Birnin gayu4

                birnin gayu

                  chapter4

Ibrahim. suka yi rainon sabir. Yana da shekara uku a duniya Auntynsa tayi aure.) ‘ , Farida da Ibrahim da masu aiki dashi  kansa Dr. Suleiman dinne sukaita rainon Sabir ya saba dasu sosai ya shaqu da Farida sosai, komai Sister: haka ya dauketa tamkar uwarsa, bashi da magana da‘ ya wuce na Sister.
‘Sun dauki son duniya sun daura masa , musamman Dr. Sulaiman yadda yake Bata Sabir abin ba,a magana  duk abin da yake so shi zai’yi, ba a sa shi ba a hanashi. Haka ya tashi sakale,  gata yayi masa yawa. a wajen
Dr. Sulaiman tamkar bashi da wasu ‘ ‘ya’yan. duk da yana  kaunarsu amma soyayyar Sabir daban take a zuciyarsa da ransa, don haka duk abin da Sabir keso ya zauna ba mai hanashi.
Farida abin na damunta, duk yadda tayi kokarin gyara Sabir sai Daddy ya rushe, tana matuqar son sabir; haka nan bata mance kaunar da Mahaifiyarsa ta nuna musu, sannan nasiharta
da burinta yana nan a tsakar kanta.
Farida, Ibrahim, Sabir tare suka tashi, suka girma cikin so da shakuwa, yayin da farida ke musu komai a matsayinta na babbar yayarsu.
Sun taso kuma sun girma a Canada, anan suka yi, karatunsu, daga Farida har; Ibrahim Medicine suka  karanta, don dukkansu wannan’ ne burinsu. ‘
Haka- tana da burin ta dawo gida Nigeria ta yi aiki a’Asibitin.‘ Mahaifinta.
Kullum tana; cikin lab din bincike akan Mata; ta kware akan sanin ciwon Mata da matsalolinsu
Ya yinda’ ‘Shi kuma Ibrahim ya karanci bangaren fata bayan ya zama cikakken ,Likita ya Sake kOmawa karatu na, ‘ shekara uku don kwarewa akan sanin ciwon Fata
Shi kuwa Sabir, bayan ya gama Secondary – School dinsa yaki karatun ma saboda duk- abin da yake’so a duniya yana da shi, kuma zai samu sabir
Mutum ne Wanda yaki jinin wahala k0 kadan, baya’son abinda zai Wahalar da shi‘. ‘ Cikin‘dabara ‘Farida da Mahaifinsa suka sa ya fara karatu  Da da farko Business‘ya soya’; karanta amma ; sai ‘ Farida‘ tace ‘masa” ‘yana, da kwakwalwa ‘mai zai hana ya Zama Likita kamar:
yadda ita da Ibrahim suka karanta (Medicine) sai , su taru su riqe Asibitin Mahaifinsu. ,ta Kara nuna masa cewa burin Mahaifiyarsa ce hakan Sabir ya amince ya ; ‘ fara karatunsa na Medicine ” a University of Albena dake Canada. ’  ; ‘  Bayan gama karatunsa ne‘ Mahaifinsa‘ ya ~ shirya musu tafiya hutu tare dan-Shi, suka tafi
yawon bude ido qasashe daban-daban suka yi Umarah a Saudi sannan suka Wuce Nigeria» Wannan karon shine karo na farko da
Sabir yazo Nigeria yaga ‘yan uwansa da danginsa na gun Uwa da Uba. Basufi Sati ba ya daga musu hankali
suka koma Canada.
Zulaiha da Rufaida na tare da Mahaifiyarsu a Nigeria haka nan duk sun gama ‘ ‘karatunsu‘ suna aiki a Kamfanin Mahaifinsa
, kafin suyi aure.
Dr Sulaiman ya kasance tsakanin Canada ‘da Nigeria. _ Farida da Ibrahim na son dawowa Nigeria amma Mahaifinsu ya hanasu sabo da kawai su zauna da Sabir a Canada, .don yace shi ba zai dawo Nigeria ba, rayuwar da- Sabir keyi a Canada yana mugun dagawa Farida hankali.
Ta shiga‘ damuwa sosai  saboda ‘ko ta hanashi bazai hanubA, haka Daddy ya hanasu’ takura masa k0 suyi mishi abin da’baya so. .
Sabir kyakkyawan Matashi ne, dogo fari tas sakalalle dan masu naira mai ji ‘da. ilimi ‘da kuma wayewa, wanda gata ta masa yawa, ‘
Yana yadda yake so da naira, ya shiga Mota mai tsadar da yaga dama, ya sa mai tsada,’ ya taka mai tsada, ba shi da wata rayuwar data. wuce najin dadi da hOlewa.
Addini dai bai damesa ba, yana dai Sallah, lokacin da yaga dama, haka ‘yan mata kuwa canjasu yake’kamar riga.
’ Duk wata ‘yar mai kudi da keji da kanta wurin kyau da ilimi da aji irin wanda iyayensu , ke‘turosu karatu daga Nigeria; ba wacce Sabir bai yi yayinta ya kyaleta ba. Tsananin suyi wata biyu zuwa uku da Mace ya yar da ita.
Haka ma sauran Matan fararen Fata, ba kalar Mace mai kyau da Sabir bai yi yayinta ya zubar ba.
Har gobe ‘yan mata binsa-suke, yana musu .
yadda yaga dama.  A cewarsa shi yanzu ya gaji da ‘yan mata . wai kyawawa sun kare, shi k0 mutum ne mai son abu mai kyau, komai nasa a rayuwa mai kyau da sha’awa yake so. _ Ya yin da yaki jinin mummunan abu, k0
da kuwa dabba ne k0 Sutura.
‘ A fili yake nuna kyamar mummunan abu.
Wani lokacin inya ga mummunan dabba bayan kyamarsu ma‘har da tsoronsu yake
‘ Akwai ran da yaje Asibitin dasu Farida da Ibrahim ke aiki suka samu an kawo hatsari ba kyan gani, mutumin kansa ya kumbura ” sosai, gaba daya halittarsa ya canja’. Koda Sabir – ya ganshi, ‘ yayi tsananin firgita, sai da ya suma sabo da firgita. a
Haka ranar yakwana yayi a tsorace ba bacci haka ya qankame Ibrahim a jikinsa ya’ kwana
Farida na masa addu’a. Da‘ taimakon Allurar
Bacci ya‘samu bacci da kyar
saida ya kusa sati kafin ya dawo daidai tun kuwa daga wannan ranan  bai sake zuwa Asibitinba ko da wasa
. .’ ’Wannan rayuwa ta’Sabir yana mummunan
,daga hankalin Farida. Sam bai san meye rayuwa ba
, ‘Sun tsoratar da Sabir ga ‘ mutuwa. ya san kwanciyar Kabari, su inganta‘
. masa’ rayuwarsa ta duniya da lahira _tun kafin ‘~ ‘lokaci ya kure musu gaba daya. ‘
_ Wannan ne yasa ‘farida ta ‘fuskanci’”
Mahaifinsu ta sanar da‘ shi illar rayuwar daya ‘ kyale Sabir yana yi, dole ya san nayi da amanar,
da Allah Ya bashi na ‘ya’yansa. ‘
Farida ta ‘yi iya qokarinta sosai nason ganin jawo hankalin Daddy ya fahimci ‘ halin da ‘Sabir yake ciki- ammai sai ya kasa ganewa har’ zuwa lokacin da suka dawo Nigeria don yin auren Farida da kannenta Rufaida-da Zulaihat.
Da‘kansa ya lura da rayuwar da Sabir yake  ba abin da ya tayar masa ‘da hankali kamar yadda yaga Sabir yana shan giya kamar ruwa
.Haka nan Sabir sosai akan abin da yake so in an hanashi
Ranar ‘da Daddy ya kamashi da giya ya hanashi sha rana ta farko kenan da ya fara hana
shi wani abu a rayuwa.
Ranar ko yaga rigimar. Sabir, nan da nan. ya birkice musu, ‘ga Sabir da wani irin fishi da zuciya mara kyau. ‘
‘ ‘Sai da ya dagawa kowa hankali a ranar. ‘ ‘ Tun daga lokacin hankalin Baban nasu ya fara
tashi sabo da  ‘yadda ’yaga Sabir na shan
giya; kuma ya saba da’ ita haka to zata iya taba lafiyarsa~
‘ ‘innalilahi’ Wa inna ilaillinaju ’un Abin’ da Daddy ke fada kenan cikin tashin hankali. ‘
Farida ta matso garesa tare da Ibrahim ‘tace, “Daddy abin» da nake kokarin- ka gane kenan  tun-tuni ka kasa. ‘
Dubi~ irin rayuwar da Sabir yake, wannan ‘ kadan ma ka gani, mu dake rayuwa da shi-mu muke ganin rayuwarsa. ..
Daddy kai iyayenka sun maka yadda kaiwa Sabir’kuwa? Na yarda suna da wani irin ‘ akida, amma basu hallaka maka rayuwa ba, don da sun maka haka da yau baka kai matsayin da kake ba. . ‘ ‘
– ‘ Kai mutum ne daya san’me yake, mai ilimi, hikima da basira. “
Kowa ya san kai dattijon kirki ne, kowa- ya San kai na Kwarai ne.
Daddy‘ ka dubi Sabir, kana ganin inya girma ya kai shekarunka ba za a dinga yi mishi kallon’ dattijon banza‘ ba?‘
Daddy wannan soyayyar da kake yiwa Sabir ta hallakar da shi, ta kashe masa rayuwa. – Daddy duba da sauran yaran Abokanka wandanda suke sa’annin juna da Sabir, dubi yanayin hankalinsu da nutsuwarsu, sunanjin maganan iyayensu‘, suna girmama na gaba dasu ‘ ‘ Daddy ~ kana Mahaifin Sabir ammn yanzu baka isa ka sa shi ko‘ ka hanashi k0 ka tsawatar masa ba, sabo da tun yana yaro baka mai haka ba sai yanzu  Daddy wannan’ rayuwar ba shi ne wacce Mahaifiyarsa taso masaba dashi“ damu. .duka, haddakai. Tana son nuna mana kyakkyawar rayuwa don! muci ribar duniya da lahira‘. . Ina jin takaicin rashin cika burinta sabo da baka bamu dama‘ ba, duk da nayi aure zanci gaba da rikon Sabir kamar dana,ne ,Mijina ba shi da matsala, ka san zai iya yiwa Sabir komai; zamu yi Kokarin gyara masa rayuwa “in har ka‘
amince”.
. Hawayen nadama ya zubowa Daddy yace‘ “Tabbas na’ tafka kuskure” babba, ’ zanyi”kokarin gyarawa. ‘ Ban san na yiwa Sabir illah ba; sai da._, na gani da idona Tabbas sa’anninsa sun masa, fintinkau A wurare da dama, duk da ya fisu da komai, ba abin da ya rasa tun daga kan dukiya, .asali, gata, kyan halitta.”   . Sai’ dai Sabir yana sakarci, ‘a gaba ba :zai’ ‘ iya aiki ba balle kula da dukiyarsa, ga gadon da Mahaifiyarsa ta bar masa mai yawa, gashi ga’ gadona dukda bamu san gawar fariba, amma – inna mutu na barsa duk da dukiyar nan haka komai .zai kare ba shi da dabara da hikimar zaman  rayuwa. Asibitin ma ba‘ aikin zai iya yi ba, ba abin da ya sani sai dai kashe kudi Yanzu sai‘ a iya cutarsa‘ Sabir ko kansa‘ba zai iya karewa ba
subhanallahi Na cuci  kaina, na cuci dana. idan ban baku Sabir ba, ba’zai iya kula da kansa ba
Nan Daddy ya fashe da kukan baqin ciki da Bacin rai. Tsananin bacin rai da tashin hankali sai da yasa hawanjininsa ya hau sosai.
Da’kyar suka samu Sukai controll din Bp’ dinsa, ya yin da suka yi ta kwantar masa da hankali
cikin hikima da dabara, don in sun ce zasu masa ta. “tsiya zai yi wuya su cimma manufarsu akansa: Hmmm sabir kenan
Sati biyu da biki ‘kowacce ta tafi gidanta
Rufaida America ta wuce da’Mijinta, sai’ .- dai Gidanta na Kaduna sunje honey moon ne
Zulaiha kuwa tana Abuja. ne‘Farida kuma Canada suka koma don daman mijinta a can yake DA zama Likitane shima, 
Yadda Sabir ya tada masu hankali akan su koma Canada ne ya tabbatar musu da cewa ba qaramar wuya zasu sha ba idansun zo dawowa Nigeria ‘ gaba daya. _
Sai dai zasu koma ta shirya masa. Sun sallama da Daddy, sun barshi cikin tashin‘ hankali da tunanin rayuwar Sabeer da hanyar da ‘ zai bi ta inda zai fara.
Bayan zaman Nigeria ba abin da Sabeer yafi tsana irin maganar Aure, a takurashi ace ya zauna da Mace har abada. Sannan Macen ma ace. ‘yar nigeri’a wacce bata waye ba, irin ‘yan garin su.
‘Don haka Mahaifinsa ya samo. hanyar da zaibi ya sashi yin abin da ya keso, k0 kuma ya masa Auren da baya so, ya kuma sa shi dawowa nan da zama.
BAYAN KOMAWAR Su DA Wata
_ biyu Farida da Ibrahim suka yi iya kokarinsu amma Sabeer fa yayi nisa don
Daddy din shi kadai zai iya lankwasa shi, ita kam tana da rauni daga ya soma mata shagwaBa da kuka sai tausayinsa ya kamata, haka za ta nemi wuri tayi ta kuka ita daya. ‘
Ibrahim shi bai data cewa sabo da dama can bai isa yayiwa Sabeer wani abin ba na tsawatarwa sai ya hadashi da Daddy ya yita masa fada.
‘ Sai dai damuwar. Farida da tashin hankalinta na damunshi, ganinta cikin damuwa da qunci.
Sabo da Kaninta na daga masa hankali, don shi a duniya bashi da wacce tafi Farida, ita ce komansa a rayuwa, don haka zai iya yin
komai don ganin ya taimaka mata, don haka ya yiwa Daddy Waya ya ce in yana so su gyara Sabeer dole sai ya dawo Gida Nigeria kuma ba a
gaban Yaya Farida ba, don kuwa tana da rauni
Daddy yace, “Dama shima da nasa shirin Yayi tunanin haka don haka zai zo yace su Shirya zai taho da Sabeer. ‘
.Lokacin da Daddy yazo tafiya ‘da Subir suka yi ta tsiya ya ce ba zai tafiba.
Daddy k0 ya Bata rai yace, dole sai ya raba’sa da Kasar nan da Abokansa na kasar ; da komai nasa da ya shafi kasar, sabon rayuwa ‘ zai zo ya fara a Nigeria, idan kuma yana son’ ‘ ‘yancinsa dole sai yayi yanda ya keso, k0 ya masa aure ya kuma ajiyesa a Nigeria. ~
Sabeer hankalinsa ya tashi ya gudu ya Buya a bayan Farida yana kuka
“Sister ki taimakeni ni ba zan iya tafia ba keba….Sister ba zan zauna da Daddy ba! Ni dake zan zauna, Sister kece Mamana da komi na…ni dai kizo mu tafi ko ki-cewa Daddy ya, : barni in zauna dake
Farida ta fashe da kuka ta rungumeshi, tausayinsa ya kamata. ‘ “Sabeer kayi hakuri kabi Daddy nima zan zo‘akwai aikin da zan gama inzo in sameka “Sister ba kya sona ne yanzu? Kinfi-son,“ aikin ki da Mijinki? Ba kya son danki? . Sister kince fa ni danki .ne shine za ki‘ rabu dani, za ki hadani da Daddy…Sisterr ni banason Daddy, ni wurinki zan zauna”. ‘ ‘ Kuka take xuciyarta na rawa ta tureshi cikin fada tace“Ya” zama dole ka tafi Saber, idan ina sonka ba zan barka a nan ka karasa
hallaka rayuwarka ba, _ dole ka ‘zama mutumin ,
kwarai, ka san Ciwon’ kanka, in kana son mu shirya dole kaje ka gyara rayuwarka, in ba haka ba ko magana ba zan sake makaba…in kana so in zauna da kai ya Zama dole ka tabbatarwa da- daddy zaka ‘gyara zaka koyi aiki, zaka rike
Asibiti, za ka zama (responsible) mutum mai ;
nutsuwa da sanin ciwon kansa. ‘ _ ‘ Kar ka sake‘ min magana in ka san. ba za kayi hakanba”. Zan yi Sister’ ‘Ya‘ fada ‘cikin sanyin murya da tausayi yana kuka irin na sakalci. “Zan yi in dai za ki kulani, zaki barni inzo zan yi duk yadda Daddy ‘ya ce…amma.ki fada masa kar ya min aure kuma zai barni in dawo wurinki  Nan ya juya ya tafi Mota yana kuka, ga’ fuskarnan jawur,yaune rananr farko DA sabir Yayi kukandabai taba irinsaba Farida tayi ciki da gudu ta fada kan gado tana kuka lbrahim yabi bayanta “”Kiyi haquri yayata dole sai kinyu haquri “Ibrahim Sabeer zai . tafi ya barni,’ zai je ya rayu inda bana’nan…lbrahim don Allah ka bisu, ban san wane hannu Daddy zai sa Sabeer ba, ban yarda; da Matarsa ba, ban yarda da wannan ‘Momin ba…Ibrahim‘ kai kadai ne zai .kula min da Sabee‘r.
ibrahim na baka amanar Sabeer, ka sashi a hanya ka nuna masa komai. a hankali, na san zaka iya”.
Ya kalleta cikin kulawa ‘yace, “Yayata kema kina buqatar ‘a kula da ke, kina cikin wani hali, ya za,_a yi ki zauna ke kadai da ciwo‘ ki Boyewa Mijinki bai sani-ba?
Dukda dauriya da jarumta irin‘na’ Ibrahim sai’ da’yayi hawaye. ‘
“Yayata kin san ina tare dake a cikin kowanne irin hali k0 wuya k0 dadi k0 ciwo k0  lafiya;
‘ Kin” “San KAUNARMU “da SHAKUWARMU tun muna Kanana ba abu ne mai sauqi rabuwarmu lokaci guda ba. Yayata me zai hana ki biyo mu nigeria?” Tayi dariyar yake. “Kar ka damu qanina, Zan iya kula da kaina, kuma bana son kowa ya fahimci halin da nake ciki.
Don Allah qanina ka rike min‘sirrin nan, ,’ sannan kayi kokarin cika min burina na ganin Sabeer ya nutsu yayi  hankali
Ya kau da kai yana share kwallah yace”Na miki alkawari…” Harya soma tafiya ta ce “Kanina kai ma ka kula da kanka, duk da kai babba ne mai hankali, wani lokacin ka cika yarinta, ba ka son
cin Abinci, wasa kake da lafiyarka ka fadamin min dukkan damuwarka kamar yadda yanzu  nima nake fada maka nawa
Ya juyo yana mata murmushin Karfin hali
Bayan sun iso’ Nigeria yaqi sabawa da Momi da Sauran jama’ar Gidan, wasu ‘yan uwan Momi‘,”‘Wasu na Daddy ‘ . Haka nan bai saba da  Kano ba, ba Abokai, ba ‘yan Mata ba Giya’,ba  fita Yawon gun Shakatawa
Wannan yasa’  Sabeer, kewada kunci har ya fara ramewa Ganin haka’Ibrahim‘ yaja shi a jiki Haka nan yana zuwa da shi ‘duk inda zaije, daga‘ Kamfanin Daddy har Asibiti. Sai ‘dai fa ba .kullum yake zuwaba , Haka nan Asibitin bai shiga duk wai bai son ganin ciwon da
zai daga masa hankali.
, Da haka‘ Sabeer ya fara sabawa da Garin Kano har ya samu Abokai biyu Wanda suke ‘yayan Abokin Daddy ne; Wanda Daddy din ya yarda da da,bi’unsu.
Bangaren Alhaji kuwa masu dafa masa Abinci da kula da sha’aninsa na Gida bama ‘yan qasarnanbane.’ Sai dai Abinci ba- irin kalar da basu iya‘ ba, musamman ya Ware su don‘kula da Sabeer da‘ Abincin da ya keso‘ Hajiya amina kuwa ‘neman Kudinta shi tafi bawa Karfi, don haka ba’ ta cika sawa Sabeer ido ba, baya gabanta  Dr. Sulaiman dinma basu,cika haduwa ba, duk da suna’Gida‘daya, ‘kuma a Mata da Miji…amma a wuni baifi su hadu sau daya zuwa ‘biyu ba, da Dare wurin Bacci ‘sai kuma safiya‘ business ‘ kawai, tasa a gaba sai harka da ‘ Kawayenta manyan Kusoshin Gwamnati ko Matan masu Kasar. Bata wasa da harkan Kudi. ‘ ‘
Lokacin da ta dauko ‘yan uwanta suka mata wata Cuta na Miliyoyin,kudi  yasa ta koresu ta soma neman bare wacce bata waye be don kula mata da lissafin Kudi da kayan da suka shiga suke fita, da kuma yi mata (Transfaring) Kudi daga wannan Banki zuwa wannan…sannan da kula mata da Bangarenta.
. Wannan yasa ta sa Tabawa ta nemo mata Deeda, kuma ta sa aka bata (Special Trainining) na Wata uku kafin ta dawo daga tafiya, wanda shima tafiyar na wani Kasuwancin ne tare da wasu Kawayenta da kuma Kanwarta daya. Sannan tana son zuwa taga yayarta
Gidan Dr. Sulaiman BIRNIN GAYU Gida ne da kowa ke rayuwarsa, ba ruwan kowa da kowa.
Yanzu ne ma Dr. Sulaiman ke kokarin jan’ Sabeer a jiki, tare suke cin Abinci.
Haka nan sukan yi Hira kadan ya bincika me yake ciki sannan ya barsa da Ibrahim Ya tafi harkokinsa.
To yanzu dai Dr. Sulaiman ya yi. tafiya ya bar Sabeer hannun Ibrahim da kuma sharadi wa  sabeer cewa in ya dawo ya samu bai canja ba to  ba shi. ba komawa Canada, kuma sai ya masa’ aure da Macen da baya so.Kudi da komai hannun Ibrahim Suke yace bai yarda Sabeer ya yi komai ba tare da Da wannan sukai sallama, Sabeer na Mita‘ an takura rayuwarsa, bai ‘san ta yadda zai fara; zuwa Kamfanin Daddy da sunan Aiki ba. – , .. ‘Asibiti kuwa shi ‘ gaskiya tsoron wasu Ciwon yake.  ‘inya‘ tuno da Aure da kuma zaman Nigeria da za a ‘sa’ shi sai ya tashi, wani lokaci ma dai tsabar jin dadi ‘har fasheWa yake da ‘kuka in yayi, yayi ya kasa qulla komai a Kamfanin da Asibitin sai ya fashe da kuka. Tabbas Ibrahim na fama da- Sabeer, ‘ ya rasa ta yanda zai Bullo masa saboda zuciyarsa da rashin-hakuri. ‘
Haka‘ nan duk girman Mutum sai yaci ’masa Mutunci, ba shi da hakurin koyon Aiki. Haka ba shi da juriyar zama a (Office),kullum yana cikin yawo a Gari da Mata, k0 kallo  k0 yin Games k0 yaita buga Snooker  Yana matukar .son (Sport) don haka kullum yana cikin Wasanni, ya yin da ya ,faki Idon Ibrahim ya sha Giyarsa amma a boye. ‘ Duk inda Ibrahim ya bi da shi sai ya zulle a hakan dai ya ke fama da shi, wataran yayi nasaran tafia da shi aiki, wani lokaci kuwa tafia; ya keya hakura ya kyaleshi. ‘ ‘ Haka nan bai son fadawa Farida ‘ya daga mata hankali, haka ba komai ya ke fadawa Daddy ba, ya dage da Addu’a da kokarin neman hanyar da zai bullo masa. ‘
                *’* *’* *’* ,
‘ Deeda ce zaune cikin daki ta baza ’ Takardu alamara tayi nisa sosai. cikin karatunta, duk da yanzu hutu suke
batada hutu, Karatu take ba wasa, wanda in sun koma Hutu zata shiga aji biyar na Sakandari kenan. ; »
Sai ” dai ta san ba tabbas din‘ komawa don kuwa ta gama Computer Classes dinta, ta‘ samu (Certificate)  kowanne lokaci za ta iya tafiya Gidan aikinta in Hajiyar ta dawo daga tafiya. . –
‘ * “Deeda!
” ~ Kakarta ta kwala mata kira. Ta’miqe
ta
fita ta sameta zaune, tasa Kwallan Fura da Nona ’a gaba tana jimami.
‘. Deedan ta kalleta.
“Lafiya Inna?’
“‘Ke dai bari ‘yar nan, kin ga masu Shagon nan har yanzu basu zo sun dauki Furan nan ba, ga shina dama da None na hada komai saura su dauka su zuba a Robobi su sa a‘firiji, amma kinga har yanzu shiru, kar ya kumbura yayi TSami ya lalace munyi Asaransa. K0 zaki dauka ki kai musu?”
“Kai Inna’ in suna so za suzo su dauka, ana sayar musu cikin saukin ma sai an bi-su dashi Shago?” ‘ ’
“Inna ta hasala. . ‘
“Inzaki dauka kikaiki dauka,inbazaki ba kuma sai in yafa Gyalena in kai musu. Bamu ke neman Ciniki ba?” a
“A’a Inna. me yayi zafi? Bari in dauko’ Hijabi inkai musu, Amma gaskiya ki raba min shi biyu, nayi sawu biyu donba zan iya daukan wannan qaton Kwallar”ba “Na ji bari in raba miki dauko Hijabin”Nan Innan ta raba “mata,’ ai’kuwa ta dauko Hijabinta ta sa ta dauki kwanon Furan ta Tafiya take‘tana Mita a‘zuciyarta saboda bataso zuwa Shagon ba, don kullum cikeyake da juma’a musamman Samari Matasa, shi yasa.
.’Bata ankare ba saiji tayi tayi karoda mutum, Kwanon Furar ya fadi,‘ Zuciyarta ya tsinke ta soma tunanin ya zata kare da Kakarta? Wani ihu taji ansa daya’firgitata tadaga kai ta kallesa “Lafiya Malam Meya faru? Yayi-mata wani mugun kallo mai cike da tsana da Bacin rai da kuma jin ,haushi, idonsa ‘ sukayi ja suka ciko da hawaye. Yace”Ke Mahaukaciyar inane so kike ki karya min Kafa, kuma kin Bata min Jiki?”Yayi kwafa”Wawiya kawai Shashasha!!!”Kai Malam Saurara Ni ba shashasha bace nina hanaka kallon gabanka? Yanzu ban da tsabar wauta don dan wannan kwanon ya fadi a
Kafarka‘shine za kayi wani  ihu?” Ta dan kwantar da kai ta leka fuskarsa‘ta‘” zaro ido
“Ba dai Kuka za kai ba, ~sai ka ce wani karamin Yaro? Amma kaji kunya,‘ nima da ka min Asaran Furar banCe zanyi Kuka ba sai kai? Dadi yayi maka yawa”. ‘ . ‘ Nan ta sa hannu ta dauki “Kwanonta ta juya. Haushi ya cikashi, ya finciko Hijabinta. – “Kin yi min laifi maimakon ki ban hakuri zaki tsaya kina min Surutun banza Dama haka kuke Talakawan nan ‘yan rainin Wayo.. ‘ Yanzunnan ki san yadda za’kiyi ki goge min wannan Kazantar da kika sa min a jikina”. Ta harareshi. “Ba za,a gogen ba sai kayi abin da zakayi
. Ta juya ta fara tafiya. Ya bita ya sha
gabanta. bai saurara’ ba .yasa hannu ya fisge Hijabinta. Tsananin mamaki yasa ta bude Baki . ta kasa magana, . Hmm! Sabeer dai dama shi «ya‘ kware ’ Wajen yiwa ‘yan Mata rashin mutunci, masu
Kudi da Aji ma balle Deeda da yake ganinta ‘yar Kauye, kuma Talaka. 
~ , Nan yasa Hijabin ya goge inda Furan ya bata masa Jiki, ya yar da Hijab din yasa kafarsa dake dauke da manya—manyan Takalma ya murkushe shi. Kallonsa ta ke zuciyarta kamar Wuta.
. ‘ Ya nunata da dan yatsa. Nan gaba kafin ki sake ma wani rashin kunya ki tsaya ki kalli kanki, ki kallesa, inkin ga irina ne to kiyi saurin shafawa kanki Ruwa don kuwa zan iya murtsike ki a maimakon wannan kaza’min Hijabin naki…” Nan ya wuce ya nufi Mota  yayin da‘ Uncle IB da Abokansa Nura da Salim suka tsaya suna kallonsu, ‘haka jama’ar dake wurin kowa ya tsaya yana kallon su. Ran Deeda yayi mummunan Baci. Ba Hijabinta daya: murtsike a kasa ne ya Bata mata; rai ba, kamar yadda ya  yaye‘ ‘ mata’ Hijabin a’ bainar jama’a da kuma kalamansa ‘marasa dadi su suka fusatata.
‘ ‘Ta yi saurin shan gabansa hannunta riKe da Kwanon Furan nan. , ,.”Kai marar mutunci  Wanda bai san darajar Mutane ba. ‘ ‘ _ Juyowa yayi zai kuma zazzaga mata rashin mutunci.
amman Kafin ya kai ga yin. ,wani abu k0 ‘cewa wani abu ta Wanke masa fuska _da jikinsa‘gaba saya ‘da wannan Nonon da Furan- da yai‘ saura’a Kwanon, ta kuma Kara wurginsa da Kwanon
Tayi Tsaki ta sunkuya’ta dauki  Hijabinta ta wuce ta barshi Baki bude, tsananin mamaki da kaduwa da bakinciki yasa ya kasa-magana. Ya yin da jama’ar gurin kowa ya mayarda hankali yana kallonsa. ‘
Abokansa ko Babu wanda ya ko motsa daga inda yake
Ya yin da Ibrahim ya harde hannu a kirji yana murmushi yana. kallon Sabeer kamar zai tashi sama don azabar zuciya da’fishi
– Sabeer ya dinga ‘waige-waige amman bai ganta ba, bai ga inda ta shiga ba, ya yin da ya huce  a kan

bakwa comment
Saboda haka inaga qila sau daya Zan dinga kawo muku a sati

www.facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE