DA MA NI CE CHAPTER 12 BY JAMILA UMAR TANKO

dan Allah kawata ki kula da hakkin aure, ki ci gaba da hakuri watarana Shamaki zai gane kurensa idan shi ya cuce ki, ai Allah ba azzalumin sarki ba ne.

Malaika ta fara shshshekar kukan Karya tana godiya.

Suka kashe waya.

Malaika ta daka tsalle tana rawa tana murna Aliyu ma ya taho da gudu yana taya ta suna ta rawa suna murna duk da bai san me yake faruwa ba, ya san tabbas yau Mamarsa na cikin farin ciki sabanin kullum da ta ke cikin fushi tana kyararsu da zagi.

Ba’a jima ba sai ga sako ya shigo wayar

Malaika tana dubawa taga sakon kati daga Nasrin, sai ta dauki mayafi ta fita wajen mai sayar da kati na kofar gidansu, anan ta siyar ya bata kudinta ta shigo gida tana ta fara’a, babu sauran fushi kuma ayau.

Ta yini tana lissafin abubuwan da zata saya da kudin nan Naira dubu uku saboda bukatarta tafi ta dubu talatin ma. Tana son ta yi

Da misalin Karfe hudu da rabi na yamma Shamaki ya fito daga cikin masallacin

B.U.K bayan ya idar da sallar la ‘asar, sai ya ji wayarsa na Kara ya dauko ya duba lambar, lamba ce kayatacciya kai kace mai lambar tsarata ya yi da kansa, daga gani babu tambaya lambar ta daban ce  musamman daga kamfanio MT, sai ya ga kamar ya taba sanin lambar amma ba zai tuna in da ya san ta ba. Gabansa na faduwa ya amsa yana mai addu’a ko waye mai kira Allah Ya sa alkhairi zai fada.

A lokaci guda suka yiwa juna sallama cikin girmamawa. Shamaki ya yi shiru yana jiran mai kira ta gabatar da kanta, kuma ta fadi dalilin kiran.

Ta ce, sunana Nasrin Abdul Nasir daga

Abuja. Ina fatan ina magana da Shamakin Malaika?” Shamaki ya yi mamaki gami da farin ciki

sai ya amsa “Eh nine.Yana tafe yana magana ya gaggauta barin jikin masallaci ya koma can gefe ya sami bishiya da kujerar zama ya zauna suka ci gaba da Magana, ya tabbatar tunda Nasrin ta kira shi da akwai wata magana mai muhimmanci.

Bayan sun gaisa Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta ce “Jiya ka kirani da daddare na fara bacci, shiyasa na kira ka yanzu, Kafin in shiga cikin irin wanna magana musamman magana ta ma’aurata ya kamata in dan san wani abu daga cikin rayuwarku ko da kuwa kadan ne, ba sai dukka ba.”

Shamaki ya gyada kai yace, “haka ne Nasrin. Ki saki jikinki mun baki amanar kanmu,mun yarda da ke ki tambaye ni komai da kike son sani in Allah Ya yarda zan amsa miki.”

Nasrin ta yi murmushin jin dadi ta ce

“na gode. Malam Shamaki zan so in ji

labariaka dana Malaika, da yadda ku ka hadu har ku ka yi aure.”Shamaki ya ji dadin tambayar nan sai yace, “Malama labarin da tsayi sai dai in kin shigo Kano mu zauna saboda kudin wayarki zai kone da yawa.”

Nasrin ta yi dariya ta ce, “kada ka damu kudin wayata zai isa muyi ta magana daga yanzu zuwa gobe da safe ba zai kare ba.

Shamaki ya gyada kai ya yi jinjina ya fada a ransa “babban goro sai magogin Karfe, sama ta yiwa yaro nisa sai dai ya daga ido ya hango ta. Allah Ya yi mana arziki ta hanyar halal. Amin.

Sharaki ya yi ajiyar zuciya gami da gyaran murya, yaci gaba, “to ba damuwa bari ki ji cikekken tarihina da na matata Malaika.

LABARINSHAMAKI:

Yace “sunana Yusuf Muhammad Yusuf, sunan garinmu MUNTSIRA garinmu bashi da nisa da Karamar hukumar Bichi, cikin jihar Kano. Na ci sunan Kakana Yusuf shi kuma

yana da lakabi da ake kiransa Shamaki, Mafarauci ne kuma gwarzo a wajen sana’ arsa.

Shiyasa nima ake kirana da Shamaki karami,ko a makaranta Shamaki Yusuf Shamaki nake rubutawa.

Na tashi a maraya mahaifina ya rasu tun ba’a yaye ni ba kuma nine dansu na fari, mahaifiyata ce kadai ke da rai, ana yaye ni sai Kakana Shamaki ya dauke ni, a wajensa na girma. Mahaifiyata ta je ta yi wani auren ta haifi kannena maza biyu, Kasim da Hashimu, da mace daya ‘yar autarmu mai suna Sadiyalle.

Babu abinda Kakana ya iya sai farauta abinda ya koya min kenan, da girmana na shiga makaranta boko amma na yi zurfi a karatun in

Yan ajinmu sun tausaya min sai su bani tsohon

Hmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE