BARIKI NA FITO CHAPTER 9

BARIKI NA FITO 
CHAPTER 9
Bariki ce cikin shiri tasa riga da wando Sun kamata ta saki gashin kanta fuskanta na d’auke da glass ba karamin kyau tayi ba, d’an karamin akwatinta ta d’auko ta Faraja domin zuwa airport, tana fita tahau taxi don a kaita airport, lokacin data shiga har,an fara shiga itama shiga tayi sanda ta shiga ta hango alh madu tayi sauri ta zauna dan karya ganta, tace tsinanne da wani katon tumbinsa,jirgi d‘agawa yayi bayan an gama jawabi akan kowa ya kashe waya tare da fad’in Kodajirgi zaiyi hatsari ga yanda za suyi, dai dai karfe 2 a kasar Nigeria suka sauka domin lokacin mu da nasu ba d’aya bane, bayanjirgi ya tsaya aka fara fita, bariki ce 3 gaban alh madu bai samu ya ganta ba, koda ta fita taxi tahau tace ya kaita garage, direct gareji aka kaita, inda tadau tashar mota golfdan a kaita kaduna. 
Yarima Aliyu ne cikin shiri dan zuwa gaida sirikin sa wato sarkin katsina, inda fadawanshi suka bishi direct inda sarki yake yaje a kasa ya zauna ya gaida Mai martaba, sarki amsawa yayi cikin sakin fuska a kullum yana kara son Aliyu saboda tarbiyanshi, Mai martaba yana ta dan jan Aliyu da surutu, ya d‘auki lokaci Mai tsawo inda yayi ma Sarki sallama tare da fad’in gobe zai koma tafiyan safe zaiyi hala ba zasu had’u ba, nan sarki yaita sa mishi albarka, direct d’akin da aka saukeshi ya nufa, bai dad‘e da shiga ba sai ga Gimbiya Wanda tunda abunda ya faru ta daina zuwa wajanshi sai dai Inya fito zashi wajan mahaifinta su had’u kuma taga yanda yake d’aure Mata baya bata fuska yanzu, zama ‘tayi kusa dashi tare da fadin Barka da Safiya, bai kulata ba tace Yarima nazc in baka hakuri akan abunda ya faru, wlh Sonka yasa nayi hakan, sai Bayan nayi kuma nayi dana sani dan Allah kayi hakuri, murmushi yayi tare da fad’in babu komai ina son mutum Wanda in yayi laifi ya bada hakuri, murmushi tayi tare da fadin nagode Sosai daka hakura, tace ya kamata mudan zagaya tare kaga gidan koh? Bai musa Mata ba yace ok tashi muje, ganin haka yasa Gimbiya taji dad’i Sosai, fita sukayi suka fara zagaya gidan fadawa na binsu a baya, Yarima Aliyu binta kawai yake amma shi matsalanshi tafi karfinshi dan baida wani buri Illa gobe ya ganshi a kaduna dan a goben yake son zuwa maraban jos k0 Allah zaisa yaga yarinyar da yake nema, ita kam Gimbiya idonta nakan Yarima tana kallonshi tana murmushi cikin jin dad‘i ta msa mai yasa take son Yarima Aliyu Sosai, bata kallon gabanta sai Yarima tun tube taci zata fad‘i tayi dan kara da sauri Yarima Aliyu ya rukota, tare da d’agota ganin haka yasa ta wani kankame shi,tana sauke ajiyan zuciya, d’an janta yayi dakajikinshi tare da fad‘in ki dinga kallon gabanki, kai ta d’aga alaman toh,yace zan koma ciki lnci gaba da shiri gobe da safe zan koma, yana fad’in haka yayi gaba, binshi tayi har d‘akinshi din tace haba taya zan barYarima da kanshi yayi aiki, wannan ba aikin kowa bane sai nawa, bai ce mata komai ba, ta bud’e wardrobe din d‘akin ta Fara zuba mishi kayanshi cikin akwati, tanayi tana kallonshi tace zanyi missing dinka Sosai ji nake kaman in bika, ya rasa mai yasa kwata kwata Gimbiya zinatu bata kama bakinta ta cika surutu, ido ya lumshe domin jin haushin maganan ta take, sai dai wani lokacin takan dan bashi tausayi,jin bai bata amsa ba yasa tace kayi hakuri na cika ka da surutu koh? Ido ya bude tare da fad’in a‘a kawai Ina bukat‘ar hutu ne, shuru tayi Kafin tace ok nama gama had’a maka kayan, saida safe, harzata fita ya kira sunanta, waigowa tayi tare da fad‘in na’am, yace zoki zauna muyi magana, zama tayi kusa dashi,yana takaicin irin halinta domin yaga kwata kwata bata kunyan son zama gab dashi, yace zinatu Ina son ki sani in kara fad’a miki wannan auran bada son raina bane, amma nayi accepting dinshi lokaci kad’an zaki zama matata in Allah ya yarda, but akwai abubuwan da kike yi Wanda ya dace in fad’a miki ni yarima Aliyu daka ranan da aka d’aura mana aure zaki fara saka hijab zaki daina sa duk wannan kayan masu fito miki da tsiraici kina ketawa cikin maza, koda bana son aurenki dole In kara mutuncin iyalina da kaina, Gimbiya zinatu tace insha Allah zan daina daga yanzu lndai hakan zai faranta maka, kai ya d‘aga alaman yaji dad‘in maganan ta, yace zaki iya tafiya gobe tafiyan safe zanyi ba lallai mu had’u ba, tace dan Allah Yarima karka tafl sai munyi sallama dan Allah, yace 0K in zaki 
iya tashi 7 dan lokacin zan wuce, tace insha Allah tare da flta, koda ta fita dariya ta saki tare da fad‘in muje zuwa da haka zan mallake zuciyar ka, sai dai irin kayan da nake sawa bana tunanin zan daina amma zan gwada inna mallaki zuciyarki sai yanda nayi dakai, ranan kwanciya tayi cikin nishad‘i domin yarima yayi dogon magana da ita, ta gefen yarima kam yaji dad’in yanda Gimbiya zinatu bata da girman kai sai dai bata da kame bakinta amma a hankali zai seta ta. 
Habib ne da hajia babba tsaye a kofargida suna tattaunawa, hajia babba ya hango bariki tana fitowa daka mota da sauri ya nufeta tare da fad’in ah ikon Allah,yana ganki a golf Inajeep din? Tace hjyta dan Allah ki barni a gajiye nake, hajia babba tabe baki yayi tare da fad‘in ai dole ki gaji tunda kin tunda daka ke sai shi cin safe daban na rana daban na maraici ma daban, habib shima karasowa yayi yana fad‘in ah oyoyo oyoyo tauraruwan gidan ta dawo, yana maganan ne yana bangare kirji, bariki shuru tayi ba‘ta ce musu komai ba, habib yace yau naga sabon iskanci ke bariki ana magana kinyi shuru, sai kace wani ne ya danneki, hajia babba tace gane min hanya y’ar uwa, bariki tace Hmmm in kuna sonjin matsalan muje amma ba‘a nan ba, binta suka farayi suna rangwada har d’akinta zama tayi katifarta su kuma suka zauna akan carpet, ij babba yace wai bariki da wani sabon iskanci kika dawo ana magana kina wani tamke fuska kaman ba’kin hadari, harara tajefa ma ij babba tare da fad’in ai duk kai kaja min ka had’ani da dan iskan mutum, ij babba ya fara salati tare da fad‘in na shiga uku an fasa aurena, wa kike nufi? Tace Mai ayabaryara mana, habib yace oh ni habiba karku lalatani, bariki ta wurga Mai harara, ij babba tace maiya miki haka? Tace ni ya Mara Wlh saina nuna mishi ni yar iskance ta gaske, ij babba yace Mari? Oh ni Wai Mai yasa mazan nan basu da tausayi ne su kama mata suyi ta duka, habib yace ai maza basu da mutunci Sun Mai damu kaman bayinsu, in sun tashi biyan bukatarsu sai Kaga y‘an banzan sunzo, ij babba yace Aini shi yasa Wlh nida maza sai nesa nesa tunda basa tausaya mana kuma sun San mu Mata rauni garemu, wayar bariki ne yayi kara dan dama bata canza sim ba, bude jakarta tayi taga alh madu, kin d’auka tayi tare da sakin tsaki, har wayan ya tsinke ya kara kira, ganin zai dameta yasa ta saka wayan a silent, ij babba tace uhm Kaga Abu Kala Kala tabe baki yayitare da fad‘in ki d‘auki wayan mana, tace bazan d’auka ba dan Wlh sai n ….. Shigowan Haulat yasa bata karasa abunda tayi niya ba, Haulat rungume bariki tayi tana fad‘in bariki Ina kikajene? Bariki tace nayi tafiya ne, bariki ta kalli Haulat tace gobe sati koh akwai rawan gwatso Haulat ta tashi ta Fara kad’a duwawu, habib yace dad’in Abun Muma muna dashi, Haulat ta saki dariya tare da tura duwawunta dai dai wajan fuskan habib ta girgiza sannan tace amma ba irin wannan ba jin karan ihu kaman ana fad’a yasa suka fita su duka da gudu, dan suga maike faruwa, wata karuwa ce ita da saurayinta suke fad’a sai jibganta yake yana fadin dan ubanki Mai kika nema kika rasa? yar iska kawai harta d’akin da kike zama ni nake biya abincin da kike ci ni nake baki amma sai kije kina kula wasu maza zabga Mata Mari ya kuma yi yana fad‘in karuwarbanza karuwar 
wofi ni nafi karfin wulakanci, bariki ce ta nufeshi tare da ture shi ta daga yarinyarwacce ya 
mata jinajina amma duk da haka bakinta bai mutu ba sai fad‘i take aurena kayi dan iska aiba sadaki na ka biya ba, balle ka hanani hulda da wasu mazan shege karamin dan iska sai naci Uwar babanka, zabura yayi zai kuma cafko ta bariki ta tareshi tare da fad’in haba malam ai wannan ba girmanka bane kaita dukan mace, ij babba tazo tana fad’in na shiga uku an fasa aurena Wai yan mazan nan Mai yasa kuke mana hakane ku kamamu kuyi ta jibga kalli yanda ka fasa mata baki ni Wlh Ina takaicin halin maza,jamil da habib suma suka karaso suna fad’in oh sai kace ana ya’kin duniya, habib yace gaskiya Malam baka kyauta ba ka kama y‘ar uwarmu mace kaitajibga sai kace ka sami gardin namiji irinka gaskiya mazan nan bakwa mana adalci,jamil ya tabe baki tare da fad’in ai wannan wulakanci ne wlh 
maza kuna cin zarafin mu haba dan Allah mutumin ganin Sun mishi ca yasa ya fita tare da kallon yarinyaryace zan kamaki yar iska mayaudariya, tace kaine dan iska shege dan zina, ij babba tace la na bani daman dan zina ne oh Kaga Abu in baka mutu ba, shewa suka saki tare da fad’in sawa suka had’a duwawu suka buga, bariki ta kalli yarinyartace haba khairat mai yasa zaki biye mishi harki Bari ya duke ki? Khairat tace haba bariki Dan kawai yaga wani yana cina sai ya fara duka na sai kace mijina Aiba aurena yayi ba ina da ikon duk Wanda naga daman ya cini in yarda, bariki tace hakane khairat amma da baki biye mishi ba jiba yanda ya ji miki ciwo, khairat tace ai Wlh shi zai biya kud‘in magani, habib yace oh kunji bariki ya jibgeki sannan kice ya biya kud‘in magani? Wucewa khaira‘ tayi tana fad’in ai dole ya biya dan uwarshi, Haulat data gama waya tazo tace kuban labari maiya hadasu? ij babba yace sai kije gidan radio a baki labari, Haulat tace Kai dai ka sani,yace dakata Waye Kai? Haulat tace wanda ya tsargu, ij babba yace cafdurun uwa Wlh zan miki rashin mutunci, Haulat tace kaima kanka dai ij babba yace Wlh Haulat kinfi kowa sanin halina nafi y‘ar iska iya iskanci ganin ij babba tayi sama yasa Haulat ‘tace haba kawata wasa fa nake miki ij babba tace banso gskya banso taya zaki dinga kaini jinsin daba nawa ba, Haulat tace bazan kara ba ij babba gaba yayi yana fad‘in iskancin banza Mai za‘,a nuna min, Haulat jan hannun bariki tayi sukai gaba tace muje inada magana dake. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE