Birnin gayu20

birnin gayu

chapter20

Sabeer yace, “Kwarai Inna; wata ran sai an samu manyan ‘yan boko, manyan yan kasuwan da za su kawo cigaba kafinTa-ankara sai gari Kauye ya zama Birni. Kinga wadannan ‘yan yar’an, wataran su ne manyan gobe. ‘ Kinga abinda muke koya musu. suna‘ fahimta cikin sauri fiye da tunani  Wannan ya’nuna alamar yara ~ne masu kWaZo, idan har gWamnati da iyayen ‘su suka basu dama da hakkin su, da ~irin su Daddy masu kudi suka taimaka musu, to za.‘ kiga wataran sune za su taso su rike- mana yaranmu, su kare mana hakkin mu da addinin mu”.
‘ Inna ta ce, “Ga mai- tsawon rai, Allah Ya tabbatar, Allah, Yasa maganar ka‘ ya zama gaskiya”! ‘ . ‘
“Amin Inna”. Ya ce
‘Wani lokacin mutum yana ‘buKatar shiga irin wuraren nan kafin ‘ya fahimci haka, ada kafin in 20 nan ban taba tunanin k0 sanin. akwai ,mutane masu rayuwa irin haka ba,_ don haka‘ ina godiya ga Deda da ta
san1 zuwa har na fahimci haka, ‘naga abinda ‘ ban ‘sani ba. Hakika Karin ilimi da haske na samu a Bangaren da ban ‘sani, ba”Inna ta ce,- “Haka ne, Allah Yasa mu dace”.
. .”Sabeer‘ya amsa’da, “Ameen”.
: Da wannan‘ hirar Suka yi sallama, Deeda na jinsu, tana.jin Inna ta shiga  ta kwanta‘ tayi‘ bacci,‘ ta mike-‘a hankal’i ‘ta fita hannuntarike da torch, ta nufi .dakin’Sabecr ‘Ta same ’Shi kWance yayi ‘dai daya alamar ya gaji, bacci mai nauyi ya dauke shi. yadda ta ga ya kwanta baki bude, bacci mai’nauyi ya “dauke shi ya bata dariya.
Ta Kara ‘haska shi tare dazura‘ masa ‘i’do tana kallon sa, a hankali tana jin Kaunar Sa na shigarta. . ‘  Rufe ido ‘tayi tana tuno rayuwar su a BIRNIN GAYU, lokacin da take masa aiki kullUm suna fada. Ta yi murmushi- tare da gyara ‘masa kwanciya, ta lulluBe shi,-»tasa’ shi gaba tana kallo, don kuWa da tana ba ta
iya‘kallon sa, ko’ da wasa‘ba ta‘yarda ya dora idon’sa cikin nata, *yanzu‘Sai-..ta*-?rikice,ta rude. Sai in ya yi bacCi take ,zama’ta yi ta kallOnsa kamar talabijim .‘ , ’ ” :Wannan__ ‘lokacin da ‘yanayin ‘ ya fl.‘ kowane  lokaci dadi da nishadi a tare da kwantair da’hankali gareta tana kallon sa, tana‘shaffa ‘kanSa,’cikinmurya-kaSa Kasa ta ce.‘
. “Saboer, ban. San Cewa daya” Bangaren’ ‘cikin ka ya f1 Wajen ka kyau ba yadda ‘nake tunaninka sam ba haka’ kake ba” (you: are such a nice and good humanbeing) Wannan side dinnaka’: ya. burge, ni, wannan‘ (personality) din naka ya;;danawa‘ zuciya ta tarko, ban “San yaushe (respect) din da nake baka ‘ ya‘ ‘koma so ba ban San; yaushe burgenin da_lWannan‘halayyar naka‘ ya. bani komai, ka mai‘ da burina naka, ka mai da ‘rayuwa ta rayuwar ka, mutane na, da kauyena ka mai da su naka, Ka ruyu damu Sabeer; ban .tabbatar da kana so naba
lallai nima zan tabbatar maka da ina  sonka: Sabeer,‘ zan run-gume ka hanhu bibbiyu,.zan so ka, Zan ~tsare maka amanar’ ‘kaina zan zame maka uwar ‘ya’yanka, zan kasace da kai ‘a kowane irin halin Kayi ‘hakuri Sabeer da “abinda ‘ nayi ‘ maka a baya, ‘yanzu” ba komai a zuciyar ’Deeda sai tsabar tsantsar sonka Sabeer”. ‘ ” – A hankali “ta’ kwanar da kanta bisa kirjinsa, ‘ta rungume’sa tare da shafar kansa,” ta lumshe ido tana. shakar sonsa tare da jin kaunar sa na bin jikinta, yana fatsa ta.
‘ Kamar kullum yauma ta riga shi tashi, sai’dai kusan tare suka shirya. Suna shirin ma zuwa makaranta ‘wata makociyar,.su’ ta shigo a rude tana KwalaWa Inna, kira; cewa ta zo ta taimaka musu
Inna’ta kalle ta a rude; ta ce.
“Talle, laflya dai k0?
“Ina lafiya’ kuwa, Ta sallah ke Ciwon ciki, duk ‘wani jiKe—jike mun bata ammah banga‘ alamar sauki ba, kin San. juna biyu gare ta, amma bana’ jin  ta kai’ lokacin haihuwa, mun rasa me ya faru? Shi ne na’ ce ki zo ‘ki duba ta‘tundakin fimu shekaru k0 za’ki‘gane meye matsalar’
’ Tuni Inna ta zari gyale; ‘ta bi tana jimamin al’amarin, yayin da Saber da Deeda suka‘bita; “
Sun samu’ Ta’sallah ‘ nata juye ‘-juye kamar za ta mutu, Inna ta kama ta tana? ~la‘tsa cikin tare da tambayar ta ina ke mata’ciwo? A mma k0. magana bata iya yi, sai numfashi .take sama-sama.
. “Deeda ce ‘ta’ tsuguna tana tofa ‘mata addu’a, dukkan su sun rasa abin yi. A nan Sabeer ya kalleta duk ta galabaita, bata da wani Sauran karfi, za a iya: rasa ta da“~ abin cikin nata. Ya lura yarinyacé ma karama.
“Nan. ya shiga ‘dUbata, ya kalle su, ya ce., “Haihuwa zata Yi; tana’bukatar asIbiti‘ cikin gaggawa
Talle .tace, “Na yi- zaton’haihuwar da saura‘? To mu‘ .ina‘ muka ga wani a’sIbi’ti? A’i wannan sai Birni,‘ ‘.Inna ta. .ce,’ “Bamu‘ da k0 ‘unguwarzoma ‘balle likita,haka“ dai ‘muke haihuwar ‘ mu a- ” KauyE, in abin yayi sanani in da halli: “mu Shiga cikin gari, in babu ‘hali kuma sai .yadda Allah Ya.yi.”.
‘ Sabeer ya bude’baki cikin’ mamaki, k0 aSIbiti_ babu balle  ‘ayi‘maganar likita;
-‘ . Ya. » kalli Tasalla da ’kyau,”Tana
bukatatae asIbiti” cikin ,gaggaWa,‘ gashi ba~ lokaci; kuma karfinta ya gama Karewa”. ., . . – ~A nan ya .mata duk’dabarun da yasan zai mata-‘a matsayin sai na- likita,sannan ba abinda zai iya‘ yi saboda- ‘ba ‘kayan aiki b‘a magani; ; ‘
Ya mike hankalinsa a tashe,yace.
..”,Deeda,”.ba ta da ‘sauran karfi, tana bukataf (drip) da ruwan naquda’ su taimaka mata, in har ba haka ba zata iya‘rasa su duka’, ga ta yarinya ce, Karama, ba za ta iya ci gaba‘da’ jurewa ba, Ina zan‘ samu (chemist)?”
,- Deeda hankalinta- a‘ tashe ta ce, “;Sai dai mu – shiga gari, shima ba‘_ kowanne irin magani 2a. mu samu ba”;
. Saber’ yace, “Bamu da lokaci’, zan je in nemo ‘ magungunan, kafin nan Inna ku kula da ita,in ta bata ruWan zaf1 kafin in dawo, zan yi KoRari in dawo da wuri . Deeda ta ce, “Saber; zan bika, don ba ka San gari‘sosai ba
_ Bai mata musu’ ba suka’ wuce, Deeda ta lura hankalin sa ya tashi sosai, ta ce
“Sabeer, abin ya yi’ tsanani ne😒
.Sosai ma Deeda, ina tsoron kar wani abu. ya Sameta(She is in 3rd stage of labour) ‘Karfinta ya‘ kare duka, ina‘ga‘ mun yi amfani da (forceps) don ya taimaka
mata, amma na san zai yi wuya mu samu”.
Deeda ta kalle shi, “Me zai hana in mun samu (Network) ka yiwa Ibrahim waya sai ya aiko mana da kayan aiki kafin mu isa kayan sun iso, sai mu taho da shi”. . .
Dariya yayi gami da sauke ajiyar- zuciya, ya ce
, “Gaskiya kin kawo shawara mai . kyauu .
Yanayinta da kyanta asIbiti ya .kamata’ a shiga da ita, amma ba zai yiwu _a daukota . ba, don ta galabaita. Sannan yadda Kauyen yake ba wuta ba wani kayan aiki, ban ” ‘ , tsammanin za mu iya bata taimakon da ya kamata, sai dai kawai muyi iya abinda zamu » iya mu barwa Allah sauran; ,
Gaskiya “ban ji dadi ba, matar- nan (is in pain and) ba zan iya mata komai ba. (I can’t do anything for her As a Doctor)”.
Deeda ta kalle shi,’ ta yi ‘mUrmushi, ta ce
“Sabeer, kayi mata abinda za ka. iya, a
haka ma ka mata Kokari’ ‘sosai ma wanda; ba‘ai taBa mana irinsa a qauyen mu ba”.
Haka ta’_dinga jinjina Kokarinsa tare da‘
bashi Karfin gwiWa, tana’ tausar’ sa – da kalamai‘ masu dadi; Da hakan ‘suka isa” inda Suka’ samu (service) ‘ya kira Ibrahim ya masa *’ ‘bayanin ciwon matar, bai Bata lokaci ‘ba kuwa ya je (store). din maganin su da ke
asibiti ya hada‘ masa . maganin
da yake bukata, harda ma karin;magunguna , kamar maganin zazzabi, malaria, ciwon ciki, *ciwon kai na ‘yara da na manya,_ duk magungunan da yasan ‘ana yawan bukatar su
ya hada su’ wuri‘ guda : cikin ‘manyan
kwalayem Da kansa yasa a bayan mota ya nufi garin su,. ‘ ‘ ‘ Sun iso cikin garin karamar hukumar .suna jira .‘sa,‘ inda suke“ ,yawan waya .yana ‘ ‘fada‘musu ga inda, yake,. yayin da ‘ Saber ‘yake“ ’kaiwa’ da. kawowa. tare da tunanin ‘wanne hali matar nan take ci-ki?
Sun yi awa guda . suna jiransa kafin
ya iso, tare suka shiga motar don ya‘ kaisu ‘iya inda za- su sauka Su Sami motar da’za’ta‘ Karasa da su’qauyen. , ‘Tunda suka shiga motar Deeda kanta na sunkuye, ‘ ~ ‘Ina kwana?“ Shi ne‘ ka’dai ya hada ta da Ibrahim, ‘ ta kau dakai gare shi, shima ya yi’ karfin’- halin daga kansa daga kallonta,‘ yayin da , ya mai da kallonsa kan Sabeer. Ya lura’ya dan rame,~ yayi duhu; Sai dai ya ga alamar “nutsuwa da -‘ girma a. tare da shi, sani wannan yarintar da ke tattare da’ shi yanzu. babu. ‘ . – Ya’ lura Sabecr k0 maganar. gida bayamasa; sai labarin’ yadda haihuwar matarya zo mata, yake ba shi. Haka sukai , ta tattaunawa yadda haihuwar. za ta ‘kasance,‘ har suka isa, suka nemi‘ shatar ‘ Wata mota da-za-ta iya shiga, da ‘su’ kauyen, sukai ,sallama da Ibrahim. ‘
Sai lokacin ya samu damar kallon Deeda, suna tafoya yayin da ta kau da‘kanta gare shi, tautsayi k0 ya juyo da Sabeer, nan ya ga irin kallon da yake- yiwa Deeda. Wani irin kishi ya turnike shi, ya ji tamkar ya juya ya shake shi. Haushin sa ya kama shi, ransa ya yi mummunan’ Baci, zuciyar na tafasa. Cikin fushi. ya shiga motar ba tare da ya sake waiwayawa ya kalle shi ba. Haka ya dinga huci a mota, idanunsa sukai Ja. ~ .
. Deeda ta lura da halin da yake, “Sabeer,laf1ya?” ‘
Kau da kai yayi bai kulata ba, duk da hakan- ba ta fasa tausar sa ba, a tunaninta ganin Ibrahim .ya sa shi tunanin gida, taflyar Ibrahim din ne ya daga masa hankali. ‘
Ta kallé shi a zuciyarta tace  yanzu in za ta ce ya koma gida sai ya hau fushi da ita, amma har yaushe Sabeer zai cigaba da
rayuwa da ita a kauye? Da irin wadannan tunane-tunane suka isa Kauyen, kowa da abinda ke zuciyar sa.
Sun samu Tasallah ta ‘galabaita gaba daya, k0 Kwakkwaran motsi ba ta‘iya yi, ga mijinta da sauran jama’ar Kauyen ‘a‘ cike
a gidan, daga mai jiqo sai mai rubutu. ,, ~
Haka akai ta dirka mata. _ Inna na ganinsu ta yi godiya ga , . Allah, ‘ a nan kuma akai ta dirama da- mijinta, don ya Ki Sabee’r, ya duba ta, duk da k0 ya nuna masa shairdar sa na likita, amma ya ce shi ba mai taba masa mata. Da ‘Kyarda kyar aka shawKo kansa .ya yarda. Sabeer ya~ kalle shi Dattijo da shi, ita kuwa yarinya Karama. – . , ‘ “Allah Ya kyauta”. Ya fada a ransa. A nan ya shiga yi‘ mata taimakon da ‘ duk ya san zai iya,. tare da dabarun su ‘na likitoci. Deeda dai ta zama, (Nurse) din dole, duk da bata san komai a aikin aslbiti
ba, ita ta dinga ‘kawo miKO, yi kaza, yi kaza, *har Allah :Ya taimaka Tasalla ta‘
haihu; yaro namiji ‘-lafiyayye; Sai dai kam’ta wahala.“
Nan kuwa Talle ta buga guxa, Wuri ya dau sowa, Inna ta harare ta. ‘ “Ni fa ban ‘son jahilci, ki- gOdewa ’Allah ba guda zaki yi ba in kin gode maSa kya yi duk abinda zaki yi”..’ .Talle ta ce, “Alada ‘ce,’ bari inyi . kayana”. ‘ ‘ ‘ ‘ .Inna ta girgiza kai, ta mike Ita‘yiwa Tasallah barka, ta nufi‘ gida, bayan Sabeer ya ,tabbatar kOmai lafiya; suka- tafl ‘Tasalla tai’ ta masa ‘godiya, Haka ‘ya kom‘a gida ransa-ba‘ dadi;~ don har yanzu yana: tare da .’ -fushin Ibrahim, , ‘- Deeda ta kalle –shi ta yi murmushi, ta ce. – ‘ “(W el done my Hero)”. Daga- kai yayi yana wani, sha mata
Kamshi; _ _ Sallamar’jama’a suka ji,~‘ hakan yasa suka fito a tare; “Yan‘uwan Tasalla ne: da” mijinta suka.ta masa, godiya, da .sauran Dattijan Kauyen.~ ‘ — ,Shi dai ‘nauyin su ya dinga’ji, ’ya ‘nuna ‘ musu ,shi baison’ godiya, aikinsa‘ ya.yi. ‘ . _ Haka.mata sukaita shigowa suna yiwa Inna godiya. A wannan ,rana. da ‘ wannan ‘lokaci kwatanta farin cikin Inna-da ;- ‘Deeda ba’mai yiwuWa bane. ‘ ‘ ” . Deeda ganin’ sabeer ‘na “wani’” sha’ – matar Kamshi yasa ‘ta” fita d0n tafiya makaranta, ta barshi; a zaton ta Zai biyota  ga mamakinta‘har’.’suka tashii‘bai
zoba- Yanaf gida tare da..-Inna har
yamma_,”sannan: :ya fice‘ yaje “ya duba‘, ‘ ” mai jego da danta, ’ ya”,fito~_ya ‘nemi :wurinda
ba ,kowai ya Zauna, zuciyarsa . na cikin ‘ Kunci da BaCin-rai;

bayan deeda ta dawo ta fito yawon neman sa, har tayi sa’ar samun shi. Nan ta nufi gurinsa ta zauna a gabansa suna kallon juna, ta lura ya daure fuskarsa
“Sabeer, mene ne?”
Ta fada murya Kasa-Kasa.
“(Please)- ka fada min, ba ka san yadda hankalina ya tashi ba ganinka cikin wannan hali. Na san dai ka tuna gida ne halan, Sabeer me zai ‘hana ka koma…”. ‘
“Ya ishe ki”.
Ya fada cikin fada. ‘
“Na fada miki cewa karki sake min wannan maganar, kin manta? Ba zan koma ba sai lokacin da na so kuma na ga dama, kuma na fada miki qafata kafar ki. Lokacin tafiya ta bai yi ba, har yanzu ina da abin yi da yawa a qauyen nan. ‘Sannan meye damuwar ki da Bacin raina tunda ba so na kike ba, ba damuwa kika yi daniba? Yau na ga irin kallon da Ibrahim yake miki na san dai kinji dadin ganin masoyin
ki, ke kuma wanne irin kallo‘ kikai’masa?” ‘. Deeda ta kalle. shi’ cikin ‘zare ido da mamaki, tace. . ‘ “Haba sabeer, .ni wallahi har na manta da Ibrahim ma, ban kalli k0 da_ ta inda yake‘ ba, ban San Ibrahim’ya kalle ni ‘ko bai kalle ni’ba Amma nina San iyaka ‘ta, na sari darajar igiyoyin aure da ‘ke kaina; ‘ na san muhimmancin aure da matsayin: Sa a addini. — deeda, yace rana ta farko da na ga Ibrahim ban yi doki k0 son ganinsa ‘ba, asali ma na fara mantawa’ da ,shi a rayuwa .A‘~ yau idanuna’ ba sa kan’ kowa sai kai ‘ Sabeér, kai nakeji da gani ,ba’waniba”. _ ‘ .~ ta ,fashe..ma;sa da kuka abinda ya- tsana‘ kenan a rayuwar sa kukan Deeda. ‘ ‘ ya ji ’ hankalin ,sa» ya tashi,_ ya ‘ ce(Please)’ . Deeda, : kar ‘ kiyi kuka, wallahi wani irin mahaukacin kiShi naji da
na- ga Ibrahim na kallonki, na dinga jin kamar zan mutu don takaici, hankalina ya tashi. .
Deeda, kar fa Uncle Ib ya kwace, min ke, da na zata ba ya son ki, amma kallon da ya miki yau ba zan? manta da shi ba har abada. Deeda,’ ba zan jure ganin wani yana son abinda nake so ba fiye .da komai a rayuwa .ta. ‘Idan Ibrahim ya Sake wannan kallon zan cire masa idanu”. Ya fada yana huci, idanun sa sun juye.
Deeda hankalin ta ‘ya tashi, ba ta taBa ganin Sabeer haka ba. . ‘ ‘ ‘ “Ta matsa gare shi, ta jawo‘ shi jikinta tana shafar ‘sa mar yaro. .
“(Relax) Sabeer, kwantar da hankalin ka, ba abinda zai faru.‘ Abinda. kake’ tunani ba’ haka bane, Ibrahim Sister yake so, ita ce‘ matar sa ba ni ba, ka cire wannan tunanin a ranka”. ‘
Ya rungume ta, Wasu hawaye masu

zafi suka zubo masa, -yace, ,. ”
“(Please) _Deeda ‘ko ba kya sona karki rabu’ dani, ba zan jure ganinki. tare da kowane, irin namiji a‘ duniya ba. (Please)- . Deeda, (be with me)”. . ,
“(I will) Sabeer, insha Allah. _, Kwantar da‘hankalin ka”. –
Ya dago kai ya. kalle ta, “Na‘ yi alqawari zan zama irin‘ mutumin da kike so, (I will’be’ kind of man that you will fall in love with)”.
Hawaye ya ciko mata ido, ta kwanar da kanSa a jikinta, ta-ce. ; ‘ _ _”Na ji Sabéar, zan‘ kasance tare da kai”. . ‘ 1
-Kalaman ta ya sa ya ji ,sanyi’a ‘ransa, ya. dada rungume ta yana shakar . sonta’, yayin da ta faShe da kuka tana tansayin sa. .”Me’ yasa kake sona; da yawa haka ‘ Sabeer? Ni bakowaba, ni ba komai ba, ni ba ‘yar boko ba, ni ba ‘yar gaye ‘ba. ba abinda
na baka sai .wahalar zaman Kauye, a halin yanzu bani da zaBi daya’wuce in bika mu koma BIRNIN GAYU. Tunda har ka iya Zuwa ka zauna,a’_ duniya ta, Zan maka
yadda. kakeso nima zan’ bika duniyar aka, in;
rungumi dukkan_ rayuwar da ke cikinta, kamar yadda ka rungumi nawa”; ‘
,Da Wannan tunani ta ja Shi suka koma ciki, zuciyar su cike da Kaunar juna. Yayin data yanke hukuncin nuna masa irin Kaunar da take masa. ‘ –
., Tun ‘ranar da ’ Sabeer ya fara taimakawa Tasalla ta haihu, Wanda yaron sunanshi aka sa masa ya zama .duk‘ ‘Wani .mai matsala kauyen na rashin lafiya zai taho ‘wurin sa; don haka ya-maida Kofar gidan Inna kamar wani dan karamin asIbitin sa. Tebur ‘da ‘kujera” ya’nema a , gindin biShiya tare da manyan tabarmai
aka shimfid‘a, haka yake -‘zama ‘da (ste‘ thoscope) a ‘wuyan’ sa, . da “kuma (Digital thermometer) :ga_ kuma kattin kwalin‘ magani a gefen sa, duk Wanda ya duba in dai ba Wani babban ciwo ba ne sai ya bashi maga’ni ya tashi, layin mata daban, na yara daban, -na‘ maza daban, har allura “yake ‘musu in ya kama. In kuwa ya lura babban ciwo ne,haka zai tara sunayen su ya shiga gari ya yi waya asIbitin su ya turo su don a duba su dakyau». . ‘-Wannan shine sabon aikin da Sabeer daya samawa kansa ba ‘ shi da hutu, k0 dare k0 rana. ba ya gaze taimakawa ama’ar Kauyen, ya duba laflyar su Ya kuma basu shawarar abinda ya kamata. su yi. Magani. kuwa Ibrahim ke turo masa akai ‘ akai, daga sun kare. Wasa gaske Sabeer ya’ Kware a harka‘r. aikinsa, ‘ya kuma .rungumi aikin -‘ hannu bIbbiyu, ‘yana taimakawa, ,jama’ar
Kauyen ba tareda gajiyawa‘ba.
. Da safe Deeda zata wuce makaranta,  shi kuwa ‘ ya tsaya. .duba, marasa, lafiya Wani lokaci‘ inya»; gama da. wuri’ da mutane, sai ya ‘WUCe – makaranta wurin Deeda, tare ‘za su karasa. Ya dan yi wasa- da dariya da yaran,?ya shiga-cikin  ajin‘” ‘ – yayila zolayar Déeda, in ya gaji; ya taya ta” koya musu, yayin da dama darasin‘._farko a fannin” Boko to sunan “Deeda ne. Duk wanda ya :koya ya rubuta ya karanta masa » har kyautar  minti, biscuit yake mUsu. Tun Deeda ‘na damuwa har. ta :daina.’
*Bangaren Arabic kuWa’ haka yake. Sa ta a gaba ,ta koya masa’kafin far-
a ina. yaran, .in sum ‘ gama ,su dawo tare, su samu- Inna ta ‘gyara‘ ‘musu gida ‘tsab, ta ‘musu. cimar kauye kala—kala, Wacce , ta ‘ kware; a .iya hada su SuCi su sha suna hira tare :da wasa da dariya;
Duk” da ’Deeda bata ‘budewa Sabeer
zuciyar ta ba, amma‘shi kansa yafara lura da kula- ‘na, musamman ‘da take masa, ga wani ’sabon shakuwa mai‘ .tSanani . da ya shiga’tsakanin su. Wani yammaci Daeda’ ta sallami yaran. Islamiyya,» tana jiran ‘zuwan‘ Sabeer amma shiru; Ya, Saba ’duk rintsi yana ,Kokarin’ zuwa su. dawo tare,‘ ganin har Karfe} biyar bai .20. ba ya; sa ta: .taho. tana mamakin me ya hana shi ‘zuwa? , ‘ _ . Tana isowa ta hango shi ‘kewaye da jama,a tare da ,wani tsoho ana .ta rigima da shi, ba shi da lafiya sos‘ai amma yakafe yaqi yardada Sabeer ya taBa shi, _balle ya san matsalar sa. . Wai ance masa- ~in’ anyi maganin asIbiti mUtuwa ake _yi, shi gara ai masa’ na gida. ‘ ‘ -NanSabeer din. ya ‘taso ‘ ya 20 ‘har gabansa  yana “ lallaBa- shi ‘ tare masa bayani da yan dabaru kafin ya‘amince a dubashi. ‘ ‘ ‘-
_ Deeda ta harde hannu, “ta-kwanar da kai tana kallon sa, tana Alfahari :da’ shi tare. ’ da jin Kaunar sa na! dada tasiri a zuciyar-ta; .son sa mai tsanani ya dinga shigar ta; ta ‘ji tamkar ta je ta’rungume shi. Kallon. sa take ‘ ba ko Kyafta ido. : . ‘ Bayan ya- gama‘ da tsohonya dawo kan yaran yana ‘lallaBa su cikin dabara “‘yana musu allura. “Sabeer dina , ya zama‘ babban mutum”. “ Ta sake kallonsa dakyau, ba wannan yarintar; ,da sakarcin, ya. Zama jarumin ~namiji,.ya zama’abinso ga kOwa a Kauyen – su. Ya Canja rayuwar mutanen Kauyen ta ~ hanYa da dama; ya canja musu tunani, tana kyautata‘ rayuwar’ ‘su, yana ‘dukkan iya Kokarin sa ‘ ‘ “‘Sabeer » dina, ABIN .alfaharina”. . Tana ,tsaye tana kallon sa tana
maganar zuci har ya gama da yara ya nufo ta, ganin tana kallonsa tana murmushi yasa ya‘taso. ya nufo ta; shima. yana murmushin. Ya ware hannu tare da rungumo ta, yace
“(My dear wife) me take kallo tana , yiwa murmushi?Na san dai (handsome)
mijinki kike kallo”. ”
– Ya harde hannu ya ce,-‘Bari in gyara ‘ miki da kyau ki Kara kallo na, dUba ni da kyau har ‘yanzu kina da (chance) kar ki yi(missing) kyakkyawan saurayi ’irina kar wata ta. Kwace ni daga baya ki 20 kina yiwa Inna kuka”. ‘
Ya ‘Karasa maganar tare da kashe mata ido, yana wa’nnan (killer smile) din nasa.
Tabbas ya yi nasarar tsuma zuciyarta, ji tayi gaba daya: yakashe ‘ mata jiki da soyayyar sa. ‘ ‘ ‘
Ta fadada murmushintata ce
“So (my dear hand’somehusband) ka
duba kanka da – kyau kuwa? (Handsome Sabeer): dina-né .na BIRNIN. GAYU ne; ba wannan na’ kauyen ba”
– Ta sa hannu tana shafa sajen fuskar sa, tare da kananan gashida suka cika masa fuska,tace. ,
“Yaushe » rabon fuskar nan da ai masa(shaving)? . Wannan ‘kai da ya tara gashi’ yaushe rabon- da ai’ masa aski? Su (handsome) manya”.
Ya ‘yi dariya, ya ce, “Ai’ .kece ;’-yar Kauye… baki – san (fashion) ba,’ ba ki san barin gemu ‘da gashi a fufska’ yanzu gayu bane? ’Yar Kauye kawai”. .
-. Ta yi’ dariya, “Na ji (Mr fashion)”,
Ta ja hannunsa, “Zo mu je in taimaka maka’, in na .gyara’ fuskar‘sai in ga da‘ gaske mijina kyakkyaWa‘ ne- kamar ‘yadda ya fadi?” ‘ . ‘
Dariya .sukai duka suka Shiga cikin gidan, Deeda ta gai da Inna. sannan ta
dauko musu” tabarma ta shimfida a tsakar.
gidan. Sabeer k0 daki ya ‘nufa Wurin Inna
. yana_’zolayar’ta»’ mar yadda ya saba, ita ko
tabiye‘masa. _ ‘
A Nan Deada‘ta finciko shi, ta ce 1
_ ‘ ” oya, muje, yau’ asiki zan maka da
reza, kwalkwal”. ‘ ‘ ‘ _’ ‘ _ ‘ .
‘ .’ ya zaro ido, ya ce, “Yanzu nan fuska’r’, Sabeer ba’ta burgekiba har saikin min kwalKWal kObo?”
_ Dariya ‘ta ‘ sa ganin, ’ yadda .yake maganar yana_ .bata fuska’ cikin shagwaba, tace. ‘ _ har yanxu Sabeer dai ba zaka canja’ba “_ – ko?”.‘
Kwai ciya yayi a cinyar ta ya‘lumshe‘ ido, yace ‘ , ‘
Haka nake Deeda, ba’zan canja ba,
sonki’ba zai taBa raguwa a zuciyata ba”.
Nan ya. bude  ido yanakallon .fuskar ta,yana jin‘sonta’a Zuciyar sa, sai dai‘ta‘ Ki ‘ ‘ ‘
su hada ido. .
Abin askin sa ta dauko mai amfani da batir ta kunna ta soma bin fuskar sa a hankali tana rage ‘masa gashi, tare da gyara masa fuska. Nan ya lumshe ido da alamar ‘ yana jin dadin hakan, har zuwa, kansa tadinga bi yana yi.
“Deeda”. Ya kira sunanta ‘idon sa rufe. .
“Ina jin dadin abindakike mini yanzu, ina jin dadin kwanciyar da nayi ‘a cinyar ki, hannunki na_ shafa fuska ta da kaina, sai ina jin ~sonki na Kara ratsa ni,‘ yana taBa zuciya ta. ‘
Deeda,ina tsananin son kasancewa tare da ke, wannan hannun naki,” wannan tatausan jikin naki mai dauke da tsantsar ni’ima tattare ‘da jin dadi, ina son jinsa a jikina”.
Nan ya kara shige mata, “Deeda, banqi mu tabbata a haka ba. Deeda(please) kar

ki motsa, ki barni inyi ta kwanciya a jikin  kinjiDeeda na?” ” ‘sunkuyowa ’yi kan, fuskar’ ‘sa, idanunsa a rufe yanamata magana -. cikin muryar’ rada. Ta zura ma’sa idanu tana ’ kallon kyakkyawar- fuskar ‘sa, tana‘ jin. sonSa da kaunar  na ratsa jijiyéyin ta, yana kashemata dukkan gaBo Bin jikinta.‘ . A. ‘hankali ‘ ta dinga. goga hancinta ‘ akan nasa, tana wasa da shi tare da ‘ goga fuskar ta akan naSa, ‘gami da  ‘yan yatsun hannayenta a. cikin nasa,‘ ta hada gam.’
.- A hankali ta ji “yana- sau’ke ajiyar zuciya, tare da Kara manna hannun nasa cikinnata. –
Bakinta ‘takai ‘ ‘kunnensa, ta sakarmasa kara, Da .sauriko ya’tashi a firgice tasa masa dariya. ‘ ,
_ “-Amma ke. muguwa ce, kin/tsorata
ni, haka kawai kin yanke min jin dadina”. ‘na ga bacci kake son yi, – ga
magariba-ya kusa. Na .san fltinarka, innace ka tashi a hankali ba‘jin wannan yaren ‘ zaka yi ba’, gara in maka ta yaren dazakaf1 ‘~’fahimta”Sai na hadaki ‘da Inna. Inna’!”.;Ya kwala mata . ‘ ‘ “Kira kinga Deeda k0?” “Me taimaka ‘yar bado?~ Zanzo. insame ta‘,.ke Deeda- . ‘ ‘ Deedan’ tai- kalle shi, “Inna na magana, na fada’ mata’ me namaka? ” Inna ta fito daga daki tana kallon su. , ,,”Me.”ta-maka-Sabeer?”- , Nan ya- hau .soshe soshe da inda inda, Deedan ta ‘kWashe da; dariya ganin yadda ” yakeyi’. Innan “ma ta ‘taya ta, daga, qarshe ‘ “shima ya ~_’taya su dariyar. A dai dai wannan lokacin suka. ji Sallama da wata bakuwar murya, ,tarae suka mai da hankalin sukan. mai‘sallamar Mahaifin Sabeer ne tare da Ibrahim
da yayar sa Farida,_ .- a tare suka mike cikeda mamaki. ‘
Inna ce_tayi karfin’ halin masu sallama tare. da yi musu maraba, ta ‘koma‘ciki. ta dauko tabarma ta shimfid‘a. musua‘baranda. .
Deeda tsaye .kanta sunkuye ta kasa ko da motsi balle ta ce wani abu. – ‘ – . ‘ Sabeer ne ya nufi inda suke, .ciki
doko ya ce._ ‘ . ‘ “Sister, Daddy”. ‘ , ~ Yayi niyyar rungume mahaifin nasa. sai kuma ya kasa, ya“ dan rusuna yace
“Daddy sannu da’ zuwa, ina ,, Sister, Uncle Ib kune da yammar nan tare ‘ ‘ da Daddy?” ‘ ‘
– “Kayi‘ mamakin ganin mu ne?” Daddyn ya fada yana kallon sa. ; ‘ .
Ya ce, “Tundaka guje ni ka daina son” mu, kayi mana hijira. ai dole mu biyo ka tunda mu muna sonka”. ‘
‘Déddy ba haka bane”. ’ ‘
‘To yaya ne?” Mahaifin nasa ya fada cikin Bacin rai,
; Ya ce,~”Dubi yaddakamai da kanka, a wanne dalili? A’ dalilin mace; macen ma wacce kaf1 qarfinta, ka” zo kana rayuwa‘ cikin dauda da datti?- . K0 maSu akin gidanmu‘ ba zasuyi rayuwa cikin wannan lalataccen wurin ba, balle kai da kanka. Ka manta. kanka, yaronda k0 sunan Kauye ya tsani ji balle mutanen kauye, amma shine ka zo ‘yau kana rayuwa ~a cikinsu
In Deeda kake so kana da iko .akanta ta fannin aure, ya zama dole ta ~yi muka biyayya.  ‘Sannan in ‘ta asaline KO  kudi da matsayi,“kana da __ikon take ta. kayi yadda kake so ko tanaso ko bata so. Amma maimakon haka ka bari tana juya ka, ka zata tana sonka take… Kai ba ka”san munafurcin talaka ba
Tana .kyashi ,da faRinciki. da’ .dukiyar da Allah Ya,bamu.don haKa ta jaWo ka cikin
wahala da . kangin. talauci, ka zauna ‘ kai kuma gaka mara wayo ka, biyo ta ku ka zauna, ka manta‘ da iyayen ka, da .‘yan uwanka?” . ‘ ‘
. Cikin Bacin rai yake maganar, Inna da .Deeda ‘hankalin su yai matukar tashi. . Dama abinda take gudu kenan. ‘ ‘

Hmmmm

www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE