DA MA NI CE CHAPTER 14 BY JAMILA UMAR TANKO

aure za’a cire ta in zo in aura idan kuma bana so zai yi mata miji, dan yaji na fara rokarsa akan ya bar ta, ta kamala sakandire.

A dole na fito aka yi aure daman na dade ina taron kayan auren. Dakin kasa guda daya jal Kakana yaba ni,anan muka zauna shi kuma da matarsa suna cikin daki daya. A haka muke zaune ban dade da yin aure ba na sami aiki a Bichi ake biyana albashi daga nan rayuwarmu ta dinga ci gaba. Mun fi karfin ci da sha da sutura sannan a hankali na yabe gidan kasarmu da siminti, na cire katagar kara na yi Katanga ta bulon

Kasa, muka ci gaba da zama na

soyayya har Allah Ya ba mu haihuwa yaronmu na farko Aliyu, muka haifi na biyu na saka masa sunan kanina Kasim.A lokacin ne abokina yaba ni shawara muka je muka zana jarabawar Jamb, muka cike B.U.K.

Abokina уа SO in karanci

Likitanci(Medicine) naqi amincewa saboda shi ya san zan iya amma ni ina ganin ba ni da damar da zan jure karatun likita saboda ga iyali, ga aikina, zan fito in je neman abinda zan ci dole. Na cike kos din Biochemistry, Allah cikin ikonsa ranar jarabawar Jamb muka je muka zana kuma na ci da yawa, abokin na kuwa bai ci ba.

Nan da nan da gudu suka ba ni abinda na zaba daman sakamakona na sakandire ya yi kyau. Na nemi izini daga wajen aikinmu suka barni na tafi da albashina (inserbice) ko da yaushe da babur dina nake zuwa daga Bichi zuwa Kano, in yi lacca in koma, da na ga da wahala sai na yi adashi na hada da rance na zo na Kama mana gida anan Kano,a unguwar Dorayi akan Naira dubu talatin da biyar haya a shekara.

Na dauko iyali muka dawo yanzu haka muna cikin shekara ta biyu kenan, anan aka haifi dan autan danmu Ahmad, kuma Allah Ya yi shi yana da sikila. Gashi dai ana ta faman zirga-zirgar zuwa asibiti.”

Nasrin ta yi shiru tana mamaki wannan labari mai kama da almara, ta ji talauci tsantsa dan ita bata san irin wannan rayuwar ba.

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “idan na lura Malaika na sonka kuma tana yi maka biyaya ko? Menene laifinta yanzu?” Ya yi dariya yace, “Jama’a da yawa tun a garinmu suna ta maganar cewa Malaika tana yi musu kallon banza, dan ta auri miji yana yi mata hidima, da na fara aiki ta fara miya da nama sai abin ya Karu har ‘yan uwana da *yan uwanta suka shiga layi suna ta jin haushi wai

“Malaika na wulakanta su in an je gidan sai taga dama ta kalli mutum, in dai ba da kai zata karu Ba bata kawance da kai. Ni dai ban gani ba dan bata yi a gabana, , in na tambaye ta ta ce karyane. Na yi fada da jama’a da yawa akan sukar Malaika a gabana. Abin nata bai higa ba sai da muka kauro Birni inda ta hadu da wayayyu, masu arziki sannan halinta ya fito fili karara, dan a kauye kowa babu, balle ta sami mai kudi ko ‘yar gayun da zate makalewa.

Idan dare ya yi sai taga kowa a unguwar yana kúnna Inji, saonan ta lura ashe sai a haske ake rayuwa, taga kullum matan birni idan zasu fita kwalliya suke ci ba’a saka kodadiyar atamfa ta ce itama sai ta yi haka, taga wasu motarsu suke shiga akai su unguwa ba kamar a kauye ba da sayyada ko da acada ake fita, nan ma ta ce itama sai ta yi haka. Ta ga ana zuwa Dubai da Saudia ayi sayayya itama ta fara sha’awar haka.

Akwai wasu masu arziki a kusa da mu a gidan ta tare nan take ganin kayan kyalkyalin duniya, kafin aka yi fada kaca-kaca ta daina shiga. Ta koma gidan wasu masu kudi a tsallaken titinmu nan ma akayu fada ta daina shiga, ni kuma ta zo ta sauke min kwandon masifa sai nayi kudi da karfin tsiya dan adaina yi mata gori. Tun daga nan nakeyi mata nasihaamma tamkar zu gata nakeyi, yanzu data hadu da ke abin ya ci tura ta sake barkacewa. Nasrin ki taimakeni ki nunawa ma Malaika yadda rayuwa take, na tabbatar ke kanki a danginku akwai talakawa dole wani ya fi wani.”

Nasrin ta yi shiru tana tunani ta rasa abinda zata ce, bayanansa kamar da kamshin gaskiya na Malaika ma ta. gasgata dan in har karya take yi ba zata dinga sharbar kuka haka ba. Me yasa Malaika zata yi mata karya? Ko me yasa Shamaki zai yi mata Karya? Dole a cikinsu akwai makaryaci.

Nasrin ta gyada kai ta ce, “tabbas uwa daya uba daya ma dole a sami wani ya fi wani arziki, Shamaki ka ci gaba da hakuri. Kenan yanzu albashinka na can kauye da shi kadai ka ke cin abinci?”

Ya gyada kai yace “Eh! Naira dubu sha takwas ne kacal kafin wata ya zagayo sai na ci bashi na bawa

Malaika, gashi na koma

makaranta-siyan Handout, da yawa ma *yan matan ajinmu da nake koyawa karatu su suka dauki nauyina ni kuma na zama bawansu, assignment da attendance dinsu nine dan ba zuwa suke yi ba kullum to a haka muke rayuwar gashi an hana Acada a Kano balle in yi da babur dina, amma na kan fita wajen gari inyi acaban. Ni dai fatana in kyautatawa Malaika kada ta tafi ta bar ni.”Nasrin ta cika da mamaki ga shamaki ma yana kokarin kece mata da kuka kamar yadda

Malaika ta yi mata.

Ta yi tagumi tayi shiru tana saurarensa wani abu take ji yana yi mata yawo a cikin

Hmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE