BARIKI NA FITO CHAPTER 4

BARIKI NA FITO 
CHAPTER 4
KAMAR YADDAH MUKA FADA PLEASE 🙏 IF UR NOT 18+ OR MATURE ENOUGH  STAY BACK banason qorafi 
Bariki sai wajan 2 ta tashi, da sauri tayi toilet tayi wanka, tare da dauro alwala tayi sallah azahar, Bayan ta idar ta tashi ta nufi falo a nan taga alh madu, dariya yayi tare da fad’in yau gaskiya kinsha bacci harna fita na dawo kina bacci, baki ta tabe tare da zama tace yunwa nake ji, abinci ya nuna mata akan dinning Wanda ya siyo Mata takeaway yace gashi can na siyo miki, tashi tayi ta nufi dinning din ta bude ledojin fried rice ne da kaza, sai su snack, Fara ci tayi shida kanshi 
ya tashi ya nufi fridge ya d’auko mata Su drinks, taci abincin Sosai sannan ta tashi Tana mika alaman ta koshi, kallonta yayi yace bariki Wai Mai zai hana ki aureni ne? Bata fuska tayi tare da fad’in dan Allah mubar wannan maganan zan wuce gida, murmushi yayi tare da fad’in toh ya maganan tafiyan mu? Tace zamu je tunda nace zanje inna fad’a magana bana canzawa, yace dakyau driver dina zai kaiki gida, amsan account number dinta yayi nan take ya Mata transfer 
din 1mil, murmushi tayi tare da fadin thanks, fita tayi driver din alh madu ya kaita har gida, koda suka karasa sanda ta fito saiga ij babba yazo yana wani tale kafa a dan dole shiga mace, wajan bariki yazo yana fad’in oh duniya Kaga Abu, kodai dadiron da Habiba ta had’a miki jiya da alh madu ne? Tace a’a da wani ne, Bayan na dawo daka can na hadu da driver din alh madu shine na bishi, ij babba tace toh mai kike kullawa ne kodai ya gyara kayan aikin nasa ne? Tace hjyta hjyta wani gyara yayi abu kaman gindin yara, manage kawai nakeyi, ij babba tace ai gwara kiyi ta maneji kina gwagurawa kiyi ta tasan kud’in dan banzan, dariya bariki tayi tace Kai hjyta ai baki San wani abuba nifa kud’i bai daman ba nafi son banana babba yafi min komai, bari kiga inje in huta jiya na ciwu na hadu da Maye, dariya ij babba yayi tare da fad’in ai irinshi ya dace dake, bata ce komai ba tayi ciki, tana shiga d’akinta ta rufe tare da d’auko sigarinta ta Fara zu’ka. 
***************************
Yarima Aliyu sai wajan isha’i suka dawo daka katsina, kai tsaye gefenshi ya nufa dan yayi mugun gajiya, yana bukatar hutu, bayan ya shiga toilet ya fad’a yayi wanka sannan yasa wata jallabiya Fara, kwanciya yayi akan lallausan gadon d’akinshi, lumshe ido yayi lokaci d’aya yayi tsaki tare da fad’in akan wannan mummunar aka sa na bata lokaci na, har zuwa garin katsina, jin karan wayanshi yasa ya tashi d’auka yayi yaga mum, dannawa yayi tare da fad’in mum, tace ka dawo shine baka shigo ba? Yace Wlh mum nagaji ne, tace maza kazo Mai martaba yana jiranka, tashi yayi tare da fad’in ganinan zuwa, manyan kaya yasa yana fita fadawa suka mara mishi baya suna mishi kirari har gefen mahafin nashi, bayan ya shiga Ya gaida iyayen nashi, mai martaba fuska a d’aure yace haba Aliyu Mai yasa daka zuwa zaka dawo yau, mai makon ka zauna kayi kwana biyu, amma babu damuwa tunda Kun dawo lafiya sannan sarkin katsina yace yarinyar ta amince toh kasan wannan karan ba yardanka nake 
nema ba dan haka saika Fara shiri domin zani katsina dakai na cikin wannan satin dan a tsaida maganan aurenku, kanshi na k’asa yace Toh Abba Allah ya taimaka, mai martaba ya amsa da Ameen tare da sama d’an nashi albarka, Yarima Aliyu 
tashi yayi yabar d’akin tare dayi musu saida safe, d’akinshi ya nufa yana ta faman sintiri domin 
shi harga Allah baya son wannan auren danshi yarinyar batai mishi ba kwata kwata, amma babu yanda ya iya dole ya yarda ya amsheta a matsayin mata, domin wacce yake so ta cikin mafarkinsa bai ma sani ba k0 Tana cikin wannan duniyar tunda har yau bai taba ganin fuskanta ba. 
Mai martaba yaje katsina ya nema ma d’ansa auran Gimbiya zinatu, sarkin katsina yaji dad’i sosai, inda akace an basu nan aka tsayar da watan biki nan da wata d’aya, domin dukansu a shirye suke, koda Gimbiya zinatu taji wannan Labarin ranan saida ta y’anta bayi hamsin dan tsabagen murna zata samu Yarima Aliyu a matsayin miji, shiko ango takaici ne ya cika shi domin ya d’auki auren da za’a mishi a matsayin auren dole, tunda bawai so yake ba, amma tunda an Mai dole 
babu yanda ya iya dole hakuri zaiyi har sanda Allah zai nuna mishi yarinyar da yake mafarki, kwanciya yayi bacci ya d’aukeshi ganinshi yayi cikin wani d’aki Wanda akwai duhu jin motsin tafiya yayi wanda kobai tambaya ba yasan mace ce ke tawo wa, jin kamshin jikinta yasa ya fara magana Mai yasa kike boyemin kanki? Mai 
yasa bakya son in ganki? Magana ta Fara cikin muryanta Mai dad’in ji tace Yarima na Ina tsoran Kaga yanda nake ka gujeni, nasan Idan ka ganni zaka tsaneni matsawa ya farayi kusa da ita yana fadin bazan gujeki ba ina sonki bazan barki 
ba saura kad’an ya karasa inda take da sauri 
ya farka yana salati duk ya had’a zufa Sosai jin karan wayanshi ne yasa ya tashi tsaki yayi tare da daukan wayan yaga number ne kashewa yayi tare dayin jifa da wayan ……. 
*Naji koraii akan ina typing kad’an insha Allah zan kara yawan rubutu, domin farin cikin masoya na shine nawa, nima saiku faranta min ta wajan comments da sharhi* 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE