukuba tun a duniya, ita Allah na Sonta da rahma tunda harta gane ta kuma yi nadama, sai dai irin hanyarda tasa kanta koda kayi nadama sai an samu masu goranta maka, in bakayi wasa ba harta jikokinka sai anyi musu gori da fad’in ai kakarsu tsohuwar karuwa ce da, ko kuma ayi ma y’ay’anki ace ai uwarsu karuwa ce, in tayi aure tama miji laifi yace ta biyo halin uwa, tasha a nono, kai Wlh rayuwan bariki batayi ba ko kad’an… Kuka ta K’ara saki cikinjin zafln bata rayuwarta da tayi duk da kaddara ne ya sameta ….. Wacce bata san yanda akayi Abun ya sameta ba ….. 
Gimbiya zinatu kam tana shiga gefenta wa’ka ta kunna Tana ta rawa cikin jin dad’i, tare da fad’in first night ya zama ranan ba’kin ciki dariya ta saki cikinjin dad’i… 
Koda su Yarima Aliyu suka lso gida, cewa yayi zai nufl gefen Zainab, duk da mum taso ya bita amma ya’ki, mum bata sa komai a ranta ba, ita a tunaninta da taji yace zashi wajan Zainab, sai tayi tunani ko abunda yayi mata d’azu yake son bata hakuri, sannan a mota ta fad’a mishi abunda Dr sukace inda badan Zainab dinba toh da zai iya mutuwa ….. Fadawa na k‘okarin rikeshi yace Nop ku barni, zan iya, tafiya yake dakyar harya shiga cikin falon bai ganta ba 
Mum ganin ya shiga yasa itama ta wuce 
Yarima bedroom dinshi yayi inda tun Kafin ya k’arasa yake jin sautin kukanta, bud’e kofar bedroom din yayi ya ganta a k’asa tana rasgan kuka a hankali cikin murya irin na marasa lafiya wanda yakejin jiki yace wannan ba kuka kike yiba.. Jin muryan Yarima yasa tayi sauri ta tashi, tare da kallonshi tana mamakin ya akayi ya 
Yarima Aliyu idonshi na kanta yana mata wani irin kallo Mai Kama da I hate you, yace Zainab oh sorry Bariki …… Jin ya kirata da Bariki yasa zuciyarta ta tsinke gaba d’aya, abunda take zargi shine ya faru an fad’amaYarima ……. 
Katse mata tunani yayi da fad‘in how dare you ……. Shuru yayi cikin kunan rai hawaye na zuba a idonshi …… Yace kin cuce ni, kin yaudareni, and ina asibiti kin kuma bina har ana fad’in da badan keba dana mutu, Mai yasa kika zo?? Mai yasa ban mutu ha, I wish da mutuwa nayi da Nasan zanga irin wannan ranan, you play with my feelings you all lies to Zatai magana Yace keep quiet, don’t try to say anything, let me speak you cheater …… Bariki kuka take Sosai Yarima Aliyu yaci gaba da fad’in do you think I will trust you again?? You break my trust, dan shuru yayi sannan yaci gaba da fad’in Zainab I love you from d bottom of my hrt, why are hidden your secret with me?? ……. Tana kokarin yin magana yace I said don’t try to speak keep your mouth shut, I don’t want to listen to  your lies again, Bariki kuka take na farko ga Tashin hankalin halinda mijinta ke ciki, gashi ya hanata yin magana 
Yarima Aliyu yace but you don’t cheat me, you cheat your self, Zainab I was shock to see your pictures with different men’s, ido ya rufe yana hawaye domin takaicin abunda yake fad’aji yake kaman zuciyarshi zata buga, I never expect dat from you, Zainab mai yasa kika bata rayuwanki nawa kike samu? mai kikeji,? mai yasa kika yaudareni,? mai yasa kika boyemin gaskiyan ko ke wacece,? Zainab how old are you kwata kwata da zaki bata rayuwanki just for money?? Mai kika samu Mai kika tara ?? Da sauri tace Yarima plz ka saurareni dan Allah tana maganan tana kuka…. Yace I don’t want to listen to  your lies, komai naki karya ne your love your affection is all a lie
shuru yayi hawaye na zuba daka idonshi Abun gwanin tausayi’ sanna yaci gaba da fad’in you break d trust dat I have for you, Zainab kwata kwata shekaranki nawa?? Har kin San ki samu iyayen Karya, ki aurar da kanki da kanki, you fool us, mai kika d’auki aure??? Do you think dat marriage is a joke?? Zainab I truly love u  but I won’t accept you d way you are ….. lhun data saki Tana bashi hakuri akan ya tsaya ya saurareta tayi mishi bayani akan duk wanda ya fad’a yayi ne danya had’asu …… 
Yace Yimin shuru, Habib zai miki karya ne? Cikin razana tace habib ….. Yarima yace eh habib call me and tell me everything All your plan …… Zainab I feel so sad when I hear d truth about you ….. Nayi takaici you never love me habib told me you marry me only for money …… Shuru yayi yana hawaye can yaci gaba da fad’in kin aureni dan ki sami kud’i bakya sona Wanda kike so yayi rejecting d’inki shi yasa kika aureni dankl nuna mishi kina da Wanda suka fishi ….. After dat he send me your pictures matsawa yayi kusa da ita ya d’auki wayarshi ya fara dannawa nuna mata yayi yace Waye wannan hotunan tane da Alh madu, gashi tsirara ya ri’keta, sai kuma wanda tayi da Hon salis …… Yarima yace have you seen it?? Ok shima wannan it all a lies ko shima wannan so ake a had’amu?? Jefa wayan yayi a K’asa ta fashe …… ldonshi ya rine yayi ja, ga zuciyarshi dake faman tafarfasa kirjinshi na mishi zafl …….. Yace you betrayed me, who did I harm to deserve all this 
punishment …… Ban kasance mazina ciba. ban taba sanadin lalacewan wata ba. why matar dana aura kowa ya Santa ……. 
Bariki kuka take Sosai tare da tunanin irin cin amanan da habib yayi mata, lallai don’t trust anyone in life, …… Bakinta na rawa ta Fara fad’in Yarima Nasan ni Mai laifi ce a gareka dan Allah kaban dama just once I need to exp …… Yace I won’t give you any chance to tell me another lies, karyan da kikayi min baya ya 
isa …… My heart only beat for you ….. Tun a mafarki na Fara sonki, but you never love me, you hurt me alot …… You marry me for money not for love …… 0k even I, Iwon’t accept you as my wife ….. You will live here as my servant har karshen rayuwarki zaki zama mai min bauta, and I will make sure to hurt you d same as you did to me, nd I promise to hurt  you, keda duk Wanda kukai wannan abun sai Nayi punishing naku, I will make sure to make you regret knowing me in ur lyf …….. Da sauri ta matsa kusa dashi tare da kokarin tabashi ya daka mata tsawa tare da fad’in 
don’t you dare try to touch me…. Karki k’ara yunkurin tabani da wannan kazamin jikin Naki
K’asa tayi da giwowinta Tana kuka tare da fad’in Yarima call me with wat ever name you like, I deserve it, Yarima just once plz ka saurareni plz ….. Yarima yace do you think zan kara sauraran wannan karyan naki?? Harda cemin kin sauke 
Al’qur’ani, Wat a funny, kin dai yi hadda a bin maza ….. Tace Yarima is true na sauke al’qur’ani tun I was 11yrs plz Yarima allow me to speak ……… 
Hmmmmmm bari dai muga ko zai bata daman fad’a mishi ko ita wacece . 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE