Birnin gayu1

Birnin gayu

Chapter1

BIRNIN GAYU.  BOOK1

tunkwal Tunkwal Tunkwal  “Sautin  dakane ke tashi daga Cikin kewayayyen  Gidan Karan wanda akayi masa danga da
itacen Dalbejiya. , , . Tafiya ta ke cike da nutsuwa dauke da
Littattafan karatunta a hannu ta” nufo Gidan, ga dukkan alamu yunwa da Gajiya ne a tattare da ita. Da sauri ta shiga Gidan tare da yin sallama.
Cikin nutsuwa, “Assalamu alaikum”.
Abin data gani ne ya sata yin sororo kamar wacce aka zarewa rai.
Inna mai Fura ce ta fara kokawar kife wani ‘ qaton Turmi wanda ga dukkan alamu itama gadon shi tayi daga Kakanninta. A qiyasi na zan iya cewa Turmin ya bata . shekaru’. ”ba adadi Inna mai Fura, kenan, yadda mutane suke kiranta ta juyo. ‘ “Au  Deeda har an taso ku?” “Eh mun taso wallahi”.
Inna ta yatsina fuska ta dan kau da kai.
“Ni wallahi banga amfanin wannan zuwa Makarantar ‘ba. yanzu in a Gida kike da tuni mun
‘ Surfe Gero yafi Kwano uku, kinga, Gidan su Talle .da suka aiko ma sai mayarwa nayi don aiki yayi min
yawa.Shiga ki cire kayanki ki zoki karasa min
sallanabku dai”. Aka yi sallama daga waje. ‘ Inna ce ta amsa sallamar. ‘ “Allah Ya yi mana. Wa na keji haka kamar Tabawa?” . ‘ , . ‘ “Ni ce wallahi cikin ranar nan “To shigo ga Tabarma nan ki zauna”. Inji Inna.  Kan wata- busasshiyar Tabarmar Kaba suka zauna Bayan sun gama gaisawa Tabawa ta dubeta  kamar .matar da aka ba ta labarin mijinta zai kara Aure, ta ce, “Wata magana nazo miki da ita idan har zaki amince  ‘ Kin san dai wannan jikar taki .duka ‘yan matan garin nan ba sa’arta,,yanzun ga shi shekararta goma sha takwas har yau ba manemi, to me zai hana ki bani ita in tafi DA ita birni don ko kinsan dai lalurar data kashe Yan,uwanta har biyu Ina tabbatar miki da harta manyanta ba zata taba samun mijin aure a kauyennan ba in banda wannan jarababbiyar bokon DA take zuwa Wanda daga ke har ita baya tsinana muku komai
kalleki Ki gani yanxune lokacin Daya dace ace kin huta Amman kinanan kullum surfe da saida fura
ya kamata Ki amincemin dan Ina tabbatar miki da akwai alkhairi acikin  wannan lamarin kika sanima ta wannan dalilin ta samu mijin aure DA maganin matsalarta
Inna tai shiru tana nazarin tayin tabawa Anya kuwa bazan amince wannan Karon DA tayin tabawaba kuwa to saidai kuma deeda miskilar gaske ce banajin zata amince
Ta kalli Tabawa tace, “To ban ki ta taki ba, ‘ amma fa kin san Deeda halinta sai ita…” “Duk halinta ai batafi karfinki ba, sai dai in
keki ka so… _ Ni fa taimako na ke son yi, don kuwa BIRNIN GAYU zan kai ta Aiki”.Inna ta zaro ido jiki rawa ta ce, “Me..me…me kika ce BIRNIN GAYU fa?” Tabawa ta gyada kai ta ce, “Kwarai ’BIRNIN GAYU zan kai ta Kin San k0  dan kammin Yaro da ke cikin Kauyen nan ya san sunan Birnin Kin san irin kudinsu ‘kuwa ba irin‘ masu kudin yanzu’bane ba, don tun zamanin da…tun xamanin da za a iya kirga masu kudi a kasar nan suke . Tuni Inna ta susuce Ta mike jiki na rawa ta ce “Ah, gaskiya na yarda kina sonmu da. arziki. Wai Ai dole Deeda k0 tana so, k0 ba ta so…ta wuce Birni.. Can kuma ta yi KaSa da murya, cikin sanyin jiki tace “To amma Tabawa ba kya ganin lalurar Deeda zai shiga tsakaninta da wannan dama da ta  samu?” ‘
‘ Tabawa ma ta mike ta ce “Karki damu, lalara ce da a Keuye kawai aka santa, kuma ya shafi
Aure ne, amma ai lafiya take ba mai kallonta ya cr ‘ tana da wani lalura..in kina son zuwanta Birni to, dole lalurarta ya zama sirri  tun da anan Kauyen ne” kawai aka sani, don haka maganar Kauye a barta a Kauye…Yanzu dai babbar matsalar Deeda ta yarda”.
“Ba zan yarda ba Suka ji muryar Deeda ta ratso kunnuwansu. Tsaye take a Kofar daki ta ‘rike kugu tana dubansu. ‘ ‘ 1 “Sanin kankine Tabawa ba inda za ni k0 da ‘kuwa Inna za tai kuli-kulin kubura da ni ba zani aiki Gidan waSu ba, k0 da kuwa zan tafi tsirara ne don talauci balle Allah Ya rufa min Asiri. In ban da son zuciya me na ke nema da zanbar Mahaifata in tafi wata uwa duniya don neman kudi…?.” “To mara kunya‘ Inna mai hura ta fada cikin hasala. Deeda ta Bata fuska .ta ce, “K0 me za ki ce sai dai ki fada amma ba mai canja min ra’ayi.
Ke kuma Tabawa ja jiki ki bar mana Gida kar
ki kuma zuwa mana Gida in kin san ba abin arziki yakawo ki ,ba.
Kuma duk na ci da maitarki ba za‘ki yi
‘ nasarar kaini Birni ba. Ba mai shiga tsakanina da ’ tushena
Tana fadin hakan ne cikin tsiwa da, daga murya. Tuni Tabawa ta harzuqa, haushi ya cikata. Ta ce”Magani na Daga yin abin arziki yarinya karama Za ta tsaya min da rashin kunya?” Nan ta fita cikin fishi tana mita.
Inna ta_ bita tana ba ta hakuri amma ba ta
saurareta ba. Nan ta juya ta hau Deeda da fada da zagi. –
Cikin zafin zuciya. ta ce, “Ai sai ki rayu ki mutu da karatun. Me karatun zai tsinana miki‘?
Ban ga uwar da ki ke daukowa a Makarantar ba, ki ci uban tafiyar Kafa ki je ki tsugunna Gindin Bishiya ga Kishi ga Yunwa duk inda ki ka wucé a garin nan Zaginki ake ana tsegumi, qatuwar Budurwa dake ba Mijin Aure, maimakon ki zauna a Gida ki rufawa kanki Asiri amman ina gara dai ki fita ki Kara tona mana Asiri.
Ni ba ki ’min amfani ba, ke baki yiwa kanki wani amfaniba.  To ni na gaji da miki Wahala, duk ran  da bakincikinki ya kasheni sai ki Huta.
Bakincikin ki da shi nake kwanaina dashi nake tashi duk kin zame min Larura, k0 Ubanki kasa ‘rike ki‘ya ” yi sai ‘ni da ki ka zamar min dole, don na uwar ki
Bakincikin’ Yayunki ya kasheta, kema
kema kikeaon naki ya karasani. To baki  isa ba
“Deeda ta ‘kalléta’ cikin_ zuciya da
tsantsar bakin ciki da Bacin rai, idonta yayi jawur.
Tayi murmushin takaici tace, “gara
. maganar jama’ar Kauyen nan ai ba komai bane kan
wanda ki ke min’kullum. . ‘
Idan bar kin ga na zame miki larura kina da
damar’ ki koreni a Gidanki…sai dai Gorinki hade da Bakaken Maganganun da kike fadamin’bazai sa na
karaya ba k0” yasa naje Birni Aikatau ba.”
“‘ Tana gama fadin haka ta juya tama bar
gidan ta nufi can wani gindin Gadah ta ,zauna kan
wani Dutse tana kukan bakinciki wanna kan dutsen shine ya Zame matar tamkar cinyar mahaifiyarta DA take hawa idan ta shiga wani hali na baqin ciki tashin hankali KO kuncin rayuwa
@@@@@@@@@
Nana khadija yar asalin kyauyen hayin hago ne dake qaramar hukumar tofa dake kanon dabo mutanen kauyen sun shahara ne akan sana ar Zuma matuqa ba boyayyu bane indai akan harkan Sana,ar Zuma ce
sun shahara wajen noman tumatir DA albasa garine Wanda ya hada Hausa fulani hakanan aure na shiga tsakanin su khadija ta fitone daga Hausa Fulani mahaifinta bahaushe inda mahaifiyarta take bafulatana
dukda qaramin kauyene Amman suna rayuwansu cikin jin dadi DA kwanciyar hankali sunada tsangayu na karatun alqur,ani a yayinda makarantar
Boko sai an yi tafiyar’ kusan kilo mita uku kafin a samu firamari daya jal sabo da karancin Dalibai da su kansu Malaman. ‘ ‘ Haka itama Sakandare (Secondary) a na daf’
Suna karatun Boko dai—dai ‘gwargwa’do; sai‘ dai da alama mutanen Kauyen bokon bai’damesu ba musamman ma sabo da wadannan abubuwan
Na- farko, ga nisan tsiya kafin akai ga zuwa Makarantar.
Wani lokacin ga rashin Malamai. da rashin ‘fahimta, don haka da yawa suka watsar do karatun.  Mahaifin Khadija ba shi da sana‘ar da ta wuce Zuma.
Mahaifiyarta kuwa tana sai da Nono ne, ya yin ” da Kakartake sana’ar Fura‘ Sunan .Mahaifin -Khadija Mallam‘ Audu: Mahaifiyarta kuwa Halima’, suna kiranta da” hali‘ , Su uku rak Mallam Audu ya haifa, dukkan su’ Mata ne Jamila ce babba sai Mariya sai kuma ‘ Khadija wacce ake kiranta da suna DIJA‘. ‘ ‘ Sunan DEEDA kuwa ya’sam’asali ne’daga wurin Kakarta Inna mai Fura lokacin da aka yayeta’ ‘
ta koma hannunta ta yayeta, in tana kukan ‘shagwaBa irin na ‘yan yayan nan sai ta yi ta mata Wasa’da; cewa Deeda na yar gidan Inna ma’iFura “. Da haka sunan ya bita duk kauyen sunan DIJAN ya Bata sai ‘DEEDA’. ‘ ’Kusan girma da wayon Deeda ta yi shine a hannun ‘Kakarta wacce ‘ta haifi Mahaifiyarta kasancewar Inna mai Fura ita kadai ce a gidanta Mijintaya jima da RasUwa-‘yan tsoffin da suke tare ko duk sun rasu, ’yan uwa kuWa kowa ya kama gabansa, don haka Deeda ke debe ma ta kewa. Kauna da shakuwata shiga tsakanin-su sosai, duk da Kaka ce Inna mai Fura ba ta yi ma ta goyon Kaka ba, tana kokarin sanyata a hanya da ba ta tarbiyya dai-dai gwargwadon tunaninta da saninta. ,. . ,Iyayen Deeda suna .rayuwa cikin kWanciyar  hankali Yayyun Deeda Jamila _da Mariya ba su damu  da_’karatun zamani ba, don haka iyaycnsu ‘ba su matsa musu ba suna dai Kokarin zuwa” na Allo, shima a kwana a tashi suka watsar.  Matsalarsu ta- fara, ne a lokacin da aka yi Auren Jamila yayar Deeda, an kaita gidan miji washe gari ta tashi da wani irin ciwo marar kyan
gani. jikinta ya dawo tamkar waccé ta yi shekaru
tana jinya. Mijinta bai Bata. lokaci ba ya dawo da ita
gida ta’dinga jinya.
‘ Duk .wani abu da suka mallaka sai da ya kare
a jinya, masu magani ko ba Kauyen da ba a shiga ba
amma ba nasara ‘kowa da irin abin da ya ke fadi
‘ wasu su ce Asiri, wasu Su ce Aljanu, amma” ba wanda ya samo maganin, da haka har’kwanan Jamila ya kare a duniya ta koma ga Mahaliccinta.
Haka abin da ya faru da Jamila ma dai  irinsa ya faru da Mariya ciwon iri: daya. ne
Daga nan fa aka camfa gidan su Deeda cewa’ Aljanu sun aure jinin gidan. ‘
Wasu kuma suce Aljani. ne ya auri uwarsu ba ‘ya’yan mutum bane
‘ . Wasu kuwa‘ su ce‘ Asiri aka yiwa Babansu wani Saurayi da aka kasa gurin ‘neman auren Mahaifiyarsu. -_
‘ Abin ka da Kauye, Kauyen ma na sosai, ’ akwai karancin-ilimi da wayewa,~haka duk maganin nan da suke ba wanda ya gwada na Asibiti don ba su yarda da shi ba. ‘
. Asalin garin ma wani ’busasshcn (Dispensary) ne don sai a dau tsawon shekaru k0 nurse babu balle Likita. ‘ Haka nan “sun fi ‘bada gaskiya ga maganin gidan akanna Asibiti.’ Wannan champi da aka yiwa gidan su’ Deeda ya kuntata rayuwar Mallam Audu da. zuri’arsa, ‘ Dukkan; jama,ar gari sukayanke huld’a dashi,
wai aljani ya auri
‘  Matarsa k0  haka baibata lokaci ba ya saketa ya  kuma ta. ..
ce ta kwashe kayanta a lokacin tabar masa  gidansa ‘ Haka nan Deeda ya yafe mata  k0 ganin .fuskarta bayasonyi wai don karta.  shafa ‘masa cutar maita ta manta ma tana da Uba. shi kuma zai dauka ‘kamar baitaba haihuwar wata’ya-Khadija. a duniya ba
Haka Inna Hali ta koma gidan Inna mai Fura , ; tana’ kuka, ta labarta mata yadda aka yi.- Inna mai Fura tai ta bata haquri ‘gami da kalamai masu ‘_kwantar. da hankali a matsayin .ta’na Uwa, ta shiga qunci .da‘ ‘bacin ran ganin ‘yarta a wannan hali ga Saki ” ga ‘ wulaqanci, ‘yar .tasa ma baya so
Sai dai Inna Hali ta fita shiga tashin bankali sabo da Mace  mai runi  yayin da Inna mai Fura ke karfi hali.‘kawai
‘ Deeda. na shckara bakwai. rabonta-da ganin Mahaifinta suna gari daya kuma guri guda amma ko.  ahan’ya bai son ganinta, daga karshe ma aurensa ya yi ya ci gaba da’ rayuwarsa da sabuwar Matarsa
Wannan bakinciki yayiwa Inna Hali-Yawa, ta _ kwanta Ciwo, haka Deeda ta ga Mahaiflyartacikin ciwo da wahala, tana- tausaya mata har kwananta ya kare ta barta a’hannun Inna mai Fara, lokaci guda Deeda ‘ta zama marainiya ba Uwa ba Yayye duk da k0 tana da Uba Amman dashi DA babu duk Daya suke’ rayuwarta ta dawo daga ita sai Kakarta. –
Deeda ta, tashi yarinya shiru-shiru da ba ta da magana kwata—kwata, in har ta bude Baki to dole ya zama-za ta. tambayi wani abu ne ko ,ta fadi wani abu ~ mai muhimmanci
Wannan abu da ya yi’ ta faruwa a gidansu ya zame mAta~ ayar tambayoyi da yawa a KwaKWalwarta .wanda ba ‘ta da amsarsu da alama idonta da zuciyarta tare da Kwakwalwarta‘ suna, fadawa duniyar yawon neman amsar ne  kowanne lokaci.
Wannan al’amari ya  dasa ’babban’ Ayar 1 “tambaYa a kwakwalWarta Haka Inna mai Fura za‘tasata’tai ta yi mata Surutu, wani lokacin Waka, wani lokacin – , Zolaya, wani lokacin ‘Ta’tsuniya,’ amma’Decda ba ta’” taba tanka ma ta ba sai in ta gaji ta fashé da‘ kuka.‘ ‘Hakan yasa tsoro ya darsu a zuciyar Inna ‘mai ‘ F ura ta fara :tunanin cewa karfa wani ciwo ya kama Deeda, tana tsoron rasata, don ita kadai ’ta mallaka duk duniya. Sannan tana tunanin idan ta mutu tabarta kuWa ya rayuwar-Deedan zata kasance? bata da kowa bata da komai? – ‘ ‘ . Inna‘mai Fura bata gaza ba, ba’ta karaya har ta tashi rokon Allah iya iliminta da kuma da rubu da addu’o’i a wurin Malaman Kauyen. ‘ . Duk ‘yan kwabbanta sun. kare-a. wurin, neman samun canji a tare da Deeda
‘Wani yammaci’ Deeda ta fita karkashin ”  gada ka’mar yadda ta saba kullum sabo
” da ba komai take yi ba ba k0 ina take;
zuwa batada DA abokan yawon Amman wani zubin takan taya Inna Mai hura surfe KO aikin Gida
rai bace ta shigo gidan Inna Mai hura tai mata tambayan duniyannan Amman taqi kulata harta gaji ta koma kan harkokinta kaman daga sama taji deed na cewa Inna menene wannan dake fitowa a jikina DA Sauri ta janyota tana dubawa cikin tashin hankali tace menene wannan deeda kuma tun yaushe ya Fara fito miki cikin tashin hankali ta jero mata tambayoyin har biyu
deeda tace na cikina yadan Dade yanxu kuma harda cinyata yanabin kafafuwata Inna mai hura ta Saki salati
deeda ta kalleta menene Inna!?tai dan murmushin DA za,a Iya kiransa DA yaqe tace ba komai gobe idan Allah ya kaimu Zan kaiki wajen me mAgani
a ranan Inna bata rintsaba don tunda take bata taba ganini irin wannan ciwonba was he gari DA sassafe suka nufi wajen Mai magani shimadai abin sabo ya zame masa amman ya basu wani magani yace a dinga shafa mata za,a dace a hanyarsu ta dawowa deeda ta dubi Inna taga yaddah hankalinta ke a tashe tace inna a kaini asibity mana Inna ta dubeta tace asibiti sai birni deeda kumama wannan ciwon naki bana asibity bane tundaga nan bata sake cewa komai ba shafa wanna maganin ake Amman Ina Abu sai qara fesowa yake anyi maganin anyi maganin Amman Ina hakan baisa an daceba tsoron kada mutane su game halin DA deeda ke ciki yasa Inna ta Fara Neman mafitar yaddah zatayi domin ta boye wannan lalura na deeda
tai dabarar dinka ma ta riguna masu dogon hannu da tsayi wadda idan ta sa har kusan rufe mata kafa takeyi, haka kuma rigunan suna da kwala wadda take rufe mata har wuya. . Abin wasa-gaske, sai da ta kai wannan abin ‘
ya bi dukkan jikinta ya gewa’ye, ya zamo fuskarta ce kawai ta tsira. ,
Wannan kalar kayan su suka zama kayan
Deeda. . ‘ ‘ Akwana a tashi bar Deeda da Kakarta suka saba da lalurarta.
Deeda na da shekara tara ta matsawa Inna mai‘ Fura akan ta sakata a makarantar Boko, yara tsiraru ‘ da take gani a garin suna zuwa boko ne hakan ya ba ‘ ta sha,awa, _ta sawa ranta’ Son karatu; Inna k0 ta ce sam ba bokon da za ta sakata in ba neman fallasa ba yanzu ma tana da lalura ta ce za ta shiga Makaranta?
Nan fa Deeda ta dage, kukan rana daban, na dare daban, haka ma na safe daban, har da rashin
lafiya. Dole Inna mai Fura ba don ta so ba ‘ta amince
akan za ta sakata a makarantar.
Ranar kasuwar dawakin Tofa ta fito ita da Deeda da kafa, ta tattara ‘yan kwabbanta ta saya ma ta irin kayan gwanjon nan biri da wando na dai-dai
shekarunta ta sai ma ta guda hudu, biyu‘masu nauyi biyu marasa nauyi. ‘
Duka kayan da Deeda za ta saka sai ta saka ‘ wadannan biri da wandon ta ciki,  idan ta sasu a ciki k0 yatsanta ba a gani balle  jikinta sai fuskarta kawai.
Inna mai Fura ta yiwa Deeda Kokari kwarai wajen sa ta a Makaranta daukan nauyinta da mata dawainiya ba ta gajiya ba, haka ta sai ma ta Littattafai, wani lokaci ta rakata wani lokacin taje ita daya har ta-saba kwarai karatu na debe mata kewa gata da naci da jajircewa akan sai ta koya don duk da ba ta kokari da fahimtar karatun naci ke sa ta ganewa. Mutanen Kauycn suyi ma ta caa! ‘Akan Makarantar Deeda, Inna mai – Fura ta tsaya, tsayin daka ta kwato ma ta ‘Yanci, kasancewarta Mace mai Baki da’ fadan tsiya, dole suka Kyalesu, har ma suka saba da ganin Deeda a . hakan, tun shigarta da take na ’kayan da take sawa naba wasu’mamaki suna tsegumi har suka gaji suka daina‘ don Inna bata bai wa kowa damar yi musu shisshigi‘ ba, kowa tana ba shi amsa’dai-dai da shi ne. .
Komai tsananin Sanyin da ake k0 Zafl shigar
Deeda ba”ta canjaWa “illa iyaka lokacin Zafi ta saka
marasa nauyi , lokacin Sanyi kuma ta sa masu ‘nauyi.
‘ Haka nan daga sun fara tsufa Inna mai Fara za tara Asusunta ta shiga kasuwa ta siyo mata wasu
Abinda kebai wa Inna mai Fara mamaki shi ne, ‘ wannan abu bai san ya tafi koya ragu ba ina illa iyaka ya ya zauna daram ne a jikinta.
Wannan da shi‘ Inna mai Fura kekwana ta tashi’ gami da adduhr Allah Ya yi musu maganin abin.
** ‘ ** *
‘ tabawa Kawa ce kuma aminiya ga Mahaifiyar Dceda kafin ta rasu, don ko abinda ke faruwa na‘ rayuwar gidansu Deeda
ba abin da ba ta sani ba dana ta auren ya mum tayi nasarar fita daga Kauyen ta sahun shiga cikin garin Dawakin Tofu, daga nan ta samu Aikatau a‘ cikin garin Kano gidan wani Alhaji ta koma can ma ‘ tana musu Girki da Shara, duk kuwa me son dan Aiki ita ce me‘ shiga kauyuka tana nema musu masu aikin ana dan biyanta wani abun, don haka ta shahara har
ta samu fili ta gina dakuna biyu da Kicin da kuma Bayi. .
_ Ta jima tana nacin daukar Decda amma Inna mai hura taki, ko da wasa har Deeda ta girma Tabawa ba ta gajiyawa da yiwa Inna mai hura maganan daukar Deeda ba ta hanyar kwadaita ma ta yadda rayuwar BIRNI ta keda yadda Deedan za ta. samu canjin rayuwa da canjin wuri, har ma dai ta ce mata in tana so sai su taho tare har da ita, in ma don ba ta son rabuwa da ita ne. .
Anan fa Inna mai hura ta fara yarda da maganar Tabawa, har ma ta fada ma ta lalurar Deeda. ‘
Nan Tabawa ta nuna ma ta tun da~ ai ba kwanciya ciwon ta yi ba da lafiyarta ai shi kenan. ‘ ‘
A wannan lokacin Deeda na aji biyu na gaba da firamire.
Ya yin da Deeda ta ji batun zuwanta Aikatau ta nuna musu ba za ta je ba, ba yadda ba su yi ba amma ta Ki amincewa. Damuwar Inna mai Fura ma ita ce yadda ake zaginta a Kauyen da yadda aka camfata da cewa ‘yar Aljani ce
Ba Mijin aure, ba Saurayi, ba Abokin wasa ba
na Hira.
Ba zai yiwu ace su yi’ta rayuwa su biyuba sa ‘ haka bada kowa’ba. ,
Tabbas tana son .yiwa Deeda canjin rayuwa, kuma hakan ba zai yiwu ba sai ta bar Kauyen.“
A tunaninta in sun dace suma za su- iya samun gida kamar Tabawa, sam ba aikin ta sowa Deeda ba, sai son barin garin, ku’ma basu da hanyar barin garin da wannan Kauyen sai ta hanyar Tabawa.
A halin yanzu Deeda na aji biyu na Sakandare (Secondary).  Duk wahala duk wuya ,duk kishirwa da yunwa baya hanata “zuwa Makaranta duk da dai ,karatu irin na Kauye amma ba laifi ta san abubuwa ‘da .dama, haka kuma. tana kokarin zuwa karatun
;Allo, daga Karshe aka ce ta yi’ girma aka korata ta
daina zuwa. Haka ta hakura don dole. ‘
Kullum Tabawa ta zo da maganar sai sun yi
fada daKarta tazageta tayi matagori wai don
ko zatayi zuciya tace zataje ammaharyanxu ba ta yi nasara’ba.
Wannan shine ,takaitaccen tarihi Deeda da Kauyensu. .
bayan Deeda‘ ta gama kukanta gab da~ Magariba ta koma gida, ba ta kula Inna ‘ ba, haka nan itama lnnan ba ta kulata. ba alamar suna fishi da juna har bayan issha. Deeda k0 Abinci ba ta ci ba’ ta kwanta.
Abin ya dami Inna ‘mai Fura kwarai, ta kasa bacci, ta samu Deedan a’ daki, shesshekar kukan da taji ne ya tabbatar‘ mata: idonta biyu, kuma har yanzu kuka ta ke. -‘
“Deeda”. Inna ta kira sunanta.
“Ki yi ‘hakuri nasan ban kyauta ba, na san bani da kirki, ina son kai ki Aikatau Birni, ki yi haquri kar ki daga rai, insha Allahu daga yau ba zan sake yi’ miki maganar zuwa’Birni ba na zama mai son kai”.
‘ Ta sake cewa
“Deeda sona  ki rabu da Kauye nan k0 ta halin kaka, ganin irin, hazakarki da irin yadda KiKeso ki yi ilimi da duk wasu bincikenki da’ amsoshin tambayoyinki’. a Kauyen ~ nan babu maganan matsalarki deeda
na miki gori amma Deeda duk bai sa kin canja ra’ayi ba, shin Deeda in na mutu ya za ki yi?”
Decda da ke kwance tana kuka tun da’ Inna ta fara magana sai lokacin tayi saurin” juyowa ta rungumi Kakarta tana kuka.
“Inna ki yi hakuri na miki mummunan fassara, ban fahimce ki ba, Inna yanzu da ki ka_ yi . min maganar mutuwa sai na ji hankalina ya tashi, wani irin tsoro ya shigeni Inna hala ma in riga ki mutuwa, idan na mutu kema za ki zama ke ’daya.
Inna kece komai na, niCe komanki, Inna Allah na tare da mu yana ganin halin da muke ciki in tafiyarmu Birni shi ne mafi alkhairi, Allah Ya tabbatar mana, ki cewa Tabawa ashirye na ke da in bita a duk lokacin da ta shirya daukana zamu bita”.
Inna mai Fura ta rungumeta Deeda cikin tsananin farinciki tana’ fadin, “Allah, Ya miki
albarka
Da sassafe k0 Inna ta daga sammako sai – masaukin Tabawa’don kar ta bata lokaci ta koma Birni. “
Ganinta da farar safiya ya bawa Tabawa‘
. mamaki, bayan sun gaisa tace; “Lafiya dai ko Inna?” ~ Inna ta yi murmushi‘ ta ce, “Tabawa yau dai andace Deeda ta yarda zamu bi ki”. ‘ – ‘ Tabawa ta washe Baki. . _ “Kai madallah, amma na ji dadin labarin nan ‘da yardar Allah kuwa ba za ta yi dana-sani ba, sai ku shirya bayan Azahar mu‘ tafi, ina ce dai kuna da kudin Mota k0?” Tabawa ta tambaya.- -. Inna ta ce “Muna da shi, duk da ba yawa, jiya nayi cinikin hur da Surfc, in ma ya kasa  sai ki yi mama ciko”. ‘tabawa ta ce, “To shi ke nan ba laifi”. Bayan, ‘A’zahar “din kuwa suka. ‘tattara’ yan kayansu da abin biyau bukatarsu, Inna ta ja gida ta rufe duk da dai ba wani abin kirki ciki,‘ Gadonta ne sai ‘yan Tukwane da suuran kayan amfanin Kicin‘ ta
ja kofar langa-langa ta rufe.
Mahaifin Deeda bai sani ba, kuma bai nemij ya sani ba, amma duk da hakan sai da Inna mai Fur ta kai ta suka yi masa sallama, ya kau dakai ya ce “In ta ga dama ma ta saida ita shi bai dameshi ba”.
A fusace Inna ta bar gidan ya yin da Deeda ta durkusa ta ce, “Baba addu’arka na ke buqata”.
‘ “Sauka lafiya Allah Ya ba da sa’a”. Abin da ya fada ke nan, ya‘ tashi ya barta a wurin. ta mike cikin kunar zuciya da Bacin rai tace “Amin”., _,.,.Ta fita-tasamesu sukai sallama-da wanda Suk”dace a garin, sannan suka kama hanyar barin Kauyen da kafa har zuwa inda za su sami mota. ‘ Rana ta farko ke nan da suka taBa shiga Mota ‘(Bus) aka sa su a kujerar .qarshe, Inna mai Fura” akai ta buga qauyanci duk lokacin da-Mota ta shiga kwana k0 gargada saita’yi ihu, Tabawa‘na mata dariya, yayin da Deeda ta kifa kai tana tunani, wani, lokacin ta dan yi dariyar‘ Inna darkanta, don itama takan dan taBa Kau’yancin, sai ’ dai- ba ta” nunawa a fili” , Lokacin da’ suka- hau titi ‘zurawa bishiyoyi ido tayi tana kallonsu suna gudu,‘ tana kallon .ikon Allah, Inna mai Fura ko tuni bacci ya kwasheta
da ta ji gargada ya Kare, Tabawa k0 saka musu ido tayi tana tunanin tabbas sai ta zauna da su na dan’wani lokaci ta gyarasu sun dan ‘waye kadan kafin ta kai ga kai su wani gidan aiki, don ta yi, niyyar Inna ma‘ko wanke—wanke kadai ta dinga yi’za ta kawo kudi, yayin da Deeda dama ’dai-dai shekarunta Hajiya ta ce ta samo ‘wanda hakan ya ma. ta wuya sabo da duk sa’anninta sunyi raure hakan ya sa zuwan’Deeda’ya ma ta dadi dOn ta san tabbas Hajiya zata ba ta’ kudi mai. tsoka, don haka ya‘ zama dole sai ta gyara Deeda ta kuma’ nuna musu yadda‘rayuwar’Birni take.Da irin wayennan. tunane-tunanen suka iso _ cikin ,Birnin Kanon Dabo, su ‘Inna mai ‘hura an sha‘ kallo, duk Wanda ya kallesu‘ dole sai ya sa musu alamar tambaya, da .Kyar Tabawa” ta samu suka tsallaka titi, ta_ sama musu Adai-daita sahu suka ‘ shiga, wannan karon da aka zo tudu da gangara da kwana har da su Deeda a ihu, sai. damai Adai-daita ‘ Sabun ya tsorata ya tsaya ya dinga masifa da kyar da, . kyar tabawa ta .rarrasheshi ya‘karasa da su gidanta ‘dake tal udu ‘  Dakuna biyu ne sai tsakar gida da kuma bayi a gefe da ‘alamar Tabawa ba ta gama ginin nata ba, ta dai
Wai cewa ake babba ya san komai, dama kullum abin na damunta, ya za a yi babba’ ya san komai bayan ba a koya masa ba?
Ta yi murmushi. . -.
Lallai idan abin da nake gani shine birni to lallai bazan taba Dana sanin shigoba da alamun burina zai-cika “.
Deeda ta fada a ranta. ‘
Kiran Sallar Magariba ne ya katse ma ta abin’da take yi, ta dawo cikin gida don yin sallah.
Kusan kwana suka yi Tabawa na ba su labarin Birni da yadda ake rayuwarsu,a ciki akwai’ banbanci sosai da na Kauye.
Ta kara da. ce musu, “-lndai suna’so su‘ji ’ dadin zama to su dage da sana’a su nemi na kanSu, banda zaman banza
Inna mai Fura -ta ‘fahimci. me Tabawa ta ke nufi  sai dai ita fa tunaninta daban, burinta shi ne ta inganta rayuwar Deeda ta kai ta. Asibiti ta kuma sakata a Makaranta irin na Birn
,’ “Amma anya Tabawa za ta yarda taci gaba DA ajemu a gidanta ba tare DA deeda ta mata amfanin data daukota musamman dominshiba kuwa?

ohhhhhhhhooooo
taya za,ai admin ya isa Sani mu hadu a next chapter donjin ci gaba

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salank

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE