DA MA NI CE CHAPTER 15 BY JAMILA UMAR TANKO

Ta yi ajiyar zuciya tace, kenan kai dalibi ne a B.U.K ba Malami ba?”

Shamaki ya fara mamakin tambayar nan alhali ya fada mata komai. Ya gyada kai, yace,”ai na fada miki in da nake aiki, anan kuma karatu nake.”

Nasrin ta gyara zama ta yatsune fuska ta ce “kà fara tunanin Kara aure ne ya sa Matarka kishi da rashin

samun zaman lafiya daa junanku?”

Shamaki ya yi dariya ya ce, ” Aure? Ina ta kaina auren me? Ko kadan bana taba• sha’ war yiwa Malaika kishiya. Ina son Malaika har cikin raina bana son bacin ranta, ta kasa yarda. Da ina da kudin da ya kai cikin duniyar nan, da zan juyewa Malaika dan ta yi farin ciki.”

Sai Nasrin ta ji gabanta ya fadi ta fada cikin firgici “Shamaki ka tabbatar abinda yake rankaka ke fada min?” Ya yi dariya yace, “Baiwar Allah baki san ni ba, ban san ki ba amma na kwashe. sirrina kacokan na fada miki. Wallahi ban da ke duk duniya ban taba yin wannan hirar. da kowa ba dan ke ma na san zaki taimake ni ki fahimtar da ita. Kin ga yanzu ina Label karatu ya yi nisa saura shekara daya in gama, gidana ba nutsuwa ina tunanin yara bana ya zama a makaranta in yini ina karatu, ba dan ma kwakwalwar mai dauka da wuri ba ce da tayaya zan dinga hayewa jarabawa, kuma ban taba samun carryover ba, babu kuma dalibin daya fini ci a department dinmu.”

Nasrin ta gyada kai ta ce,dakyau

Shamaki na jinjina maka, in Allah Ya so zan taimaka maka cikin dabara zan fahimtar da matarka. ba tare da ta san mun taba magana da kai ba.” Ya ce

“na ji dadi na gode.”Nasrin ta ce,”tambayata

ta karshe shekarun Malaika nawa? Naka nawa?”

Ya yi murmushi ya ce, Shekarun

Malaika ashirin da shida, ni kuma talatin da biyu. Ke fa shekarunki nawa?”Nasrin, ta yi dariya, ta ce, “ni sa’ar Malaika ce shekaruna ashirin da biyar, gobe ne

Birthday dina. Na gode sai anjima.” Nasrin ta kashe waya tabar Shamaki a zaune yana ta murmushin jin dadi shi kadai. Ji yake tamkar matsalarsa ta zo karshe, gyara yazo Malaikarsa zata shiryu. Ya yiwa Nasrin

addu’a Allah Ya bata dama da ikon shawo kan

Malaika. Dan tunkarar Malaika da zunmár

gyara abu ne mai wuya dan bata jin Magana.

Ya isa gida da mura ya iske Malaika

cikin farin ciki, hatta cimar gidan ta canza

abinci da kaza ta yi musu, sai ya ji gabansa ya fadi ya tambayi in da ta sami kudi ta sayi kaza,

ko zakka makwabcinsu ya yi musu daman ya

saba basu? Malaika ta ce kawai ya ci ba sai ya tambaya ba. Shamaki ya girgiza kai ya ce ba zai ci ba sai ya sani.Ta gara zama ta yi fari da ido ta

dauko wayarta ta bude sakon Nasrin ta nuna masa. Ya kalla ya duba ba tare da ya gane ba.

Ta yi masa bayani kati ta turo mata na Naira

dubu uku.

Sai ya ji jikinsa ya yi sanyi ya fara tunani

aransa “anya Nasrin gyara zata yi ko kuwa bata min mata take? Na fara nadamar labarina dana kwashe na fada mata dazu. Ashe ta turowa matata kati sannan ta kira ta ji ta bakina.”

Sai ya shiga zulumi yana mai tsananin takaici, yaga dakyar ya nemo Naira dari biyu ya bayar a yi cefane,yanzu ta zo ta turo mata da dubu uku. Yanzu ta ina Malaika zata ga mutuncinsa? Ta ina zata ji maganarsa? Ta ina zai hanata ta hanu ? Me yasa ba zata yi sha’awar ziyartar Nasrin a Abuja ba? Shiyasa ta fi sha’ awar saki maimakon zama da shi dan ta koma ta zauna da Nasrin.

“Malaika kada in Kara ganin kin kira

Nasrin balle ki roke ta kati.” Shamaki ya fada a

fusace.

Malaiaka ta zabura ta tashi tsaye cikin tsiwa ta ce “Lallai ma, au haka zaka ce? Bakin ciki ne abin dan kaga na sami mai tamaka min?

Wallahi baka kaunata saboda baka kaunar ci gabana. Babu mai raba ni da Nasrin Aminiyata.”

Sai ya fusata ya kai mata hannu kamar zai mare ta, ya fasa. Tayi tsalle ta fada kan kujera tana makerketa ta zaci dukanta zai yi. Ya fice daga gidan a fusace, Malaika ta tashi tsaye ta tsaya a falo ta kama Rug ta rasa abinda yake yi mata dadi zuciyar ta na tafasa ga tukikin masifa ya taso mata amma babu abokin fafatawa.

Tsaki take tana kwafa tana fadin “cafdi jam! Ashe za’ayi ta yau a gidan nan. Daman ka mare ni da ka mari aurenka wallahi. Nasrin kuwa bazan rabu da itaba sai dai ka mutu.

Shamaki bai shigo gida ba sai da daddare bayan Sallar isha ‘i, ya shigo da fara’a ya iske yara sun yi bacci sai Malaika a zaune a tsakar gida tana cin tsire.

Ya yi sallama bata amsa ba, ya yi dariya yace,

“kaga madam an sami kudi ana ta cin dadi bayan kaza ma kuma tsire ake ci, ai dadin zai yi yawa a rage na gobe mana. Ke kadai za ° ki ci dan rashin imani sai da kika bari yara sun yi bacci, mi bana nan?”

Tayi kamar ba da ita yake ba ta dinga kai tsoka lunkuma-lunkuma bakinta. Ya ga da gaske cinyewa zata yi ya zabura ya kai hannu zai dauki yanka daya, ta dauke namanta da

Hmmm

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE